Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran wasanni na BBC Hausa daga 20 zuwa 26 ga watan Satumbar 2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 20 zuwa 26 ga watan Satumbar 2026.
Taƙaitattu
- Carrick ya ja kunne kada kuskuren VAR ya shafi sauran wasanninsu
- Premier League: Manchester City 5-3 Sunderland
- Iraola ya je ya doke tsohuwar kungiyarsa Bournemouth a Premier League
- Me zai faru a wasan hamayya tsakanin Atletico Madrida da Real Madrid?
- Barcelona za ta taya Haaland, Liverpool ba ta da niyyar sallamar Wirtz
- Man United na fatan komawa kan ganiya a wasan Fulham
- Latsa nan don shiga zauren BBC Hausa WhatsApp
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
, Najeriya 2-1 Madagascar
An tashi wasan Super Eagles ta samu nasara da cin 2-1 a Uyo.
, Najeriya 2-1 Madagascar
An yi wa mai tsatron baya, Onyemaeci keta ya fadi yana ta wani juye-juye kamar dai salon bata lokaci.
, Najeriya 2-1 Madagascar
An kara minti hudu, kuma kamar karfin Madagascar ya ragu ba kamar yadda ta fara a farkon zagaye na biyu, watakila ta hakura da an doke ta 2-1 a wasan na farko a cikin rukuni na 12 a neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka da za a yi a 2027 a Kenya da Uganda da kuma Tanzaniya.
, Najeriya 2-1 Madagascar
Najeriya tana ta kora kara kwallo na uku, amma idan aka tashi haka tana da maki uku a wasan farko, zai taimaka mata fuskantar karawa ta biyu nan gaba a gidan Guinea Bissau.
, Najeriya 2-1 Madagascar
Super Eagles ta kara yin sauyi, inda Ola Aina ya fita aka mayr gurbinsa da Osayi Samuel.
, Najeriya 2-1 Madagascar
Kasa da minti 10 a tashi daga karawar, ya kamata Super Eagles ta kara daya a raga, domin komai zai iya faruwa a fannin taka leda.
, Najeriya 2-1 Madagascar
Super Eagles sai kai kora take kuma canjin da ta yi ya yi kyau sosai, inda Awoniya ya fto da wata kwallon amma mai tsaron raga ya kula da abinda aka yi nufi ya kamata a kwance.
, Najeriya 2-1 Madagascar
Dama mai kyau da Najeriya ta samu ta kara kwallo, sai dai Arokodare ya rufe ido ya buga kwallon da karfi ta yi sama ta fita waje.
, Najeriya 2-1 Madagascar
An fitar da Ademola Lookman an saka Taiwo Awoniyi mai taka leda a Coventry City mai buga gasar Premier League a bana.
Super Eagles ta kara ta hannun Usor, Najeriya 2-1 Madagascar
Kwallo ce mai kyau da Moses Uzor ya samu tun daga tsakiya ya dunga ja zuwa gefe daga nan ya ratsa har cikin akwatin Madagascar a tsakanin masu tsaron baya biyu ya buga kwallon da karfi ta kuma fada raga.
Wasansa na farko kenan a Super Eagles, wanda ya shiga karawar daga baya, haka wanda ya farke kwallon Najeriya, Ilenikhena shima a yau ya fara buga mata wasan.
, Najeriya 1-1 Madagascar
Ga jerin Alkana da suke budsa wasan:
Rafli:Alhadi Allaou MahamatAssistant Mataimaka na daya:Ali DaoudAssistant Mataimaki na biyu:Moussa Hafiz Mai jiran ko ta kwana:Abdelkerim Ousmane
, Najeriya 1-1 Madagascar
Super Eagles ta yi canji ta fitar da Adams ta maye gurbinsa da Moses Usor.
, Najeriya 1-1 Madagascar
An bai wa Ademola Lookman katin gargadi, saboda keta da ya yi.
Har yanzu wasan yana 1-1, kuma Madagascar ce ta fara cin kwallo daga baya Super Eagles ta farke.
, Najeriya 1-1 Madagascar
Kadan ya rage Najeriya ta kara kwallo na biyu, bayan wata kwana da aka buga, inda Chukwueze ya so ya zura a raga, amma babu wata matsala.
, Najeriya 1-1 Madagascar
Nan da nan itama Najeriya ta samu dama ta hannun Adams, wanda ya kamata ya kwantar da hankalinsa, amma sai ya buga kwallon ta tashi sama sosai.
, Najeriya 1-1 Madagascar
Kadan ya rage a karawa Najeriya kwallo ta biyu ta hannunn, Raveloson amma sai ya ta jan kwallon har gaban Nwabali, wanda ya sa hannu ya taba ta, sannan ta zama ta shi.
, Najeriya 1-1 Madagascar
Bayan wannan karawar Super Eales za ta je Guine-Bissau, domin buga wasa na biyu a cikin rukuni a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2027 a Kenya da Uganda da kuma Tanzaniya.
Tawaga daya ce za ta kai Afcon kai tsaye a wannan rukunin, bayan da Tanzaniya take daga cikin masu masaukin baki.
An koma zagaye na biyu, Najeriya 1-1 Madagascar
Yadda aka gara wasan, Najeriya 1-1 Madagascar