Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 19/11/2024

Taƙaitattu

Ukraine ta harba makami mai cin dogon zango zuwa Rasha - Kremlin

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Annur Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. An buƙaci ƙasashe su ƙara ƙaimi wurin yaƙi da sauyin yanayi

    Shugaban Brazil ya yi kira ga shugabannin ƙasashen G20 da ke taro a birnin Rio de Janeiro da su ƙara ƙaimi don rage yawan hayaƙi mai gurɓata muhalli da ake fitarwa.

    Shugaba Lula ya shaida wa taron cewa ba zai yiwu a bar batun magance matsalar ɗumamar yanayi har zuwa baɗi ba da za a yi taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi a Brazil.

    Shugaba Biden ya ce sauyin yanayi na tattare da gagarumar barazana ga bil adama.

    Shugabannin G20 sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa amma ba su yi magana ƙarara game da buƙatar daina amfani da makamashi mai ɗumama yanayi ba.

    Shugaban na Brazil ya ce taron COP 25 zai zama dama ta ƙarshe da za a kare ɓarnar da ba za a iya gyarawa ba ga duniya.

  2. Iran ta saki matar da aka tsare bisa laifin bayyana tsiraici

    Wata ƴar ƙasar Iran ba za ta fuskanci hukunci ba bayan ta tube rigarta a wata zanga-zangar adawa da dokar sanya hijabi a wata jami'a a birnin Tehran.

    A farkon watan Nuwamba, wani bidiyo ya ɓullo a shafukan sada zumunta wanda ya nuna lokacin da matar, mai suna Ahoo Daryaei, ta cire rigarta a harabar jami'ar.

    Mai magana da yawun ma'aikatar shari'a ta Iran ya ce matar ta yi jinya a asibiti kuma ta koma ga danginta.

    Kamen nata dai ya janyo suka daga ƙasashen duniya, inda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International na daga cikin waɗanda suka yi kira da a sake ta ba tare da wani sharaɗi ba.

  3. An kama ɗan gimbiyar Norway bisa zargin fyaɗe

    An kama yaron gimbiya mai jiran gadon sarautar Norway Mette-Marit, wanda tuni ya ke fuskantar tuhumar tayar da hatsaniya a wani bincike da ake gudanarwa, bisa zargin aikata fyaɗe.

    Marius Borg Høiby, mai shekaru 27, shi ne ɗan matar magajin sarautar Norway, Yarima Haakon, amma ba shi da mukamin sarauta ko wani aiki a hukumance.

    A ranar Talata, ƴansandan Norway sun ce an tuhumi Mista Høiby da laifin yin jima'i da "wani wanda ba ya cikin hayyacinsa ko kuma saboda wasu dalilai ya kasa hana afkuwar lamarin".

    Mista Høiby, wanda rahotanni suka ce ya musanta zargin fyaɗe, yana fuskantar tuhume-tuhume da dama kan laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa kan wasu mutane huɗu.

    Rahotannin cikin gida sun ce fadar ƙasar Norway ta ƙi cewa komai kan batun kama Mista Høiby. Ƴan sanda sun kama Mista Høiby ranar Litinin a cikin wata mota, tare da wata da ake zargin ya taɓa cimma zarafi a baya.

    A watannin baya an tuhumi Mista Høiby da laifin cin zarafi ga tsoffin ƴan matansa Juliane Snekkestad da Nora Haukland, da kuma yin barazana ga rayuwar wani mutum.

  4. Netanyahu ya ce Isra'ila ta kai hari kan wani ɓangaren shirin nukiliyar Iran

    Firaministan Isra'ila ya ce ƙasarsa ta kai hari kan wani ɓangare na shirin nukiliyar Iran a watan da ya gabata, duk da buƙatar da Amurka ta yi na kada ta yi hakan a hare-haren da ta kai a matsayin martani kan harin makami mai linzami.

    “Ba siiri ba ne. Abu ne da aka wallafa,” Benjamin Netanyahu ya fadawa majalisar dokokin Isra’ila. "Akwai wani yanki na musamman a cikin shirinsu na nukiliya da aka kai wa hari."

    Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daga Iran, amma a baya ta ce harin da Isra'ila ta kai ya yi takƙaitaccen ɓarna.

    Ita ma Iran ta dage kan cewa ba ta ƙera makaman nukiliya, duk da cewa shaidun da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta tattara sun nuna cewa har zuwa shekara ta 2003 tana gudanar da ayyukan da suka shafi kera bama-bamai.

    Hukumar ta ce har yanzu Iran ba ta amsa wasu fitattun tambayoyi da suka shafi ayyukanta na nukiliya ba.

  5. An kama mutane biyar kan yunƙurin kashe shugaban Brazil

    Ƴan sanda a Brazil sun kama mutane biyar -- huɗu daga cikinsu sojoji da aka yi masu horo na musamman -- kan zargin yunƙurin kashe shugaba Lula jim kaɗan kafin rantsar da shi shekaru biyu da suka gabata.

    Makircin da ake zargin ya kunshi kitsa kashe mataimakin shugaban ƙasar mai jiran gado, Geraldo Alckmin, da kuma alƙalin kotun ƙoli ƙasar.

    Za a kafa wani ofishin kula da rikice-rikice na hukumomi don magance matsalolin da ke ɓullowa sakamakon wannan yunƙurin juyin mulkin.

    Shugaba Lula ya doke Jair Bolsonaro a zaɓen da aka gwabza. Dubban magoya bayan Mista Bolsonaro ne suka mamaye gine-ginen gwamnati a Brasilia a wani yunƙuri na tayar da ƙayar baya mako guda bayan Lula ya hau mulki.

  6. Gwamnan Jigawa ya mayar da Kwamashina Dalladi Sankara kan muƙaminsa

    Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamashinansa na ayyuka na musamman Auwalu Dalladi Sankara.

    Cikin wata sanarwa da fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, ta ce Gwamna Umar Namadi ya janye dakatarwar ce nan take.

    "Idan ba a manta ba, an dakatar da kwamashinan nan ne saboda zarginsa da ake yi da hannu a wani lamari da aka kai ƙara hukumar Hisba ta jihar Kano, kamar yadda Sakataren Gwamnati Bala Ibrahim bayyana," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya ɗauki matakin ne wata kotun Shari'ar Musulunci a Kano ta wanke shi daga zargin.

    Bayanai sun nuna cewa mijin matar da ake zargin kwamashinan ya yi mu'amala da ita ne ya kai ƙara kotun bayan Hisba ta gaza sasanta batun.

  7. Tinubu ya nemi majalisa ta amince masa ciyo bashin naira tiriliyan 1.7

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi majalisar dokokin ƙasar ta amince masa karɓo bashin naira tiriliyan 1.767 daga ƙasashen waje domin cike gurbin kasafin kuɗi na 2024.

    Tinubu ya nemi hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, wadda kuma suka karanta ta a yau Talata.

    Kuɗin da majalisar zartarwa ta amince da su, za a yi amfani da tiriliyan 9.7 daga ciki wajen cike giɓin kasafin na 2024, idan majalisar ta amince.

    Haka nan, Tinubu ya miƙa daftarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 zuwa 2027 ga 'yanmajalisar, da kuma ƙudirin kafa dokar shirin kyautata rayuwar jama'a domin mayar da rajistar 'yan ƙasa a matsayin wadda za a dinga amfani da ita wajen kyautata rayuwar 'yan Najeriya.

    A makon da ya wuce ne gwamnatin ta ce za ta ciyo bashin ƙasashen waje da ya kai dala biliyan biyu domin yin amfani da su a ɓangarori daban-daban.

  8. Sojojin Sudan sun yi fatali da ƙudurin Birtaniya na dakatar da yaƙin ƙasar

    Rundunar sojin Sudan ta yi maraba da daƙile wani sabon ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya mai neman kawo ƙarshen rikicin da ake yi a ƙasar.

    Gwamnatin sojin ta Sudan ta zargi Birtaniya wadda ta gabatar da ƙudurin a kwamitin tsaro na majalisar, da shiga sharo ba shanu a cikin harkokinta Sudan ɗin na cikin gida.

    Gabatar da ƙudurin ke da wuya a jiya Litinin a gaban kwamitin, sai Rasha ta hau kujerar-na-ƙi a kanshi.

    A wannan makon ake sa ran jakadan musamman na Amurka a Sudan Tom Perriello zai yi bayani bayan da ya ziyarci ƙasar ta Sudan da kuma maƙwabciyarta Djibouti domin tattaunawa.

  9. Rasha ta kawo tsaiko kan yunƙurin tsagaita wuta a Sudan

    A wani mataki wanda Burtaniya da Amurka da yi Allah-wadai, Rasha ta hau kujerar na-ƙi kan yunkurin Majalisar Ɗinkin Duniya na tabbatar da an tsagaita wuta a Sudan.

    Sakataren harkokin wajen Burtaniya, David Lammy ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana matakin na Rasha a matsayin "rashin hankali."

    Sai dai ita ma Rasha a nata ɓangaren ta zargi Burtaniya da shiga yaƙin na Sudan ba tare da sanin ƙasar ba.

    Ana tunanin yaƙin na Sudan wanda zuwa yanzu aka ɗauki wata 19 ana fafatawa ya ci dubban mutane, sannan sama da mutum miliyan 11 suka rabu da muhallansu tun bayan ɓarkewar yaƙin a watan Afrilun bara tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.

    Yunƙurin samar da maslahar, wanda Burtaniya da Saliyo suka gabatar, ya buƙaci kowane ɓangare ya mayar da kubensa, sannan a fara tattaunawa kan yadda za a tsagaita wutar, sannan suka yi kira ga ɓangarorin sojin da RSF da su girmama yarjejeniyar da aka yi a baya na daina kai hari kan fararen hula.

    Bayan Rasha, dukkan sauran ƙasashe 14 da ke cikin majalisar tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince da daftarin, amma kuma kujerar na-ƙin da Rasha ta hau na nufin ƙudurin bai tabbata ba.

  10. Pakistan za ta hana amfani da hanyoyin samun intanet na VPN

    'Yan siyasa a Pakistan na tuhumar shirin hukumar kula da harkokin sadarwar ƙasar na hana amfani da manhajojin shiga intanet na VPN marassa rijista a ƙarshen watannan na Nuwamba.

    Yawanci ana amfani da waɗannan manhajoji ne wajen kauce wa tsaro da sanya ido da hukumomi ke yi a intanet.

    Kuma a yanzu ana samun karuwar amfan da waɗannan hanyoyi a ƙasr ta Pakistan.

    Masu sukan shirin haramcin suna zargin hukumomi na yunƙurin hana magoya bayan tsohon firaministan ƙasar da aka ɗaure Imran Khan, daga sukar gwamnati ko sojoji a shafukna da aka haramta amfani da su kamar X.

    Miliyoyin 'yan Pakistan ba sa iya shiga shafin X tun watan Fabarairu na 2023, lokacin da gwamnati ta toshe shafin kafin zaɓen majalisar dokoki, sai kawai ta hanyar NPN ake samun shafin

    Hukuma ta ce dole ne duk masu amfani da hanyoyin na V-P-N su yi rijista zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, kuma a yanzu na masu zaman kansu ne kawai waɗanda ake amfani da su a harkokin kasuwanci aka karɓa.

    Babbar majalisar malaman addini ta Pakistan ta ayyana amfani da hanyoyin na VPN da cewa ya saɓa wa Musulunci - kamar yadda jami'ai suka bayyana jiya Litinin.

    Shugaban majalisar malaman Musuluncin, Raghib Naeemi, majalisar da ke bai wa gwamnati shawara kan harkokin addini, ya ce Shari'ah ta bai wa gwamnati damar hana duk wani aiki da zai kai ga yaɗa saɓo ko mugun abu.

    Ya ƙara da cewa duk wata kafa da akr amfani da ita wajen yaɗa abubuwa masu janyo surutai ko saɓo ko zubar da kimar ƙasa dole ne a dakatar da shi kai tsaye.

  11. Kwalara ta kama aƙalla mutum 27 a Kamaru

    Wata annobar kwalara da ta kunno kai a cikin asibitoci 2 na birnin Maroua da ke can ƙurya ta arewacin ƙasar Kamaru. Alƙaluman baya-bayan nan da hukumomi suka bayyana na cewa mutane 27 wannan annobar ta shafa.

    Sannan kuma ta yi sanadiyyar mutuwar wani yaro ƙarami mai shekara 5 a duniya.

    Annobar kwalarar ta kunno kai ne bayan jama’a sun yi fama da ambaliyar ruwa a watan jiya wadda daga bisani ta janyo mutuwar mutane 40.

  12. Ukraine ta harba makami mai cin dogon zango zuwa Rasha - Kremlin

    Rasha ta ce Ukraine ta harba mata makamai masu linzami masu cin dogon zango da Amurka ta ba ta, a karon farko a yau Talata.

    Ma'aikatar lafiya ta Rasha da ke Moscow ta sanar cewa Ukraine ta harba makamin a wani hari da ta kai kan yankin Bryansk da ke Rashar.

    Ta ce, ta yi nasarar kakkaɓo biyar daga cikin makaman ta kuma lalata ɗaya, inda tarkacen makamin suka haddasa wuta a wani waje na soji, kuma nan da nan aka kashe ta ba tare da ta haddasa wata asara ba.

    Haka kuma kafofin yaɗa labaran Ukraine ma sun bayar da rahoton harba makaman na Amurka cikin Rasha, amma zuwa yanzu hukumomin Ukraine ba su ce komai ba.

    Tun da farko hukumomin sojin Ukraine sun tabbatar da cewa sun kai hari kan wani gidan ajiye makamai a yankin Bryansk na Rasha, amma ba su bayyana ko da makaman na Amurka suka kai harin ba.

    Sanarwar ta kuma ce harin da suka kai a nisan kusan kilomita 100 a cibiyar sojin da ke garin kusa da kan iyaka na Karachev, ya haddasa manyan fashewa 12.

  13. Kwalara ta kashe mutum 25 a jihar Sokoto - Kwamishina

    Aƙalla mutum 25 ne suka mutum aka kwantar da wasu da dama kuma a asibitoci sakamakon ɓarkewar cutar kwalara - amai da gudawa - a ƙananan hukumomi uku a jihar Sokoto.

    Kwamishinar lafiya ta jihar Asabe Balarabe wadda ta bayyana haka ga manema labaraai a Sokoto, ta ce ana yi wa mutum 15 da suka kamu da cutar daga yankunan ƙaramar hukumar Sokoto ta Arewa da Silame da kuma Kware, magani.

    Asabe ta kuma ce annobar ta kama mutum 1,160 ne kuma tuni 25 sun rasu a sakamakon cutar.

    Kwamishinar wadda ta ce tuni an raba magunguna a ƙananan hukumomi 18 ta ce kwamitocin taimakon gaggawa na jihar na aiki tuƙuru tare da gwamnatin jiha domin dakatar da bazuwar cutar.

  14. Ana tuhumar ma'aikatan lafiya 47 a kotu kan mutuwar jarirai a Turkiyya

    An gurfanar da mutum 47 a gaban kotu a Turkiyya bisa zargin hannu a wata badaƙala ta sauya wa jarirai sababbin haihuwa asibitoci domin samun kuɗi.

    Masu gabatar da ƙara sun ce likitoci da ma'aikatan jinya da direbobin motocin ɗaukar marassa lafiya sun haddasa mutumawr aƙalla jarirai goma a sanadiyyar badaƙalar.

    Ana zargin mutanen ne da bayar da bayanan ƙarya na rashin lafiyar jarirai domin sauya wa jarirai 19 asibiti daga na gwamnati zuwa na 'yan kasuwa, inda ake ajiye su wajen kulawar gaggawa tsawon lokacin a kan yi musu maganin da bai zama wajibi ba.

    Takardar tuhumar ta nuna cewa waɗanda ke da hannu a cuwa-cuwar suna raba kuɗin da ake bayarwa daga shirin tallafi na gwamnati, da ake biya kullum na kwanan jariri a asibitin.

    Mutane sun musanta zargin da ake yi musu da cewa duk abin da suka yi sun yi ne domin ceto ran jariran

    Idan aka same su da laifi za a iya yanke musu hukuncin ɗauri mai tsawo a kan laifin kisan kai ta hanyar sakaci da zamba da kuma ƙarya.

    'Yansanda sun ƙaddamar da bincike ne bayan da aka tsegunta musu badaƙalar a watan Maris na 2023, lamarin da da ya kai ga soke lasisin asibiti goma.

  15. Ɗantakarar hamayya ya kayar da shugaban ƙasa mai-ci a Somaliland

    Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar hamayya a yankin Somaliland da ya ayyana cin gashin-kansa daga Somalia, Abdirahman Mohamed Abdillahi (Irro) ya kayar da shugaban ƙasar mai-ci, Muse Bihi Abdi, a zaɓen da aka yi, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar a yau Talata.

    Jagoran jam'iyyar hamayya, Waddani - Abdirahman, ya samu kashi 63.92 cikin ɗari yayin da Shugaba Bihi ya ci kashi 34.81 cikin ɗari, na ƙuri'u kamar yadda hukumar zaɓen ta sanar.

    An haifi Abdirahman Irro a Hargaisa, babban birnin ƙasar ta Somaliland, ranar 29, ga watan Afirilun 1955, inda ya yi makarantar elimantare a Somalia, kuma daga nan ya je kwaleji a Amurka, har ya yi digiri na biyu a fannin kula da harkokin kasuwanci.

    Irro ya yi aikin diflomasiyya a ofishin jakadancin Somalia a Moscow, inda ya fara aikin diflomasiyya a ma'aikatar harkokin wajen Somalia a 1981.

    A lokacin yaƙin basasa a 1991 na Somalia ya kasance muƙaddashin jakadan Somalia a tsohuwar Tarayyar Sobiyet.

    Daga baya ya tafi Finlad inda ya je ya zauna da iyalinsa a can har ya samu takardar zama ɗan ƙasar.

    Irro ya fara shiga siyasar Somaliland a 2002, a jam'iyyar UCID.

    Ya kasance shugaban majalisar dokokin Somaliland tsawon shekara 12 daga 2005.

    Irro ya kafa jam'iyyar Waddani a 2012, inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2017, amma ya sha kaye a hannun Muse Bihi Abdi.

    A wannan shekarar kuma ya sake yin takarar inda ya yi nasarar kayar da shugaban mai-ci.

    Somaliland ta kasance ƙarƙashin mulkin kanta da ta ayyana tun bayan da ta sanar da yankewa daga Somalia a 1991.

    Sai dai har yanzu ba ƙasar da a duniya ta amince da ita a matsayin ƙasa nai cin gashin-kanta, wanda hakan ya taƙaita mata samun kuɗaɗe daga waje da kuma ƙalubale ga al'ummarta miliyan shida wajen tafiye-tafiye.

  16. Mutum uku ke magana da yawuna - Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaba Tinubu ya yi garambawul game da ayyukan jami'ansa da ya naɗa a sashen hulɗa da kafafen yaɗa labaru, domin bunƙasa ɓangaren.

    Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labaru da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar ta ce a yanzu dukkanin mutane uku da aka naɗa a muƙaman yaɗa labaru za su zamo masu magana da yawun shugaban ƙasa.

    Sai dai sanarwar ta ce Mista Sunday Dare a yanzu shi ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan kafafen yaɗa labaru da hulɗa da jama'a.

    Haka nan Mista Daniel Bwala, wanda a makon da ya gabata aka bayyana a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafaen yaɗa labaru da sadarwa yanzu zai riƙe muƙamin mai bayar da shawara na musamman kan yaɗa manufofin gwamnati.

    Sanarwar ta ce idan aka yi la'akari da cewa akwai kuma Bayo Onanuga, wanda shi ne mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa dabarun gwamnati "za a ga cewa babu mutum ɗaya tilo da ke riƙe da muƙamin mai magana da yawun shugaban ƙasa".

    "Saboda haka dukkanin mashawartan na musamman uku za su zamo masu magana da yawun gwamnati."

    An dade dai ana raɗe-radin cewa akwai rashin jituwa a ɓangaren masu taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labaru, inda ayyukan wasu jami'an ke shiga cikin na wasu.

    A cikin watan Satumban da ya gabata ne, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Nagelale ya ajiye muƙaminsa 'bisa wasu dalilai na ƙashin kai' kamar yadda ya bayyana.

    Sai dai kafafen yaɗa labaru da dama sun yi bayanin cewa ajiye muƙamin nasa ba zai rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin jami'an da shugaba Tinubu ya naɗa a ɓangaren yaɗa labarun na fadar shugaban ƙasa ba.

  17. Trump ya lashi takobin amfani da sojoji wajen korar baƙi

    Shugaban Amurka mai jiran-gado Donald Trump ya tabatar da cewa zai yi amfani da sojojin ƙasar wajen fitar da tarin ɓakin haure da ba su da rijista, daga ƙasar.

    A jiya Litinin ne shugaban ya tabbatar a shafinsa na sada zumunta, a martanin da ya yi game da wani mai shahi mai ra'ayin riƙau da ya rubuta cewa Trump zai ayyana dokar-ta-ɓaci tare da amfani da sojoji wajen aiwatar da gagarumin shirinsa na korar baƙi.

    Sau da dama a tarukansa na yaƙin neman zaɓe, Trump ya sha nanata cewa zai yi amfani da jami'an tsaro domin su taimaka wa jami'an kula da shige da fice da kuma kwastan - hukumomin da doka ta amince su fitar da baƙi, wajen aiwatar da shirinsa na korar baƙi.

    Trump ya ce tun a rana ta farko da hawan mulki - 20 ga watan Janairu na 2025, zai fara aiwatar da shirin nasa wanda ya ce zai kasance mafi girma a tarihin Amurka kan korar baƙi.

  18. An dakatar da malami a jihar Neja 'saboda wa'azi irin na Boko Haram'

    Gwamnatin jihar Neja ta ce za ta gabatar da rahoto ga jami'an tsaro domin su ci gaba da bincike kan wani malamin addini musulunci da ta dakatar bayan zargin sa da yaɗa 'aƙidar Boko Haram'.

    Shugaban Hukumar lura da al'amuran addinai ta jihar Neja, Umar Faruk ya shaida wa BBC cewa an dakatar da malamin ne bayan binciken da gwamnatin jihar Neja ta yi a kansa.

    Ya ce "kwamitin da muka kafa ya kira shi kuma mun tattauna da shi, mun gano cewa bai ma yi karatu ba."

    A cewar sa malamin na gudanar da ayyukansa a garin Tafa da ke jihar Neja, inda ya mallaki Islamiyya kuma yana da mabiya wadanda ke halartar darussansa.

    "Da muka lura cewa tafiyarsa da aƙidarsa da da'awarsa akwai hatsari ga tsaron jihar Neja da tsaro na kasa, shi ne muka yanke hukuncin cewa a dakatar da shi kuma a rufe makarantarsa har sai jami'an tsaro sun yi bincike a kansa," in ji Sheikh Faruk.

    Ya ƙara da cewa malamin yana kira ne ga magoya bayan sa da su ƙaurace wa zaɓuka da duk wani abin da ya shafi dimokuraɗiyya.

    Najeriya dai ta kwashe sama da shekara 10 tana fama da matsalar mayaƙan Boko Haram waɗanda suka addabi arewa maso gabashin Najeriya da kuma wasu ƙasashen yammacin nahiyar Afirka.

    Haka nan ƙasar na fama da matsaloli na ƴan fashin daji masu garkuwa da kisan mutane a arewa maso yammacin ƙasar.

    Dama dai malamin ya riƙa janyo cece-ku-ce a yankin arewacin Najeriya sanadiyyar kalaman da ya riƙa furtawa kan malaman addinin Musulunci da dama na yankin.

  19. Dubban mutane na zanga-zangar ƙin sauyi a dokar da ta kafa ƙasar New Zealand

    Dubban mutane ne suka yi dandazo a kusa da ginin majalisar dokokin New Zealand a yau Talata domin yin zanga-zangar ƙin ƙudurin da zai sauya yarjejeniyar da ta samar da ƙasar.

    Masu suka sun ce sauye-sauyen za su danne wasu haƙƙoƙin al'ummar Māori - ƴan ƙasar na asali.

    Daga cikin masu zanga-zangar akwai Sarauniyar al'ummar ta Māori da wasu ƴan majalisa da dama.

    Wakiliyar BBC ta ce abin da masu fafutuka ke nuna damuwa a kai shi ne yarjejniyar da ake son sauyawa an samar da ita ne tun 1840, a lokacin mulkin mallaka domin kare haƙƙin mutanen na Māori.

  20. Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi ba ne - Fadar Shugaban Ƙasa

    Fadar gwamnatin Najeriya ta ce tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo ba shugaba ba ne da za a yi koyi da shi a fannin gudanar da mulki da ma sauran harkokin shugabanci.

    Gwamnatin ta yi wa Obasanjo wannan kakkausar suka ne a martanin da ta mayar masa na sukar gwamnatin Bola Tinubu da Muhammadu Buhari da ya yi a wata lacca da ya gabatar ta tunawa da marigayi Chinua Achebe a Jami'ar Yale ta Amurka.

    A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasar shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar a jiya Litinin, gwamnatin ta soki Obsanjo kan abin da ta ce ya saba na nuna shi gwani ne, tare da bayar da shawarar da ba a nema ba a wajensa a kan shugabanci da mulki a Najeriya, inda yake ɗora alhakin matsalolin da ƙasar ke ciki a kan waɗanda suka hau mulki bayan gwamnatinsa.

    Sanarwar ta yi nuni da irin tarin matsaloli na cin hanci da rashawa da almundahana da keta haddin tsarin mulki da dokoki da gazawar shugabanci da ta ce duk an samu a lokacin gwamnatin Obasanjo da Atiku amma kuma a yau Obasanjon kamar kullum ya kawar da kai daga wannan gazawa ta mulkinsa yana zargin gwamnatocin da suka biyo bayan tashi musamman ta Bola Tinubu da Buhari kan gazawa.

    Gwamnatin ta ce idan da Obasanjo ya magance yawancin matsalolin da yake suka yanzu a kai, a tsawon shugabancinsa na shekara takwas to da yanzu Shugaban Buhari da Shugaba Tinubu da sun samu sauƙi wajen ƙoƙarin gyara ƙasar nan.