Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya,

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 18/10/2025

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Asabar.

    Za mu kawo wasu rahotonnin gobe da safe.

  2. Hamas za ta miƙa ƙarin gawawwakin Isra'ilawa biyu a yau

    Ƙungiyar Hamas ta ce za ta miƙa ƙarin gawawwakin Isra'ilawa biyu da ta yi garkuwa da su a daren yau Asabar.

    Ana dai nuna ɓacin rai a Isra'ila kan rashin miƙa ragowar gawawwakin 'yan kasar 18 daga Gaza kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da aka ƙulla makon da ya wuce.

    Hamas ta ce tana faman lalubo inda gawawwakin suke a karkashin ɓaraguzai. Tun da farko ofishin firaministan Isra'ila ya bayar da umarnin cigaba da rufe mashigar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar har sai abin da hali ya yi.

    Ya ce buɗewar za ta dogara ne ga mayar da ragowar gawawwakin Isra'ilawan.

  3. Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki

    Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce raɗe-raɗin juyin mulki da wasu kafofin yaɗa labarai ke ruwaitowa ba gaskiya ba ne.

    Wata sanarwar da kakakin hedikwatar tsaron, Janar Tukur Gusau, ya fitar ta ce wasu kafofin yaɗa labarai na intanet ne suka ruwaito batun ta hanyar kafa hujja da soke faretin soji na bikin Ranar 'Yancin Kai, da kuma wasu jami'an rundunar da ake bincika da zargin karya ƙa'idar aiki.

    "Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa rahoton na ƙarya ne baki ɗayansa," a cewarsa. "An dakatar da faretin Ranar 'Yanci ne saboda a bai wa shugaban ƙasa damar halartar wani taro a wajen Najeriya, da kuma mayar da hankali wajen yaƙi da ta'addanci da 'yanfashin daji.

    "Binciken da ake yi wa jami'ai 16 kuma na yau da kullum ne da aka saba domin tabbatar da ɗa'a da ƙwarewar aiki. An kafa kwamatin bincike kuma za a sanar da sakamakon bincikensa."

    Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwar dakatar da faretin soji na al'ada da aka saba yi duk ranar bikin 'yancin kai na ranar 1 ga watan Oktoba ba tare da wani takamaiman dalili ba.

    Bayan bikin ne kuma rundunar sojin ƙasar ta sanar a ranar 4 ga watan Oktoba cewa ta tsare jami'anta 16 bisa laifuka daban-daban da suka shafi rashin da'a da kuma karya ƙa'idar aiki.

  4. Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto mutum 21 da 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kwara da ke tsakiyar ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da kakakin bataliyar 2 Division ya fitar, Kanal Polycarp Okoye ya ce rundunar Operation Fansan Yama ce ta samu nasarar ranar Juma'a.

    Kanal Okoye ya ce mutanen sun ƙunshi maza 14, da mata biyar, da jariri ɗaya, da 'yan ƙasar China huɗu. "Mutanen sun ce an yi garkuwa da su daga sassa daban-daban na jihohin Kwara da Kogi," in ji shi.

    "Bayan dakaru sun tsananta farmaki, dole ta sa 'yanfashin suka saki mutanen da ke hannunsu, waɗanda wasunsu suka shafe sama da wata huɗu a wajensu."

  5. Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koma gida a yau Asabar daga taron yaƙi da ta'addanci da ya halarta a ƙasar Italiya.

    Tinubu ya tafi taron na Aqaba Process ne a ranar Lahadi 12 ga watan Oktoba, inda ya halarci taron da ƙasar Jordan da Italiya suka jagoranta a birnin Rome.

    Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu ya gana da Firaministan Italiya Giorgia Meloni a gefen taron, da kuma mai mai bai wa shugaban Amurka shawara kan ƙasashen Larabawa da Afirka Massad Boulos.

  6. Yadda dakarun Civil Defense ke koya wa ɗalibai dabarun kare kai

    Wata tawagar dakaru mata ta hukumar tsaron Civil Defense a Najeriya na aikin tsaron makarantu da kuma wayar da kan ɗaliba da malamnsu game da matsalar tsaro.

    Babban aikinsu shi ne taimakawa wajen ƙarfafa tsaron makarantun firamare da sakandare daga masu garkuwa da ɗaliban, matsalar da Najeriya ta sha fama da ita a 'yan shekarun nan.

    BBC ta bi tawagar wurin aiki a Abuja domin ganin yadda suke koya wa ɗalibai dabarun kare kan su idan tsautsayi ya sa suka shiga wata matsala.

    Latsa hoton ƙasa ku kalli bidiyo:

  7. Za a buɗe mashigar Rafah ranar Litinin, in ji jami'an Falasɗinawa

    Ofishin jakadancin Falasɗinu a Masar ya ce za a buɗe mashigar Rafah da ke tsakanin Masar ɗin da Zirin Gaza domin bai wa Falasɗinawa damar komawa zirin.

    Zuwa yanzu babu wata alama da ke nuna ko za a ƙyale Falasɗinawan su fita daga Gaza ta mashigar. Isra'ila ba ta tabbatar da hakan ba zuwa yanzu.

    A baya, ita kaɗai ce mashigar Gaza da ba ta ƙarƙashin ikon Isra'ila, kuma ita ce ke taimakawa matuƙa wajen shigar da kayan agaji.

    Yanzu haka ɗaruruwan motocin agaji na kan layi a mashigar suna jiran izinin shiga Gaza.

  8. 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'

    Ma'aikatar tsaron farin kaya da ke ƙarƙashin Hamas a Gaza ta ce aƙalla mutum 11 ne suka rasu a ranar Juma'a bayan wata motar yaƙin Isra'ila ta yi harbi wata mota ɗauke da Falasɗinawa a daren ranar.

    Sai dai sojojin Isra'ila sun ce sun yi harbin ne kan wata mota da suka ce ta tsallake bakin iyakar yankin da ke ci gaba da zama a ƙarƙashin ikonsu.

    Wannan ne hari mafi muni tun bayan da yarjejeniyar tsagaita tsakanin Hamas da Isra'ila ta fara aiki kimanin kwana takwas da suka gabata.

    Amma a ɗayan ɓangaren, ana tunanin Falasɗinawa da yawa ba sa iya gane ina ne bakin iyakar da sojojin suka shata, wanda bai rasa nasaba da rashin ingantaccen layin sadarwa.

    Runduar tsaron Isra'ila ta ce za ta saka alamomi da ke nuna inda sojojinta suke jigbe.

  9. Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike

    Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya musanta maganar da ake yaɗawa cewa zai yi takarar shugaban ƙasa, inda ya ce shi burinsa ya goyi bayan shugaban na yanzu, Bola Tinubu domin domin ya sake lashe zaɓe.

    An fara rade-radi ne cewa wasu jagororin PDP suna kira ga tsohon gwamnan na Rivers da ya tsaya takara, lamarin da ya fara jan hankali a daidai lokacin da aka fara lissafin zaɓen na 2027.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da tashar Channles ta ruwaito daga mai magana da yawunsa, Lere Olayinka, inda a ciki ya ce "labarin ƙarya ne kawai da wasu marasa aikin yi suke yaɗawa."

    "Minista ya sha nanatawa cewa Bola Tinubu yake so, kuma shi ne zai goya wa baya a babban zaɓen ƙasar na 2027.

    "Kowa ya san Wike ba ya ɓoye-ɓoye, yana bayyana duk wani abu da zai yi, kuma a fili yake yi," in ji shi kamar yadda ya bayyana a sanarwar.

    Olayinka ya ce taron da Wike ya yi da wasu jiga-jigan PP a ranar 20 ga watan Agustan 2025, taro ne tsakaninsa da wasu manyan ƴan jam'iyyar daga kudancin Najeriya, sannan ya ce an fitar da sakamakon taron ga manema labarai.

  10. An fara zaman sulhu tsakanin Pakistan da Afghanistan a Doha

    Afghanistan da Pakistan sun fara tattaunawa kan ɓullo da hanyoyin da za su bi domin samar da zaman lafiya a tsakanin ƙasashen biyu.

    Tattaunawar wadda ake yi a birnin na Qatar, gwamnatin ƙasar ta Qatar ce ke jagoranta domin sasanta ƙasashen biyu maƙwabtan juna.

    Wannan na zuwa ne bayan jiragen Pakistan sun yi luguden wuta a bakin iyakar Afghanistan na Paktika a ranar Juma'a.

    Pakistan ta zargi Afghanistan da taimakon mayaƙa suna kai mata hare-hare, zargin da Kabul ta musanta.

    Afghanistan ta ce daga cikin waɗanda aka kashe a hare-haren na Pakistan na ƴan kwanakin nan, har da wasu ƴanwasanta na cricket.

  11. Me ya sa maza ke mafarkin jima'i, kuma hakan alama ce ta rashin haihuwa?

    Akwai jita-jita da yawa da ake yi kan batun kawowa da kuma tafiya yayin barci, kuma maza da yawa sun yi imanin cewa jin mutum yana tafiya lokacin barci, alama ce ta rashin haihuwa ko rashin wadataccen maniyyi a wurin maza.

    Kawowa yayin barci abu ne da aka saba ji a wajen mutane, a cewar masana kiwon lafiya.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a daidai lokacin da yara maza suka fara balaga, yawan ƙwayoyin halittan namiji na ƙaruwa, wanda wani lokaci zai kawo tsaiko wurin barci.

  12. Kotu ta yi watsi da buƙatar hana zanga-zangar sako Nnamdi Kanu

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar rundunar ƴansandan Najeriya ta a hana zanga-zangar sakin Nnamdi Kanu.

    A wani rahoto da jaridar The Guardian mai zaman kanta ta ruwaito, ta ce ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya Omoyele Sowore ne ya shirya kuma zai jagoranci zanga-zangar a ranar 20 ga watan Oktoba zuwa kusa da fadar shugaban Najeriya domin buƙatar lallai sai an saki Kanu, wanda ya kwana biyu a ɗaure.

    Shugaban ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ne ya garzaya kotu, inda ya buƙaci babbar kotun ta hana su Sowore gudanar da zanga-zangar.

    Sai dai kotun ta ce ba za ta yanke hukunci ba har sai ta ji daga ɗayan ɓangaren, inda ta yi umarni a miƙa takardar ƙarar zuwa ga Sowore, sannan ta ɗage shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba

    Sowore ya ce za su yi zanga-zangar ne domin nuna rashin jin daɗinsu kan ci gaba da riƙe da Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar Ipob, wanda ke tsare tun a shekarar 2021.

  13. An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

    Wani sabon bincike ya nuna cewa wani sabon gwajin jini mai sauki zai iya gano nau'ukan ciwon kansa fiye da 50 tun a matakin farko da suke da sauƙin magancewa.

    Gwajin da ake kira Galleri Test an bayyana cewa zai iya gano kansa cikin sauki da ke cikin jini.

    Sakamakon gwajin da aka yi a Arewacin Amurka ya nuna cewa, kashi uku cikin huɗu na ciwon kansar da aka gano sun kasance ga waɗanda ba su cikin tsarin gwaji kamar a hanta da ciki da mafitsara.

    Wakilin BBC ya ce gwajin ya kawar da kansa a sama da kashi casa'in da tara cikin 100 ga waɗanda gwaji ya tabbatar da ba su da ciwon na kansa

  14. Trump ya hana Ukraine makamin Tomahawk

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gaza samun babban makami mai linzami na Tomahawk daga Amurka bayan tattaunawarsa da shugaba Trump a Fadar White House.

    Mr Zelensky ya kai ziyara Washington ne tafe da fatan zai samu makamin domin kai wa Rasha hari.

    Mr Trump ya ce ba wai ya yi watsi da bukatar ba ne - amma yana son kawo karshen rikicin., Bayan ganawarsu, shugaban Amurka ya bukaci Rasha da Ukraine su dakatar da kisa su cimma yarjejeniya.

    Wakiliyar BBC ta ce Mr Trump ya fi nuna bukatar cimma masalaha tun zantawar da ya yi da shugaba Putin ta wayar tarho tsawon sa'a biyu da rabi kwanaki biyu da suka gabata inda suka amince su hadu a Budapest

  15. Hamas na fuskantar matsin lamba kan gawarwakin Isra'ilawa da ta yi garkuwa da su

    Hamas ta ba Isra'ila gawar daya daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su, kuma tuni gawar ta isa Tel Aviv domin tantancewa.

    Kungiyar Agaji ta Red Cross ce ta karbi akwatin gawar a kudancin Khan Younis a yau Asabar. Idan har aka tabbatar, zai kasance saura gawar mutum 18 da Hamas ta bayar.

    Hamas na fuskantar matsin lamba domin dawo da dukkanin gawarwakin mutanen amma ta ce tana fuskantar kalubalen zakulo gawawwakin wadanda baraguzai suka danne.

    Rahotanni sun ce wata tawaga ta musamman ta shiga Gaza tare da sa idon Isra'ila kuma jami'an na shirin soma aiki domin gano sauran gawarwakin

  16. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiya, barkanmu da sake haduwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye na BBC Hausa.

    Da fata za ku kasance tare da mu.