Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/09/2024

Taƙaitattu

  • Hezbollah ta ce ta harba makaman roka zuwa arewacin Isra'ila
  • Gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a Isra'ila
  • Jagoran adawar Venezuela ya fice daga ƙasar
  • An kashe Isra'ilawa uku a kan iyakar Jordan da Gabar Yamma
  • Jihohin Kano da Edo su ɗage ranakun komawar ɗalibai makarantu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Bankwana

    Ƙarshen rahotannin shafin kai tsaye na BBC Hausa kenan a yau Lahadi.

    Ku tara gobe Litinin domin samun wasu sabbin rahotannin.

  2. An tsinci gawar wani ɗan adawa a Tanzania

    An tsinci gawar wani ɗan adawar siyasar Tanzania Ali Mohamed Kibao, kwanaki bayan rahotannin sace shi da ake zargin jami'an tsaro ne suka yi.

    Jam'iyyar Chadema ta ce an tilasta wa Mr Kibao shiga mota yayin da yake balaguro zuwa Tanga.

    An tsinci gawarsa a Uninio da ke arewa da Dar-es-Salaam.

    yanzu haka ana bincike domin gano abin da ya yi sanadin mutuwarsa.

    A kwanakin baya an kama shugaban jam'iyyar Chadema Tundu Lissu da wasu jami'ai, inda ake bayyana fargaba kan manufofin shugaba John Magufuli.

  3. An bayyana sunan mutumin da ya kashe ƴan Isra'ila uku a gaɓar Yamma

    Ma'aikatar harkokin wajen Jordan ta ce direban babbar motar da ya kashe jami'an tsaron Isra'ila uku a gaɓar Yamma da kogin Jordan ɗan ƙasar Jordan ne.

    Ta ce sunan mutumin, Maher al-Jazi kuma shi kaɗai ya aikata laifin.

    Ta kuma ce tana aikin haɗin gwiwa da Isra'ila domin dawo da gawarsa Jordan don a yi mashi jana'iza.

    Isra'ila da Jordan sun rufe gadar sarki Hussein - Allenby wadda ta haɗa bangarorin biyu.

    Isra'ila ta kuma rufe duk iyakokin ta da Jordan.

    Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana wanda ya aikata kisan a matsayin ''ɗan ta'adda da ya cancanci tsana''

  4. Bangladesh ta buƙaci a gaggauta samar da matsugunni ga musulman Rohingya

    Shugaban riƙon ƙwaryar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya yi kiran a gaggauta samarwa musulman Rohingya matsugunni a wata ƙasa mai tasowa.

    Da yake ganawa da hukumar kula da masu yin ƙaura ta Majalisar Dinkin Duniya, Muhammad Yunus wanda ya taɓa lashe lambar yabo ta Nobel, ya ce ya kamata a yi tsari mai kyau na samarwa al'ummar Rohingya matsugunni cikin sauƙi kuma a kan lokaci.

    Ƴan Rohingya dubu takwas suka tsallaka Bangladesh a watannin nan, yayin da faɗa ya yi ƙamari a maƙwabciya Myanmar, inda ake fafatawa tsakanin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

    Sabbin ƴan gudun hijirar ƙari ne a kan fiye da miliyan ɗaya da suke zaune a sansanonin ƴan gudun hijira a Bangladesh.

    Mafi yawan su sun tsere daga Myanmar ne a 2017, domin gudun cin mutumci daga sojoji.

  5. Ana zargin an samu ɓullar cutar mpox a India

    An samu wani mutum da ake zargin ya kamu da cutar ƙyandar biri a India.

    Ma'aikatar lafiyar India ta ce mutumin ya yi tafiya zuwa wata ƙasa da aka samu ɓarkewar cutar kuma yanzu haka an killace shi inda ake kula da lafiyar sa.

    Ta ce an gudanar da gwaje-gwaje domin tabbatar da ko cutar ƙyandar biri ce yake dauke da ita.

    Ma'akatar ba ta bayyana wajen da aka killace marar lafiyar ba, kuma babu cikakken bayanin nau'in cutar da ake zargin ya kamu da ita.

    Ta dai ce ana ci gaba da ƙoƙari domin hana yaɗuwar cutar a India.

    Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta ɓaci a kan cutar ƙyandar biri, wadda aka yi wa laƙabi da mpox, bayan ɓullar cutar a wasu ƙasashen Afirka.

  6. Jagoran adawar Venezuela ya isa Sifaniya

    Ɗan takarar ƴan adawa a zaɓen shugaban ƙasar Venezuela, ya isa Sifaniya bayan tserewa daga ƙasarsa.

    Wani jirgin sojin saman Sifaniya ɗauke da Edmundo González ya sauka a filin jirgin sama na Torrejon a birnin Madrid, bayan amincewa da bashi mafakar siyasa.

    Mr González ya daɗe yana ɓoyo a Venezuela, inda aka bayar da umarnin kama shi bayan ɓangaren ƴan adawa ya wallafa wani sakamakon zaɓe da ya ci karo da wanda hukumomi suka sanar, da ya bai wa shugaba Nicolás Maduro wa'adin mulki na uku.

    Babbar jagorar ƴan adawar Venezuela, María Corina Machado, ya tsere ne domin "kare ƴancinsa na walwala da mutumcinsa da kuma rayuwarsa".

    Ya tsere ne bayan jami'an tsaro a Venezuela sun zagaye ofishin jakadancin Argentina da ke Caracas, babban birnin ƙasar, inda manyan ƴan adawa shida ke zaman mafaka.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi zargin cewa ana kitsa ayyukan ta'addanci a cikin ofishin.

  7. Duk wanda ya takali ƙasarmu za mu mayar da martani - Abiy Ahmed

    Firaminitan Ethiopia, Abiy Ahmed ya sha alwashin kare ƙasarsa daga mutanen da ya kira ''masu niyyar mamaya''.

    Cikin wani jawabi da ya yi wa ƙasar ta gidan talbijin a bikin ranar tunawa da 'yancin kan ƙasar, Mista Abiy ya gargaɗi duk wanda ke shirin kai wa ƙasarsa hari da ya ''ƙara tunani'', yana mai cewa a shirye ƙasarsa take domin mayar da martani ga duk wanda ya takaleta.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ciki gaba da samun ƙaruwar zaman tankiya tsakanin ƙasar da makwabciyarta Somaliya kan ɓallewar yankin Somaliland.

    Rahotonni sun ce ƙasar Masar - wadda ta jima tana takun saƙa da Ethiopia kan wata madatsar ruwa a kusa da tekun Nilu - na duba yiwuwar aika dakaru zuwa Somaliya.

  8. SERAP ta buƙaci Tinubu ya tilasta wa NNPCL janye ƙarin kuɗin man fetur

    Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi amfani da ''matsayinsa ya tilasta wa babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da ƙungiyar ta kira 'wanda ya saɓa wa doka'.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi ta ce ƙarin kuɗin man fetur ɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulki tare da dokokin ƙasar game da kare haƙƙin bil-adama.

    SERAP ta kuma buƙaci shugaba Tinubu ya ''umarci babban lauyan gwamnatin ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su binciki zarge-zargen cin hanci da almabazzaranci a ake yi wa kamfanin NNPCL.

    Ciki har da kuɗin tallafin ƙwatar kai (bailout), na dala miliyan 300 da kamfanin ya karɓa daga gwamnatin tarayya a watan Agustan da ya gabata, da kuma zargin kamfanin da rashin saka ribar mai a asusun gwamnati.

    SERAP ta ce “ya kamata a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifi a NNPCL a gaban kotu domin su fuskanci hukunci, idan har an same su da laifi, tare da ƙwato duk abin da suka sata''.

    ƙungiyar ta kara da cewa cin hanci da rashawa da ake zargin samu fannin man fetur da kuma kashe kuɗin gwamnati ba bisa ƙai'da ba, da kuma yin ƙunbiya-ƙunbiya ko rufa-rufa sun taimaka wajen ƙarin taɓarɓarewar al'amura a kamfanin, wanda kuma shi ke haifar da ƙarin kuɗin man fetur a koyaushe a ƙasar.

  9. Ana fargabar ƙyandar biri ta ɓulla a Indiya

    Indiya na fargabar samun ɓullar cutar ƙyandar biri a ƙasar.

    Ma'aikatar Lafiyar ƙasar ta ce mutumin da ake zargi na ɗauke da cutar, ya koma Indiya ne daga wata ƙasa da ta fuskanci ɓullar cutar.

    Ta kuma ƙara da cewa an killace mutumin a wani asibiti inda yake samun kulawar likitoci.

    To sai dai ma'aikatar lafiyar ƙasar ba ta bayyana nau'in cutar da ake zargin mutumin ya kamu da ita ba.

    Ma'aikatar lafiyar ta kuma ce tana koƙarin ganin cutar ba ta yaɗu a cikin ƙasar ba.

    Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin babbar barazana ga duniya, yayin da aka samu barkewarta a wasu ƙasashen Afirka da dama.

  10. Sudan ta yi fatali da ƙudirin MDD na samar da jami'an tsaro na musamman don kare fararen hula

    Sudan ta yi watsi da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya na girke jami'an tsaron ƙasashen duniya a ƙasar domin kare fararen hula.

    Wata tawagar ƙwararru ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton gano mummunan halin tsananin cin zarafi da ta ce fararen hular ƙasar na fuskanta daga ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar, a lokacin wani bincike da ta gudanar a wasu yankunan ƙasar.

    Lamarin da ya sa ta bayar da shwarar smar da wata rundunar jami'an tsaron ƙasashen duniya da nufin kare fararen hula a ƙasar.

    To sai dai ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi watsi da shawarar, inda ta kira ƙudurin da siyasa kuma haramtacce, sannan ta zargi ƙudurin da saɓa wa dokokinta.

    Fiye da mutum miliyan 20 ne suka rasa muhallansu sakamako yaƙin da aka ɗauki fiye da shekara guda ana gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF masu sanye da kayan sarki.

    Yaƙin Sudan ya kasance ɗaya daga cikin manyan yaƙoƙin da suka ta'azzara ayyukkan jin-ƙai a duniya.

  11. Jam'iyyar PDP ta mutu a fagen siyasar Najeriya - Kwankwaso

    Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyar PDP mai hamayya a ƙasar ta mutu a fagen siyasar ƙasar.

    Yayin da yake jawabi a ofishin jam'iyyar NNPP na jihar Katsina ranar Asabar, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam'iyyar APC ta jefa kanta cikin abin da ya kira ''halaka''.

    ''Jam'iyyar PDP dama kowa ya sani a yanzu dai matacciya ce, dama mu ne a cikinta, kuma tun da ta saki layi, muka sake'', in Sanata Kwankwaso.

    Ya kuma zargi jagororin gwamnatin APC da nuna halin ko- in-kula game da halin da ƙasar ke ciki, musamman ta fuskar matsalar rashin tsaro.

    ''Kuna gani yanzu idan kana son fita daga cikin Katsina, duk inda za ka bi, to tunani kake ta inda za ka bi''. in ji shi.

    Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira ga talakawan Najeriya su kauce wa karɓar taliya ko wasu kuɗi da ya ce ba su taka kara suka karya ba a ranar zaɓe domin sarayar da haƙƙoƙinsu.

    ''Ku tabbatar cewa ba a sake kawo taliya mutane sun karɓa, sun je sun dafa, sun ci, sun kuma faɗa wahala na shekara huɗu su da 'ya'ya da jikoki, kun dai ga duka wannan wahalar a kan talaka take ƙarewa,'' in ji jagoran Kwankwasiyyar.

  12. Najeriya ta kai zagayen 'yan 16 a gasar Kofin Duniya ta Mata 'yan ƙasa da shekara 20

    Tawagar 'yan matan Najeriya ta kai matakin zageyen 'yan 16 a gasar Kofin Duniya ta Mata 'yan ƙasar da shekara 20 da ke gudana a ƙasar Columbia.

    Hakan na zuwa ne bayan da Falconets ta caskara Venezuela da ci 4-0 a wasan ƙarshe na cikin rukuni.

    Tun da farko 'yan matan Najeriyar sun samu nasara kan Jamhuriyar Koriya da ci 1-0, inda kuma ta yi rashin nasara a hannun Jamus da ci 3-1.

    A yanzu Falconets za ta fafata da Japan ko Austria a zagen 'yan 16, ranar 13 ga watan Satumban da muke ciki.

  13. Jihohin Kano da Edo sun ɗage ranakun komawar ɗalibai makarantu

    Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da ɗage ranar komawa hutun ɗaliban makarantun sakandire da na furamare a faɗin jihar.

    Tun da farko dai an tsara cewa ɗaliban makarantun kwana a faɗin jihar za su koma makarantun a yau Lahadi 8 ga watan Satumba, yayin da ɗaliban makaratun je-ka-ka-dawo za su koma ranar Litinin 9 ga watan Satumbar.

    To sai dai cikin wata sanarwa da darakta wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilimin jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ranar Asabar, ya ambato kwamishinan ilimin jihar, Umar Haruna Doguwa, na cewa an ɗage ranar komawa makarantun, sakamakon wasu dalilai da ya ce za su ''taimaka wajen inganta harkar koyo da koyarwa a makarantun jihar''.

    ''Nan gaba kaɗan za a sanar da sabuwar ranar komawa makarantar'', in ji sanarwar.

    Can ma a jihar Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar gwamnatin jihar ta sanar da dakatar da komawa makarantun har sai abin da hali ya yi sakamakon ƙarin farashin man fetur.

    Cikin sanarwar matakin da babban sakataren ma'aikatar ilimin jihar, Ojo Akin-Longe, ya fitar ranar Asabar, ya ce matakin ya zama wajibi sakamakon halin da iyaye ciki bayan ƙarin kuɗin man fetur da wasu ƙarin matsaloli.

  14. Sojojin Rasha sun ƙwace wani ƙauye a gabashin Ukraine

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarun ƙasar sun ƙwace iko da wani ƙauye a kusa da garin Pokrovsk na gabashin Ukraine.

    Ƙauyen Novohrodivka na da nisan kilomita 10 gabas da garin Pokrovsk, mai muhimmanci ga sojojin Ukraine a yankin Donetsk.

    A makonnin baya-bayan nan sojojin Rasha na ƙara dannawa cikin Ukraine.

    To sai dai dakarun Ukraine sun faɗa cikin wani rahoto da suka fitar a baya-bayan na cewa sun daƙile harin sojojin Rasha a ƙauyen Novohrodivka da sauran yankunan da ke kusa.

    A ranar Asabar, Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce yanayin da ake ciki a kusa da Pokrovsk ya munana, to amma ya ce an samu sauƙi cikin kwanakin da suka gabata, sai dai bai bayar da hujjoji ba.

  15. An kashe Isra'ilawa uku a kan iyakar Jordan da Gabar Yamma

    Jami'an Isra'ila sun ce an kashe fararen hularta uku a wani hari da aka kai kan iyakar Jordan da Gaɓar Yamma.

    Rahotonni sun ce maharin - wanda tuni sojojin Isra'ila suka kashe - direban motar dakon kaya ne, wanda ya taso daga Jordan, sannan ya tsaya a shingen binciken ababen hawa ya kuma buɗe wuta bayan ya sauko daga motar.

    Ma'aikatan lafiya sun ce mutanen uku da aka kashe maza ne masu shekaru aƙalla 50, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Isra'ila suka ruwaito.

    Ƙasar Jordan ta ce ta ƙaddamar da bincike tare da rufe babbar gadar King Hussein, da ke mashigar Gaɓar Yamma, inda abun ya faru.

    Lamarin ya faru ne a yankin da Isra'ila ke iko da shi, kuma nan ne motocin Jordan ɗauke da kaya ke bi don shiga Gaɓar Yamma.

    Mashigar ta kasance ita kaɗai ce mashiga a hukumance tsakanin Gaɓar Yamma da Jordan.

    Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman ɗarar da fargaɓar ɓarkewar yaƙi a yankin Gabar ta Tsakiya.

    Ko a cikin daren da ya gabata ma an samu musayar hare-haren makamai masu linzami tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbolla ta Lebanon.

  16. Wata sabuwar gobara ta tashi a wata makarantar kwana a Kenya

    Aƙalla ɗaliban uku ne suka jikkata bayan wata sabuwar gobara ta tashi a wata makarantar kwana ta mata da ke tsakiyar ƙasar Kenya.

    'Yansanda sun ce gobarar ta lalata ɗakunan kwanan ɗalibai. Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

    Lamarin na zuwa ne ƙasa da kwana uku da wasu ɗalibai 21 suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwanan ɗalibai ta maza a gundumar Nyeri da ke gabashin birnin Nairobi.

    Gobara a makarantun kwana a Kenya na neman zama ruwan dare, inda a lokuta da dama hukumomi ke ɗora alhakin hakan kan bata gari.

  17. Jagoran adawar Venezuela ya fice daga ƙasar

    Gwamnatin Venezuela ta ce ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar adawa, Edmundo González, ya fice daga ƙasar zuwa Sifaniya domin neman mafaka.

    Cikin wani saƙo da mataimakiyar shugaban ƙasar, Delcy Rodríguez, ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta ce ''bayan neman zaman gudun hijira da ya yi bisa raɗin kansa a ofishin jakadancin Sifaniya da ke birnin Caracas a kwanakin da suka gabata, mista Gonzalez ya nemi gwamnatin Sifaniya ta ba shi mafakar siyasa''.

    Ta ƙara da cewa gwamnatin Venezuela ta amince da ficewarsa daga ƙasar, kuma tuni ya yi hakan.

    Ministan harkokin wajen Sifaniya, José Manuel Albares, ya ce Mista González ya fice daga Venezuela ne bisa raɗin kansa, kuma ya fice ne a jirgin rundunar sojin Sifaniya.

    Mista González ya kasance yana wasan ɓuya da jami'an tsaro a Venezuela, bayan da aka bayar da sammacin kama shi sakamakon zaɓen shugabar ƙasar da ya gabata mai cike da taƙaddama.

    Hukumar zaɓen ƙasar dai ta ayyana shugaba Nicolás Maduro a matsayin wanda ya lashe zaɓen, duk da ayyana samun nasara da mista González ya yi, gabanin sanarwar hukumar zaɓen ƙasar.

  18. Gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a Isra'ila

    Wata gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a biranen Isra'ila, don neman gwamnatin ta dawo da 'yan ƙasar da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.

    Masu shirya zanga-zangar sun ce kusan mutum 500,000 ne suka fantsama kan tittuna a Tel Aviv, tare da yi wa ginin ma'aikatar tsaron ƙasar ƙawanya.

    Sannan ana gudanar da makamaciyar wannan zanga-zanga akai-akai a biranen Kudus da Haifa.

    Daya daga cikin masu zanga-zangar ta ce sun gaji da jira kimanin wata 11 da ake garkuwa da mutanen, waɗanda wasu daga cikinsu suka riga suka mutu.

    Kusan a kullum ake irin wannan gangamin tun bayan gano gawarwakin 'yan Isra'ila shida a Gaza kwanaki takwas da suka gabata.

    Masu boren na son Firaminita Netanyahu, ya amince da cimma yarjajaniyar da za ta bayar da damar sako sauran mutanen da ake garkuwa da su.

  19. Hezbollah ta ce ta harba makaman roka zuwa arewacin Isra'ila

    Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, ta ce ta harba makaman roka cikin arewacin Isra'ila, a matsayin martani kan harin Isra'ilar na ranar Asabar.

    Ƙungiyar da ke samun goyan-baya daga Iran ta ce makamanta sun fada a garin Kiryat Shmona da ke Isra'ila.

    To amma jami'ai a yankin na cewa makaman roka biyar aka harba, sai dai babu wanda aka bayar da rahotan jikkata ko rasa rayuka.

    Kafin wannan lokaci, ma'aikatar lafiyar Lebanon ta bayar da rahoton cewa an kashe jami'an agajin gaggawa uku da kuma jikkata wasu biyu a harin da Isra'ila ta kai musu da jirage marasa matuƙa.

    The ministry said the crew had been putting out fires caused by earlier Israeli strikes in a village in southern Lebanon.

    Ma'aikatar ta ƙara da cewa ma'aikatan agajin na ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi sakamakon hare-haren Isra'ila a wani ƙauye da ke kudancin Lebanon.

  20. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.