Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Usman Minjibir

  1. Sojojin Chadi sun kashe mayaƙan Boko Haram aƙalla 300 a yammacin ƙasar

    Sojojin Chadi sun ce sun kawo ƙarshen yaƙin da suka shafe watanni huɗu su na yi da mayaƙan Boko Haram a yammacin ƙasar.

    Sojojin sun ce sun kashe aƙalla masu iƙirarin jihadi 300, kuma a yanzu ƙungiyar ba za ta sake yin tasiri a yankin ba.

    Shugaba Mahamat Idris Deby Itno ne ya ƙaddamar da hare-haren a watan Oktoban da ya gabata bayan gagarumin harin da Boko Haram ta ka wa sansanin soji a yankin tafkin Chadi.

    Ƙungiyar Boko Haram ta fara ayyukan ta'adanci ne a Najeriya a shekarar 2009 wanda tuni ya bazu zuwa ƙasashe makwabta.

  2. 'Fafaroma na fama da cutar sanyin haƙarƙari'

    Fadar Vatican ta ce Fafaroma Francis na fama da cutar sanyin haƙarƙari a huhunsa biyu, yayin da ya ke ci gaba da karɓar magani a asibitin da ke Rome.

    Vatican ta kuma ce cutar hanyoyin numfashinsa ta ɗan yi tsanani, amma dai ya na samun sauƙi.

    An kwantar da Fafaroma Francis ɗan shekara 88 ne a asibiti tun ranar Juma'a.

    Tuni aka soke ayyukan da ya shirya zai gabatar a ƙarshen mako.

  3. Senegal na shirin rage albashin ma'aikata

    Senegal na shirin rage albashin ma'aikatan ƙasar, matakin da gwamnatin ta ce zai daidaita albashin da yanayin tattalin arziƙin ƙasar.

    Sai dai shugabannin ƙungiyoyi sun ce ba za su amince da hakan ba.

    Shirin, wanda babban sakataren gwamnatin Senegal Al Aminou Lo ya fara ambatawa, ya janyo ce-ce-kuce tsakanin ma'aikata da ke cewa hakan zai kara ta'azzara halin matsi da su ke ciki da tsadar rayuwa.

    A cewar sa: domin daidaita lamurran ƙasar da manufofin da gwamnatin Senegal ta ke son cimmawa nan da shekarar 2050 '' za a aiwatar da sauye-sauye saboda rayuwar ƴan ƙasar ta dawo yadda ya kamata''.

    A cewar sa ''wasu lokutan mutane na ƙorafi kan albashi mai yawa a wasu hukumomi'' inda ya kara da cewa akwai buƙatar masu albashi mai yawa su yi wani ƙokari, ko na wucin-gadi ko kuma na dindindin domin rage albashinsu.

    Sai dai ya kuma tabbatar da cewa ''Ba za mu taɓa masu ƙananan albashi ba, saboda hakan ba zai yiwu ba''.

  4. An kafa kwamitin magance matsalar hantara tsakanin ɗalibai a makarantun Najeriya

    Ma'aikatar ilimi ta Najeriya ta kafa wani kwamiti mai mutane bakwai wanda zai lalubo hanyar magance matsalar hantara tsakanin ɗalibai a makarantun ƙasar.

    Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Boriowo Folashade, a ranar Litinin, ta ce an yi hakan ne domin "tabbatar da cewa makarantu sun zamo masu aminci ga ɗalibai.

    Sanarwar ta ƙara da cewa "ministan ilimi na Najeriya, Maruf Olatunji na ganin cewa akwai buƙatar duba matsalar hantara tsakanin ɗalibai da aka samu a baya domin a ɗauki mataki cikin gaggawa musamman idan aka yi la'akari da yadda lamarin ke cutar da tunanin ɗalibai."

    Hantara, matsala ce da ake samu a kai a kai a makarantun Najeriya, sai dai sau da dama lamarin kan wuce ba tare da ɗaukar matakan da suka dace ba.

  5. Ana buƙatar dala biliyan 50 domin sake gina Gaza

    An ƙiyasta cewa aikin sake gina Zirin Gaza da Gaɓar Yamma zai laƙume kuɗi sama da dala biliyan 50 kuma zai kwashe tsawon shekara 10.

    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da kuma Bankin Duniya ne suka yi wannan ƙiyasi.

    Ƙiyasin ya nuna cewa za a buƙaci dala biliyan 20 domin aikin sake gina yankin a shekara uku na farko.

    Kashi 60 cikin ɗari na gine-ginen da ke Gaza ne hare-haren Isra'ila suka lalata, lamarin da ya bar ɓaraguzai da yawansa ya kai tan miliyan 50.

  6. Ribadu ya miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 59 da aka yi garkuwa da su

    Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro (NSA) Malam Nuhu Ribadu ya miƙa wa gwamnatin jihar Kaduna mutane 59 da jam'ian tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane.

    Mutanen sun haɗa da maza 24, mata 28, da yara 6 da aka ceto daga wurare daban-daban a jihar Kaduna inda ɗaya daga ciki ke asibiti domin samun kulawa.

    Ribadu ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin dukkanin hukumomin tsaro karƙashin umurnin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    Ya kuma jinjina wa gwamnatin Jihar Kaduna na aiki tare da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin magance rashin tsaro a jihar.

    Da yake karɓar mutanen da aka ceto, shugaban ma'aikatan jihar Sani Kila, wanda ya wakilci gwamnan jihar Uba Sani ya gode wa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ganin cewa dukkan wanda aka yi garkuwa da su sun koma ga iyalansu.

  7. Ƴan tawayen M23 sun kashe yara a Bukavu - MDD

    Ofishin kare hakkin bil'adama na MDD ya ce ƴan tawayen M23 da Rwanda ke goyon baya sun kashe yara ya yinda zasu shiga Bukavu a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo.

    Kakakin hukumar ya ce yanayin ya ƙara tsanani, bayan samun rahotannin cin zarafi da tilasta ɗaukar aiki.

    Ƴan jarida da masu fafutuka na fuskantar barazana inda su ke neman kariya daga harin M23.

    A watan Janairu ƙungiyar yan tawayen ta karɓe yankuna da dama da suka haɗa da birnin Goma da ke Arewacin Lardin Kivu.

  8. An gurfanar da ma'aurata ƴan Birtaniya a gaban kotu a Iran

    Kafar yaɗa labaran Iran ta ce an gurfanar da ma'aurata ƴan Birtaniya a gaban kotu da laifin leƙen asiri, waɗanda ake tsare da su tun watan da ya gabata.

    An kama Craig da Lindsay Foreman a watan Janairu bayan sun tsallaka iyaka daga Pakistan a wani yawon zagaye duniya da mashin.

    A makon da ya gabata ne aka samu labarain tsare su.

    An ruwaito wani mai magana da yawun ɓangaren shari'a na Iran ya na cewa ma'auratan na kwasar bayanai domin kaiwa hukumomin leƙen asiri na ƙasashen yamma su na fakewa da yawon buɗe ido.

    Akwai ƴan ƙasashen Turai da dama da ake riƙe da su a Iran, ƙasar da a shekarun baya ta gudanar da musayar fursunoni da dama da ƙasashen yamma.

  9. An soma bincike kan musabbabin haɗarin jirgin sama a Canada

    Masu bincike na duba abin da ya jawo hatsarin jirgin sama na Delta Airlines a filin jirgi na birnin Toronto, lamarin da duk mutanen da ke ciki su 80 suka tsira da ransu.

    Har yanzu jami'ai ba su faɗi abin da ya janyo hatsarin ba, sai da ƙwararru na ganin cewa akwai yiwuwar yanayin sanyi da kuma iska mai ƙarfi na daga cikin dalilan.

    Mutane 18 sun ji rauni amma mutane kaɗan ne ake ganin sun samu munanan raunuka, wani abu da masu sharhi ke ganin abin al'ajabi ne.

    Wani ƙaramin yaro na daga cikin waɗanda su ka sami rauni, amma ya fara samun sauƙi kamar yadda asibitin yara na Toronto ya shaidawa kafar yaɗa labaran CBS, abokiyar hulɗar BBC.

    Fasinjoji 76 tare da ma'aikata 4 ke cikin jirgin samfurin CRJ900 mai shekaru 16, wanda kamfanin Bombardier na Canada su ka haɗa.

  10. Hamas za ta miƙa wa Isra'ila gawar mutane huɗu

    Ƙungiyar Hamas ta bayyana cewa a ranar Alhamis za ta miƙa wa Isra'ila gawar Isra'ilawa huɗu da suka mutu a lokacin da take garkuwa da su.

    Haka nan ƙungiyar ta ce za ta saki sauran mutane shidda da take garkuwa da su waɗanda ke raye a ranar Asabar.

    Shugaban Hamas, Khalil al-Hayya ya ce mutanen shida da za a saki ranar Asabar sun haɗa da Hisham al-Sayed da Avera Mengistu, waɗanda ake riƙe da su a Gaza tsawon shekara 10.

    Cikin gawarwakin da za a miƙa a ranar Alhamis sun haɗa da iyalan Bibas.

  11. Dole a guji tafka kuskure a zaman sulhu - Zelensky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce shi da shugaban Turkiyya, Recep Erdogan na " tattaunawa kan hanyoyin samar da zaman lafiya a duniya.da manufar kawo ƙarshen wannan yaƙi."

    Zelensky wanda ke zaune kusa da shugaban na Turkiyya yayin wani taron manema labarai ya ce suna yin duba ne ga hanyoyin warware matsalolin ta fuskoki daban-daban inda ya ƙara da cewa "duk wasu tattaunawa da za a yi na samar da zaman lafiya bai kamata a yi su ba tare da waɗanɗa al'amarin ya shafa ba."

    Domin ɗorewar zaman lafiya, Zalensky ya ce "yana da muhimmanci a guji yin kowane irin kuskure."

    Dole ne a samu wakilcin dukkannin ɓangarorin a kan teburin wato ya zama akwai Amurka da Turai da Ukraine, in ji Zelensky.

  12. Amurka da Rasha sun amince su ci gaba da tattaunawa kan yaƙin Ukraine

    Amurka da Rasha sun amince za su ci gaba da tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙi a Ukraine.

    An cim ma matsaya ne yayin taro tsakanin wakilan ƙasashen a Saudiyya, karon farko bayan mamayar Rasha a Ukraine shekara uku da suka gaabata.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce sun amince za su sanya wakilai daban-daban a tattaunawar.

    Taron wanda aka gudanar a birnin Riyadh, ya fusata Ukraine da ƙawayenta na Turai waɗanda aka ware a tattaunawar.

    Wakilin BBC ya ce Amurkawa na kallon wannan a matsayin matakin farko da za a fahimci ko da gaske Rasha take game da tattaunawar sulhu.

    A nata ɓangaren, Rasha ta yi wa ganawar kallon buɗe sabon babin gyaran dangantakarta da Amurka.

    Marco Rubio, sakataren harkokin wajen Amurka, ya ƙi amsa tambayar da wakilin BBC ya yi masa kafin fara taron, cewa ko Amurka ta tsame Ukraine ne daga tattaunawar?

  13. 'Yansandan Najeriya na neman mawaƙi Portable ruwa a jallo

    Rundunar sojin Najeriya reshen jihar Ogun ta ayyana mawaƙi Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zargin sa da hannu a kai wa ofisoshin gwamnati hari.

    A cewar wata sanarwa da runudnar ta fitar ranar Litinin, ana zargin Portable ne da jagorantar wani gungun 'yandaba don kai hari kan jami'an ma'aikatar tsare birane ta jihar Ogun lokacin da suka je aiki yankin Ota na jihar.

    Sanarwar ta ce an ga mahaifin Portable a wani wurin cin abinci da ke kusa da wurin, kuma ya faɗa wa mutane cewa ɗan nasa ba shi wurin.

    "Sai dai jim kaɗan mawaƙin ya bayyana a wurin ɗauke da bindiga da sauran makamai kuma ya jagoranci kai hari kan jami'an hukumar," a cewar 'yansanda.

    Rundunar ta ƙara da cewa ta kama tara daga cikin maharan, yayin da Portable ya gudu kuma yake ci gaba da ɓuya.

  14. Labarai da dumi-dumi, An kammala tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka a Saudiyya

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta faɗa wa manema labarai cewa an kammala tattaunawa tsakaninsu da wakilan Rasha a Saudiyya.

    Sun gana sama da awa huɗu a birnin Riyadh, har da ɗan hutun cin abinci.

  15. RSF za ta haɗa kai da sauran ƙungiyoyi don kafa gwamnatin tawaye a Sudan

    Ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF) mai rikici da gwamnatin Sudan ta ce za ta ƙulla yarjejeniya da wasu jam'iyyun siyasa ƙawayenta a Nairobi babban birnin Kenya ranar Juma'a mai zuwa.

    Ƙungiyoyin sun taru ne domin rattaba hannu kan "daftarin gudanar da gwamnatin haɗin kai da zaman lafiya", wadda suka ce za ta share fagen kafa gwamnatin tawaye a yankunan da RSF ke riƙe da su a Sudan.

    Mai bai wa RSF shawara kan harkokin siyasa Basha Tabiq ya wallafa a shafinsa na X cewa sun fara yunƙurin ne tun 18 ga watan Fabrairu, kuma za su ci gaba har tsawon kwana biyu.

    Gamayyar ta ƙunshi ƙungiyoyin fararen hula, da na siyasa, da masu ɗauke da makamai da ke son "kafa gwamnatin zaman lafiya da haɗin kai" a yankunan da ke ƙarƙashin ikon RSF.

    Daga ciinsu akwai Sudan Revolutionary Front (SRF), ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka tafka yaƙin Darfur, da kuma wasu da suka saka hannu wajen hamɓarar da gwamnatin farar hula a 2021.

  16. Hauhawar farashi a Najeriya ta koma 24.48 a sabon tsari - NBS

    Hukumar ƙididdiga ta ƙasa a Najeriya ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma 24.48 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.

    Wannan ne karon farko da National Bureau of Statistics (NBS) da fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.

    Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

    Kafofin yaɗa labarai na Najeriya sun ruwaito shugaan hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, na faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda "daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya".

    Ya ce karo na ƙarshe da Najeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.

    Hakan na nufin yanzu za a dinga kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka dinga amfani da ita a baya.

    "A sabon tsarin, ba matso da alƙaluman kusa da halin da ake ciki kawai muka yi ba, mun kuma ƙaddamar da sabuwar hanyar tattara bayanai don inganta yadda muke adana su da kuma sahihancinsu," in ji shi.

  17. Putin zai iya tattaunawa da Zelensky idan akwai buƙata - Kremlin

    Fadar Kremlin ta gwamnatin Rasha ta ce Shugaba Putin a shirye yake domin ya tattauna da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky "idan ya zama dole".

    Mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov, ya faɗa wa manema labarai cewa: "Putin da kansa ya ce zai tattauna da Zelensky idan hakan ya zama dole.

    "Amma kuma akwai buƙaytar tattaunawa game da yadda za a yi hakan ganin cewa akwai maganar halaccin shugabancin na Zelensky," a cewarsa.

    Putin ya sha yin magana game da halaccin mulkin Zelensky, wanda wa'adin mulkinsa ya ƙare a watan Mayun da ya gabata. Jami'n Ukraine na cewa mamayar Rasha da kuma dokar soja da aka saka sun sa ba zai yiwu a iya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ba.

  18. Rasha da Amurka sun fara tattaunawa kan yaƙin Ukraine

    An fara tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka game da yaƙin Ukraine a Saudiyya.

    Wakilan Amurka sun jaddada cewa tattaunawar ta yau ba ta da niyyar fara maganar sasantawa, kawai dai za ta duba ne idan har "da gaske" Rashar take wajen kawo ƙarshen yaƙin.

    Rasha ta ce abin da ta saka a gaba shi ne kyautata alaƙa da Amurka.

    Babu tabbaci game da tsawon lokacin da za a ɗauka ana tattaunawar a asirce, amma dai za mu ci gaba da kawo muku abubuwan da muka sani yayin da suke ci gaba da ganawa.

  19. Dattijo Edwin Clark ya rasu yana da shekara 97

    Dattijo a yankin Neja Delta da ke kudancin Najeriya kuma tsohon kwamashina, Edwin Clark, ya rasu yana da shekara 97 da haihuwa.

    A cewar wata sanarwa da kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito daga iyalinsa, tsohon shugaban ƙungiyar rajin kare yankin Neja Delta ta Pan Niger Delta Forum (PANDEF) ya rasu ranar Litinin da dare.

    "Mutumin da aka haifa a Kiagbodo da ke yankin Ijaw na jihar Delta, Clark ya yi aiki tare da gwamnan mulkin soja Samuel Ogbemudia, da Janar Yakubu Gowon tsakanin shekarun 1966 zuwa 1975," a cewar sanarwar.

    Ya riƙe muƙamin kwamashinan yaɗa labarai a shekarar 1975.

  20. Saudiyya ta bai wa Najeriya kyautar tan 100 na dabino

    Saudiyya ta bai wa gwamnatin Najeriya kyautar tan 100 na dabino a matsayin tallafin da ta saba bayarwa duk shekara.

    Wata sanarwa da ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya ya fitar ranar Litinin ta ce tallafin kyauta ce daga Sarki Salman na Saudiyya.

    Sanarwar ta ƙara da cewa jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Al-Ghamdi, shi ne ya jagoranci miƙa kyautar, wadda aka bayar ta hannun ƙungiyar King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre (KSrelief) domin taimaka wa talakawa.

    "Jakada Al-Ghamdi ya yi bayanin cewa a wannan shekarar an ba wa Abuja tan 50, Kano ma tan 50," in ji sanarwar.