Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku aabaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Na yi nadamar saya wa marigayi Janar Lagbaja fom ɗin shiga soja - Kawunsa

    Shugaban iyalan gidan su tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftana Janar Taoreed Lagbaja, Pa Tajudeen Lagbaja, ya ce ya yi nadamar saya wa marigayin takardar neman shiga makarantar horad da ƙananan hafsoshin sojan Najeriya, (NDA).

    Pa Tajudeen, wanda ƙani ne ga mahaifin marigayin ya ce da ya san hakan zai kai ga rasuwar Janar Lagbaja da tun da farko bai sai masa fom ɗin ba.

    Haka kuma wasu dangi ko iyalan marigayin sun yi zargin cewa wataƙila an kashe Laftana Janar Lagbaja ne ta wata muguwar hanya saboda rikicin wani fili a garinsu.

    Jaridar Daily Trut ta ruwaito cewa jaridar The Nation, ta bayar da labarin cewa a 2023 wani rikici ya tashi a garin Ilobu, hedikwatar ƙaramar hukumar Irepodun da ke jihar Osun, a lokacin da wakilan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya suka shirya gina asibiti a garin.

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa marigayi Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ƙasar a watan Yuni na 2023,inda ya maye gurbin Laftanar Janar Faruk Yahaya, wanda tsahon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya naɗa a 2021.

    Rahotanni sun ce tun bayan ba shi muƙamin, ya riƙa fama da rashin lafiyar da take kawo masa tsaiko wajen gudanar da aikinsa, lamarin da ke sanyawa yana yawan fita ƙasashen ƙetare neman magani.

    Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa cewa babban hafsan sojin na ƙasa ya rasu ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

  2. Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu'a

    Matar shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta musanta rahoton da ke cewa za ta jagoranci taron yi wa ƙasa addu'a saboda tarin matsalolin da Najeriya ke fama da su.

    A ranar Lahadi da ta wuce wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa matar shugaban ƙasar tare da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu za su jagoranci taron kwana bakwai na yi wa ƙasar addu'a kan halin da take ciki.

    Rahoton ya bayyana cewa Darakta Janar na Taron yi wa kasa Addu'a, Segun Afolorunikan, shi ne ya yi sanarwar a wani taron manema labarai a Abuja, ranar Lahadi da ta wuce.

    A waccan sanarwar Afolorunikan ya ce taron wanda aka tsara tare da jagororin addinin Kirista da Musulmi, zai buƙaci Allah Ya shiga al'amarin ƙasar kan matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da kuma tsaro.

    Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun maiɗakin shugaban ƙasar, Busola Kukoyi, ta fitar a yau Asabar, ta ce, maganar ba ta da tushe balle makama.

  3. Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu ministoci tare da wasu shugabannin hukumomi za su bar Abuja a gobe Lahadi domin halartar taron koli na hadin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulmi wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2024, a babban birnin Saudi Arabia, Riyadh.

    Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a birnin a bara.

    Taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya.

    Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da tafiyar a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a yau Asabar.

    Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris da kuma shugaban hukumar bayanan sirri ta Najeriya, Mohammed Mohammed.

    Sanarwar ta ce ana sa ran a wajen taron Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar dakatar da bude wuta nan take.

  4. Qatar ta janye daga tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Hamas

    Rahotanni na cewa Qatar ta janye daga tattaunawa tsakanin Isra'ila da Hamas, inda take da matsayin babbar mai shiga tsakani.

    Qatar ta zargi bangarorin biyu da zaman tattaunawar ba sa zuciya daya ba, a don haka ta ce ita ba za ta iya ci gaba da shiga tsakanin ba.

    Qatar ta ce ta gaya wa Hamas ce ofishinta na Doha a yanzu ba ya aikin da ya sa aka kafa shi.

    Wannan na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da manyan jami'an gwamnatin Amurka suka ce gwamnatin Amurkar ba za ta sake amincewa da kasancewar wakilan Hamas a Qatar ba.

    Qatar ta kasance mai shiga tsakani a tattaunawar a tsawon shekarar da ta gabata tare da Amurka da Masar.

  5. Harin Isra'ila ya kashe mutum bakwai da jikkata gommai a Lebanon

    Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce aƙalla mutum bakwai aka kashe ciki har da ƙananan yara biyu, yayin da 46 suka jikkata bayan hari ta sama da Isra'ila ta kai birnin Tyre na gaɓar tekun kudancin ƙasar.

    Ma'aikatar ta ce tawagar aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo gawarwakin mutanen da suka mutu a harin.

    Harin na zuwa ne bayan kwanan luguden hare-hare ta sama a kudancin birnin Beirut.

    Tun da farko Isra'ila ta gargaɗi mazauna wurin su fice da yankin, wanda ƙungiyar Hezbollah ke da ƙarfi.

    Kafofin yaɗa labaran Labanon sun ruwaito cewa jakadan Amurka na musamman, Amos Hochstein zai ziyarci yankin a makon gobe, a wani sabon yunƙuri na cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikici da Irs'ila.

  6. An karɓi kashi 85 cikin 100 na katin zaɓe a jihar Ondo - INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce kashi 85 cikin 100 na al'ummar jihar Ondo sun karɓi katin zaɓensu, yayin da ya rage mako gudanar da gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

    Cikin wani saƙo da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na X, ya nuna cewa mutum 2,053,61 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar.

    INEC ɗin ta kuma ce mutum 1,757,205, wato kashi 85 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar ne suka karɓi katin zaɓen nasu, yayin da mutum 295,856 suka gaza karɓar katunan nasu.

    Tuni dai hukumar zaɓen ta fara horas da masu aikin zaɓe na wucin gadi da za su jagoranci gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓen jihar.

  7. Jam'iyyu sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen gwamnan Ondo

    Jam'iyyun siyasa da 'yan takara sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    An yi bikin sanya hannun ne ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaman lafiya na ƙasa NPC, a cibiyar raya al'adu da ke Akure, babban birni jihar.

    Shugaban kwamitin, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga duka masu ruwa da tsaki su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

    Ya kuma buƙaci shugabannin jam'iyyu da 'yan takara su amince da sakamakon zaɓen matsawar an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana.

    A nasa ɓangare shugaban hukumar zaɓen kasar, Farfesa Mahmood Yakubu ya yaba wa kwamitin bisa ƙoƙarinsa na haɗa kan jam'iyyun da 'yan takara a teburin yarjejeniyar zaman lafiya a lokutan zaɓukan ƙasar.

    Farfesa Yakubu ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da sarakuna da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa hannu da hukumarsa don gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin kwanciyar hankali da lumana.

    A ranar 16 ga watan Nuwamban da muke ciki ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar ta Ondo.

  8. Ambaliyar Sudan ta Kudu ta shafi mutum miliyan 1.4 - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ambaliyar da Sudan ta Kudu ta fuskanta ta shafi mutum miliyan 1.4, tare da gargaɗin ƙara yaɗuwar cutar Maleriya.

    Hukumar bayar da jin ƙai ta Majalisar, OCHA ta ce ambaliyar ita ce mafi muni da aka taɓa samu a ƙasar cikin gomman shekaru.

    A watan Mayu, gwamnatin ƙasar ta ankarar da ƙasashen duniya kan hatsarin da ke tattare da mummunar ambaliyar, da ƙasar ta shafe watanni tana fuskanta.

    Hukumar OCHA ta ce kusan mutum 400,000 ne ambaliyar ta tilasta wa barin gidajensu a ƙasar, yayain da fiye da rabin al'ummar ƙasar ke fama da matsalar ƙarancin abinci.

    Haka kuma ɓarkewar rikice-rikice a ƙasar ya tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa zuwa makwabciyar ƙasar Sudan.

    Ana dai alaƙanta batun sauyin yanayi da wannan ambaliyar, yayin da ake zargin shugabannin ƙasar mai arzikin man fetur, da mayar da hankali wajen tsawaita wa'adinsu a kan mulkinsu, maimakon magance matsalolinƙasar.

  9. Na yi mamakin sauke ni daga muƙamin minista - T Gwarzo

    Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa.

    Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, sabod a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi.

    ''Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la'akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin.

    Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam'iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam - da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu.

    Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, don haka ya ce yana gode wa shugaban ƙasar, bisa damar da ya ba shi a gwamnatin tasa

  10. Dole ne Ukraine ta haƙura da yankin Crimea - Mashawarcin Trump

    Wani babban mashawarcin zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump, ya faɗa wa BBC cewa manufar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ita ce samar da zaman lafiya, ba wai ƙwato yankuna ba.

    Bryan Lanza ya ce dole ne Shugaba Zelensky na Ukraine ya haƙura da yankin Crimea da Rasha da ƙwace.

    Ya ƙara da cewa babban abin da Amurka ta sanya a gaba shi ne dakatar da kashe-kashe.

    Dangane da yaƙin Gaza kuwa, Mista Lanza ya ce Falasɗinawa ne ke shan wahala a yaƙin, sannan ya goyi bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kan yin duk mai yiwuwa don ƙwato Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su.

  11. 'Yansandan Kano sun kama waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane

    Rundunar 'yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane da take zargi sun shiga jihar ne da nufin yin yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama mutanen a garin Kwanar Dangora, kuma yanzu suna hannun 'yansanda, bayan da ya ya ce sun shiga jihar da nufin yin garkuwa da mutane.

    Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ''wannan kasuwancin fa na satar mutane ba zai yi tasiri a Jihar Kano ba Insha Allah''.

    Ya kuma gode wa al'ummar jihar bia addu'o'in da ya ce suna yi a koyause.

    Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ba ta cikin jihohin yankin da ke fama da masu garkuwa da mutane, kodayake ana ɗan samu jifa-jifa, amma ba kamar sauran wasu jhohin yankin, da matsalar ta yi ƙamari ba.

  12. Gawuna ya kamata a bai wa minista bayan saukeni - T Gwarzo

    Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya kamata a bai wa muƙamin minista bayan sauke shi.

    A wata hira da BBC ya ce tsohon ministan ya ce dalilin da aka bayar na sauke shi, shi ne wai yankin Kano ta arewa da ya fito, 'yan siyasa masu muƙamai a tarayya sun yi yawa don haka ana son mayar da kujerarsa yankin Kano ta tsakiya.

    ''Kuma indai da gaske ake kano ta tsakiyar za a yi wa, ai ga ɗan takararmu nan na gwamnan - wanda shi ne jagoranmu a yankin Kano ta tsakiyar, me zai hana a ba shi''?

    Ya ce muƙamin da ka bai wa Gawuna a yanzu, ba zai iya riƙe magoya bayansa da shi ba.

    ''Kuma duka sauran takwarorinsa da suka yi takara a wasu jihohin an ba su muƙamai, misali ga ɗan takarar jihar Plateau, da na Zamfara duk, an ba su minista'', in ji T Gwarzo.

    Ya ƙara da cewa ya kamata a fara yi wa Gawuna tayin muƙamin, sai dai in shi ne ya ce ba ya so, to sai a bai wa wani.

    ''To amma shi ma wannan da aka bai wa ni bani da wani haufi da shi, tare muke komai a siyasa kuma ina yi masa fatan alkairi''.

  13. Biden ne ya janyo wa Kamala Harris faɗuwa zaɓe - Nancy Pelosi

    Tsohuwar kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi, ta ɗora alhakin faɗuwar da jam'iyar Democrat ta yi a zaɓen da ya gabata kan shugaba Biden.

    Ms Pelosi ta ce inda Biden ya janye daga takara da wuri da Kamala Harris ba ta faɗi zaɓe ba.

    Madam Pelosi ta taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan Biden na janye takararsa.

    Sai dai ta shaida wa jaridar New York Times cewa da ya janye da wuri da jam'iyyar ta samu isasshen lokacin da za ta zaɓo wanda zai maye gurbinsa.

    Hakan dai na zuwa ne bayan da Donald Trump ya samu nasara kan ƴar takararsu Kamala Harris a zaɓen.

  14. NHRC ta wanke sojojin Najeriya daga zargin tilasta wa mata 10,000 zubar da ciki

    Kwamitin bincike na Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, NHRC ya kafa ya wanke sojojin Najeriya bisa zarginsu da tilasta zubar da cikin mata aƙalla 10,000 a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    Shugaban kwamitin binciken, Abdul Aboki - wanda tsohon alƙalin kotun ƙolin ƙasar ne, tare da sauran mambobin bakwai, sun bayyana zargin da cewa ''ƙarya ce maras tushe'' da ke cikin wani rahoto na musamman da wata kafar yaɗa labaran ƙasar waje ta wallafa.

    A zaman ƙarshe da kwamitin ya yi ranar Juma'a a Abuja, ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da wannan zargi da ke ƙunshe cikin rahoton.

    “Dangane da batun tilasta zubar da ciki, kwamitin bai samu wata hujja da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun aikata abin da ake zargnsu da shi na tilasta zubar da ciki a asirce na kusan mata 10,000 a yankin arewa maso gabas, babu wata hujja da ta nuna hakan a iya binciken da muka yi,'' kamar yadda babban sakataren hukumar NHRC, Tony Ojukwu ya bayyana.

    A watan Disamban 2022 ne kamfanin dillancin labarai na Reuters cikin wani rahotonsa ya zargi sojojin Najeriya da aikata laifukan keta haƙƙin bil-adama - ciki har da zargin tilasta wa mata da 'yan mata aƙalla 10,000 zubar da ciki - a lokacin da suke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas tun 2013.

    Rahoton ya ce an zubar da cikin ne ba tare da so ko izinin matan ba.

  15. An yi jana'izar mutum 15 da Lakurawa suka kashe a Kebbi

    An gudanar da jana'izar mutanen da Lakurawa suka kashe a garin Mera na jihar Kebbi.

    A ranar Juma'a da rana ne dai aka samu arangama tsakanin mutanen gari da Lakuwaran a wajen garin Mera na jihar Kebbi.

    An samu arangamar ne dai bayan da aka zargi Lakuwaran da ƙwace wa wani mutumin gari Mera dabbobin da ke yake kiwo a wajen garin, lamarin da ya sa 'yan garin suka fusata, suka kuma fita bayan gari da nufin yin arangama da Lakuwaran domin ƙwato dabbobin.

    Arangamar ta haifar da asarar rayuka da jikkata daga mutanen garin da kuma ɓangaren Lakuwaran, kamar yadda wani ɗan jarida ya tabbatar wa BBC.

    Cikin waɗanda suka halarci jana'izar har da mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida tare da Maimartaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammad Mera.

    A cikin makon nan ne dai hadikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da ɓullar ƙungiyar Lakurawan, bayan da mazauna yankin suka koka game da ayyukan 'yan ƙungiyar, waɗanda ke ƙwace wa mutane dabbobi da nufin samun ''ganima'' ko fitar da ''zakka''.

  16. Rasha za ta yi taro da ƙasashen Afirka

    Rasha na shirin jagorantar taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Afirka.

    Taron - wanda zai gudana birnin Sochi na a ƙasar Rashar na da nufin inganta alaƙar siyasa da tattalin arziki da tsaro na Moscow da kuma rage tasirin ƙasashen Yamma a nahiyar.

    Shugaba Vladimir Putin ya yi alƙawarin gina cibiyoyin Nukiliya a ƙasashe da dama na Afirkar domin faɗaɗa ƙarfin faɗa a ji a yankin.

    Shugabannin ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun mayar da hankali kan Rasha domin samun tallafin soji bayan yanke alaƙa da ƙasar Faransa.

  17. Amurka na tuhumar wani mutum kan zargin haɗa baki da Iran don kashe Trump

    Ma'aikatar shariar Amurka ta ce tana tuhumar wani mutum da take zargin yana da hannu kan zargin yunƙurin da dakarun juyin juya hali na Iran suka yi na kashe zaɓaɓɓen shugaban Amurkar Donald Trump.

    Farhad Shakeri ya shaida wa ƴansandan Amurka cewa an ba shi umarnin aikata kisan ne a watan Oktoba.

    Rahotonni sun ce an ba shi damar yin tsarin da zai ɗauki waɗanda za su taimaka wajen aiwatar da kisan cikin mako guda.

    Sai dai ana zargin ya shaida wa waɗanda ke ɗaukar nauyin kisan cewa yana da tabbacin Trump zai faɗi zaɓe, kuma zai fi kyau a kashe shi bayan faɗuwar.

    Hukumomin Amurka sun ce ba su kama Mista Shakeri ba, sai dai sun yi amannar yana Iran, bayan da aka kama wasu mutum biyu da suke aiki tare.

  18. Aƙalla mutum 25 sun mutu bayan fashewar bom a Pakistan

    Hukumomi a Pakistan sun ce aƙalla mutum 25 ne suka mutu bayana fashewar wani bom mai ƙarfi a tashar jirgin ƙasa ta Quetta, babban birnin Balochistan da ke yammacin ƙasar.

    Bidiyon da aka yaɗa na inda lamarin ya faru ya nuna gawarwakin mutane kwance cikin ɓaraguzai, yayin da wani ɓangare na rufin tashar jirgin ya faɗi.

    Fashewar ta auku ne a daidai lokacin da fasinjoji ke jiran hawa jirgin safe.

    'Yansanda sun ce wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ya kai harin, inda ya tayar da bom ɗin da ke jikinsa a tsakiyar fararen hula da sojoji.

    Ƙungiyar 'yan awaren 'Balochistan Liberation Army' ta ɗauki alhakin kai harin, inda ta ce ta yi hakan ne da nufin kai wa sojoji hari.

    Lardin Balochistan na fuskantar ƙaruwar munanan hare-hare a baya-bayan nan, sakamakon ƙaruwar buƙatar cin gashin kan yankin da kuma mallakar ma'adinan lardin.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmy da safiyar ranar Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku halin da wasu sassan duniya ke ciki.

    Kuna tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta