Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/09/2025.
Usman Minjibir da Umar Mikail
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Amurka ta hau kujerar na-ƙi a ƙudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar kan buƙatar gaggauta tsagaita wuta ta dindindin a Gaza, tare da ƙara yawan kayan agajin da ake shigarwa yankin.
Wakiliyar Amurka a zaman ta ce kwamitin ya gaza yin Allah wadai da ayyukan Hamas ko amincewa Isra'ila na da ƴancin kare kanta - amma sai kwamitin ya yi kuskuren gaskata abin a ya kira ''ƙarairayin da za su amfani Hamas''.
Wannan ne karo na shida da Amurka ke hawa kujerar na-ƙi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yaƙin Gaza.
Tun da farko Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin ''mummunan bala'i''.
Olga Cherevko ta shaida wa BBC cewa ta ga yadda ake nuna Falasɗinawa na tururuwan ficewa daga Gaza zuwa kudanci, amma har yanzu dubbai na zaune a yankin.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya shawarci firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya yi amfani da sojoji don hana kwararar baƙin hauren da ba su da takardu.
Trump ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar tare da Mista Starmer a lokacin ƙarƙare ziyara wuni biyu da ya yi a Birtaniya.
Shugaban na Amurka ya yi jawabi kan tsare-tsarensa na rufe kan iyakokin Amurka, yana mai cewa Birtaniya ma na fama da makamantan matalolin da Amurka ke fuskanta na tsallakawar baƙin haure a ƙananan jiragen ruwa.
"Kuna da mutanen da ke shigo muku a kullum, kuma na faɗa wa firaminista akwai yadda za a magance hakan, koda kuwa ta wace hanya ce, ciki kuwa har da ta soji.'', in ji Trump.
"Kwararar baƙin haure na lalata ƙasashe, don haka ne muka fara fitar da dama daga cikinsu daga ƙasarmu."
Tun bayan komawarsa Fadar White House a watan Janairu, Shugaba Trump ya ƙaddamar da korar baƙin haure da waɗanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
Shugaban mulkin sojin Sudan ya yi watsi da kiran da Amurka ta jagoranta na tsagaita wuta na wucin-gadi ta yadda za a ci gaba da tattaunawar kawo ƙarshen ƙasar basasar ƙasar.
Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana shirin tsagaita wutar da ke samun goyon bayan Amurka da Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar a matsayin wana ajanda da ƙasashen wajen ke son ƙaƙaba wa mutanen Sudan.
Ya ƙara da cewa a shirye sojojin Sudan suke ga shirin zaman lafiya, idan har abokan faɗansu na rundunar RSF za su ajiye makamansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa mummunan faɗa a birnin El-Fasher da aka mamaye a arewacin Darfur, inda aka kashe dɗaruruwan fararen hula tare da raba dubbai da muhallansu.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta huɗu sun mutu, yayin da wasu uku suka jikkata bayan motarsu ta taka wani abin fashewa a Rafah da ke kudancin Gaza.
A wani labarin kuma rundunar sojin ƙasar ta ce wani mutum ɗan ƙasar Jordan da ke tuƙa motar ɗaukar kayan agaji ya kashe sojojinta biyu a mashigar sarki Hussein da ke kan iyaka.
Jami'an tsaro sun ce mutumin ya soma ne da harbin sojojin kafin ya caccaka musu wuƙa.
Sun ce daga bisani wani mai gadi ya harɓe direban.
Hukumomi a Jordan sun ce an kulle mashigar, wadda ake kira mashigar Allenby a Isra'ila, saboda cunkoson ababen hawa.
Ƴan'uwa da abokan arziƙin wani ɗan wasan guje-guje na Kenya sun ce sun yi mamaki matuƙa bayan samun labarin kama shi da aka yi a Ukraine yana yi wa Rasha yaƙi.
A cikin wani bidiyo da sojojin Ukraine su ka wallafa, Evan Kibet ya ce an yaudare shi ne domin ya shiga yaƙin a yayin da ya ke wata ziyara a st Petersburg.
Ya ce an ƙwace fasfo ɗinsa da wayarsa, kuma aka tilasta masa sanya hannu kan wasu takardu da aka rubuta da harshen Rasha, ba tare da sanin amincewa yake yi ya shiga aikin soja ba.
Ɗan'uwan Evans, Isaac Kipyego ya yi kira ga gwamnatin Kenya ta shiga cikin lamarin.
Zuwa yanzu dai babu martani daga Moscow.
Shugaban Amurka Donald Trump da mai ɗakinsa, Melania Trump sun bar Bitaniya domin komawa ƙasarsu bayan kammala ziyarar aiki ta yini biyu da suka kai Birtaniya.
Ziyarar mai cike da tarihi ta ƙunshi yarjejeniyoyin diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu da ziyarar fadar sarkin Birtaniya.
A lokacin ziyarar Shugaba Trump ya gana da Firaminista Kier Starmer tare da sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi
Shugaban Amurka, Donald Trump na shirin komawa Amurka bayan kammala ziyarar yini biyu a Birtaniya.
Tuni shugaban ya isa babban filin jirgin sama na London Stansted, inda zai hau bababn jirginsa don komawa ƙasar.
A lokacin ziyarar Trump ya samu gagarumar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya.
Majalisar dokokin jihar Rivers ta buƙaci gwamnan jihar Similanayi Fubara ya aike mata da sunayen mutanen da yake son naɗawa a muƙamn kwamishinonin domin ta amince da su.
Ƴanmajalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Martin Amaewhule sun bayayna hakan ne a lokacin da suka koma aki daga dakatarwar wata shida da Shugaba Tinubu ya yi musu bayan sanya dokar ta-ɓaci a jihar cikin watan Maris.
Rahotonni daga jihar na cewa ya zuwa yanzu gwamnan jihar da kuma mataimakiyarsa ba su shiga ofishinsu ba.
Daruruwan mutane ne suka taru a harabar gidan gwamnatin Rivers domin tarbar zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Similanayi Fubara, wanda ke komawa aiki yau bayan dakatarwar da aka yi masa ta tsawon wata shida.
A ranar 18 ga watan Maris ne Shugaba Tinubu ya ayyana doka ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da duka zaɓaɓɓun masu riƙe da muƙaman jihar, da kuma naɗa kantoman riƙo a jihar.
Matakin ya zo ne bayan saɓanin siyasa da aka riƙa samu a jihar na tsawon watanni, tsakanin gwamnan jihar da ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rahoton kungiyar agaji da kare haƙƙin yara ta Save the Children ya bayyana cewa fiye da kashi ɗaya cikin uku na yara a Turkana, arewacin Kenya, suna fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki sakamakon fari da tsananin yunwa da hare-haren kada a tafkin Turkana da kuma yanke tallafin agaji.
Kungiyar ta ce iyaye mata a yankin suna wahala wajen samun abincin da za su ciyar da yaransu.
A cikin watanni biyu da suka gabata, kungiyar tare da Ma’aikatar Lafiya ta Kenya sun gudanar da bincike kan yara 2,780, inda aka gano yara 990, wato kusan kashi 36 kenan na fama da rashin abinci mai gina jiki.
Rahoton ya nuna cewa a Turkana sama da kashi 70 na al’umma ba sa samun abinci yadda ya kamata, lamarin da ya haifar da barazana ga rayuwar yara ƙanana da mata masu juna biyu da masu shayarwa.
Wasu iyaye mata a yankin sun bayyana halin ƙunci da suke ciki.
Dinah, wata uwa mai yara biyar ciki har da tagwaye, ta ce "mijina yana fita kamun kifi amma sau da yawa yana dawowa ba tare da wani kifi ba saboda tsoron hare-haren kada."
Haka kuma, Josephine, wata uwa mai yara huɗu da ke da juna biyu, ta ce "fari da rashin tallafin ƙungiyoyin agaji sun sa rayuwa ta ƙara tsananta fiye da da.
Shugaban ƙungiyar a Kenya da Madagascar, Jib Pornpun Rabiltossaporn, ya ce canjin yanayi da ambaliyar ruwa a tafkin Turkana, da kuma mamayewar ƙwaro sun taimaka wajen lalata amfanin gona da rage kiwo.
Wanna ya ce ya ƙara tsananta yunwa da matsalolin lafiya.
Ɗan takarar shugaban kasa ta jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ɗage dakatar da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da mambobin majalisar dokokin jihar da shugaba Tinubu yayi ba abin murna ba ne.
Atiku ya ce dakatar da su tun watanni shida da suka gabata ya saɓawa ƙundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ko yanzu da aka ɗage dakatarwar, hakan bai halatta ba.
Tun a ranar Laraba ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kawo ƙarshen dokar-ta-ɓaci da ya ayyana a jihar Rivers, inda ya ce daga Alhamis, 18 ga watan Satumba, gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisa, Martins Amaewhule, za su koma bakin aiki.
Sai dai Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka ga matakin gwamnatin Tinubu, inda ya bayyana cewa "Shugaban kasar bai da hurumin dakatar da gwamna da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya, haka kuma bai cancanci ya dakatar da majalisar dokoki ba."
"Wannan mataki ne na nuna danniya da kama karya daga gwamnatin Tinubu.
Idan za a tuna, rikicin siyasa a jihar Rivers ya samo asali ne daga saɓanin da ya kunno kai tsakanin gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu haka shi nemMinistan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.
Wannan saɓani ya jawo rabuwar kawuna tsakanin magoya baya da mambobin majalisar dokokin jihar.
A cewar Atiku, "Wannan ba dimokuraɗiyya bace, kuma ɗage dakatarwar bai canza gaskiyar cewa an karya ƙundin tsarin mulkin kasa ba.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nuna alhininsa dangane mutane 12 da suka rasa rayukansu a lokacin ibtila'in gobarar da ta tashi a dogon ginin Afritower a birnin Legas.
Gobarar wadda ta tashi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata ta shafi ginin hukumar tattara haraji ta FIRS da bankin UBA da kuma Capital UNited waɗanda dukkanninsu suke aiki a rukunin ginin.
Ofishin hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS da ke Legas ya tabbatar da rasuwar ma'aikatan nasa sakamakon tashin gobarar..
A cikin wata sanarwar da ofisihin ya fitar a shafinsa na X, ya ce bayan tashin wutar ne sai ma'aikata suka rinƙa durowa daga ofishin da ke hawa na bakwai al'amarin da ya sa wasu suka rasu sannan wasu da dama suka samu raunuka.
Duk da cewa hukumar ba ta faɗi adadin mutanen da suka mutu ko jikkata ba amma rahotanni na cewa waɗanda suka mutu sun kai mutum huɗu.
Tsutsotsin suna naɗe kamar abin kama gashi.
Ana kyautata zaton cewa cin naman alade da bai dahu sosai ba da rashin wanke hannu a kodayaushe na iya kasancewa sanadin fitowar tsutsotsin.
Mutumin mai shekara 52 ya kasa jure ciwon kan nasa, lamarin da ya sa ya nemi likitoci bayan magungunan da aka ba shi ba su yi aiki ba.
Likitocin sun yi masa hoton kwakwalwa inda suka gano farar tsutsa da ke haddasa cutar 'cysticercosis'.
Ma'aikatan hukumar tattara haraji ta Najeriya da na kamfanin United Capital Plc 10 ne suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke birnin Legas.
Gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito sanarwar da hukumar FIRS ta fitar tana cewa ta yi rashin ma'aikata huɗu, yayin da United Capital Plc ya tabbatar da mutuwar ma'aikatansa shida.
Ma'aikatan FIRS ɗin na aiki ne a hawa na shida da bakwai na ginin a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata.
Sanarwar ta ƙara da cewa gobarar ta shafi ofishinta mai kula da bincike kan haraji da ke ginin.
Hotuna da bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ma'aikata suka dinga dirowa daga dogon benen yayin da wutar ke ci.
Kamfanonin fasaha na Amurka da dama sun sanar da shirin zuba jari na biliyoyin dala a Birtaniya.
Mafi yawan adadi ɗaya da za a zuba shi ne na kamfanin Microsoft, wanda ya sanar da dala biliyan 30 - kuma shi ne adadi mafi yawa da zai kashe a wata ƙasa ba Amurka ba.
Shi ma Google ya yi alƙawarin zuba fan biliyan biyar a fannin bincike kan ƙirƙirarriyar basira ta AI cikin shekara biyu.
Shi kuma Nvidia ya ce zai zuba fan miliyan 500 wajen gina cibiyoyin tattara bayanai da za su taimaka wa AI ɗin a Birtaniya.
Kuɗaɗen wani ɓangare ne na yarjejeniyar fan biliyan 31 tsakanin Amurka da Birtaniya da suka ƙulla yayin ziyarar da Shugaba Donald Trump ke yi a Birtaniyan.
Gwamnatin Najeriya ta sake mayar da darasin tarihi a matsayin darussan dole da ɗalibai za su dinga yi makarantun firamare da sakandare na ƙasar.
Wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a ranar Laraba ta ce an ɗauki matakin ne domin "ƙarfafa kishi, da haɗin kai tsakanin 'yan ƙasa".
"A karon farko ɗaliban Najeriya za su fara yin darasin tarihi tun daga aji 1 na firamare zuwa aji 3 na ƙaramar sakandare [JSS3], yayin da 'yan aji 1 zuwa 3 [SS1 zuwa SS3] za su dinga yin darasin ilimin rayuwa da tsatso [Civic and Heritage Studies]," in ji sanarwar da ta wallafa a shafukan zumunta.
"'Yan aji 1 zuwa 6 na firamare za su san asalin Najeriya, da gwanayenta, da shugabanni, da al'adu, da siyasa, da addini, da mulkin mallaka, da kuma mulki bayan samun 'yancin kai.
"Ɗaliban JSS1-3 za su nazarci al'ummomi, da masarautu, da kasuwanci, da zuwan Turawa, da dunƙulewar Najeriya, da 'yancin kai, da dimokuraɗiyya, da kuma ɗabi'un mutum."
A shekarar 2007 ne gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sabuwar manhajar karatu, inda a ciki ta cire darasin tarihi daga firamare da sakandare.
Dakarun sojan Isra'ila na ƙara nausawa cikin wani yanki mai cike da jama'a a birnin Gaza, yayin da suke ci gaba da kai farmaki ta ƙasa domin ƙwace iko da babban birnin mafi cunkoson jama'a.
Ana iya ganin yadda hayaƙi ya turnuke sararin samaniya yayin da sojojin ke harba makaman atilare da luguden bama-bamai.
Dubban mutane sun gudu, wasu kuma sun maƙale saboda haɗarin da ke tattare da guduwar. Sama da mutane sittin ne aka ce an kashe a jiya kadai.
Isra'ila ta ce tana gudanar da bincike kan rahotannin da ke cewa dakarunta sun kai hari kan asibitin yara na Gazan.
Ta ce tana son kubutar da mutanenta da Hamas ta rike da su, da kuma fatattakar mayaƙan Hamas 3,000 a wurin da ta bayyana a matsayin "tungar mayaƙan ta ƙarshe".
Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Laraba - ta bawa ranar samu.
Shafin zai mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da kuma maƙwabtansu, yayin da za mu leƙa sassan duniya.
Ku biyo mu.