Ƙungiyar ƙasashen Sahel ta bikin ɗaga tutar AES
Shugaban majalisar mulkin sojin Nijar da takwarorinsa na Burkina Faso da Mali sun jagoranci bikin ɗaga tutar ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES) a hukumance a fadarsu.
An ɗaga tutar ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel ɗin a hukumance a wannan Litinin, kwanaki kaɗan bayan amincewa da ita.
Tutar na ƙunshe da ƙudurin baiɗaya na al'ummar ƙasashen uku wajen tabbatar da ƴancin kai da zaman lafiya da kuma ci gaban yankin.
Ƙaddamar da wannan tuta alama ce mai kyau ga ƙasashen na AES, wanda ke nuna sabon zamani na haɗin gwiwa da juriya ga mutanen Sahel.
Shuwagabannin ƙasashen na AES Abdourahamane Tchiani da Ibrahim Traoré da Assimi Goïta, sun yi na'am ga wannan sabuwar alamar da suka kira ta "haɗin-kai.
An gudanar da bukukuwan lokaci guda a Bamako da Ouagadougou da kuma Yamai, lamarin da ke nuna wani muhimmin mataki na tabbatar da wani gagarumin aiki: na tabbatar da wata ƙungiyar da za ta iya tinkarar kalubalen tsaro, tattalin arziki da kuma zamantakewa a yankin.
Shuwagabannin ƙasashen uku sun saka hannu kan kafa "Kungiyar Ƙasashen Sahel" a ranar 6 ga Yuli, 2024, a ƙarshen taron ƙoli na farko na ƙawancen ƙasashen yammacin Afirka (AES).
Ƙasashen sun ɗauki wannan mataki ne bayan lalacewar dangantaka da ƙungiyar Ecowas, wadda ƙasashen uku suka fice daga cikinta a watan Janairun 2025, inda suka zargi Faransa - tsohuwar uwargijiyarsu da amfani da ƙungiyar.