Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Saudiyya da Qatar za su biya wa Syria bashin Bankin Duniya

    Ƙasashen Saudiyya da Qatar sun ce za su biya wa Syria bashin dala miliyan 50 da Bankin Duniya ke bin ƙasar.

    Matakin zai bai wa Bankin damar komawa ayyukan bayan dogon lokaci da ya ɗauka da dakatar da ayyukansa a ƙasar.

    Hakan zai taimaka wa ƙasar samun kuɗaɗen da yake buƙata na sake gina ƙasar bayan kwashe shekara 14 ana yaƙin basasa.

    Matakin wata alama ce da ke nuna yadda ƙasashen yankin Gulf masu arziki ke shirin tallafa wa sabuwar gwamnatin Syria - da ta hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a shekarar da ta gabata.

  3. Shugabar Namibia ta kori ministan noman ƙasar saboda zargin aikata fyaɗe

    Shugabar ƙasar, Namibia - Netumbo Nandi-Ndaitwah - ta kori ministan noman ƙasar, Mac Hengari, bayan kafofin yaɗa labaran ƙasar sun bayar da rahoton cewa yana fuskantar bincike kan zargin fyaɗe

    A watan da ya gabata ne Ms Nandi-Ndaitwah, shugabar ƙasar mace ta farko ta naɗa Mista Hengari a muƙamin.

    Ministan na fuskantar matsin lambar sauka daga muƙaminsa, bayan da aka zarge shi da yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe.

    Mista Hengari dai ya musanta aikata ba daidai ba.

    A ranar Asabar ne kakakin rundunar ƴansandan ƙasar ya ce an kama ministan bayan zargin bai wa wata mata cin hanci domin janye tuhumar zargin da ke yi masa.

  4. Labarai da dumi-dumi, Liverpool ta lashe kofin Premier na bana

    Ƙungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe kofin Premier na kakar 2024/25.

    Ta samu nasarar ce bayan doke Tottenham da ci 5-1 a filin wasa na Anfield.

    Ɗan wasan Tottenham Dominic Solanke ne ya fara ci wa Spurs kwallo a minti na 12, inda Liverpool ta farke ta hannun Luiz Diaz a minti na 16.

    Daga nan ƙungiyar ta Anfiled ta fara zura sauran kwallaye ta hannun Mac Allister da Gakpo da kuma Mohammed Salah - sai kwallo ta karshe kuma Tottenham ta ci gida jimilla kwallaye biyar kenan a ragarta.

    Wannan ne kofin Premier na 20 da Liverpool ta lashe a tarihinta.

  5. Sojojin Pakistan sun kashe masu iƙirarin jihadi 54 a ƙasar

    Rundunar sojin Pakistan ta ce dakarunta sun kashe masu iƙirarin jihadi 54 da suka yi yunƙurin shiga ƙasar daga kan iyakarta da Afghanistan.

    Rundunar ta ce sojojinta sun far wa mayaƙan a gundumar Waziristan da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa.

    Kawo yanzu babu wani martani daga ƙungiyar masu iƙirarin jihadin.

    A shekarar da ta gabata ne mayaƙan Taliban da ke Pakistan suka fara ƙaddamar da hare-hare kan jami’na tsaron Pakistan.

    Fiye da mutum 200, mafi yawansu jami’an tsaro aka kashe a hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi tun farkon shekarar nan.

    Pakistan na zargin gwamnatin Taliban a Kabul da kasa ɗaukar matakai kan ƙungiyoyin ƴanbindiga a Afghanistan, zargin da shugabanninTaliban suka musanta.

  6. Amnesty ta zargi gwamnatin Najeriya da kasa kare rayukan ƴan ƙasar

    Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya ta kasa kare rayukan ƴan ƙasar.

    Zargin na zuw ane bayan da rahotonni suka ce ƴanbindiga sun kashe fiye da mutum 20 a wani ƙauye da ake haƙar ma'adinai a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa ta Daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ya fitar ya ce aƙalla mutu 54 aka kashe a hare-hare daban-daban a yankunan arewacin ƙasar a ƴan kwnakin nan.

    Mallam Isa Sanusi ya shaida waa BBC cewa mutum 26 aka binne a ƙauyen Gobirawan Chali, inda ake haƙar ma'adinai, bayan ƴanbindiga sun kai hari kan mutanen ƙauyen.

    "Hare-haren baya-bayan nan da ake kai wa mazauna ƙauyuka sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa ba su yi shirin ƙwarai na kawo ƙarshen ayyukan ƴanbindigar da suka kwashe shekaru suna addabar jama'an, yayin da maharan ke ta zubar da jini a wasu sannan Najeriya.'' In ji Isa Sanusi.

    A mako mai ƙarewa ne wasu mahara haye a kan babura suka auka wa wuraren da ake haƙar ma'adinai ƙauyen Gobirawan Chali da ke ƙaramar hukumar da Maru, ta jihar Zamfara, inda suka buɗe wa mutane wuta, daga baya kuma suka fara bi gida-gida suna kashe mutane.

    Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ce maharan sun kuma kai hari wasu garuruwa biyu masu makwabtaka da ƙauyen.

    Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ba ta amsa tambayar BBC ba kan hare-haren, sannan ba ta ce komai ba game da halin da ake ciki a yankin.

    A makonnin baya-bayan nan ƴanbindiga riƙa kai hare-hare tare da kashe mutane da ƙona gidaje da amfanin gona a jihohin Benue da Plateau.

    Haka a jihohin Sokoto da Zamfara an yi ta samun rahotonnin yadda ƴanbindiga ke aza wa mazauna garuruwa haraji da sauran dokoki ta hanyar amfani da bakin bindiga.

    "Ganin yadda a yanzu matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara a Najeriya, a bayyane take cewa kare rayuka da dukiyoyi ba ya cikin manyan batutuwan da gwamnati ke bai wa fifiko''.

    ''Bai kamata a bar mutane cikin fargabar fuskantar hari ko sacewa ba. An bar mutane a hannun ƴanbindiga,'' a cewar ƙungiyar Amnesty International.

    Ɗaruruwan mutane ne aka kashe tare da sace wasu a yankin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekara biyu, sakamakon ƙaruwar matsalar tsaro a yankin.

    To sai dai a lokuta da dama gwamnati ta sha iƙirarin yin bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar.

  7. Adadin mutanen da suka mutu a fashewar tashar jirgin ruwan Iran ya kai 40

    Adadin mutanen da suka mutu a fashewar da ka samu a tashar jirajen ruwan Iran - ranar Asabar - ya kai 40.

    Ɗaruruwan mutane ne suka jikkata a fashewar da ta auku a kusa da birnin Bandar Abbas da ke kusa da gaɓar ruwa.

    Tuni dai hukumomi ƙasar suka ayyana makokin kwana uku.

    Kawo yanzu hukumomi sun shawo kan gobarar da ta tashi bayan fashewar. Shugaban Iran, Masoud ya kai ziyara zuwa yankin.

    Har yanzu ba a san abin da haddasa da fashewar ba. Ma'aikatar tsaron ƙasar ta musanta zargin cewa an ɓoye jirgin dakon kayan sojin a wurin da fashewar ta auku.

  8. Ƴansanda sun ce sun kuɓutar da mutum 10 da aka sace a titin Funtua-Gusau

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta kuɓutar da mutum goma da ake zargin ƴanbindiga sun yi garkuwa da su a kan babban hanyar Funtua zuwa Gusau.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce an samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan bindigar - inda suka kuma daƙile wani yunkurin garkuwa da mutane a kan hanyar ta Funtua-Gusau.

    Olumuyiwa ya ce ƴansandan shiyyar Faskari da ke jihar Katsina ne suka yi nasarar kuɓutar da mutanen goma, bayan artabu da masu garkuwan - abin da ya sa suka tsere da munanan raunuka.

    "Jami'an mu sun fafata da ƴanbindigar, abin da ya janyo wasu suka tsere da raunuka. Sakamakon haka muka yi nasarar ceto mutum goma, ciki har da direbobi biyu da kuma fasinjoji takwas. Ba su samu rauni ba kuma mun miƙa su ga iyalansu," in ji sanarwar ƴansandan.

  9. Girgizar ƙasa ta hallaka mutum huɗu, ta jikkata 13 a Aljeriya

    Mutum huɗu sun mutu yayin da 13 suka jikkata bayan afkuwar girgizar ƙasa a birnin Oran na ƙasar Aljeriya, a cewar hukumomi.

    Sun ce girgizar ƙasar ta afku da maraicen ranar Asabar a lardin na Hai Essanouber.

    "Shekarun waɗanda suka mutu yana a tsakanin biyar da kuma 43... yayin da 13 da suka jikkata kuma suna tsakanin shekara 12 zuwa 75, sun samu munanan raunuka," a cewar sanarwar hukumomi.

    Hukumomin ba su bayyana abin da ya haddasa girgizar ƙasar ba, wanda ministan harkokin cikin gida ya ce "ya janyo rugujewar gidaje biyar".

  10. Mutum tara ne suka mutu bayan da mota ta kutsa cikin taron jama'a a Canada

    Ƴansanda sun tabbatar da cewa da cewa mutum tara ne suka mutu bayan da wata mota ta kutsa cikin taron jama'a a Canada.

    Motar ta kusta ne a daren jiya a wani biki a Vancouver.

    "Muna jajantawa waɗanda lamarin ya shafa," kamar yadda sanarwar ƴansandan ta bayyana.

  11. Fitaccen jarumin Kannywood Baba Hasin ya rasu

    Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood Muhammad Shuaibu wanda aka fi sani da Baba Hasin ya rasu - yana da shekara 68 a duniya.

    Baba Hasin ya rasu ne ranar Asabar a gidansa, bayan shafe tsawon lokaci yana jinya a Asibitin Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.

    Ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa 17.

  12. Dole ne jiragen ruwan Amurka su riƙa bin mashigar tekun Panama a kyauta - Trump

    Shugaba Donald Trump, ya ce duk wasu jiragen ruwa na sojin Amurka da kuma na kasuwanci a ƙasar dole ne su rika bi ta mashigar teku ta Panama da Suez a kyauta ba tare da sun biyo wani kuɗi ba.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta da muhawara -Truth Social, Mista Trump, ya ce an umarci sakataren harkokin wajen ƙasar, Marco Rubio ya kula da batun.

    Trump ɗin ya ce babu wani dalili da zai sa a ce jiragen ruwan sojin Amurka ko ma na kasuwanci su riƙa biyan kuɗi don bin hanyar karkashin teku ta Panama mai kilomita 82 da ta haɗa tekun Carribean da kuma ta Pacific - da kuma irinta a tekun Pacific har ma da na tekun Suez a Masar.

    Sai dai Mista Trump bai bayyana dalilin da ya sa Amurka ba za ta riƙa biyan kuɗin ba.

    Hukumomin da ke kula da hanyoyin karkashin tekun na cajin kuɗi dala dubu 500 ga kowane jirgin ruwa mai ɗaukar manyan sundukai ko kwantenoni.

    Ƙasashen da ke da waɗannan hanyoyi na samun biliyon dala a duk shekara daga wannan kuɗi da ake biya na bi ta hanyoyin.

  13. Za a iya dakatar da Rudiger tsawon lokaci bayan jifan alkalin wasa da ƙanƙara

    Antonio Rudiger na fuskantar barazanar dakatarwa daga buga wasanni bayan da alkalin wasa ya ba shi jan kati a wasan karshe na Copa del Rey.

    Real Madrid ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 3-2 a wasan da aka buga a filin wasa na Seville.

    Rudiger da Lucas Vasquez sun samu jan kati a wasan duk da cewa an sauya su, saboda nuna fushi da suka yi kan rashin hura wa Mbappe keta da aka yi masa, jim kaɗan kafin a tashi a wasan.

    Har ila yau, an sallami Jude Bellingham daga bisani - saboda nuna rashin ɗa'a.

    Alkalin wasa Ricardo de Burgos Bengoetxea ya rubuta a rahotonsa cewa an kori Rudiger ne "saboda jifa na da wani abu - ƙanƙara - wanda bai same ni ba".

    Ɗan wasan na iya fuskantar dakatarwa na tsawon lokaci, kamar yadda dokokin hukumar kwallon kafa ta Sifaniya suka tanadar ga wanda ya yi irin laifin.

    ''Idan aka duba sashi na 104 na dokar, wanda ya bayyana cewa idan aka ci mutuncin alkalin wasa - hukuncinsa shi ne dakatarwa na watanni uku zuwa shida - idan har bai yi wa alkalin wasa lahani ba," a cewar RFEF.

    Sai dai ɗan wasan ya fito ya ba da hakuri kan lamarin a shafinsa na sada zumunta a yau Lahadi.

  14. Saudiyya ta kama mutum kusan 13,000 da suka shiga ƙasar ba bisa ka'ida

    Saudiyya ta ce ta kama mutane 19,328 da suka shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba a makon da ya gabata kaɗai.

    Ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ce ta sanar da haka ranar Asabar, inda ta ce an samu nasarar kama mutanen ne bayan samame da haɗin gwiwar jami'an tsaro suka yi daga ranar 17 zuwa 23 ga watan Afrilu.

    "An iza ƙeyar mutum 12,866 zuwa ƙasashensu yayin da aka miƙa wasu da suka aikata laifuka daban-daban hannun ofishoshin jakadancin ƙasashensu domin su samu takardu da suka kamata," in ji ma'aikatar.

    A ɗaya gefen, ma'aikatar jarkokin cikin gidan Saudiyyar ta ƙara da cewa mutanen da aka kama a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasar sun kai 1,360 - inda kashi 44 daga cikinsu suka kasance ƴan Yemen, kashi 54 kuma ƴan Habasha sannan kashi biyu daga sauran ƙasashe.

    Haka kuma sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce an kuma kama mutum 22 da ke da hannu wajen bai wa mutanen matsuguni da kuma ɗaukar su aiki.

  15. Ko shan ruwan nono na da alfanu ga mazan da ba jarirai ba?

    Masana kimiyya sun amince cewa ruwan mama yana gina jikin jarirai da kuma kare garkuwar jikinsu daga cutuka. Sai dai wasu manyan maza na tunanin cewa su ma za su iya amfana da ruwan nonon.

    Jameson Ritenour, mai shekara 39 da ke da ƴaƴa uku, ya ɗanɗani ruwan nono karon farko lokacin da abokiyar zamansa Melissa ke shayarwa - kuma take fitar da ƙarin ruwan maman da ba ta so.

    Jameson ya zaƙu don sanin irin alfanun da ruwan mama ke ɗauke da shi bayan da ya kalli wani bidiyo a dandalin YouTube - inda wani mai motsa jiki ya yi magana kan tasirin shansa.

  16. NAPTIP ta kuɓutar da ƴan Najeriya tara da aka yi niyyar safarar su zuwa Libya

    Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP ta ce ta kuɓutar da wasu ƴan Najeriya da aka yi niyyar safararsu zuwa Libya.

    Kwamandan hukumar a jihar Zamfara, Aliyu Abubakar ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen tara ne a iyakar Babura da ke jihar Jigawa, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

    Aliyu ya ce akwai mata guda uku cikin mutanen tara - waɗanda ƴan asalin jihar Zamfara ne.

    Sun tserewa gidajensu ne sakamakon hare-haren ƴanbindiga, inda suka koma zama a Kaduna.

    NAPTIP ta ja hankalin mutane kan faɗawa makomar masu safarar mutane - inda ta ce kowa ya yi taka tsantsan.

    Safarar mutane dai ba sabon abu bane a kan iyakokin Najeriya, inda a watan Fabrairu, gwamnatin jihar Neja ta karɓi yara 21 da hukumar shige da fice ta kuɓutar da su - waɗanda ba su haura shekara tara ba lokacin da ake tafiya da su Nijar.

  17. Mota ta kutsa cikin taron jama'a, ta hallaka mutane da dama a Canada

    Ƴansand a ƙasar Canada sun ce mutane da dama ne suka mutu, wasu kuma suka jikkata bayan da wata mota ta kutsa cikin taron jama'a a wani biki a Vancouver.

    Rahotanni a shafukan sada zumunta sun ce biki ne na nuna al'adun Philippines.

    Zuwa yanzu bayanai sun nuna cewa direban ya tsere.

  18. An kama ɗan Ukraine kan zargin kashe Janar ɗin Rasha

    Jami'an tsaron Rasha sun ce sun kama wani mutum da ake zargi da kashe wani babban Janar ɗin ƙasar a wani hari da aka kai wata unguwa da ke wajen birnin Moscow ranar Juma'a.

    Janar Yaros-lav Moska lik mataimaki ne ga shugaban sashen gudanar da ayyuka na ofishin Babban Hafsan Sojin ƙasar.

    An kashe shi ne ranar Juma'a bayan da wata mota ƙirar Golf Volkswagen da aka faka a kofar gidansa ta fashe a lokacin da yake wucewa.

    Hukumar leƙen asirin Rasha ta FSB ta ce ta kama jami'in ɗan ƙasar Ukraine mai suna Ignat Kuzin da hannu a lamarin.

    Ta ce ya ɗana bom ne ƙirar cikin gida a motar, sannan ya tashe shi daga Ukraine.

    Sai da Ukraine ɗin ba ta ce uffan ba game da lamarin.

  19. Assalamu Alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkan mu da hantsin Lahadi.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya - har ma da Najeriya da makwabtanta.

    Ahmad Bawage ne ke tare da ku a wannan lokaci.