Rufewa
Masu bibiyarmu nan za mu rufe shafin namu a yau.
Kuna iya dubawa ƙasa domin karanta rahotonnin da muka kawo muku a wunin na yau.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwana da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/09/2025
Daga Aisha Babangida da Habiba Adamu
Masu bibiyarmu nan za mu rufe shafin namu a yau.
Kuna iya dubawa ƙasa domin karanta rahotonnin da muka kawo muku a wunin na yau.
Mu kwana lafiya.
Masana'atar shirya fina-finan Amurka ta Hollywood na jimamin rasuwar Robert Redford.
Jarumin kuma mai shirya fina-finai da ya lashe lambar yabo ta Oscar ya mutu ne a gidansa da ke Sundance a Utah yana da shekara 89.
A saƙonta, Meryl Streep ta ce giwa ta faɗi. Ita kuwa Jane Fonda a cikin wata sanarwa da ta fitar mai sosa zuciya, ta ce labarin mutawar Redford ya kaɗa ta sosai.
Mai shirya Fina-finai, Ron Howard, ya kira shi da mutum mai matuƙar tasiri.
Redford ya fito a fina-finai kamar ''All the Presidents men'', da fim ɗin ''The way we were'', da sauransu.
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yaƙin Gaza, abu ne da ba za a lamunta ba bisa doron sanin ya kamata da na siyasa.
Antonio Guterres na jawabi ne ga manema labarai yayin da dakarun sojin Isra’ila suka ƙaddamar da wani gagarumin farmaki ta ƙasa a birnin Gaza kan abin da suka kira babban tambarin ikon Hamas.
An ga ga tankoki yaƙi suna kusantar tsakiyar birnin Gaza.
Falasɗinawa na ta ƙoƙarin barin birnin cikin motocin da ke maƙare da mutane da kayayyakinsu, wasu kuma a kafa.
Gagarumin farmakin da Isra'ilar ta ƙaddamar ya zo dai dai lokacin da wani binciken Majalisar Dinkin duniya ya tabbatar da cewa Isra'ilar ta aikata kisan ƙare dangi a Gaza.
Sai dai Isra'ila ta yi watsi da rahoton.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe aƙalla mayaƙan ISWAP 11 a farmakin da ta kai jihohin Borno da Adamawa.
Cikin wata sanarwa da rundunar haɗin gwiwa da ke yaƙi da mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta fitar a yau Talata ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan na ISWAP a wani artabu a hanyar Baga da ke jihar Borno da kuma yankin Magagali a jihar Adamawa.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a jiya Litinin bayan da mayaƙan Iswap suka yi wa dakarun sojin kwanton ɓauna a kusa da Garin Giwa a ƙaramar hukumar Kukawa, inda suka dasa bom tare da buɗe wuta.
Amma sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar murƙushe harin tare da kashe mayaƙan ISWAP takwas ciki har da kwamandojojin ƙungiyar biyu, kuma sojojin sun yi nasarar kwato makamai da Babura a cewar sanarwar.
Haka kuma rundunar sojin ta Najeriya ta ce dakarunta tare da taimakon mafarauta da yan sakai sun kashe wasu ƙarin mayaƙan uku tare da karɓe makamansu a jihar Adamawa.
Sai dai sanarwar rundunar haɗin gwiwar ba ta bayyana ko an kashe sojojin ba a artabun. Najeriya ta daɗe tana fama da matsalar Boko Haram a arewa maso gabashi da kuma ISWAP da ta ɓalle daga ƙungiyar.
Al'ummar Malawi na dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa bayan kammala kaɗa ƙuri'unsu.
Dubban mutane ne suka yi dogayen layuka a wajen rumfunan zaɓen, inda ake ƙirga sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da na ƴanmajalisar dokoki da ƙananan hukumomi.
Mutanen sun zaƙu domin samun sauyi a ƙasar da ke fama da matsalolin tattalin arziki.
A yaƙin neman zaɓensa na wa'adi na biyu, shugaban ƙasar, Lazarus Chakwera ya alkawarta saita tattalin arzikin ƙasar, kamar yadda babban abokin hamayyarsa Peter Mutharika.
Idan ba a samu ɗan takarar da ya lashe fiye rabin ƙuri'un da aka kaɗa ba, manyan ƴantakarar biyu za su tafi zagaye na biyu.
Jami'an hukumar hana fasa ƙaurin jama'a ta Najeriya ta kuɓutar da wasu ƙananna yara takwas da ake zargin an sace su daga wani gidan marayu a Kano da wasu jihohin arewacin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a a hukumar, Vincent Adekoye ya fitar ranar Talata ya ce an yi safarar yaran ne zuwa yankunan kudu maso kudanci, da kudu maso gabashin ƙasar amma aka kuɓutar da su a jihar Delta.
“Bayan samamen da muka kai gidan marayun Delta, mun gano cewa akwai ƙananan yara fiye da 70 a cikin gidan marayu, ciki har da jarirai 15, daga nan muka gano cewa takwas daga ciki akwai zargin cewa daga Kano aka kawosu, daga nan muka kuɓutar da su,'' in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce tuni aka mayar da yaran da aka gano zuwa Kano, inda tuni aka gano su tare da sada su da danginsu.
Batun satar ƙananan yara musamman a Arewacin Najeriya, wata matsala ce da take ci gaba da addabar ƙasar, inda a wasu lokuta ake sayar da su.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta shigar da ƙarar Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar, kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore kan wasu zarge-zarge biyar.
Hukumar ta kuma lissafo shafukan X da na Meta a matsayin waɗanda take ƙara.
Daraktan shigar da ƙara na ma'aikatar shari'ar ƙasar, Mai shari'a, Muhammad Abubakar, da wasu lauyoyin DSS ne suka shigar da ƙarar a madadin hukumar DSS da gwamnatin Najeriya.
A ranar 8 ga watan Satumba ne aka bai wa Sowore wa'adin mako guda ya goge wani saƙo da hukumar ta bayyana da ''ƙarya, marar tushe da nufin haddasa rigima' a shafinsa na sada zumunta kan shugaba Tinubu.
A ranar Litinin ne wa'adin ya cika ba tare da Sowore ya goge saƙon ba.
Haka ma shafukan X da Meta an saka su a ƙarar ne saboda sun ƙi bin umarnin hukumar DSS na goge shafukan Sowore.
Aƙalla mutum guda ya rasa ransa sannan wasu tara kuma sun samu rauni a birnin Zaporizhzhia da ke kudu-maso gabashin Ukraine, bayan wasu sabbain hare hare ta sama da Rasha ta kai da daddare.
A yankin Mykolaiv, rahotanni sun ce wani manomi ya rasa ransa bayan sakamakon harin da Rasha ta kai ya fada kan motar taraktar da ya ke tukawa.
Shugaban Argentina, Javier Milei ya bayyana cewa tura ta kai bango a yayin da ya ke sanar da batun sabon kasafin kuɗin ƙasar.
Ya ce ya ƙara kuɗin da za a kashe a ɓangaren fansho da ilimi da kuma lafiya.
Gwamnatin Milei da ke tsuke bakin aljihu ta rage yawan hahhawar farashin kayan da ake samu tun bayan da shugaban kasar ya hau mulki a 2023.
Haka kuma jam'iyyarsa na rasa rinjaye a watannin baya bayannan inda ta samu koma baya sosai a lokacin da aka yi zaben kananan hukumomi a lardin Buenos Aires
Yajin aikin sai baba-ta-gani da ƙungiyar likitocin masu neman ƙwarewa reshen Abuja, babban birnin Najeriya ta fara tasiri a wasu asibitocin birnin.
Yajin aikin wanda ya shiga rana ta biyu, a ranar Talata ya gurgunta ayyuka a wasu daga cikin asibitocin da kuma cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a birnin.
Wannan ya biyo bayan cikar wa’adin yajin aikin gargadi na mako guda da ‘kungiyar ta ARD ta gindaya wa gwamnatin a kan ta biya musu buƙatunsu.
BBC ta ga marasa lafiya a asibitin Maitama da ke cikin wani hali sakamakon rashin likitoci a asibitin.
Sai dai lamarin yajin aikin ya sha bambam a asibitin Garki, Inda marasa lafiya da dama suka je asibitin, kuma likitoci ke ci gaba da kulawa da su.
Jami'ar hulda da jama'a ta asibitin, Uche Francis ta ce tun kafin a baiwa likita takardar samun aiki za a gargaɗe su ba yajin aiki, shi ne dalilin da yasa basa shiga yajin aiki.
Matsalolin da ƙungiyar ta koka a kansu sun haɗa da rashin kula da walwalar ma’aikata da biyan albashi da yadda ake yanke musu kuɗi ba tare da bayani ba da kuma ƙarancin ma’aikata.
Sauran dalilan sun haɗa da yin aiki fiye da kima, da rashin ɗaukar sabbin ma’aikata a asibitocin babban birnin tun daga shekarar 2011.
Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani kan fargarwar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ya yi na cewa za a iya samu juyin-juya-hali, sakamakon matsananciyar yunwa da matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.
Fadar ta yi watsi da kalaman a matsayin tsohon tunani da aka riga aka wuce.
Inda ta bayana kalaman tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin na siyasa ne tsagwaran sa.
Gwamnatin ta kuma jaddada cewa matakan da gwamantin ke ɗauka tuni suka fara ɗora ƙasar kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki a ƙasar.
Alhaji Atiku Abubakar ya zargi gwamantin Bola Ahmed Tinubu da samar da manufofi da ke ƙara ta’azzara hauhawar farashi, da rashin aikin yi, da ƙarancin abinci a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar ƙawancen tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika, ECOWAS, kuma shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, na wata ziyarar aiki a ƙasar Burkina Faso a ranar Talata.
Shugaba Bio na yunƙurin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙungiyar ƙawance ƙasashen Sahel (AES) da ƙungiyar ta ECOWAS.
Ƙasashen na Sahel waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji, Burkina Faso da Mali da kuma Nijar sun ɓalle ne daga ECOWAS sannan suka kafa tasu ƙungiyar.
Manufar ziyarar shugaban ECOWAS ɗin shi ne, ƙarfafa dangantakar tsaro a yankin domin yaƙi da mayaƙa masu ikirarin jihadi da ke barazana ga yankin na Sahel.
Ƙasar Ghana ta sanar da tsaurara bayar da biza ga ƴan ƙasar Sin, a wani ɓangare na magance matsalar haƙar ma'adanai da ake yi a ƙsarta ba bisa ƙa'ida ba.
Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa ya bayyana cewa ofisoshin jakadancinsu da ke Beijing da kuma Guangzhou ba za su ƙara ƙarɓar takardun neman biza ba daga ƴan ƙasar ta China da suka haura mutum guda.
Haka kuma ya zama dole ɗaiɗaikun ƴan ƙasar ta Sin da ke neman biza, su halarci ganawa domin yi musu tambayoyi.
Zuwa amsa tambayoyin ya shafi duka masu neman izinin zuwa Ghana daga China bisa kowane irin dalili ne na ziyarar.
Matakin baya rasa nasaba da lalata muhalli da hanyoyin ruwa da ayyukan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba ke yi a ƙasar ta Ghana.
Wata kotu a ƙasar Zambia ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin ɗaurin shekara biyu a kurkuku, bisa yunƙurin kashe shugaba Hakainde Hichilema ta hanyar asiri.
An samu Leonard Phiri ɗan ƙasar Zambia da kuma Jasten Mabulesse Candunde ɗan ƙasar Mozambique da laifi ne ƙarƙashin dokar da ta haramta asiri, bayan an kama su a watan Disamba da wasu abubuwan suddabaru, ciki har da hawainiya mai rai.
A lokacin yanke hukuncin, mai shari'a Fine Mayambu ya ce waɗanda aka samu da laifin ba kawai maƙiyan shugaban ƙasar ba ne, maƙiya ne kuma na al'ummar ƙasar.
Shari'ar dai ta ja hankali a ƙasar, kasancewar ita ce irin ta ta farko da aka taɓa samun wani da laifin yunƙurin amfani da asiri a kan shugaban ƙasar.
Kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin ma'aikatan jami'o'i a Najeriya (SSANU) da NASU ya baiwa gwamnatin ƙasar wa'adin mako guda kafin su tsunduma yajin aiki.
A wata wasiƙar da suka aike wa ministan ƙwadago da samar da ayyukanyi, Muhammad Dingyaɗi, ƙungiyoyin su ne idan gwamnati baya warware matsalolin da ke damunsu ba, za su tafi yajin aiki a ƙarshen wa'adin.
Ƙorafe-ƙorafen ƙungiyoyin sun haɗa da rashin biyansu kuɗaɗen alawus da ya kai naira biliyan 50 da wasu albashin da aka riƙe musu, rashin biyansu cikon ƙarin albashin da aka yi lokacin da aka yi ƙarin kashi 25/35 da rashin cika yarjejeniyar da gwamnati ta cimma da su a shekarar 2009.
A cewar kamfanin dillacin Najeriya,(NAN) wa'adin da ƙungiyoyin suka bayar ya fara aiki ne daga ranar litinin, 15 ga watan Satumba, 2025.
Hukumar ƙididdiga ta Naajeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki ya faɗo karo na biyar a jere a ƙasar, a watan Agusta 2025, lamarin da ya kawo sauƙi ga mutanen ƙasar.
Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, farashi ya sauko daga 21.88 a watan Yuli zuwa 20.12 a watan Agustan 2025.
Abin da ke nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 cikin ɗari daga watan na Yuli zuwa Agusta. Hakan kuma na nufin farashin ya rikito idan aka kwatanta da 32.15 ciki ɗari da aka samu a watan Agustan 2024.
Sai dai alƙaluman ba su yi wani tasiri na azo-a-gani ba a yankunan karkara, inda kuɗin mota da rarraba kayayyaki ke ci gaba da janyo tsadar kayayyaki fiye da a birane.
Sai dai abinci, wanda shi ne ja gaba wurin kayayyakin da farashinsu ke ƙaruwa ya dawo matsakaici a watan na Agusta a ƙasar, ko da yake yana kan gaba.
Al'ummar ƙasar Malawi na jefa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴanmajalisar dokoki, bayan shekara biyar da ƙasar ta yi tana fuskantar matsalar tattalin arziki.
Shugaba Lazarus Chakwera na neman wa'adi na biyu, yayin da Peter Mutharika ya zama babban abokin hamayyarsa, mutumin da ya ke da shakaru 80 da ɗoriya, wanda kuma ya taɓa riƙe muƙamin gwamnati a baya.
A birane da dama na ƙasar matsalolin ƙarancin man fetur da tsadar rayuwa ne suka kankane yaƙin neman zaben.
Matsalar man fetur ɗin dai ta janyo dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.
Za a tafi zagaye na biyu, idan a cikinsu babu wanda ya samu kashi 50 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa, a zaɓen na ranar Talata.
Kwamitin bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙasar Isra'ila ta aikata kisan ƙare dangi a kan Palasɗinawa a Gaza.
Sabon rahoton ya ce an samu isassun hujjojin da ke nuna cewa, an aikata huɗu a cikin abubuwa biyar na ayyukan kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa, tun fara yaƙi a kan Hamas a shekarar 2023.
Abubuwa huɗun su ne: kashe wasu rukunin mutane, jikkatasu matuƙa tare da janyo musu matsalar da ta shafi lafiyar ƙwaƙwalwa, aikata abubuwa da gangan don ɗaiɗaita su da kuma hana su haihuwa.
Rahoton ya ba da misalai da kalaman shugabannin Isra'ila da yadda suke tafiyar da dakarun tsaron ƙasar, a matsayin hujjar da ke nuni da aniyar aikata kisan ƙare dangi.
Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Isra'ilar ta yi fatali da rahoton, tana mai bayyana shi a matsayin "mara tushe balle makama."
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta ɗauki matakin tallafawa ƴanbindigar da suka tuba ne domin ganin ta kawar da rashin ilimi da rashin aikinyi a tsakaninsu.
Hakan a cewarta na daga cikin dalilin da yasa suka shiga ayyukan da suka haifar da matsalar tsaro a jihar.
Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Matazu, ya ce ƴanbindigan da suka tuban sun nemi gwamnati ta gina musu makarantu waɗanda ƴaƴansu za su dinga zuwa da asibitoci da kuma wuraren da shanunsu za su dinga shan ruwa.
Matakin a cewarsu zai taimaka wurin ganin cewa ƴanbindigar da suka tuba basu koma ruwa ba.
Sai dai masana a harkar tsaro na ganin akwai buƙatar tallafawa al'ummar da matsalar ta shafa irin wannan tallafin.
Haka kuma bai kamata a yiwa ƴanbindigar kuɗin goro ba saboda a cikinsu akwai waɗanda suka mayar da sata sana'a, amma akwai kuma waɗanda aka sacewa shanu.
A cewar Dokta Kabiru Adamu rarrabewar wurin tallafawa ƴnbindigar da suka tuba zai sa ba za a ƙarawa mai aikata laifi ƙwarin guiwar ci gaba da yi ba.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan sulhun da wasu al’ummomin jihar suka yi da ƴan bindiga a jihar.
Sai dai sulhun bai hana ƴan bindigar kai hare-hare, a sauran jihohin da ke makwabtaka da Katsinan ba.
Isra'ila ta ƙara zafafa hare- harenta a birnin Gaza, sa'oi bayan firaiministanta, Benjamin Netanyahu, ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio a birnin Kudus.
Wasu rahotanni daga kafar yaɗa labaran ƙasar na cewa, sojojin Isra'ilan sun kai hare-haren ne ta sama da makaman atilari tare da buɗe wuta a birnin na Gaza.
Babu wani tabbaci a hukumance a game da rahotannin da ke cewa yanzu sojojin Isra'ilan sun ƙaddamar da farmaki ta kasa domin mamaye birnin baki daya.
Iyalan mutanen da ake tsare da su a Gaza sun taru a kofar gidan firaiministan cikin dare, inda suka ce lugudan wutar da sojojin ke yi a yanzu na iya sanya rayuwar 'yan uwansu da ke tsare cikin haɗari.
Rubio zai ƙarasa Qatar, inda Isra'ila ta kai hari kan jagororin ƙungiyar Hamas a makon da ya gabata.