Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 11/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Muhammad Annur Muhammad

  1. Birtaniya ta ƙaƙabawa wasu dakarun ƙungiyar RSF na Sudan takunkumi

    Biritaniya ta kara wasu manyan jami'ai biyu na dakarun RSF daga Sudan cikin jerin sunayen wadanda ta ƙaƙabawa takunkumi.

    A ranar Litinin gwamnati ta sanar da 'kwace dukiyoyin Janar Abdel Rahman Juma Barkalla da Osman Mohamed Hamid Mohamed.

    Burtaniya ta dauki wannan mayaki ne kwanaki ƙalilan bayan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da bukatar Amurka ta hana shugabannin biyu tafiye-tafiye da kuma tsare dukiyarsu sakamakon rawar da suka taka a rikicin da ya kashe dubban mutane da kuma raba sama da mutane miliyan ɗaya da muhallansu

  2. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutane 15 a Lebanon

    Ma'aikatar Lafiya a Lebanon ta aƙalla mutane 15 da suka hada da mata da yara ƙanana sun mutu sakamakon wasu hare-hare da Isra'ila ta kai a Kudanci da Arewacin ƙasar.

    Tun da farko Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Sa'ar ya ce an samu ci gaba a yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila ta ke yi da Hezbollah.

    To amma sabon Ministan tsaron Isra'ila Isreal Katz ya ce babu batun tsagaita wuta a Lebanon har sai Isra'ila ta cimma duk burin da ta sanya a gaba

  3. Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

    Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce mambobinta sun kammala cimma matsaya domin fara siyan tataccen man fetur daga matatar man Dangote kai tsaye.

    Sun bayyana haka bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta domin bin bahasin yarjejeniyar da suka cimma da matatar da kuma hanyoyin samun man cikin sauki.

    Alhaji Zarma Mustapha, wani jigo a ƙungiyar ta IPMAN ya shaidawa BBC shirin da suka yi bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin matatar a ranar litinin, inda ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai haifar da wadatan man fetur a duk faɗin ƙasar.

    ''Ina bayar da tabbacin cewa muddin muka fara sayen mai kai-tsaye daga Dangote, ba za a rika samun ƙarancin man fetur a ƙasar nan ba, kuma muna sa ran cewa matatan gwamnati ma za su fara aiki nan bada jimawa ba'', In ji shi

    Alhaji Zarma Mustapha, ya ƙara da cewa, ƙungiyar ta na sa ran cewa za su man fetur da sauki daga matatar ta Dangote, domin a cewarsa a matsayinsu na ƴan kasuwa dole ne su bi yadda za su sami riba kuma samun man da sauki na cikin abubuwan da za su tabbatar da hakan.

    Ya ce har yaila yau akwai mabobin ƙungiyar da za su ci gaba da sayen mai daga Kamfanin NNPC, muddin za su same shi da sauki, amma ba zai iya bayar da tabbaci kan yadda farashin man zai kasance a kasuwa ba

    Ya ce'' Maganan farashi dai ba zan iya cewa komai a kan yadda za ta kasance ba saboda kasuwa ce za ta tabbatar da haka, yadda muka samu a kasuwa shi zai tabbatar da ko akan nawa ne za mu sayarwa jama'a.''

  4. 'Babu wanda ya taɓa tunkara ta da batun cin hanci'- Babbar alƙaliyar Kenya

    Alkaliyar alƙalan ƙasar Kenya ta yi martani kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma rashin iya aiki da ya dabaibaye bangaren shari'ar ƙasar.

    Martha Koome ta shaida wa BBC cewa "A cikin shekaru 22 da na yi a matsayin alƙaliya kuma na riƙe mukamin alƙaliyar alƙalai, babu wanda ya taɓa tunkara ta da batun cin hanci. Da sai na sanya an kama su."

    A baya-bayan nan ne aka zargi babbar alƙaliyar wadda ita ce mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami a ƙasar da gaza gudanar da bincike da kuma magance zarge-zargen cin hanci da rashawa a bangaren shari’a.

    Sai dai ta kare kanta da abokan aikinta, inda ta buƙaci duk wanda ya yi irin wannan zargi ya gabatar da shaidu ga hukumomin tsaro ko kuma hukumar sa ido kan ɓangaren shari’a.

    Ma’aikatar shari’ar Kenya ta daɗe tana fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa kuma a shekarar 2021 Mai shari’a Koome ta shaida wa BBC cewa cin hanci da rashawa “abin kunya ne na kasa a ciki da wajen ɓangaren shari’a.

    Ta ce tana da burin buɗe kotuna 11 a faɗin ƙasar waɗanda suka ƙware kan laifukan cin zarafi ta hanyar lalata - inda ta riga ta kafa biyu daga cikinsu a yammacin Kisumu da lardin Siaya.

    A baya-bayan nan dai an samu ƙaruwar laifukan cin zarafin mata, inda ƴan sanda suka sanar da cewa an kashe mata 100 a cikin watanni uku da suka gabata.

  5. Burkina Faso ta ƙaddamar da bincike kan bidiyon da ke nuna cin zarafin gawa

    Dakarun sojin Burkina Faso sun ce suna gudanar da bincike kan wani mumunan bidiyo da ke nuna yadda sojojin sa kai ke sarar wata gawa da adduna.

    Ana ci gaba da aiki don tabbatar da sahihancin bidiyon da mutanen da aka nuna a cikinsa "domin a tuhume su da abin da suka aikata, idan an tabbatar da gaskiyar lamarin," in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa.

    Sojoji ne ke mulkin ƙasar da ke yammacin Afirka, waɗanda suka ƙwace mulki kusan shekaru uku da suka gabata tare da alƙawarin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta tilastawa mutane miliyan biyu barin gidajensu.

    Amma dai ya zuwa yanzu ƙoƙarin da ake yi na fatattakar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ya ci tura, inda aka yi kiyasin kashi 40% na ƙasar na ƙarƙashin ikonsu.

    Bidiyon da ake magana ya fara yawo ne a ƙarshen makon da ya gabata.

    Ya nuna gawar da aka yankewa kai da hannuwanta, kuma aka huda mata ciki.

  6. Trump ya naɗa wasu sabbin jami'ai guda biyu

    Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya sake naɗa wasu muhimman jami'ai guda biyu gabanin komawar sa fadar White House a watan Janairu.

    Tom Homan, mai shekaru 62, zai yi aiki a matsayin jami'in kula da iyaka na Trump, wanda a baya ya taɓa riƙe mukamin mukaddashin daraktan kula da shige da fice da kwastam.

    Ita ma ƴar majalisar dokokin New York, Elise Stefanik, mai shekaru 40, ta zama jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda takwarar BBC ta Amurka CBS News ta tabbatar.

    A halin da ake ciki kuma, jam'iyyar Republican ta Trump na ƙara kusantar samun cikakken rinjaye a majalisar wakilan Amurka.

    Sun riga sun sami rinjaye a Majalisar Dattawa kuma suna buƙatar samun kujeru ƙalilan ne kawai don samun cikakken rinjaye a majalisar wakilai.

    Jam'iyyar na buƙatar kujeru 218 don samun rinjayen Majalisar.

    Ƴan Republican suna da 215 idan aka kwatanta da ƴan Democrat da ke da kujeru 210, a cewar CBS.

    Samun rinjaye a majalisar na baiwa jam'iyya ikon zartar da dokar kashe kuɗi da kuma ɗaukar matakan tsige jami'an gwamnati.

  7. Jam'iyyar Firaministan Muaritius ta sha kaye a zaɓen majalisa

    Firaministan Mauritius ya amince da cewa kawancensa, ta L'Alliance Lepep, ta sha "babban kaye" bayan zaɓen ƴan majalisar dokoki da aka gudanar ranar Lahadi.

    Firaminista Pravind Jugnauth ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa "Al'ummar ƙasar sun yanke shawarar zaɓar wata tawaga ta daban''.

    Jugnauth na neman wa'adi na biyu na shekaru biyar, amma babban abokin hamayyarsa, Navin Ramgoolam, wanda shi ne shugaban gamayyar 'Alliance of Change', na shirin zama shugaba na gaba a tsibirin da ke Tekun Indiya.

    An san ƙasar Mauritius a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka mafi kwanciyar hankali a tsarin dimokuradiyya amma wannan zaɓen ya fuskanci wata badaƙala ta kutsen wayar tarho tare da fallasa bayanan wasu manyan jami'an gwamnati a shafukan intanet.

    Gwamnatin ta ɗauki matakin sanya dokar hana amfani da shafukan sada zumunta har sai an kammala zaɓen, amma hakan ya haifar da cece-kuce kuma aka janye dokar a cikin sa'o'i 24.

    Ya zuwa yanzu ba a fitar da sakamakon ƙarshe na zaɓen ba, amma da alama jam'iyyar Ramgoolam za ta yi nasara.

  8. Macron da Starmer sun sha alwashin bai wa Ukraine cikakkaen goyon baya

    Faransa da Birtaniya za su bai wa Ukraine cikakken goyon baya "domin daƙile cin zarafin Rasha", in ji shugaban Faransa Emmanuel Macron da Sir Keir Starmer.

    Firaministan ya ya kasance bakon shugaban Macron a bikin tunawa da sojojin da suka faɗ a fagen daga a birnin Paris ranar Litinin, kuma ya yi wata ganawa da takwaransa na Faransa don tattaunawa game da mamayar da Rasha ta ke yi wa Ukraine.

    Sanarwar da fadar Elysee ta fitar ta ce shugabannin biyu sun jaddada aniyarsu ta "marawa Ukraine baya ba tare da wani tantama ba".

    Ganawar tasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sanya alamar tambaya game da goyon bayan da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump zai bai wa Ukraine bayan da ya ce zai iya kawo ƙarshen yaƙin a cikin kwana guda.

    Babu cikakken bayani kan ko shugabannin biyu za su goyi bayan bai wa Ukraine damar amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango a cikin yankunan Rasha.

  9. Taron sauyin yanayi na duniya : COP29 : An soki Azerbaijan mai masaukin baƙi kan take haƙƙin ɗan'adam

    An soki Azerbaijan mai masaukin baƙi a taron sauyin yanayi na duniya saboda take haƙƙin ɗan'adam a kudirorin gabanin taron na COP29.

    Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun nemi shugabannin duniya su tuhumi mai masaukinsu game da yadda take cin zarafin yanjarida, da masu fafutika wadanda suke sukar shugabanincin 'kasar.

    Kungiyoyin sun ce sama da 'yansiyasa 300 ake tsare da su a 'kasar. Sun kuma bukaci mahalarta taron daga 'kasashen ketare su matsa wa mahukuntan Azerbaijan lamba don su sako su.

    Yar fafutukar kare muhalli Greta Thunberg, wadda ta halarci wata zanga-zanga kusa da ofishin jakadancin Azerbaijan da ke Georgia, ta ce "ai kamata ƙasa kamar Azerbaijan wadda ta hana kungiyoyin fararen hula sakewa ta karbi bakuncin taron muhalli ba".

  10. Za a binne gawar tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya a Abuja ranar Juma'a

    Ana sa ran binne marigayi babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Taoreed Lagbaja ranar Juma'a a Abuja.

    Yayansa da yake bi, Moshood Lagbaja, ne ya bayyana haka a garin Osogbo, jihar Osun a lokacin da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar St Charles Grammar School Osogbo, (SCOBA), ta kai wa iyalan ziyarar ta'aziyya.

    Moshood ya ce hukumomin soji sun ce ba za su ba iyalan gawar marigayin ga, amma sun bayar da tabbacin cewa za a yi masa jana'iza da ta dace a Abuja, ranar Juma'a.

    Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar rasuwar babban hafsan sojin na ƙasa ne da ta ce ya rasu ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

    Kafin tabbatar da rasuwar, an fara raɗe-raɗin cewa babban hafsan ya rasu a sanadiyar cutar kansa a wani asibiti a ƙasar waje, inda masu yaɗa maganganun suka riƙa cewa an ɓoye rasuwar ne saboda masu rububin neman maye gurbinsa.

  11. Hukumar shari'a ta hukunta ma'aikatanta takwas a jihar Kano

    Hukumar kula da harkokin shari'a ta jihar Kano a arewacin Najeriya ladaftar da wasu ma'aikatanta takwas ciki har da alkalai.

    Wani kwamitin ladaftarwa na hukumar ne ya bayar da shawarar ɗaukar matakin bayan kammala bincikensa kan ƙorafe-ƙorafen da wasu suka gabatar waɗanda suka haɗa da zarge-zargen karɓar rashawa.

    Kwamitin karɓar korafe-korafen jama'a na hukumar kula da harkokin shari'ar ya ɗauki matakin ladaftawar ne kan ma'aikatan shari'a su takwas ciki har da alkalan kotunan majisteret.

    Kakakkin hukumar Baba Jibo Ibrahim ya ce bincike ya gano yadda wani alkalin kotun majistare ya gudanar da wata shari’a ba tare da an rubuta ta ba, abin da ya saba dokokin shari’a.

    Bayanai na cewa an jima ana kokawa da jami’an kotu a jihar game da yadda suke karbar toshiyar baki da sauran laifuka.

  12. Harin Rasha ya kashe aƙalla mutum shida da jikkata 21 a Ukraine

    Mutum aƙalla shida ne suka mutu, wasu 21 kuma suka ji rauni a wasu hare-hare na baya-bayan nan da Rasha ta kai ta sama a Ukraine.

    BIyar daga cikin mutanen sun mutu ne a birnin Mykolaiv, na kudanci, yayin da ɗayan ya rasu a Zaporizhzhia, in ji hukumomi.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce aƙalla mutum bakwai ne da suka haɗa da yara suka jikkata bayan da wani makami mai linzami ya faɗa wa wani gida a birnin Kryvyi Rih da ke tsakiyar ƙasar.

    Haka kuma Rashar ta ce ta lalata jiragen sama marassa matuƙa na Rasha 13 a kusa da yankunan yamma na Kursk da Belgorod, to amma ba wanda ka ce ya mutu.

    Shugaba Zelensky ya ƙara yin roƙo na makamai daga ƙawayen ƙasar tasa, tare da neman ƙasashen duniya kan su matsa wa Rasha ta dakatar da mamayar da take yi wa ƙasarsa.

  13. Rasha ta musanta tattaunawar Shugabanta da Donald Trump

    Fadar gwamnatin Rasha ta musanta rahoton da ke cewa Donald Trump ya tattauna ta waya da Shugabanta Vladimir Putin, inda a rahoton aka ce sabon zaɓaɓɓen shugaban Amurkan ya gargaɗi shugaban na Rasha a kan ci gaba da yaƙi a Ukraine.

    An ce tattaunawar wadda jaridar Washington Post ta fara bayar da rahotonta a jiya Lahadi, an ce an yi ta ne ranar Alhamis.

    An kuma ce a yayin tattaunawar Trump ya faɗa wa Putin ƙarfin sojin Amurka a Turai.

    Da aka tambayi darektan sadarwa na Trump, Steven Cheung kan gaskiyar rahoton tattaunawar, ya gaya wa BBC cewa: ''Ba ma magana a kan kiran waya tsakanin na ƙashin kai wanda Shugaba Trump ya yi da sauran shugabannin duniya."

  14. Inec ta kai muhimman kayan zaɓe jihar Ondo don zaɓen gwamna

    Hukumar zaɓe ta Najeriya ta ce ta kai muhimman kayan zaɓe zuwa jihar Ondo da ke kudancin ƙasar domin gudanar da zaɓen gwamna.

    Hukumar Independent National Electoral Commission (Inec) ta tsara gudnar da zaɓen a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamban nan.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Inec ta ce jami'an Babban Bankin Najeriya CBN ne suka karɓi kayan a Akure babban birnin jihar.

    Jirgin sojin sama na Najeriya ne ya yi jigilar kayan, a cewar Inec.

  15. Gwamnatin Kwara ta ce duk ma'aikacin da bai yi rijistar jiha ba ba za ta ba shi albashi ba

    Gwamnatin Kwara ta ce duk ma'aikacinta da bai yi rijista ya samu lambar hukumar rijistar mazauna jihar ba ba zai samu albashin watan nan na Nuwamba ba ko kuma alawus.

    Gargaɗin na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamishinar kuɗi ta jihar Dr Hauwa Nuru ta fitar, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta, a yau Litinin, a Ilori, inda ta buƙaci dukkanin ma'aikata na gwamnati da su tabbatar sun yi rajistar ba tare da ɓata wani lokaci ba.

    Kwamishinar wadda ta ce tun a watan Yuli aka fara rijistar, ta ce gwamnatin jihar ta ɓullo da tsarin ne domin tattara bayanai a kan dukkanin mazauna jihar domin inganta tsare-tsare da ɗaunin albarkatunta da gudanar da ayyuka da tabbatar da lafiyar jama'a da sauran muhimman abubuwa.

    Dr Hauwa ta ƙara da cewa rijistar, muhimmin mataki ne wajen samar da cikakken rumbun bayanai, da zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen gudanar da harkokinta yadda ya kamata tare da tabbatar da gaskiya da amana tsakaninta da jama'a.

  16. Trump ya tattauna da Shugaba Putin na Rasha kan yaƙin Ukraine

    Ofishin yaƙin neman zaɓen Donald Trump ya ce ba zai yi tsokaci ba kan rahotannin da ke cewa Trump ɗin ya tattauna da shugaban Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho bayan nasarar zaɓe da ya samu.

    Jaridar Washington Post ta ce a zantawar, Trump ya yi gargaɗi ga Putin kan batun yaƙin Ukraine tare da sanar da shi ƙarfin sojin Amurka a Turai.

    Wakilin BBC ya ce Washinton Post ta ce Donald Trump da Vladimir Putin sun tattauna a ranar Alhamis da ta gabata kan yanayin da ake ciki a Ukraine.

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya yi iƙirarin kawo ƙarshen yaƙin a ranar da zai karɓi ragamar mulki, sai dai bai yi bayanin hanyoyin da zai bi ba.

  17. Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Lakurawa

    Mai riƙon muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Olufemi Oluyede ya nemi da a haɗakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin arewa maso yamma.

    Janar Oluyede ya yi kiran ne a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a jihar Sokoto a jiya Lahadi, inda ya ziyarci sansanin dakarun da ke Tangaza da Illela.

    A kwanakin nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ta addabi yankin jihar Sokoto da Kebbi, wadda ake wa laƙabi da Lakurawa, da aka ce ta fito ne daga yankin Sahel.

    A ranar Juma'a al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka rasa mutum aƙalla 15 a wani artabu da suka yi da mayaƙan ƙungiyar ta Lakurawa.

    Yayin da ya ziyarci sansanonin Janar Oluyed, ya yaba wa sojojin tare da ba su tabbacin samun cikakken goyon baya a aikinsu na yaƙar 'yan ta'adda tare da magance ƙalubalan da ke fuskantarsu a aiki, bayan da aka yi masa bayani kan halin tsaron da ake ciki a yankin.

    Babban hafsan sojin na ƙasa ya nemi a samar da haɗin kai tsakanin al'ummomin yankin da jami'an tsaro a lokacin da yake ganawa da shugaban ƙaramar hukumar Tangaza, inda ya yi kira ga jama'a da su riƙa bai wa dakarun goyon baya da kuma bayanai masu amfani, inda ya ce da taimakon jama'a ne za a iya tabbatar da tsaro a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.

  18. NLC ta nemi a shiga yajin aiki a jihohin da ba su aiwatar da sabon mafi ƙanƙantar albashi ba

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC, ta Najeriya ta umarci ma'aikata a jihohin da gwamnatocinsu ba su aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanta ba su tafi yajin aiki daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.

    Umarnin na ƙunshe ne a wata takardar bayan taro da shugaban ƙungiyar ta NLC, Mista Joe Ajaero ya fitar bayan taron majalisar zartarwa ta ƙungiyar a Fatakwal.

    A sanarwar ƙungiyar ta nuna rashin amincewa da jinkirin da ta ce wasu jihohi a ƙasar na yi wajen aiwatar da tsarin na 2024, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da ya saɓa doka kuma na rashin adalci.

    Ajaero ya ce ƙin aiwatar da tsarin yana ƙara tsananin wahalar da ma'aikatan Najeriya ke sha yayin da rayuwa ke ƙara tsada.

    Ƙungiyar ta NLC ta lashi takobin maganin abin da ta kira rashin tausayi na gwamnati da gwamnonin wasu jihohi a ƙasar kan ƙin amincewa da sabon tsarin, inda ta ce za ta ɗauki tsauraran matakai a kai ciki har da na yajin aikin, idan gwamnatocin jihohin ba su aiwatarba nan da farkon watan na Disamba.

  19. Ƙasashen Musulmi sun fara taro kan yaƙin Gaza da Lebanon a Saudiyya

    A yau Litinn ne aka fara taron ƙasashen Musulmi da Larabawa wanda Saudiyya ke karɓar baƙunci, domin tattauna batun yaƙin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza da hare-haren da take kai wa a Lebanon.

    Ministan harkokin waje na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al-Saud shi ya shugabanci taron share fage na ministoci wanda ya shirya ajandar da za a tattauna, bayan da gwamnatin ƙasarsa ta kira taron ƙolin don bincike kan rikicin Isra'ila da Hamas a Gaza da kuma na Hezbollah a Lebanon, inda yanzu taron ke gudana a Riyadh.

    Taron na yanzu a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar zai ɗora ne a kan abubuwan da aka tattauna a taron da shugabannin ƙasashen Larabawa da Musulmi suka yi a babban birnin na Saudiyya a shekarar da ta wuce.

    Haka kuma taron zai mayar da hankali sosai wajen samar da tartibiyar hanya da za a bi domin kawo ƙarshen yaƙin na Gaza da kuma na Lebanon kamar yadda Saudiyyar ta sha alwashin yin duk abin da ya wajaba don cimma wannan buri.

    Saudiyya ta shirya wannan taron ne bayan da a baya-bayan nan da karɓi baƙuncin wani taro na farko na haɗakar duniya domin matsa lamba ta ganin an samar da ƙasar Falasdinu.

    Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta ce ana sa ran shugaban ƙasar Bola Tinubu wanda ke wajen taron zai gabatar da jawabi a kan kawo ƙarshen rikicin na Gaza da Lebanon.

  20. Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu - Fadar Shugaban Ƙasa

    Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa, muƙamin da ɗantakarar jam'iyyar PDP na muƙamin a 2023, ta ce yake ta faman nema har sau shida amma bai yi nasara ba.

    Fadar shugaban ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙon Tweeter da ya sanya kwanan nan.

    Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam'iyyarsa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa maganganu da shawarwarin da Atiku yake bayarwa a kan tattalin arziƙi sun nuna tsananin rashin fahimtarsa da ainahin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki, abin da sanarwar ta ce shi ne jagorancin Shugaba Tinubu ke magancewa.