Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 25/08/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin namu.

    Sai kuma gobe idan Alah ya kai mu, za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku abbin labarai.

    Amma kafin nan, a madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. MDD ta buƙaci hukumomin Mali su saki mai fafutikar yaƙi da rashawa a ƙasar

    Wata ƙungiyar ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci hukumomi a Mali su yi gaggawar sakin wani mai fafutikar yaƙi da rashawa wanda ke gidan yari na tsowan kusan shekara biyu.

    Ana ci gaba da riƙe Clement Mamadou Dembele duk da umurnin kotu na sakin sa watanni huɗu da suka gabata.

    A cewar ƙwararrun, lamarin na nun yadda matsalar take hakkin bil'adama musamman kan ƴan adawa, da ƴan jarida da kuma masu kare hakkin bil'adama ke ci gaba da ta'azzara.

    An zargi mista Dembele da yin barazanar kashe shugaban gwamnatin sojin Mali, sai dai Alƙalin da ya yi shari'ar ya ce babu wata shaida da ke nuna hakan.

  3. Syria ta zargi Isra'ila keta ƴancinta

    Syria ta zargi Isra'ila ta keta ƴancin ikonta tare da neman tayar da zaune-tsaye a yankin ta hanyar tura sojojinta 60 zuwa cikin wani yankinta da ke kusa kan iyaka.

    Rundunar sojin Isra'ila ta dage cewa sojojin nata na gudanar da wani samame da ta ce sun saba ne a yanzin.

    Yankin , wanda ke kusa da Dutsen Hermon da ke kan iyakar Lebanon, ya yi fice wajen safarar makaman ƙungiyar Hezbollah.

    Ce-ce-ku-cen ya taso ne bayan da Amurka ta jagoranci wata tattaunawar sulhu tsakanin ƙasashen biyu, da nufin yayyafa ruwa ga rikin da ake yi a Syria.

  4. Isra'ila ta ce ta yi nadamar kisan ƴanjarida a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta nuna nadamarta kan kisan ƴanjarida a wani hari da ta kai asibitin Nasser da ke Gaza.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana taƙaicinta kan yadda harin ya shafi mutanen da tace ba sa cikin waɗanda ta hara.

    Haka shi ma ofishin firaministan ƙasar cikin wani aƙo da wya wallafa a shafinsa na X, ya nuna nadamar kisan ƴanjaridar.

    Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira ga Isra'ila ta dakatar da hare-hare kan cibiyoyin lafiya, bayan asibitin na Nasser da ke Gaza, tare da kashe aƙalla mutum 20.

    Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce "Ba za mu daina cewa ku dakata ba''.

    An kashe ƴan jarida aƙalla biyar - ciki har da na kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Wasu daga cikin mutanen an kashe su ne a hari na biyu, yayin da ƴanjaridar suka isa wurin da aka kai harin na farko.

  5. PDP ta ware wa kudancin Najeriya kujerar ɗantakarar shugaban ƙasa a 2027

    Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta ware kujerar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ga yankin kudancin ƙasar.

    Jam'iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron majalisar zartarwarta karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Haka kuma jam'iyyar ta tabbatar da Umar Iliya Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance.

    Damagum - wanda ya shafe fiye da shekara guda a matsayin shugaban riƙo na jam'iyyar a yanzu ya zama shugaban jam'iyyar mai cikakken iko gabanin babban taron jam'iyyar na ƙasa da za a gudanar a ranakun 15 a 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na jihar Oyo.

    A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu ƴan jam'iyyar suka riƙa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan ya yi wa jam'iyyar takara a zaɓen 2027.

  6. Wasu dattawan Katsina sun buƙaci gwamnati ta sauya salon yaƙi da ƴanbindiga a jihar

    Wasu dattawan jihar Katsina da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar kula da sha’anin tsaron ta Katsina wato Katsina Security Community Initiative ta yi kira ga duka gwamnatocin jihar da tarayya su ɗauki wani sabon salo wajen tunkarar matsalar ‘yan fashi daji a jihar.

    Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a wajen wani taron da ta yi a Abuja a jiya Lahadi inda ta ce ci gaba da ƙaruwar matsalolin kashe-kashe da sace-sacen jama’a a jihar na nuna cewa matakan da ake ɗauka yanzu ba su aiki.

    Dr. Bashir Kurfi shi ne shugaban ƙungiyar, inda ya bayyana wa BBC Hausa cewa ƴanbindiga suna da ƙarfi a wasu ƙananan hukumomin jihar, wanda hakan ya sa suke so a sabunta salo, tare da nemo wasu sababbin hanyoyin na yaƙi da matsalar tsaro.

  7. Mahaukaciyar guguwa ta yi ɓarna a Vietnam

    Wata guguwa mai ƙarfin gaske haɗe da ruwan sama na ɗaiɗaita yankunan da ke gaɓar teku a Vietnam.

    Guguwar mai suna Kajiki ta isa birnin Ha Tinh tare da iska mai ƙarfi da kuma mamakon ruwa waɗanda ke ta karya bishiyoyi da karafunan igiyoyin wutar lantarki, da kuma ɗaga rumfunan gidaje.

    An tilastawa dubun dubatar mutane barin gidajen su tare da taimakon jirage masu saukar ungulu.

    Wakiliyar BBC ta ce an yi gargaɗin cewa za a sami ambaliya a ƙananan koguna da kuma zaftarewar ƙasa a larduna 6 da ke Vietnam.

    Masu hasashen yanayi sun ce duk da dai ƙarfin iskar ya ɗan ragu, guguwar na ci gaba da tafiya cikin sauri kuma ta na da matuƙar haɗari.

  8. Tinubu ya gana da Shugaban Brazil Lula

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Brazil, Luiz Inacio Lula da Sailva a birnin Brasilia bayan shugaban na Najeriya ya isa ƙasar.

    Shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka ce zai amfani ƙasashen biyu.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da Brazil, inda ya ce a watan Maris na 2025, ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeninyar inganta noma da kasuwanci da tsaro da makamashi da ilimi da ma'adinai.

  9. An kama mutum uku da zargin fataucin miyagun ƙwaya a Nijar

    A jamahuriyar Nijar jami’an tsaro na ƴansanda na ofishin yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (OCRITIS) reshen Konni a JIhar Tahoua sun yi nasarar kama wasu gungun mutum 3 da ake zargi masu fataucin miyagun ƙwayoyi.

    Tuni aka gabatar da mutum 3 da ake zargi cikin wannan aiki tare da wasu ƙwayoyi da dama da suka haɗa da sama da kilogiran 30 na tabar wiwi.

    Wannan matsala ta fataucin miyagun kwayoyi ta zama ruwan dare a kasar ta Nijar dake zaman hanyar masu safarar mayigun ƙwayoyi da ke kwarara zuwa Turai ta hanyoyin da suka ratsa sahara.

  10. Rasha da Isra'ila sun fi ƙarfin Majalisar Ɗinkin Duniya - HURIWA

    Ƙungiyar marubuta kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya HURIWA, ta zargi ƙasashen Rasha da Isra'ila da neman fin ƙarfin Majalisar Ɗinkin Duniya.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce an wayi gari da mutuwar ƴanjarida guda huɗu a sanadiyar wani hari da Isra'ila ta kai a wani asibitin Gaza, bayan ƴanjarida biyar da aka kashe a kwanakin baya.

    Ƙungiyar ta ce wani rahoton sirri na sojojin Isra'ila ya nuna cewa yawancin waɗanda aka kashe a Gaza fararen hula ne.

    Sanarwar ta ce alƙaluman da binciken haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai na The Guardian da Mujallar +972 da Local Call suka gudanar ya gano cewa, "zuwa watan Mayun 2025, kimanin wata 19 da fara yaƙin Isra'ila a Gaza, sojojin Isra'ila sun daddale mayaƙan Hamas 8,900 da na PIJ da ko dai suka tabbatar da mutuwarsu, ko kuma suke tunanin sun mutu, sannan ma'aikatar lafiyar zirin ta ce aƙalla mutum 53,000 ne suka mutu."

    HURIWA ta ce hakan ke nufin cewa kashi 17 ne kawai na waɗanda aka kashe ne mayaƙa, sannan sauran kashi 83 fararen hula ne.

    Haka kuma ta ce tun bayan fara yaƙin Rasha a Ukraine, dubban ƴan ƙasar Ukraine, waɗanda HURIWA ta ce fararen hula sun fi yawa.

    "Yadda Rasha da Isra'ila ke kai hari kan ƙananan ƙasashe irin su Ukraine da Falasɗinawa, da yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ke zama tarukan majalisar tsaro, ta fitar da sanarwa da matakai amma ba sa haifar da ɗa mai ido ya nuna akwai lauje cikin naɗi. Kasancewar Rasha na da kujerar na-ƙi, sannan Isra'ila na samun goyon bayan Amurka wadda ita ma take da kujerar na-ƙi, hakan ya sa Rasha da Isra'ila ba sa jin ɗarɗar kan barazanar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke musu na karya dokokin duniya."

  11. Ƴanjarida huɗu na cikin mutum 15 da suka rasu a harin Isra'ila a asibitin Gaza - Jami'an Falasɗinu

    Ma'aikatan lafiya a Falaɗinu sun ce aƙalla mutum 15 ne suka rasu a dalilin wasu hare-haren Isra'ila a asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza.

    Wakilan gidajen jarida da dama - ciki har da na Reuters - na cikin waɗanda suka rasu a asibitin.

    Sun ce an kashe ƙarin mutane ne a harin na biyu a daidai lokacin da masu aikin ceto da ƴanjarida suka isa wajen domin aikin ceto da ɗauko rahoto.

    Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba kan harin.

    Asibitin dai ya daɗe yana tsira daga hare-hare da luguden wuta a yaƙin da Isra'ila a Gaza.

  12. Al'ummar Maiduguri na shirin ko-ta-kwana kan ambaliyar ruwa

    A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya NIMET ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohi 19 da ke ƙasar, sakamakon yadda ake samun mamakon ruwan sama a baya bayan nan.

    Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar da aka samu mummunar ambaliya a bara, na cikin jihohin da a yanzu ma ake hasashen za a iya samun ambaliyar.

    Mahukunta a jihar na cewa tuni suka fara daukar matakan da suka kamata, don kaucewa faruwar hakan.

    Sai dai domin fuskantar matsalar, mutane da dama a garin sun tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan gayya musamman wajen buɗe magudanar ruwa da sauran su.

    Malam Musa Ibrahim Gilabo ya shaida wa BBC cewa sun tara kuɗi domin gudanar da ayyukan gayya a unguwarsu, sannan ya yi kira ga sauran jama'a su tahi tsaye ba sai sun jira gwamnati ba.

    A nasa ɓangaren, Abdullahi Yusuf Bukar ya ce suna buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi, domin a cewarsa, ya kamata gwamnati ta ware wuraren zubar da shara da kwashewa.

    A zantawar BBC da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya ce ya ziyarci tushen matsalar, inda ya ce, "muna neman kariya daga Allah, amma a kwnanan nan na je madatsun ruwan da kaina, kuma tuni ake ta aikin buɗe hanyayoyi da za a iya karkatar da ruwan domin kiyaye aukuwar ambaliyar."

  13. Gamayyar likitoci ta zargi RSF da kashe fararen hula 13 a Sudan

    Likitoci a Sudan sun zargi dakarun RSF da ke yaƙi da sojojin ƙasar da kashe fararen hula ƴan ba-ruwanmu guda 13 a Arewacin Dafur, a daidai lokacin da yaƙi ke ƙazancewa a yankin El Fasher, wanda shi kaɗai ne ya rage a hannun sojojin ƙasar a cikin manyan biranen Dafur a yanzu.

    A wata sanarwa da gamayyar likitocin suka fitar, sun ce daga cikin waɗanda mayaƙan suka kashe akwai ƙananan yara biyar.

    Lamarin ya auku ne a wata babbar hanyar da ta raba birnin El Fasher da Tawila, inda likitocin suka ce, "yunƙurin kisan ƙare dangi ne."

    An daɗe ana zargin RSF da kai hari kan garuruwan da ba Larabawa ba ne a Dafur, duk da cewa sun sha musanta zargin.

    Ana dai ci gaba d gwabza yaƙi tsakanin RSF da sojojin Sudan a ƙasar tun bayan da yaƙin basasa ya ɓarke a ƙasar.

  14. Trump ya girke sojoji da dama a Washington domin daƙile laifuka da baƙin haure

    Dakarun tsaron ƙasa da shugaba Trump ya aike Washington domin daƙile masu aikata laifuka da baƙin-haure sun soma aiwatar da ayyukansu a birnin.

    Wata sanarwa daga dakarun haɗin-gwiwar na cewa sojoji na kewaye birnin ɗauke da bindigogi, amma dai ba za su yi harbi ba, sai an kai su maƙura.

    Sojoji kusan dubu biyu aka girke a birnin Washington, matakin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

    Wannan yanayi ne da ba a saba gani ba a Washington, Shugaba Trump ya kuma yi barazanar sake aike sojojin wasu yankunan manyan birane da democrats ke mulki, ciki harda Chicago da New York da kuma Baltimore.

    Trump na ganin waɗannan matakai na shi ne za su kawo sallama da mataimaka masa wajen cimma manufofinsa.

  15. Tinubu ya isa Brazil domin ziyarar kwana biyu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Brasilia da ke ƙasar Brazil domin ziyarar aiki ta kwana biyu a ƙasar daga birnin Los Angeles na Amurka, inda ya samu tarba daga manyan jami'an gwamnatin Najeriya da takwarorin su na Brazil a filin jirgin Brasilia.

    Ana dai sa ran Tinubu da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Sailva za su tatttauna su biyu ƙadai, sannan daga baya su fito su gudanar da taron manema labarai daga baya.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da Brazil, inda ya ce a watan Maris na 2025, ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeninyar inganta noma da kasuwanci da tsaro da makamashi da ilimi da ma'adinai.

  16. An kama dattijuwa da zargin safarar hodar iblis a juna-biyu na ƙarya

    Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA sun kama wata mai shekara 50 bisa zarginta da yunƙurin safarar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.3 ta hanyar amfani da ciki na karya.

    An kama wacce ake zargin, Misis Ifeoma Ezewuike a tashar mota da ke unguwar Jibowu, a unguwar Yaba kan hanyarta na safarar hodar zuwa Abuja.

    A nan gaba ne bayan an kammala bincike ne za a gurfanar da ita a gaban kotu.

  17. An buƙaci Netanyahu ya amince da musayar fursunoni da Hamas

    Kafofin yaɗa labarai a Isra'ila sun ruwaito cewa Babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Eyal Zamir na cewa akwai wata yarjejeniya da aka gabatar ta sakin ƴanƙasar da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su, wadda ya ce ya kamata su karɓa.

    A gobe Talata ake sa ran majalisar tsaro ta Isra'ila za ta tattauna daftarin yarjejeniyar ta baya-bayan nan da masu shiga tsakani suka gabatar - wadda kuma Hamas ta amince da ita tun makon da ya gabata.

    Janar ɗin na soja ya buƙaci Firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu ya amince da buƙatar, domin a cewarsa hakan zai ba su damar ceto ƴan ƙasarsu.

    Babban hafsan ya ce rundunar sojin ƙasar tana jira ne ta ji matakin da Netanyahu zai ɗauka kan batun.

    Ana dai sa ran cewa akwai aƙalla Isra'ilawa 20 da ke hannun Hamas da har yanzu suke raye.

  18. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya laƙawa shafukanmu na sada zumunta domi karanta wasu labaran da tafka muhawara.

    Ku kasance a tare da mu.