Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Fadar White House ta fitar da rahoton likitoci mai tabbatar da ƙoshin lafiyar Kamala Harris

    Fadar White House ta wallafa wani bayanin lafiyar asibiti na Kamala Harris, wanda ke cewa mataimakiyar shugaban Amurkan tana cikin ƙoshin lafiya kuma za ta iya tafiyar da ofishin shugaban ƙasar.

    Bayanin ya ƙunshi muhimman rahoton binciken lafiyar ƴar takarar shugaban ƙasar mai shekara 59.

    Ba dole bane Ms Harris ta fitar da bayanan lafiyar nata, amma rahotanni na cewa wata dabara ce ta yi domin tilastawa abokin takarar ta, Donald Trump fitar da nasa bayanan.

    Kawo yanzu dai bai bitar ba, amma ofishin yaƙin neman zaɓen sa ya ayyano likitansa ya na cewa Mr Trump na cikin ƙoshin lafiya.

  2. Kenya na ƙoƙarin ceto ƴan ƙasarta 45 da ake tsare da su a Myanmar

    Hukumomi a Kenya sun ce akwai ƴan ƙasar 45 da ake tsare da su a Myanmar bayan an yaudare su ta kafar intanet da sunan ɗaukar aiki.

    Ofishin jakadancin Thailand a Kenya ya ce ya tura jami'ansa kan iyakar Burma domin tattauna yadda za a sako jama'ar ƙasar da ake tsare da su a can.

    Hukumomi sun yi gargadin cewa akwai ɗaruruwan ƴan Kenya da aka yaudara da sunan samar masu ayyukan yi a Thailand, amma da zarar sun isa Bangkok sai a karkatar da su zuwa Myanmar.

    Ana tsare mutanen ne a wasu gidaje masu tsananin matakan tsaro, inda ake tilast masu shiga hada-hadar ƙwayoyi da karuwanci.

    Duk da gargaɗi da hukumomin Kenyan ke ci gaba da yi a kan illar wannan abu, ana ci gaba da samun mutanen da ke faɗawa wannan tarko, inda ake kai su Myanmar da kuma Laos.

  3. Bam ya kashe manoma 30 a Somalia

    Manoma aƙalla biyar ne suka mutu bayan motar da suke ciki ta taka wani abin fashewa a garin Afgoye mai nisan kilomita 30 daga Mogadishu babban birnin Somalia.

    Fashewar da ta tayar da motar da suke ciki ta kuma raunata wasu mutum goma da ke kusa da wajen.

    Ana ci gaba da kulawa da waɗanda suka samu raunin a asibiti.

    Rahotanni sun ce mutane suna kan hanyar zuwa gona ne lokacin da abin ya faru.

    Mayaƙan ƙungiyar Al-Shabab sun saba binne bama-bamai a kan titi domin kai nwa jami'an gwamnati da dakarun wanzar da zaman lafiya hari, amma ba su cika ƙaddamar da hari a kan fafaren hula ba.

  4. MDD ta ce an raunata jami'anta biyar a kudancin Lebanon

    An raunata wani jami'in wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon, wanda kuma shi ne mutum na biyar da aka raunata a ƴan kwanakin nan a cikin dakarun da ke aiki a kudancin Lebanon.

    Sanarwar da dakarun UNIFIL ta fitar ta ce an raunata jami'in ne a hedikwatarta da ke birnin Naqoura na kudancin Lebanon a ranar Juma'a. Sai dai ta ce babu tabbacin ko daga aka yi ina harbin da ya raunata shi.

    Ta ce "An yi masa aiki a asibitin mu da ke Naqoura domin a cire harsashin kuma a yanzu ya fara murmurewa''

    Can ma a yankin Jabalia da ke Gaza, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutane aƙalla 20 harin Isra'ila ya kashe a ranar Juma'a da dare.

    Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da faɗa a kudancin Lebanon, inda dakarun Isra'ila suka umarci rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya su tashi daga wajn da suke.

    Sai dai kakakin UNIFIL ya ce an cimma matsayar bai ɗaya ta ci gaba da zama a wajen da suke aikinsu tuntuni.

  5. Yadda Falasɗinawa da aka ɗaiɗaita ke tserewa arewacin Gaza

    Hotuna sun nuna yadda Falasdinawan da suka rasa matsugunansu ke tserewa daga yankunan arewacin zirin Gaza, ɗauke da kayakinsu.

    Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin kwashe mutanen Jabalia da kuma yankunan da ke kusa, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane sama da 400,000 ne suka maƙale.

    Jami'an Falasɗinawa da na MDD sun ce babu wasu wurare masu kariya da za a tsere zuwa wajensu a zirin Gaza.

    Sun kuma bayyana damuwarsu dangane da matsalar matsanancin ƙarancin abinci da man fetur da kuma magunguna a arewacin Gaza.

  6. An kashe manoma huɗu a wani hari a Filato

    Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wasu manoma huɗu tare da jikkata wasu biyar a wani hari da aka sake kai wa wurin hakar ma'adinai kusa da kauyukan Kuba da Maikatako da ke karamar hukumar Bokkos na jihar Filato.

    Shugaban ƙungiyar matasan yankin Butura, Sabastine Majit, shi ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos ranar Asabar, inda ya ce an kai harin ne da misalin karfe na dare ranar Alhamis.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa maharan sun tsere bayan kai harin, kafin isar jami'an tsaro.

    "Wanna hari ya zo ne kwanaki huɗu bayan wani mummunan hari a kauyen Wumat, inda aka kashe mutum biyar ƴan gida ɗaya, ciki har da wata mata mai ciki," in ji Sabastine.

    Ya ce wannan hari shi ne na baya-bayan nan da ake kai wa al'ummomin yankin, wanda ya janyo mutuwar mutum 20 a cikin wata ɗaya kaɗai.

    Ya ƙara da cewa wannan na cikin hare-hare da yawa da ake kai wa ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Riyom da Bassa da Jos ta Arewa da kuma ta Kudu da Wase da kuma Mangu a baya-bayan nan, inda ake kashe mutane.

    Sai dai babu wani ƙarin bayani daga rundunar ƴansandan jihar ta Filato kan wannan hari da aka kai.

  7. Muna rokon shugaban ƙasa ya rage farashin fetur, ƴan Najeriya na cikin wahala - Sanata Ndume

    Ɗan majalisar dattijan Najeriya mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya rage farashin man fetur, inda ya ce ƴan Najeriya na cikin wahala.

    Ndume ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya kuma ce ci gaba da ƙara farashin man fetur da abinci da kuma kayan amfani na yau da kullum na ƙara jefa ƴan Najeriya cikin kunci da wahala, musamman ma talakawa.

    Tsohon mai tsawatarwa na majalisar ya ce wasu ɓata-gari cikin gwamnati na ƙoƙarin haddasa fitina tsakanin mutane da gwamnatin Tinubu ta hanyar ɓullo da tsare-tsare masu tsauri da kuma mara kyau maimakon shawo kan matsalar hauhawar farashi da kuma tashin kuɗin dala da ke ci gaba da kassara ƴan ƙasar.

    "Wasu ne kawai ke son ɓata Tinubu a idon jama'a ta hanyar ɓullo da waɗannan tsare-tsare daga karshe kuma laifi ya koma kan shugaban.

    "Ina kira ga shugaban ƙasa da ya daina kula waɗannan mutane da ke son kawo cikas ga gwamnatinsa.Halin kunci da mutanen ke sa ƴan Najeriya ba zai misaltu ba," in ji Ndume.

    Ya ce mutane na cikin matsanancin wahala musamman ma jihar sa ta Borno.

    "Mutane na cikin matsi, akwai yunwa, ɓacin-rai da kuma fushi cikin al'umma," in ji Sanatan.

    Ya ce ya san shugaba Tinubu yana da manufa mai kyau ga ƴan Najeriya, sai dai wasu masu ba shi shawara ne ke son kassara ƴan ƙasar ta hanyar ba shi shawara mara amfani.

    Sanata Ndume ya buƙaci shugaban ƙasar da ya duba batutuwan da zarar ya koma daga hutun da ya tafi da nufin shawo kan su.

  8. Babu tallafin abinci da ya shiga arewacin Gaza a watan Oktoba - WFP

    Yayin da Isra'ila ke zafafa kai hare-hare a arewacin Gaza, Shirin Samar da Abinci na Majlisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya ce hare-haren sun yi mummunar tasiri kan samar da abinci ga dubban iyalai Falasɗinawa.

    Ta ce Isra'ila ta rufe hanyar da ta tsallaka zuwa arewacin Gaza kuma babu wani tallafin abinci da aka kai tun ranar 1 ga watan Oktoba.

    "Muna da zimmar kai abinci a kowace rana duk da irin wahalhalu da ake fuskanta," in ji Antoine Renard, babban darektan WFP a yankin Falasɗinu.

    "Sai dai ba tare da samun hanya mafi sauki ba, zai yi wuya a kai ga waɗanda ke matukar bukatar abinci."

  9. Sojojin Isra'ila sun ce sun kakkaɓo rokoki da aka harba daga Lebanon

    Ma'aikatar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce an harba rokoki kusan 30 zuwa cikin ƙasar daga Lebanon, kuma ta kakkaɓo wasu daga ciki.

    Tun da farko a wani sako a shafin Telegram, IDF ta ce ta kakkaɓo "rokoki da yawa" da aka harba cikin ƙasarta daga Lebanon - bayan samun gargaɗi daga yankin Galilee da ke aewacin ƙasar.

    Kafin haka, IDF ta ce wani jirgi mara matuki ya ratsa cikin Isra'ila daga Siriya, inda kuma ya faɗi a wani yanki.

    Ta ce sojojin saman ƙasar sun samu nasarar kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragen, inda ɗayan kuma ya lalata wani gini a Herzliya da ke Tel Aviv.

  10. Peter Obi ya yi Alla-wadai da sake ƙara kuɗin fetur

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya kwatanta sake ƙara kuɗin fetur a matsayin "abin takaici", inda ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta janye ƙarin kuɗin fetur da ta yi.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ɗora alhakin halin matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke ciki kan gwamnatin tarayya.

    Ya ce gwamnati mai ci na kawo tsare-tsare marasa kyau waɗanda ba su dace ba, inda ya ce ƙara kuɗin fetur da kamfanin mai na NNPCL ya yi ba daidai bane.

    Martanin Obi na zuwa ne a daidai lokacin da NPPCL ya sanar da sake ƙara kudin mai.

    "Ƙarin kuɗin fetur abin Alla-wadai ne ganin cewa ƴan Najeriya na cikin matsin rayuwa wanda gwamnati mai ci ta janyo. Bai dace a ƙara kuɗin mai ba tare da wani bayani ba," in ji Obi.

    Ya ce lamarin abin takaici ne matuka, ganin yadda hakan zai shafi ƴan ƙasar da kuma tattalin arzikinta.

    "Ba haka ya kamata a lura da tattalin arziki ba, ba kuma haka ya dace a mulki ƙasa ba. Babu abin da wannan ƙarin zai janyo illa wahala ga ƴan Najeiya," in ji Peter Obi.

  11. Hezbollah ta ce ta harba rokoki zuwa cikin Isra'ila

    Hezbollah ta ce ta harba tarin rokoki zuwa cikin Isra'ila, inda ta ce ta nufi wani sansanin soji ne a kudancin birnin Haifa da ke arewacin Isra'ila.

    Ƙungiyar ta ce ta kai harin ne da sanyin safiyar yau Asabar, a cewar wata sanarwa a shafin Telegram.

    Sai dai ma'aikatar tsaron ƙasar Isra'ila ba ta yi magana kan abin da ya faru a Haifa a safiyar yau.

  12. Gane Mini Hanya: Bikin cikar Gidauniyar McArthur shekara 30

    A baya-bayan nan ne, Gidauniyar McArthur mai samar da tallafi wajen kawo sauye-sauyen rayuwa, ta yi bikin cika shekara 30 tana ayyukan da suka shafi sauyin yanayi da ƙarfafa mulkin dimokraɗiyya da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

    Gidauniyar ta kuma ce a tsawon shekarun da ta kwashe, ta yi aiki wajen inganta kula da lafiyar mata da ƙananan yara, da kuma rage mace-macen mata masu juna biyu.

    Ta ce tana alfahari da tallafi da kuma gudunmawar da ta samarwa Nijeriya, wanda a cewarta, ya taimaka wajen inganta rayuwar al'umma.

    Yayin bikin da aka yi cikin makon nan a Abuja, masu ruwa da tsaki daga fannoni daban-daban ne suka halarci taron, inda suka yi matuƙar yaba wa Gidauniyar da jajircewar da ta nuna a kan burin da ta sanya gaba.

  13. Ambaliya ta ɗaiɗaita al'ummomi da dama a jihar Kogi

    Ambaliya ta ɗaiɗaita al'ummomi sama da 60 a karamar hukumar Ibaji na jihar Kogi.

    Da yake tattaunawa da manema labarai, shugaban al'ummar yankin, ya ce lamarin ya yi munin gaske, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Kogi da ta ɗauki mataki nan take don shawo kan ambaliyar.

    "Ruwa ya ci al'ummomi sama da 60 da ke yankin a halin yanzu," in ji shi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ibaji na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar da ke fuskantar mummunar ambaliya a kowace shekara.

    Ita ma shugabar wani kwamiti cikin ƙungiyar al'ummar yankin, Farfesa Joy Ede ta yi kiran kai musu ɗaukin gaggawa, ciki har da kirkiro da wani asusun tallafi domin taimakawa al'ummomin da ambaliyar ta shafa.

    A cewarta, yawan ambaliyar da al'ummomin yankin suka fuskanta musamman waɗanda ke zaune kusa da Kogin Neja, ya fi karfin gwamnatin jihar ita kaɗai har sai an samu ƙarin taimako.

  14. Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe mutum 49 cikin sa'o'i 24 da suka gabata

    Ma'aikatar lafiya a Gaza karkashin ikon Hamas, ta ce an kashe mutane 49 yayin da aka jikkata wasu 219 a hare-haren guda biyar da Isra'ila ta kai zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

    Ma'aikatar ta ƙara da cewa ana ci gaba da ayyukan ceto, kuma har yanzu mutane na cikin ɓaraguzan gine-gine.

    Ta yi kiyasin cewa aƙalla mutum 42,175 ne aka kashe tun harin ranar 7 ga watan Oktoban bara, yayin da aka jikkata wasu 98,336.

  15. Yadda aka kai waɗanda Isra'ila ta jikkata a Gaza ranar Juma'a zuwa asibiti

    Hotuna sun nuna yadda aka kai mutanen da hare-haren Isra'ila ta kashe da kuma jikkata zuwa asibitin Al Ahli Baptist.

  16. Kamfanin Boeing na shirin sallamar ma'aikata 17,000

    Kamfanin ƙera jiragen sama na Boeing ya sanar da cewa zai sallami ma'aikata dubu goma sha bakwai -- kusan kashi 10 cikin ɗari na ma'aikatansa - a daidai lokacin da yake fama da yajin aikin ma'aikata na tsawon wata ɗaya.

    Matsalolin Boeing sun haɗa da damuwar da ake ci gaba da nunawa kan ingancin jiragensa da kuma tasirin yajin aikin da mambobin ƙungiyar ma'aikata ke yi.

    Sama da ma'aikatan Boeing dubu talatin ne ke yajin aikin neman karin albashi.

    Boeing ya ce zai yi asarar dala biliyan biyar a cikin zango na uku na wannan shekarar.

  17. Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 30 a Gaza

    Jami'an Hamas sun ce aƙalla Falasɗinawa 30 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan Jabaliya a arewacin Gaza.

    Ana kuma fargabar cewa akwai ƙarin mutane da suka maƙale a karkashin ɓaraguzan gine-ginen da aka lalata.

    A cikin 'yan kwanakin nan dai sojojin Isra'ila sun sake zafafa kai hare-hare a yankin.

    A wani ɓangare kuma, sojojin Isra'ila sun ce sun daƙile ɗaya daga cikin jiragen sama marasa matuka biyu da ƙungiyar Hezbollah ta harba a cikin dare daga Lebanon, inda na biyun ya lalata wani gini, amma ba a samu asarar rai ba.

  18. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Asabar.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da sauran sassan duniya.