Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarai daga duniyar wasanni na 26/06/2024

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 26 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. An fara wasan Rukunin E

    Slovakia 0-0 Romania

    Ukraine 0-0 Belgium

  2. Rukunin E na cike da ruɗani, Slovakia (5:00) Romania ~ Ukraine (5:00) Belgium

    Rukunin E na gasar kofin ƙasashen Turai cike yake da ruɗani, da zaƙuwa, da fata, da kuma fargaba.

    Rukunin ya ƙunshi: Romania, Belgium, Slovakia, Ukraine.

    Kowacce a cikinsu na da maki uku cikin wasa biyu. Yayin da Romania ke saman teburi, Ukraine ce a ƙasa kamar yadda teburin ke nunawa a hoton ƙasa.

    Nan da ƙarfe 5:00 agogon Najeriya da Nijar za su fara fafatawa a tsakaninsu.

    Slovakia (5:00) Romania

    Ukraine (5:00) Belgium

  3. Labarai da dumi-dumi, Foden ya bar sansanin Ingila 'saboda matsala a gidansu', England

    Ɗan wasan tsakiyar Ingila Phil Foden ya bar sansanin tawagar ƙasar da ke buga Euro 2024 "na ɗan lokaci" kuma ya koma Ingila.

    Cikin wata sanarwa, hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila, Football Association (FA) ta ce ɗan wasan na Manchester City ya tafi gida ne "saboda wata matsala da ta shafi iyalinsa".

    Foden wanda ya buga wa ƙasarsa wasa 37, ya buga duka wasa uku da Ingila ta yi a gasar Euro da ke gudana a Jamus.

    A jiya Talata ne tawagar ta Three Lions ta ƙare wasannin cikin Rukunin C a matsayin jagora da maki biyar, bayan ta ci wasa ɗaya ta yi canjaras biyu.

    Zuwa yanzu ba a bayyana tawagar da Ingila za ta kara da ita ba a zagayen 'yan 16, wanda za a yi ranar Lahadi.

  4. Magoya bayan Ingila sun yi wa 'yan wasansu ihu

    Martanin da wasu magoya bayan Ingila suka mayar kan rawar da tawagarsu ke takawa a gasar Euro 2024 na jawo "yanayi na musamman" da ke "taɓa 'yan wasan", in ji koci Gareth Southgate.

    Tawagar ta kammala wasannin rukuni a saman teburin Rukunin C ranar Talata duk da 0-0 da suka buga da Slovenia. Kafin haka sun buga 1-1 da Denmark.

    Magoya baya sun yi wa 'yan wasan ihu kuma aka dinga jefa wa kociya Southgate fankon kofuna bayan tashi daga wasan na Slovenia.

    "Ba zan kawar da kai daga wannan ba," a cewarsa. "Abu mafi muhimmanci shi ne magoya baya su ci gaba da mara mana baya."

    Southgate ya ce ya fahimci dalilin da ya sa magoya bayan ke nuna ɓacin rai da sakamakon wasannin, wanda ya ƙunshi 1-0 da suka ci Serbia.

    Magoya baya sun yi wa 'yan wasan ihu bayan hura hutun rabin lokaci, sannan shi ma Southgate ya sake fuskantar tsiya lokacin da ya je gode wa magoya baya bayan tashi daga wasan.

    "Na fahimci abin da suke nufi da ni kuma hakan zai fi amfani gare ni sama da 'yan wasan," in ji shi.

    "Amma hakan na ta'azzara yanayin da ake ciki. Ban taɓa ganin tawagar da ta tsallake ba kuma ake yi mata irin wannan abin. Na fahimta kuma ba zan kawar da kai ba, amma dai ina alfahari da 'yan wasan a yanzu."

  5. Argentina ta tsallaka zagaye na biyu a Copa America

    Argentina ta zama ƙasa ta farko da ta samu gurbin buga zagaye na biyu a gasar Copa America ta 2024 da ke gudana a Amurka.

    Tawagar ta samu nasarar kaiwa zagayen kwata fayinal ne sakamakon doke Chile 0-1 a wasan da suka buga da tsakar daren da ya gabata, bayan Lautaro Martinez ya ci ƙwallo a mintunan ƙarshe.

    Argentina mai riƙe da kofin ta mamaye baki ɗayan wasan da aka buga a filin wasa na MetLife Stdaium da ke birnin New Jersey, inda ta buga shot har 22.

    Ɗan wasan gaba na Manchester City Julian Alvarez, da na tsakiyar Fiorentina Nicolas Gonzalez ne suka fara kai wa golan Chile Claudio Bravo hari tun da farkon wasan.

  6. Dalilin da ya sa Denmark ta ƙare a mataki na biyu a Rukunin C, Euro 2024

    Tawagar Denmark ta samu matsayi na biyu a Rukunin C na gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 ne saboda ta zarce Slovenia ɗa'a bayan sun tashi 0-0 da Serbia.

    Ɓangarorin biyu ba su yi wani ƙoƙari ba a wasan na daren jiya, amma kuma Denmark ce ta wuce gaba a wasan da suka buga a birnin Munich.

    An bai wa duka ɓangarorin katin gargaɗi shida-shida tare da bai wa kocin Slovenia Novakovic Milivoje katin gargaɗi a wasansu na farko - duk da Uefa ba ta ƙirga da shi ba - kuma shi ne abin da ya bai wa Denmark damar ɗara Slovenian.

    Duk da cewa duka Denmark da Slovenia sun wuce, an fitar da Serbia - duk da cewa babu wadda gta ci wasa a rukunin.

  7. Barka

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye tare da Umar Mikail.

    Ku biyo mu domin sanin yadda take kasancewa a duniyar wasanni.