Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 29/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/09/2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonnin kenan

    Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Lahadi.

    Za mu kawo muku wasu labaran a wani shafin daban gobe da safe.

  2. Mun kashe shugabannin Hezbollah 20 tare da Nasrallah - Sojin Isra'ila

    Isra'ila ta ce ta kashe shugabannin Hezbollah 20 masu muƙamai daban-daban lokacin da ta kai harin da ya kashe Hassan Nasrallah a hedikwatar ƙungiyar ranar Juma'a.

    Kamar yadda muka ba da rahoto, cikinsu akwai Ali Karaki shugaban bataliyarta ta kudanci.

    Rundunar sojin Isra'ila ta kuma ce ta kashe Ibrahim Hussein Jazini, shugaban tsaron Nasrallah, da Samir Tawfiq Dib, wanda ta ce mai bai wa Nasrallah shawara ne.

  3. Hare-haren Isra'ila sun raba mutum miliyan ɗaya da gidajensu - Mikati

    Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce akwai yiwuwar hare-haren Isra'ila sun haifar da gudun hijirar da ƙasarsa "ba ta taɓa gani ba".

    A cewarsa yayin wani taron manema labarai a yau: "Adadin mutanen da aka raba da gidajensu...zai kai miliyan ɗaya."

    Mikati ya ce an samu dandazon mutane da ke barin kudancin Lebanon da yankin Bekaa a gabashi, yana mai cewa da yawa daga cikinsu ba 'ya Lebanon ba ne.

    Kalaman nasa na zuwa bayan hukumar tallafin abinci ta MDD ta ce ta ƙaddamar da aikin gaggawa na bayar da agaji ga mutum miliyan ɗaya.

  4. Labarai da dumi-dumi, An zaƙulo gawar Hassan Nasrallah daga ɓaraguzai

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton cewa an zaƙulo gawar shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah daga wurin harin da ya yi ajalinsa a kudancin birnin Beirut na Lebanon.

    Wasu majiyoyi daga asibiti da kuma na tsaro sun shaida wa Reuters cewa gawar "ba ta ɗauke da wani rauni".

    A jiya Asabar ne Hezbollah ta tabbatar da mutuwarsa bayan harin da aka kai da tsakar dare a ranar Juma'a.

  5. Hanya uku da za mu rage ɓarnar abinci a gidajenmu

    Ƙiyasi nya nuna cewa ana yin asarar kashi 40 cikin 100 na abincin da ake samarwa a duniya.

    Albarkacin Ranar Wayar da Kai kan Ɓarna da Asarar Abinci ta Duniya, mun zaƙulo muku waɗansu hanyoyi na rage ɓarnar abinci a gidaje da kantunanmu.

    Ana tunawa da ranar ne duk 29 ga watan Satumban kowace shekara.

  6. Dakarun MNJTF sun daƙile harin Boko Haram a jihar Borno

    Dakarun rundunar ƙawance ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) sun yi nasarar daƙile wani hari da Boko Haram ta yi aniyar kaiwa a jihar Borno, a cewar rundunar cikin wata sanarwa ranar Asabar.

    Kakakin rundunar, Laftana Kanal Olaniyi Osoba, ya ce bayanan sirri sun nuna mata cewa mayaƙan ƙungiyar na shirin kai harin ne a yankin Magumeri zuwa Maiduguri.

    Ganin haka ne ya sa dakarun suka ƙaddamar da harin ba-zata, inda suka yi wa maharan kwanton ɓauna.

    "Wannan yunƙurin ya sa dole suka haƙura da kai harin kuma suka zubar da makamai da baburan da suke kai kafin su haddasa fitina a yankin." in ji kanar ɗin.

    Osoba ya ƙara da cewa sojojin sun karaɗe yankin bayan ɓarin wutar da suka yi kuma suka gano bindigogi ƙirar AK-47, da jakar harsasai 51, da miyagun ƙwayoyi daban-daban da 'yanbindigar suka gudu suka bari.

  7. Isra'ila ta ce ta kashe wani babban jami'in Hezbollah

    Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ce ta kashe wani babban jami'in Hezbollah a harin da ta kai Lebanon ranar Asabar.

    Wata sanarwa ta ce Nabil Qaouk, shi ne shugaban sashen tsaro kuma ɗanmajalisar ƙungiyar.

    Zuwa yanzu Hezbollah ba ta tabbatar da mutuwarsa ba tukunna.

    IDF ta ce Qaouk na da kusanci sosai da manyan jagororin Hezbollah, tana mai cewa "da hannunsa a shirya hare-haren ta'addanci kan Isra'ila da 'yan ƙasarta".

  8. Real Madrid ta ziyarci Atletico a wasan hamayyar birnin Madrid

    Real Madrid ta je gidan Atletico Madrid domin buga wasan mako na takwas a gasar La Liga da za su kara ranar Lahadi a Metropolitano.

    Shi ne wasan farko na hamayya tsakanin manyan ƙungiyoyin birnin Madrid a bana. Real tana mataki na biyu a teburin da maki 17 bayan cin karawa biyar da canjaras biyu.

    Atletico tana mataki na ukun teburi da maki 15 bayan nasara huɗu da canjaras uku cikin karawa bakwai.

    Har yanzu Barcelona ce ta ɗaya mai maki 21 a karawa takwas, wadda ta ci wasa bakwai a jere kafin Osasuna ta doke ta 4-2 ranar Asabar.

  9. Zaki ya yagalgala mai gadinsa a gidan gonar Obasanjo

    Zaki ya kashe wani mai kula da shi a gidan gonar tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    A cewar rahonnin, mai magana da yawun rundunar 'yansanda a jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce babban jami'in tsaron wurin ne ya kai musu rahoton faruwar lamarin a ranar Asabar.

    An bayyana mutumin da suna Babaji Daule mai shekara 35, wanda ɗan asalin jihar Bauchi ne.

    "Daga baya an lura cewa mai gadin ya yi sakaci wajen rashin kulle kejin da zakin yake da mukulli kafin ya matsa kusa da shi domin ciyar da shi," a cewar sanarwar.

    "Wannan sakacin ne ya sa zakin ya fito kuma ya ji masa raunika a wuya kafin ya rasu daga baya. Sai da aka harbi zakin kafin ya saki mai gadin, kuma an kai gawarsa mutuware da ke babban asibitin Ijaye," kamar yadda ta ƙara bayani.

  10. Iran ta tabbatar da kashe janar ɗinta a Lebanon

    Rundunar sojin Iran ta musamman Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta tabbatar da mutuwar Birgediya Janar Abbas Nilforoushan yayin harin da ya kashe Hassan Nasrallah, shugaban Hezbollah.

    Cikin wata sanarwa, ba a yi wata magana kan ɗaukar fansar kisan nasa ba, duk da cewa IRGC ta siffanta harin da "laifukan gwamnatin Yahudawa" a Lebanon.

    IRGC ta sha yin alƙawarin rama kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh da aka kashe a Tehran a watan Yuli, wanda aka yi imanin Isra'ila ce ta aikata.

    Sanarwar ta ce janar ɗin mai ba da shawara ne na IRGC a Lebanon.

  11. Abubuwan da aka fi muhawara kansu game da gyaran tsarin mulkin Najeriya

    Alamu na nuna cewa abubuwa uku ne suka fi jan hankali a taron bitar da aka shirya kan yi wa tsarin mulkin ƙasar na 1999 gyaran fuska a birnin Kano.

    Taron wanda takensa shi ne "tsarin tarayyar Najeriya, batutuwan da ke tasowa don yi wa tsarin mulki gyara", ya tattauna batutuwa da dama ciki har da batun ƴan sandan jihohi.

    An samu ra’ayoyi mabanbanta yayin taron wanda aka kammala a jiya Asabar.

    Sanata Ali Ndume mamba ne a kwamtin yi wa tsarin mulkin Nijeriya garambawul, kuma ya yi wa BBC karin bayani.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hirarsa da Zahradden Lawan:

  12. Iran ta nemi a gudanar da taron kwamatin tsaro na MDD kan kisan Nasrallah

    Iran ta nemi a gudanar da taron kwamatin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) cikin gaggawa sakamakon kashe shugaban ƙungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.

    Cikin wata wasiƙa da ya aike wa mambobin kwamatin 15, jakadan Iran Amir Iravani ya yi gargaɗi kan "duk wani" kan ofishin jakadancin ƙasarsa, yana mai cewa ba za su amince da hakan ba.

    "Iran ba za ta yi shakku ba wajen kare haƙƙinta ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa domin ɗaukar duk wani mataki na kare kadarori da tsaronta," in ji Iravani.

    Ya kuma nemi kwamatin ya ɗauki mataki kan Isra'ila "domin kada ta jefa yankin cikin mummunan yaƙi".

    Iran na mara wa Hezbollah baya da kuma ba ta taimakon kuɗi da makamai.

    Tun da farko Shugaban Addini na Iran Ayatpllah Ali Khamenei ya ci alwashin cewa mutuwar Nasrallah ba za ta tafi "a banza ba".

  13. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum tara 'yan gida ɗaya - Rahotonni

    Kafofin yaɗa labarai a Lebanon sun ce aƙalla mutum shida aka kashe a kudancin ƙasar sakamakon hare-haren Isra'ila.

    An kai hari na baya-bayan nan ne a yankin Bekaa, unguwar da Hezbollah ke da rinjaye sosai.

    Jaridar Larabci ta An-Nahar ta ce an jikkata wasu mutum tara a wani harin a garin Anqoun da kuma raunata wasu uku a Nabatieh.

    A wani rahoton daban, jaridar ta ce an kashe wasu mutum tara 'yan gida ɗaya 'yan asalin Syria a yankin Bekaa.

  14. Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon bayan kisan Nasrallah

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare da dama a kan wuraren kungiyar Hezbollah a kasar Lebanon cikin sa'o'i 12 da suka gabata.

    A cikin wani sako da ta wallafa a shafukan sada zumunta, rundunar IDF ta ce hare-haren sun hada da wuraren harba makamai masu linzami da ake kai wa Isra'ila hari.

    A jiya Asabar ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe mutum 33 tare da jikkata wasu kusan 200.

    Daya daga cikin hare-haren da aka kai ta sama shi ne kan wani dakin ajiyar kaya da ke kusa da filin jiragen sama na Beirut.

  15. Barka

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da ni Umar Mikail.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da maƙwabtanta a yau Lahadi.