Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/12/2025

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

  • Kenya ta aike da ƙarin ƴansanda Haiti
  • Najeriya ta ce jirgin ta ya yi saukar gaggawa ne a Burkina Faso
  • Faɗa na ci gaba da tsanani tsakanin Thailand da Cambodia
  • Burkina Faso ta tsare jirgin sojin Najeriya kan keta sararin samaniyar ƙasar
  • Paramount ya miƙa sabon tayin sayen Warner Bros
  • Majalisar dattijan Najeriya ta amince Tinubu ya tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin
  • Mutane da dama sun jikkata bayan girgizar ƙasa a arewacin Japan
  • An yanke wa wani ɗan tawayen Sudan hukuncin ɗaurin shekara 20

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Aisha Babangida

  1. M23 na yunkurin kutsawa birnin Uvira na DR Congo

    Ana can ana gwabza fada a gabashin jamhuriyar dimokuradiyyar Kongo, inda da mayakan M23 masu samun goyon bayan Rwanda ke ci gaba da nausawa cikin birnin Uvira da ke lardin kudancin Kivu.

    Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka kungiyar na da nisan akalla kilomita 15 daga birnin, kusa da iyakar kasar da Burundi.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum dubu dari biyu ne suka tsere daga gidajensu a kwanakin baya bayan nan, bayan da aka ci gaba da samun tashin hankalin.

    Shugaba Felix Tshisekedi ya zargi Rwanda da saba alkawarin da ta dauka, kwanaki kadan bayan da kasashen biyu suka sanya hannu, kan yarjejeniyar zaman lafiya a Washington.

  2. Ba ma neman taimakon Amurka wajen ceto dimokuradiyya - Firaministan Birtaniya

    Shugabannin kasashen Turai sun soma caccakar kalaman da Trump ya yi. Fira Ministan Birtaniya Keir Starmer ya musanta cewa Turai maganganu kawai take yi game da Ukraine amma har yanzu ba ta yi wani abun arziƙi ba.

    Shi kuwa shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya soki sabon tsarin tsaron Amurka, da kuma batun cewa Amurka za ta taimakawa Turai wajen ceto dimokuradiyyarta.

    A cewarsa, Turai ba ta neman taimakon Amurka kan hakan.

  3. Masu rauni ne suke shugabantar kasashen turai - Trump

    Shugaba Trump ya bayyana kasashen Turai a matsayin ruɓɓaɓun ƙasashe da mutane masu rauni ke jagoranta, wadanda kuma suka kasa shawo kan kwararar baƙi, sannan ya ce nahiyar ba ta taɓuka wani abin a-zo-a-gani ba game da batun Ukraine.

    Ya ce na san shugabannin su na kwarai da wadanda ba na kwarai ba, masu hankali na san marasa hankali, kuma Turai ba ta aikata abin da ya kamata a wurare da dama.

    Mista Trump ya faɗi hakan ne a ya yi wata hira da shafin intanet na Politico, bayan da aka wallafa sabon tsarin tsaron Amurka, wanda a ciki aka bayyana cewa Dimokradiyya na fuskantar barazana a Turai.

  4. Gwamnan jihar Osun, Adeleke ya koma Jam'iyyar Accord

    Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya bayyana komawarsa Jam'iyyar Accord, inda ya ce a cikinta ne zai yi takarar neman wa'adin mulkinsa na biyu a zaɓen da za a yi a shekarar 2026.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana a fadar gidan gwamnatin jihar, inda ya yi maraba da jagororin jam'iyyar na jiha da na ƙasa.

    "Tun a ranar 6 ga watan Nuwamba na yanke shawarar komawa Jam'iyyar Accord domin in yi takarar tazarce bayan tattaunawa da na yi da masu ruwa da tsaki da mazauna jiharmu ta Osun."

    Ya ce ya zaɓi jam'iyyar ne saboda tsarinta na taimakon al'umma, "tsarin da ya yi daidai da tsarinmu na ba jin daɗin ma'aikatanmu da ma al'ummarmu muhimmanci."

    "Mutanen Osun sun zaɓa mulki mai kyau ne a zaɓen shekarar 2022, kuma ina da yaƙinin za su sake zaɓenmu domin ci gaba da mulki a zaɓen shekarar 2026. Mutane suna ƙaunar mu ci gaba, kuma Jam'iyyar Accord ce jam'iyyarmu a zaɓen baɗi," in ji gwamnan a sanarwar da mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed ya fitar.

  5. Fararen hula 1700 aka kashe tun fara yaƙin basasar Sudan - Bincike

    Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa an kashe fararen hula 1700 a hare-hare ta sama da sojojin Sudan suka kai tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar fiye da shekaru 2 da suka gabata.

    Binciken ya ce an kai hare hare kan gidajen jama'a da kasuwanni da makarantu da kuma sansanonin ƴan gudun hijirah inda aka kashe adadin waɗannan mutanen.

    Sojojin Sudan ɗin ne dai kawai suke da irin waɗannan jiragen da suka kai hare haren.

    Mayaƙan RSF da ke faɗa da sojojin Sudan kuma ake zarginsu da aikata kisan kiyashi ba su da irin waɗannan jiragen.

    Wakiliyar BBC ta rawaito cewa rundunar sojin Sudan ɗin ba ta ba wa BBC amsa akan bukatar da ta yi na mayar da martani akan wannan binciken da aka yi ba, kodayake a baya ta sha musanta zarge zargen kai wa fararen hula hari.

  6. Labarai da dumi-dumi, Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya koma APC

    Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

    Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa Fubara ya sanar da sauya sheƙar ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke birnin fatakwal na jihar Rivers.

    Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da ƴan majalisar jihar 15 tare da kakakin majalisar suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ta APC.

    Masu fashin baƙi dai na ganin sauya sheƙar ta Fubara ba lallai ta yi wa ministan Abuja, Nyesom Wike daɗi ba kasancewar shi ne babban abokin hamayyarsa, inda rikici ya kai har shugaba Tinubu ya saka wa jihar dokar ta-ɓaci ta watanni shida da ta tilasta Fubara sauka da kujerar gwamnan na tsawon watannin.

    A watan Satumbar da ya gabata ne Fubara ya koma bakin aikinsa bayan ƙarewar wa'adin watannin shida na dokar ta ta-ɓacin da ta fara aiki a watan Maris.

    Bisa tsarin siyasa, gwamnan jiha shi ne jagoran jam'iyya inda yanzu haka Fubara zai kasance jagoran jam'iyyar APC a jihar Rivers.

  7. Aƙalla mutum 20 sun mutu sakamakon gobara a Indonesia

    Wata gobara da ta tashi a wani gini mai tsawo a babban birnin Indonesia, ta yi ajalin mutum aƙalla ashirin.

    Shugaban yansandan Jakarta ya ce masu kashe gobara na ci gaba da duba ginin ko akwai sauran mutanen da ke makale a ciki.

    Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa hukumomi sun ce da alama gobarar ta samo asali ne bayan da wani batir ya fashe a wani kamfanin da ke ƙera jirage marasa matuƙa da ke ginin.

    Hukumomin sun ƙara da cewa akasarin waɗanda suka mutu mata ne, ɗaya daga cikinsu tana da juna biyu, kuma da alama sun mutu ne sakamakon shakar hayaƙi.

    Hayaki mai kauri ya turniƙe saman benen yayin da masu kashe gobara suka yi amfani da motocin kashe gobara 28 da kuma ma'aikata kusan 100 domin shawo kan gobarar.

    An dai kashe gobarar kuma ma'aikatan agaji na mayar da hankali kan neman waɗanda ake tunanin sun maƙale a cikin ginin.

  8. Ƙasashen Turai sun yi watsi da daftarin sabon tsarin tsaron Amurka

    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce ƙasashen Turai za su iya kare dimokradiyyarsu, kuma ba sa buƙatar wani katsalandan daga Amurka.

    Mista Merz na mayar da martani ne kan sabbin tsare tsaren tsaron Amurka da ta wallafa, wanda a ciki a ka ce Turai na fuskantar barazanar shafewar ala'adu saboda yawaitar baƙi.

    Mista Merz ya ce ba za su amince da wasu sassan tsare tsaren ba, kuma hakan na sake nuna buƙatar ƙasashen Turai su tsaya da ƙafarsu a fannin tsaro.

  9. Ukraine na shirin gabatar da sabon daftarin zaman lafiya

    Ukraine na shirin gabatar da wani shirin zaman lafiya da aka yi wa kwaskwarima ga fadar White House, yayin da take ƙoƙarin kaucewa miƙa was yankunan ta ga Rasha.

    Kyiv na shirin ba da shawarar bin wasu hanyoyi na daban ga Amurka bayan da Shugaba Volodymyr Zelensky ya sake yanke hukuncin cewa ƙasarsa ba za ta hakura da wasu yankunan ta ba, yana mai cewa "ba shi da ƴancin yin hakan a ƙarkashin dokokin Ukraine ko na kasa da kasa.''

    Ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ganawa da shugabannin ƙasashen Turai da NATO a ranar litinin, a wani ɓangare na yunƙurin hana Amurka goyon bayan yarjejeniyar zaman lafiya da za ta buƙaci Ukraine ta yi babbar sadaukarwa, wadda ƙawayenta ke fargabar zai bar ta cikin hadarin mamayewa nan gaba.

    A halin da ake ciki kuma, birnin Sumy da ke arewa maso yammacin Ukraine ya kasance babu wutar lantarki cikin dare bayan wani harin da jiragen saman Rasha suka kai.

    Gwamnan yankin ya ce sama da jirage marasa matuƙa 12 ne suka kai hari kan kayayyakin samar da wutar lantarki, wanda shi ne na baya bayan nan a hare-haren da Rasha ke kai wa cikin dare.

    Ba a dai bayar da rahoton mutuwar mutane ba.

  10. Paramount ya miƙa sabon tayin sayen Warner Bros

    Paramount Skydance ya sake gabatar da wani tayin sayen kamfanin fina-finai da tababijin na Warner Bros Discovery yayin da yake yunƙurin doke Netflix a fafatawar da suke ne na mallakar kamfanin.

    Paramount, ya ce yana yin tayin kai tsaye ne ga masu hannun jari na dala $30 kan kowane hannun jari na Warner Bros.

    Ya ce tayinsa ya fi na Netflix armashi domin zai bai wa masu hannun jari kuɗi a hannunsu kai tsaye.

    Shugaba Donald Trump ya ce "za a iya samun matsala" da tayin Netflix, yana mai nuni da damuwar yadda za a iya kawo cikas ga gasar kasuwanci idan aka yi la'akari da giman kamfanonin biyu.

    Masu sharhi kan al'aumuran kasuwannin hannun jari sun daɗe sun ce suna iƙirarin cewa haɗewar Paramount da Warner Bros zai yi ma'ana, saboda zai ba kamfanin damar fafatawa da abokan hamayya irin su Netflix da Disney.

    Warner Bros ya ce zai sake duba tayin amma a halin yanzu bai canza shawararsa ba.

    Ya ce zai sanar da matsayarsa cikin kwanaki 10.

  11. Majalisar dattijan Najeriya ta amince Tinubu ya tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin

    Majalisar dattawan Najeriya ta amince da buƙatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike ma ta na neman a tura sojojin Najeriya zuwa jamhuriyar Benin domin kwantar da tarzoma bayan wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a baya bayan nan.

    Sanatocin dai sun kaɗa kuri’ar amincewa da tura sojojin da gagarumar, inda suka bai da goyon bayan majalisa kan batun tabbatar da tsaro a yankin.

    Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya bayyana matakin a matsayin matakin da ya dace, yana mai cewa rashin zaman lafiya a kowace ƙasa da ake maƙwabtaka da ita yana barazana ga ɗaukacin yankin.

    Shugaba Tinubu dai ya miƙa buƙatar ne a cikin wata wasiƙa da aka karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.

    A cikin wasikar, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatin Benin ta yi gaggawar neman tallafin jiragen sama na musamman daga rundunar sojojin Najeriya bayan da sojoji suka yi yunƙurin hamɓarar da shugaba Patrice Talon.

    Shugaba Tinubu ya yi gargaɗin cewa Jamhuriyar Benin na fuskantar "yunƙurin ƙwace mulki ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar ruguza cibiyoyin dimokraɗiyya".

    Yunƙurin juyin mulkin Jamhuriyar Benin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da wasu sojoji suka kutsa gidan talabijin na ƙasar su ka kuma sanar da tsige shugaban ƙasar Patrice Talon.

  12. Mutane da dama sun jikkata bayan girgizar ƙasa a arewacin Japan

    Aƙalla mutane 30 ne suka jikkata bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin 7.5 da ta afku a arewa maso gabashin ƙasar Japan a daren jiya Litinin, lamarin da ya tilastawa dubban mutane barin gidajensu.

    Hukumar kula da yanayi ta ƙasar Japan ta ce girgizar ƙasar ta afku ne da daren Litinin a yankin da ke da tazarar kilomita 80 daga gaɓar teku. Ya haifar da gargadin tsunami wanda a yanzu janye. An dakatar da wasu ayyukan jiragen ƙasa kuma an bar dubban gidaje babu wutar lantarki sakamakon haka.

    Hukumomin ƙasar sun kuma yi gargadin cewa za a iya samun girgizar ƙasa mai ƙarfi a cikin kwanaki masu zuwa - tare da yin kira ga jama'a da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana na aƙalla mako guda, a cewar rahotannin kafafen yaɗa labaran ƙasar.

    Da ta ke jawabi ga ƴan ƙasar, Firaminista Sanae Takaichi ta shawarci su da su kasance cikin shiri a kodayaushe.

    An ba da umarci mazauna kusan 90,000 da su nemi mafaka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

  13. An yanke wa wani ɗan tawayen Sudan hukuncin ɗaurin shekara 20

    Kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Hague ta yanke hukuncin ɗaurin shekara ashirin kan wani jagoran ƴan tawayen Sudan da aka samu da laifin aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil adama a watan Oktoba.

    Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, an same shi da laifuka ashirin da bakwai da suka haɗa da kisan kai, azabtarwa, da kuma fyaɗe.

    Suna da alaƙa da ta'asar da mayaƙan Janjaweed suka aikata a yankin Darfur na ƙasar Sudan sama da shekara ashirin da suka gabata.

    Yayin yanke hukuncin alƙaliyar kotun Joanna Korner, ta ce Mista Al-Rahman ya yi wa mutane dukan tsiya da kansa, ya kuma bayar da umarnin zartar da hukuncin kisa kan fararen hula.

    Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai.

    Al-Rahman dai ya musanta cewa shi babban jigo ne a ƙungiyar Janjaweed, dakarun da gwamnatin Sudan ta marawa domin murƙushe masu tayar da ƙayar baya a yankin Darfur, inda aka kashe sama da mutane dubu ɗari uku, kuma kusan miliyan uku suka tsere daga gidajensu.

  14. Kenya ta aike da ƙarin ƴansanda Haiti

    Ƙarin wasu ƴansanda daga Kenya su 230 sun isa Haiti a wani ɓangare na nuna goyon baya ga dakarun wanzar da zaman da lafiya da Majalisar Dinkin Duniya wajen magance rikicin ƴan daba da ake fama da shi a ƙasar.

    Maƙasudun zuwansu shi ne su yaƙi ƙungiyoyin ƴan dabar da ke iko da mafi yawancin babban birnin ƙasar Port au Prince,wanda kuma suke ƙara faɗaɗa mamayar da suke yi a ƙasar.

    Yanzu haka an tura ƴan sandan Kenya kusan dubu ɗaya ƙasar.

    Ana dai zargin ƴan dabar da aikata kisan ƙare dangi da fyade da dai sauran muggan laifuka.

    Rikicin ƴan dabar ya tursasawa kusan ƴan Haiti miliyan ɗaya da rabi tserewa da muhallansu.

  15. Najeriya ta ce jirgin ta ya yi saukar gaggawa ne a Burkina Faso

    Mahukunta a Najeriya sun ce jirgin NAF C-130 da ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal.

    Sanarwar da rundunar Sojin saman Najeriya ta fitar ta ce ma’aikatan jirgin sun taso ne daga Legas amma sun lura da wata matsala wanda hakan ya sa aka yi taka-tsan-tsan da sauka a Bobo-Dioulasso na Burkina Faso, filin jirgin sama mafi kusa, lamarin da ya yi daidai ƙa'idojin tsaro da ka'idojin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa, "Ma'aikatan rundunar saman Najeriya suna cikin ƙoshin lafiya kuma sun samu kyakkyawar kulawa daga hukumomin da suka karɓi baƙuncinsu, ana ci gaba da shirye-shiryen ci gaba da tafiyar da aikin da suka sanya a gaba.''

    Rundunar sojojin saman Najeriya ta yaba da tallafin da aka samu a wannan lokaci tare da tabbatar wa da jama'a cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen bin ƙa'idojin aiki da ƙa'idojin tsaro, tare da tabbatar da kare lafiyar ma'aikatanta yayin da take kiyaye dokikoin da kundin tsarin mulki ya tanada."

    Sai dai da alama labarin Najeriya na yadda lamarin ya auku ya ci karo da matsayin gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso da kuma ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel, waɗanda suka ce jirgin ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ne ba tare da izini ba kuma aka tilasta masa sauka.

    Kungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta yi alla-wadai da lamarin a matsayin "ketare sararin samaniyarta da kuma keta ƴancin kasashe mambobinta," tare da bayyana saukar jirgin a matsayin "aikin rashin abokantaka da aka yi ba tare da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da ƙa'idojin sufurin jiragen sama ba."

    Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar rashin aminta da kuma sauya ƙawance a faɗin yammacin Afirka.

    Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne suka kafa Ƙungiyar AES, lamarin da ya sa suka fice daga Ƙungiyar ECOWAS a farkon wannan shekarar.

  16. Faɗa na ci gaba da tsanani tsakanin Thailand da Cambodia

    Cambodia da Thailand sun ce sun ƙaddamar da sabbin hare-hare kan juna a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ya sake barkewa.

    Shugaban Cambodian, Hun Sen, ya ce dakarunsa sun mayar da martani cikin daren jiya da kuma safiyar yau Talata akan harin da aka kai musu.

    Ya ce Cambodia na faɗa ne domin kare kanta bayan haƙurin da ta yi a kan harin da aka kai mata a baya.

    Thailand ta ce jiragenta na yaƙi sun kai hari kan wuraren da sojojin Cambodia suke, tana mai cewa manufar hakan ita ce karya lagon sojojin Cambodia.

    Abin da muka lura da shi kawo yanzu shi ne dukkan ƙasashen na zargin juna da fara takalar faɗan sannan kuma kowanne a cikinsu yanzu haka na kai wa juna hari.

    Aƙalla fararen hula bakwai da kuma sojan Thailand daya ne aka kashe a yayin faɗan.

  17. Burkina Faso ta tsare jirgin sojin Najeriya kan keta sararin samaniyar ƙasar

    Gwamnatin Burkina Faso ta ce an tilasta wa wani jirgin saman sojin saman Najeriya ɗauke da sojoji 11 sauka a ƙasar a ranar Litinin bayan da aka ce ya keta sararin samaniyar ƙasarta.

    Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin ƙasar ta ce jirgin sojan na ɗauke da ma’aikata biyu da fasinjoji tara a cikinsa kuma dukkansu jami’an soji ne.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, binciken da hukumomin ƙasar Burkina Faso suka gudanar ya nuna cewa jirgin ba shi da izinin shawagi a sararin samaniyar ƙasar.

    Ƙungiyar AES ta yi Alla-wadai da lamarin a matsayin keta haddin kasar, tana mai cewa "ta yi suka da kakkausan lafazi kan keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke cikin ƙungiyarta".

    Ƙungiyar, ta yi gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wani jirgi da ya keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke yankin ba tare da izini ba.

    Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daga rundunar sojin saman Najeriya ko gwamnatin tarayya.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya Litinin na kawo mu ku abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.