Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/07/2027

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/07/2027

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Lahadi.

    Za mu kawo wasu rahotonnin gobe da safe.

    Umar Mikail ne ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnan Katsina Dikko Radda ya ce a Daura za a yi jana'izar Buhari

    Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce iyalan Muhammadu Buhari sun yanke shawarar yi masa jana'iza a garin Daura mahaifarsa da ke jihar ta Katsina.

    Da yake magana da kafar yaɗa labarai ta DW Hausa, Dikko Radda ya ce yana birnin na Landan ya samu labarin rasuwar inda ya je duba shi.

    "Na zo ranar Juma'a domin duba shi, muna shirin dawowa gida kuma sai ga labarin rasuwar tasa," in ji shi.

    "Yanzu muka rabu da iyalansa a asibitin da ya rasu kuma an yi ittifaƙi za a kai shi gida Daura a jihar Katsina domin yi masa sutura. Insha Allau za su baro Ingila da safe.

    "Muna sa ran gobe Litinin za a yi jana'izar tasa saboda muna sa ran mataimakin shugaban ƙasa zai iso Ingila cikin dare, su taho da mamaci da safe."

    Fadar shugaban Najeriya ta ce Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya je Landan domin raka gawar Buhari zuwa gida Najeriya.

  3. Buhari ya yi rayuwa maras ƙyale-ƙyale - Tajudeen Abbas

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Tajudeen Abba ya miƙa ta'aziyyar mutuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai siffanta da "mutumin da ba shi aikata cin hanci".

    Tajudeen ya ce Buhari ya yi rayuwa "mai sauƙi maras ƙyale-ƙyale, mai wadatar zuci wadda kuma ta sama masa girmamawa da amincewa a faɗin ƙasa".

    Buhari ya rasu yau Lahadi a birnin Landan bayan fama da jinya.

    Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce za a yi jana'izarsa a garin Daura mahaifarsa.

  4. Buhari: Najeriya ta yi rashin dattijo, in ji Atiku Abubakar

    Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin "mutumin da ya ƙarar da rayuwarsa wajen nuna kishin ƙasa da haɗin kan ƙasarmu".

    "Najeriya ta yi rashin dattijo wanda ya ɗauki ɗawainiyar shugabanci a lokutan fargaba da na nasara, wanda kuma ba za a manta da sadaukarwarsa ba a tsawon lokaci," kamar yadda Atiku ya bayyana cikin wata sanarwa a shafukan sada zumunta.

    Ya kuma yi addu'ar "Allah ya yafe masa kurakuransa kuma ya ba shi Aljannar Firdausi", sannan ya miƙa ta'aziyya ga iyalansa.

    Atiku ya yi hamayya da Buhari a takarar shugabancin Najeriya a lokuta daban-daban, ciki har da na 2019 lokacin da Buhari ke neman wa'adi na biyu.

  5. Za a dinga tuna Buhari a matsayin tsayayyen shugaba - Tarayyar Afirka

    Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta aike da saƙon ta'aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari ga iyalansa da gwamnatin Najeriya bayan mutuwar tsohon shugaban Najeriya a yau Lahadi.

    "Za a dinga tuna Shugaba Buhari a matsayin mutum mai ɗabi'u na gari kuma tsayayyen shugaba, wanda ya hidimta wa Najeriya da alfahari," a cewar shugaban tarayyar ta African Union Mahmoud Ali Youssouf cikin wata sanarwa.

    Ya ƙarra da cewa "a baki ɗayan mulkinsa, ya kasance mai kishin Afirka, mai kishin haɗin kai da shugabanci na gari".

  6. Labarin mutuwar Buhari ya kaɗa ni sosai - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da "ɗan kishin ƙasa, soja, kuma dattijon ƙasa wanda ba za a taɓa mantawa da sadaukarwar da ya yi ba".

    Cikin wata sanarwa a yau Lahadi, Tinubu ya ce ya "kaɗu sosai da jin labarin mutuwar", yana mai cewa "hidimar ƙasa, da alfarma, da sadaukar da kai ga haɗin kai da cigaban ƙasa" ne za a ci gaba da tunawa da tsohon shugaban da su.

    Buhari ya rasu a yau Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan yana da shekara 82. Fadar shugaban ƙasa ta ce ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya.

    Nan gaba Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai je Landan ɗin domin yi wa gawar Buhari rakiya zuwa Najeriya, inda za a yi jana'izarsa.

    Shugaba Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa na gaggawa a yau Lahadi domin girmama marigayin.

  7. Hare-haren Isra'ila sun ji wa Shugaban Iran Pezeshkian rauni a lokacin yaƙi

    Wani rahoto ya ce hare-haren Isra'ila sun ji wa Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ƙaramin rauni yayin yaƙin da suka gwabza na kwana 12 a watan Yuni.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars mai alaƙa da rundunar juyin juya hali ta Iran ya ce a ranar 16 ga watan Yuni ne bamabamai shida suka faɗa kan ƙofofin shida da fita na wani gidan ƙasa da ke Tehran, inda Pezeshkian ke halartar taroin gaggawa a majalisar ƙoli ta ƙasar.

    Rahoton ya ce shugaban ƙasar ya ji rauni a ƙafarsa yayin da suka yi ƙoƙarin ficewa daga ginin ta wata hanyar gaggawa.

    Zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba game da batun.

  8. ADC ta buƙaci Tinubu ya yi wa ƴan Najeriya bayanin inda ya tsaya bayan taron BRICS

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban Ƙasar Boa Tinubu bisa abin da ta bayyana "ɓacewar kwana biyar ba tare da bayani ba" bayan ya halarci taron BRICS na 2025 a ƙasar Brazil.

    Tinubu wanda ya halarci taron a birnin Rio de Janeiro da ke Brazil, ya koma ƙasar a ranar Lahadi, kwana biyar da kammala taron.

    A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce babu wani bayani a hukumance da aka fitar game da kwana biyar ɗin da aka yi shugaban bai koma ba bayan kammala taron.

    "ADC na ƙalubalantar Bola Tinubu ya bayyana wa ƴan Najeriya ina ya tsaya ya yi kwana biyar bayan kammala taron BRICS a Brazil," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    "Bayan kammala taron a ranar Litinin 7 ga watan Yuli, sauran shugabannin ƙasashen da suka halarta sun koma ƙasashensu, inda suka yi wa ƴan ƙasarsu bayanin abin da ya faru a can, sannan suka koma bakin aiki.

    "Amma shugaban ƙasarmu fa? sai a ranar Lahadi 13 ga watan Yuli muka gan shi, kuma ba tare da wani bayanin me ya sa ya yi jinkirin dawowa ba."

    Bolaji ya ce kwana biyar na da matuƙar muhimmancin ganin yadda Najeriya ke fama da matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.

  9. Tarayyar Turai za ta yi jinkirin mayar da martani ga Amurka kan haraji

    Shugabar ƙungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce za su yi jinkirin mayar da martanin lafta wa Amurka haraji.

    Asali ƙungiyar ta ayyana ƙudurinta na mayar da martani kan lafta mata harajin kashi 30 kan kayayyakin ƙasashen tarayyar, wanda ta ƙuduri aniyar sanarwa a ranar Talata.

    Amurka ta ƙaƙaba harajin kashi 30 ne nan ƙarafa da ake shiga da su Amurka daga ƙasashen turai.

    Ursula ta ce ƙasashen turai na tattaunawa domin samun maslahar alaƙar kasuwanci da Amurka, duk kuwa da barazanar Trump ta lafta musu harajin.

    An dai fara kiraye-kirayen ƙasashen turai nu mayar da martani ne domin nuna ƙwanji ga Amurka.

    Ministar kuɗi ta Jamus ta ce lallai akwai buƙatar ƙasashen turai su ɗauki mataki.

    Ƙasashen dai za su sake zama a gobe Litinin sake tattauna mataki na gaba da za su ɗauka.

  10. Ma'aikatan Najeriya adalci suke buƙata ba barazana ba - Atiku

    Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya, Atiku Abubakar ya zargi shugaban ƙasar, Bola Tinubu da yunƙurin tauye haƙƙin ma'aikatan ƙasar, tare da hana su bayyana halin ƙuncin rayuwa da suke ciki.

    Atiku ya bayyana cewa janye tallafin man fetur da Tinubu ya yi a ranar rantsar da shi ne ya haifar a matsalar tattalin arziki a ƙasar, wanda a cewarsa ya jefa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar cikin yunwa da rashin tabbas.

    Ya ce domin Tinubu ya yi yunƙurin rage raɗaɗin da ƴankasar ke ciki ne ta hanyar ɗaukar alƙawarin ƙara albashi ga ma'aikatan ƙasar, "amma alƙawarin, kamar sauran alƙawura da ya ɗauka, sai da aka yi wata 10 kafin aka samu matsaya a sabon mafi ƙarancin albashi."

    A cewarsa, ya kamata ne gwamnati ta biya bashin cikon albashin na wata goma, "amma sai na wata shida kawai gwamnatin ta biya. Ke na ma'aikatan suna bin bashin cikon albashi na wata huɗu.

    Atiku ya zargi gwamnatin da amfani da ƙarfi wajen "hana furta albarkacin baki maimakon neman matsaya ta hanyar tattaunawa."

    "Mako biyu da suka gabata an kama tare da tsare Andrewa Uche Emelieze saboda ya yi yunƙurin shirya zanga-zangar lumana. Cigaba da tsare ba ƙaramin cin fuska ba ne ga dimokuraɗiyyar Najeriya, har da cin fuska ga dukkan ma'aikatan ƙasar.

    "Ya kamata a fahimci cewa ba a isa a doki ma'aikatan Najeriya sannan a hana su kuka ba, ballantana a musu barazana ko a manta da buƙatunsu. Lallai matsain tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya gaskiya ne, kuma yunwa na ƙara katutu, wanda hakan ya sa gwamnati matakan gyara ya kamata ta ɗauka, ba daƙile masu magana ba."

  11. Ko kun san me ya sa ake gulma?

    Gulma ka iya ɓata maka suna. Za ta iya bayyana halayyarka. Aba ce mai daɗi a wajen wasu. Amma kuma a wajen wasu mutanen da dama, ɗabi'a ce maras kyau - ko ma a ce laifi ce.

    Gulma wata ɗabi'a ce da masana halayyar ɗan'Adam suka lura cewa al'ummomi da dama suna yint, kama daga yankuna na karkara da birane da ma ƙauyukan ƙayau.

    "Kusan kowa na yin gulma idan har damar yinta ta samu,'' in ji Dr Nicole Hagen Hess, masaniyar halayyar ɗan'Adam da ke Jami'ar Jihar Washington a Amurka.

    Idan aka yi maganar gulma abin da zai zo mana a rai shi ne, maganar wani a bayansa da nufin ɓata shi. Ko kuma a ce cin naman wani kamar yadda ake kira a wata al'adar.

  12. Amurka ta janye tuhumar likita da ɓartana riga-kafin Covid-19

    Atoni Janar ta Amurka, Pam Bondi ta ce ta bayar da umarnin a janye tuhume-tuhumen da ake yi wa wani likita da ke fuskantar shari'a kan zargin lalata allurar riga-kafin cutar korona na dubban daloli da bayar da takardar shaidar bogi na rigakafin ga masu sha'awar biya.

    Ma'aikatar shari'a ce ta tuhumi Dokta Micheal Kirk Moore a lokacin gwamnatin Shugaba Biden yayin da aka soma shari'arsa a wannan makon a Utah.

    Wakilin BBC ya ce Ms Bondi ta ce Dokta Moore ya bai wa mutane zaɓi ne lokacin da gwamnati ta ƙi yin hakan - a don haka bai kamata ya fuskanci barazanar ɗauri ba.

    Annobar korona dai ta haifar da rarrabuwar kai a Amurka tsakanin masu goyon bayan rigakafinta da waɗanda suke ganin matakan da aka ɗauka na taƙaita yaɗuwar cutar sun ci karo da ƴancin jama'a.

  13. 'Harin Isra'ila ya kashe ƙananan yara masu ɗibar ruwa a Gaza'

    Hukumar bayar da agajin gaggawa a Gaza ta ce aƙalla mutum 10, ciki har da ƙananan yara guda shida ne suka rasu a sanadiyar harin da Isra'ila ta kai ta sama a Gaza a safiyar Lahadi.

    An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin Nuseirat's al-Awda, inda wani likita ya ƙara da cewa sun yi jinyar wasu mutum 16, ciki har da ƙananan yara guda bakwai.

    Wani ganau ya ce jirgi mara matuƙi ne ya harba makami mai linzami a kan dandazon mutanen da suka yi layi riƙe da jarkunansu domin ɗibar ruwa daga wata tankar ruwa a sansanin ƴangudun hijira na al-Nuseirat.

    Har zuwa haɗa wannan rahoton, rundunar tsaron Isra'ila ba ta ce komai ba kan batun.

    Wani faifan bidiyo da BBC ba ta tantance ba ya nuna ƙananan yara jina-jina, da gawarwakin wasu, wasu kuma suna ta ihu, sannan wasu suka zo daga bisani suna kwashe mutanen zuwa asibiti a motoci da amalanke.

    Isra'ila ta fara kai hare-hare ne a Gaza tun bayan harin Hamas a ƙasar a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda ƴan Hamas ɗin suka kashe 1,200, sannan suka yi garkuwa da wasu 251.

    Zuwa yanzu Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 57,882 a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiyar yanki ta bayyana.

    Haka kuma an tarwatsa sama da kashi 90 na gidajen zirin, sannan an lalata asibitoci da cibiyoyin ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa, wanda hakan ye jefa yankin cikin ƙarancin abinci da magani da man fetur.

  14. Ƴantawayen ADF sun kashe gomman mutane a Congo

    An ba da rahoton kisan mutane da dama a ƴan kwanakin da suka gabata da ƴantawayen ADF na Uganda suka yi a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

    Gidan rediyon Okapi da Majalisar Ɗinkin Duniya ke tafiyar da shi ya ruwaito cewa hare-haren da aka alaƙanta da mayaƙan na ADF sun yi ajalin mutum sittin da shida a lardunan arewacin Kivu da Ituri.

    Lamarin na zuwa ne sakamakon samamen haɗin gwiwa da sojojin Congo da Uganda suka kai kan sansanonin ADF a wannan watan.

    Masu sharhi sun ce mayaƙan na amfani da tashin hankalin da ke faruwa a gabashin Congo domin ƙarfafa ayyukansu na haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

  15. Dakarun RSF da sojojin Sudan na cigaba da gwabza yaƙi

    Ana ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a birnin El Fasher na Sudan inda sojoji ke ƙoƙarin fatattakar ƴantawayen RSF.

    Bayan rushewar ƙoƙarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi na ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, dakarun RSF sun ce sun nausa cikin birnin ta kudanci da kuma yammaci.

    A cewar wakilin BBC, RSF sun yi iƙirarin ƙwace iko da hedikwatar ƴansanda da wata babbar kasuwar shanu.

    Sai dai sojojin Sudan sun ce sun daƙile hare-haren mayaƙan na tsawon kwana uku kuma har yanzu suke da iko da hedikwatar ƴansandan.

    El Fasher shi ne babban birni da ya rage a Darfur da har yanzu yake ƙarƙashin ikon sojoji.

  16. Shugabar Mexico ta ce za su samu maslaha da Trump kan haraji

    Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum ta ce tana da yaƙinin za a cimma yarjejeniyar kasuwanci domin kawar da sabuwar barazar Donald Trump ta ƙaƙaba harajin kashi talatin cikin ɗari kan kayayyakin da Mexico ke shigar da su Amurka daga watan Agusta.

    Gwamnatin Trump ta gabatar da shawarar ƙaƙaba sabbin haraji kan ƙasashe ashirin da biyar har da Tarayyar Turai.

    Cikin wata wasiƙa zuwa ga Shugaba Sheinbaum, Mista Trump ya ce Mexico ba ta yi wani abin a zo a gani ba na hana Arewacin Amurka zama abin da ya kira dandalin safarar miyagun ƙwayoyi.

  17. Ana buƙatar jam'iyyar hamayya mai ƙarfi a dimokuraɗiyya - Shugaban ma'aikatan Tinubu

    Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ƴansiyasa a jam'iyyar ADC alheri ce ga siyasar Najeriya, wanda a cewarsa hakan zai taimaka waje hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam'iyyar ƙwaya ɗaya tal.

    Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Sai dai tsohon shugaban majalisar wakilan ƙasar ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani.

    "Muna maraba da samar da haɗakar. Ai ba wannan ba ne karo na farko da aka samu haɗakar ƴansiyasar a wannan ƙasar tamu," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa "a dimokuraɗiyya ana buƙatar hamayya mai ƙarfi, domin idan babu hamayya mai ƙarfi, za mu iya faɗawa siyasar jam'iyyar ɗaya," in ji shi.

    A Najeriya dai fitatun ƴan jam'iyyun hamayya irin su Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu ne suka haɗu a jam'iyyar ADC domin fuskantar zaɓen 2027, inda suke fata za su kayar da Bola Tinubu.

  18. Koriya ta Arewa za ta ba Rasha ƙarin sojoji domin yaƙin Ukraine

    Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi wa Rasha tayin cikakken goyon bayan ƙasarsa a yaƙin Ukraine.

    Ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a Ukraine.

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta wallafa wani bidiyo na ganawar da aka yi a birnin Wonsan.

    Manazarta sun ce wataƙila Koriya ta Arewa tana shirin tura ƙarin dakaru domin taimaka wa Rasha a yaƙin da take a Ukraine.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyarmu shafinmu na BBC Hausa muna muku lale a yau ranar Lahadi, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya a wannan shafin namu da muke kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu