Majalisar Dokokin Najeriya ta amince Tinubu ya ciwo wani sabon bashi
Majalisar Dokokin Najeriya ta amince wa shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ci wani ƙarin bashi a cikin gida na naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin da ke cikin kasafin kuɗin 2025.
Makonni biyu da suka gabata ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya buƙaci majalisar ta amince da ciyo bashin, inda ya kafa hujja da ƙarin da aka samu a giɓin kasafin kuɗin ƙasar daga naira tiriliyan 12.95 da ya gabatar, zuwa naira tiriliyan 14.10 da majalisar dokokin ta amince da shi.
Kasafin kuɗin Najeriya na 2025 ya kai jimillar kudi naira tiriliyan 59.99, inda ake sa ran cike giɓin ta hanyar cin bashi a ciki da kuma wajen ƙasar.
A makon da ya gabata ƙasar ta samu kuɗi dala biliyan 2.35 ta hanyar takardun lamuni na Eurobond.