Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni game da jana’izar Khamenei da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/07/2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello

  1. Bowen: Trump ba shi da wani zaɓi da ya wuce tattaunawa da Iran

    Sabbin kalaman Donald Trump game da Iran da yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu ta hanyar tattaunawa ya kamata a ɗauke su da muhimmanci, domin shi ne shugaban ƙasar Amurka.

    Ga abin da ya faɗa a taron ƙasashen Nato da aka gudanar a Turkiyya:

    "Ba na son mu ci gaba da mu'amala da su. Su miyagu ne. Kun san abin da ake nufi da miyagu? Miyagu ne. Mutane ne marasa hankali. Mutane marasa hankali ne ke jagorantarsu. Kuma mutane ne masu mugunta da tashin hankali.

  2. An aikata laifukan cin zarafin bil’adama a Darfur - ICC

    Mataimakiyar mai gabatar da ƙara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ce kotun ta samu ‘ƙwararan hujjoji’ da suka nuna an aikata laifukan cin zarafin bil’adama a yankin Darfur yayin yaƙin basasar Sudan.

    A hirarta ta farko tun bayan da ICC ta ƙaddamar da binciken, Nazhat Shameem Khan ta ce dakarun (RSF) sun aikata munanan laifuka a biranen El-Geneina da El Fasher.

    Ta ce mun samu ƙwararan hujjoji da ke nuna alaƙa tsakanin abubuwan da ke faruwa a fili da wasu jagorori,

    Ana zargin dakarun RSF da kashe dubban fararen hula tun bayan barkewar fada tsakaninsu da sojojin kasar a shekarar 2023.

    Sai dai ƙungiyar RSF ta musanta zargin.

  3. Brazil za ta mayar da ɗan Rasha da take zargi da leƙen asiri

    Gwamnatin Brazil ta yanke shawarar mayar da wani mutum da ake zargi ɗan leƙen asirin Rasha ne zuwa gida Rasha bayan ya kammala zaman hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari.

    Rahotanni sun ce Sergey Vladimirovich Cherkasov ya yi amfani da fasfo na bogi na kasar Brazil da kuma sunan ƙarya a wani yunƙuri na kutsawa cikin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) da ke birnin Hague na kasar Netherlands.

    Wakiliyar BBC ta ce an kama shi ne a Netherlands bayan ya isa ƙasar domin fara wani shirin samun horo a kotun ta ICC.

    Ana zarginsa da ƙoƙarin tattara bayanai kan shari'o'in laifukan yaƙi domin ya aikawa Moscow

  4. Dole mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin yaƙi da matsalar tsaro a arewa - Sarkin Musulmi

    Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar II ya ce akwai buƙatar jihohin arewacin Najeriya da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin yaƙi da matsalolin tsaron da ke addabarsu.

    Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wajen taron gwamnoni da sarakunan yankin a jihar Kaduna, inda ya ambaci garkuwa da mutane da ƴanbindiga da Boko Haram a matsayin matsalolin da suka yi wa yanki dabaibayi.

    “Kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar da tsaro. Dole ne mu haɗa kai domin yaƙi da wannan matsalar ta tsaro musamman ta ta'addanci, garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro."

    A game da kafa kwamitin amintattu kan tsaron yankin a matsayin wani mataki na musamman domin nemo mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.

    Ya ce kwamitin, wanda ya ƙunshi fitattun mutane daga jihohin Arewa 19, zai zo da sabbin dabaru da hanyoyin aiki wajen magance rashin tsaro.

  5. Waɗanda suka kamu da cutar Ebola a DR Congo sun haura 1700 tare da kashe aƙalla mutum 600

    Yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya karu zuwa dubu daya da dari bakwai da hamsin da tara.

    Ya zuwa yanzu, mutum 600 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar ta yanzu.

    Haka kuma an tabbatar da samun mutum biyu da suka kamu da cutar a wani lardi, lamarin da ke nuna cewa cutar na ci gaba da bazuwa lardin Tshopo da ke yammacin kasar.

    A baya dai cutar ta fi kamari a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

  6. Yau za a yi jana'izar yatollah Ali Khamenei a Hubbaren Imam Reza na birnin Mashhad

    A yau Alhamis ne za a binne gawar Ayatollah Ali Khamenei a makeken Hubbaren Imam Reza na birnin Mashhad, mahaifar marigayin. An kwashe kimanin kwana shida ana tarurrukan addu'o'i da kuma bankwana da gawar a biranen Iran da Iraƙi.

  7. Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare a wurare 90 a Iran

    Sojojin Amurka sun ce sun kammala hare-harensu na baya baya nan a kasar Iran wanda suka kai da jiragen sama , inda suka ce sun kai farmaki a wurare casain, kuma wasu daga cikinsu na kusa da mashigin Hormuz.

    Wakilin BBC ya ce kafar talibijin ta gwamnatin Iran ta ce an kai hari a tsi-birin Abu Musa da ake takadama akai wanda kuma ke kusa da Mashigin hormuz

    An kuma ji karar fashewar abubuwa a yankunan da ke bakin teku ciki harda Bandar Abbas da Cha-ba-har

    Haka kuma an samu katsewar wutar lantarki a wasu yankuna, ciki har da arewacin ƙasar, inda aka lalata wata gadar layin dogo.

    A dayan banagren Iran ta maida martani inda ta ce,dakarunta sun kai hare-hare a sansanonin Amurka da ke wasu ƙasashe makwabta.

  8. Ɓudewa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai kan jana'izar Ali Khamenei da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.