Shugaban Najeriya,
Bola Tinubu ya sanar da rage yawan tawagar wakilan ƙasar da za su
halarci taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79, da za a gudanar a birnin
New York na Amurka cikin watan Satumba mai zuwa.
Shugaban ma’aikatar
fadar shugaban kasar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan ranar Asabar, lokacin wani taron bita da fadar
shugaban ƙasar ta shirya wa shugabannin hukumomin gwamnati da ke ƙarƙashin kulawar
fadar, kamar yadda kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya bayyana cikin sanarwa da ya fitar.
Gbajabiamila ya ce Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin
ne domin rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa a lokacin tafiye-tafiyen jami’an
gwamnatin.
Da yake ƙarin haske kan ƙudurin, ya ce fadar shugaban
ƙasar da hukumomin da ke ƙarƙashin kulawarta, na gudanar da
ayyukansu bisa tsarin doka da ƙa’ida, da kuma bin umarnin shugaban ƙasar,
Gbajabiamila ya ce shugaban ya ɗauki matakin ne da nufin tabbatar da
ingantaccen tsari wajen gudanar da gwamnatinsa
”Na tattauna da shugaban ƙasa kan wannan, kuma ya sanar da ni cewa za mu ga haka cikin makonni masu
zuwa lokacin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin
New York’’.
Mista Gbajabiamila ya ƙara da cewa a lokacin
zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a ƙasar, an yi maganar rage yawan kuɗin
da gwamnati ke kashewa, don haka ya ce yanzu kowa na jiran ganin yawan
tawagar da Najeriya za ta je da ita taron na Majalisar Dinkin Duniya.
”A baya mun sani cewa, wasu na amfani da
taron wajen tafiya harkokinsu na ƙashin kai, don haka ne shugaban ƙasa ya
bayar da umarnin cewa, a wannan karon duk wanda ba shi da abin yi a taron, to
kada ya kuskura ya shigar tawagarmu zuwa Amurka, wannan shi ne umarnin Shugaban
ƙasa’’, in shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar.