Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/07/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Haruna Kakanki

  1. Bankwana

    Masu bibiyar shafinmu Usman Minjibir da Buhari Muhammad Fagge ke muku fatan mu kwana lafiya daga nan BBC.

  2. Ba mu san inda zanga-zangar nan za ta kai mu ba - Kashin Shettima

    Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya nemi masu shirya zanga-zanga da su yi amfani da hanyoyin suka dace wajen neman mafita ga matsalolin da ƙasar ke ciki, maimakon shirin zanga-zanga.

    Kashim Shettima ya bayar da wannan shawarar lokacin da ya sanar da shigar Najeriya cikin wani shiri na GCN, na samar da abinci mai lafiya da kawo ƙarshen fama da yunwa da matsalar abinci a duniya da ma Najeriya.

    Mataimakin shugaban ya nemi a yi tunanin yadda za a kawo ƙarshen matsalolin da ƙasar ke fuskanta, ya kuma amsa cewa kasar na cikin mawuyacin hali saboda sauye-sauyen tattalin arzikin da suka gabatar, musamman sakamakon cire tallafin man fetur.

    "Lokaci ne da ya kamata a yi tunanin shawo kan matsalar ta hanyoyyin da suka dace. Dimokradiyya ta bai wa 'yan ƙasa damar su yi zanga-zanga a duka faɗin duniya, amma idan ka fara babu wanda ya san inda za ta ƙare, turba ce da za ta kai ƙasar ga yanayin rashin doka".

  3. Farashin gari da jan wake ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya - NBS

    Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce farashin wake da tumatir da dankalin Turawa da gari da doya da dai wasu kayyakin abinci sun yi mummunan tashi a watan Yunin 2024.

    NBS ta ce ta zaɓi wasu ne daga cikin kayan abincin sannan ta yi rahoto a kansu a watan Yunin 2024.

    Rahoton ya gano cewa kilogiram ɗaya na jan wake ya ƙaru da kashi 252.13 cikin 100, wato ya tashi daga naira 651.12 a watan Yunin 2023 zuwa naira 2,292.76 a watan Yunin 2024.

    "Jan wake ya rinƙa ƙaruwa da kashi 14.11 cikin ɗari a kowane wata a watan Yuni, ya zama naira 2,009.23 a watan Mayu 2024".

    Rahoton ya ce farashin dankalin Turawa ya karu da kashi 288.50 a shekara daga naira 623.75 a watan Yunin 2023 zuwa naira 2,423 a watan Yuni 2024.

    Kilogiram na tumatiri ya ƙaru da kashi 320.67 cikin shekara ɗaya, daga naira 547.28 a watan Yunin 2023 zuwa 2,302.26 a watan Yunin 2024.

    A cewar NBS kilogiram ɗaya na farin gari ya tashi da kashi 181.66 a shekara guda daga naira 403.15 a watan Yunin 2023 zuwa naira 1,135.51 a watan Yunin 2024.

  4. Zanga-zanga: An gayyato sojojin haya daga ƙasashen - Ƴansanda

    Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya shawarci masu shirya zanga-zanga da su sake tunani gabanin fara zanga-zangar.

    A yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja babban birin ƙasar a yau Juma'a, Egbetokun ya ce rahotannin sirri sun tabbatar musu sojojin hayar ƙasashen ƙetare na shirin shiga zanga-zangar.

    Sai dai shugaban 'yan sandan bai yi wani ƙarin bayani kan zargin shigowar sojojin hayar ƙasashen ketare ba cikin zanga-zangar.

    "Muna bibiyar yadda lamura ke faruwa kan zanga-zangar da take mana barazana, yayin da wasu ƙungiyoyi ke neman a yi zanga-zangar tashin hankali irin ta Kenya, wasu kuma na kira a kwantar da hankali a yi ta cikin nutsuwa ba tashin hankali.

    "Wasu na kiran a yi zanga-zangar nutsuwa amma da kausasan kalamai, wani abu da yake sa mu nazari kan gaskiyar lmarinsu. Muna da tarihin zanga-zangar da aka yi ta rikici a Najeriya. A ganina ya kamata mu kalli wasu zanga-zangar da ake yi a wasu ƙasashen da suka zama masu haɗari.

    "Muna kira ga 'yan Najeriya masu kishin ƙasa da su janye daga wannan zanga-zanga, saboda illar da ke cikinta da ta fito ƙarara da kuma rashin sani ga matasan da suke kira a yi tashin hankali," in ji Egbetokun.

    Wasu matasa ne ke shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar daga 1 gawatan Agusta zuwa 15, saboda tsadar rayuwa.

  5. Yadda bam ɗin da aka binne ya tashi a kasuwar Buni Yadi a jihar Yobe

    Wata fashewa da ake zaton wani bam ya haddasa ta tsayar da al'amura cak a kasuwar dabbobi ta Buni Yadi da ke ƙaramar hukumar Gujiba a jihar Yobe.

    Wani mazaunin garin na Buni Yadi ya ce al'amarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 1:30 na ranar Juma'a, ya jikkata wata yarinyar da aka ce ita ce ta taka bam ɗin wanda yake binne a ƙasa.

    "Wata yarinya ce ta taka bam ɗin wanda ke binne, abin da ya yi sanadiyyar fashewar inda kuma ta samu rauni a ƙafarta sakamakon tashin..

    "Bayan fashewar bam ɗin sai sojoji suka zo suka tashin ragowar bama-baman da ke binne domin ka wani ya sake takawa." In ji wani mazaunin Buni Yadi.

    Hukumomi dai har yanzu ba su tabbatar da girman matsalar da fashewar ta haddasa ba da kuma adadin mutanen da al'amarin ya shafa.

    Fashewar dai ta sanya fargici a zukatan ƴan kasuwar inda hada-hada ta tsaya cak a kasuwar dabbobin.

  6. Ƴansandan Afirka ta Kudu sun kama ƴan Libya a wani sansanin soji na bogi

    Ƴan sandan Afirka ta Kudu sun ce sun kama wasu ƴan ƙasar Libya guda 95 a wani sansanin sojin da ba na ƙa'ida ba a Afirka ta Kudun.

    Jami'an tsaron dai sun kai farmaki wata gona a wani gari mai suna White River da ke arewacin lardin Mpumalanga ranar Juma'a.

    Ƴansandan sun ce sun gano tanti-tantin soji da bindigogi masu lisisi da sauran kayan sojoji.

    Sun kuma ce sun samu tabar wiwi da hodar iblis a sansanin.

  7. Zanga-zangar tsadar rayuwa: Za a girke jami'an 'yansanda 4,200 a Abuja

    Rundunar 'yansandan birnin tarayya, Abuja ta ce za ta jibge isassun 'yansanda a faɗin birnin, gabanin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.

    “Za mu ɗauki matakin ne da nufin tabbatar da tsaron al'umma da masu zanga-zangar da kuma magance shigar ɓata-gari cikin zanga-zangar domin aikata ɓarna'', kamar yadda kakakin rundunar 'yansandan birnin, SP Josephine Adeh ta bayyana cikin sanarwa.

    "Haka kuma za mu girke kayan aiki ciki har na'urorin gano ababen fashewa, da ƙwararrun ma'aikata a fannoni daban-daban a sassan birnin''.

    “Sannan kuma jami'anmu za su dirar wa duk wasu mutane ko wuraren da ba ta yarda da su ba, kamar gine-ginen da ba a kammala ba da sauran wurare, haka kuma jami'anmu za su riƙa binciken mutane da ababen hawa ta hanyar aiki da sauran jami'an tsaro'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa rundunar 'yansandan birnin ta ce ba za ta lamunci tayar da rikici ko saɓa wa doka don kauce wa tashin hankalin da ka iya janyo asrar rayuka da dukiya a lokacin zanga-zangar.

  8. Ya kamata Pakistan ta koyi darasi kan abin da ya faru a baya - India

    Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya zargi Pakistan da rashin ɗaukar darasi kan abin da ya faru tsakanin ƙasashen biyu a can baya, yana mai cewa ƙasar na ƙoƙarin tallafa wa 'yan ta'adda.

    Mista Modi na jawabi ne a birnin Kargil na yankin Kashmir - da ake taƙaddama a kai - domin tunawa da nasarar da Indiya ta samu kan Pakistan shekara 25 da suka gabata, a wani babban yaƙi da ya auku tsakanin ƙasashen biyu.

    Duka ƙasashen biyu na iƙirarin mallakar yankin Kashmir, inda ake ci gaba da samun arangama.

    Indiya na zargin Pakistan da mara wa ƙungiyoyin mayaƙan da ke yankin, zargin da ƙasar ta sha musantawa.

  9. Birtaniya ta janye adawa da sammacin kotun ICC na kama Netanyahu

    Birtaniya ta ce za ta janye rashin amincewarta kan sammacin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta bayar na kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    Gwamnatin jam'iyyar conservative da ta shuɗe ta ƙalubalanci hurumin da mai gabatar da ƙarar kotun ke da ita na bayar da sammacin kan Mista Natanyahu da ministan tsarona Yoav Gallant.

    Sai dai sabuwar gwamnatin Labour ta mista Starmer, ta ce ta ɗauki lamarin a matsayin wani batu na kotu.

    Amurka - wadda kamar Isra'ila, ba mamba ce a kotun ta ICC ba - na ci gaba da adawa da sammacin na kama Mista Natanyahu

  10. 'Yansandan Afirka ta Kudu sun kama 'yan Libya 95 a wani samame

    'Yansanda a lardin Mpumalanga na Afirka ta Kudu sun kama tare da tsare wasu 'yan Libya 95, bayan wani samame da suka kai a wata gona da ake zargin ana amfani ita a matsayin sansanin soji ba tare da izini ba.

    Samamen - wanda aka gudanar a White River mai nisan mil 220 gabas da birnin Johannesburg - ya bankaɗo tantuna da kayan aiki irin na sojoji, da kuma miyagun ƙwayoyi ciki har da hodar iblis.

    Hukumomi a lardin sun ce waɗanda ake zargin sun yi iƙirarin cewa sun samu bizar shiga ƙasar ne da nufin horas da su a matsayin masu gadi, amma sai suka tsinci kansu a wani wuri da ya yi kama da sansanin sojoji.

    Cikin wata sanarwar da rundunar 'Yansandan Afirka ta Kudu ta fitar, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan batun, tana mai cewa duk wani abu da zai zame wa ƙasar barazana, to ba za ta ɗauke shi da wasa ba.

    Gidan gonar, wanda tun farko an yi shi ne a matsayin wurin horar da wani kamfanin tsaro na cikin gida, an gano an mayar da shi wajen horar da sojoji ba bisa ƙa'ida ba.

    Ƙasar Libya na fama da matsalar tsaro tun bayan tumɓuke tsohon shugaban ƙasar, Muammar Gaddafi shekara 12 da suka gabata.

    Masu sharhi sun ce a baya Libya ta sha ɗaukar 'yan ƙasashen waje a matsayin sojoji, wani abu da a yanzu ya jefa fargba game da tsaron kan iyakokin Afirka ta Kudu

  11. Amurka ta ƙaƙaba wa shugabannin 'yan tawayen DR Kongo takunkumi

    Amurka ta ƙaƙaba takunkumai kan ƙawancen ƙungiyoyin 'yan tawayen DR Kongo da shugabanninsu, saboda rawar da suke takawa wajen rikicin da ya raba fararen hula masu yawa da muhallansu.

    Shafin Jaridar Politico CD a ƙasar ya ruwaito cewa shugabannin ƙungiyar ƙawancen AFC, Corneille Nangaa da shugaban ƙungiyar M23, Bertrand Bisimwa na daga cikin waɗanda takunkuman Amurkan suka shafa.

    Nangaa - wanda tsohon shugaban hukumar zaɓen DR Kongo ne - na daga cikin mutanen da yanzu haka ke fuskantar shari'ar zargin haɗa baki don cin amanar ƙasa, da aikata laifukan yaƙi.

    A baya-bayan nan ne dai aka kama tsohon shugaban shirin sake tsugunar da mutanen da suka rasa muhallansu a ƙasar, Jean-Bosco Bahala.

    An yi zargin cewa jami'an hukumar leƙen asirin ƙasar ne suka kama shi a filin jirgin saman Kinshasa jim kaɗan bayan komawarsa ƙasar daga Uganda mai makwabtaka.

    A ranar 23 ga watan Yuli ne aka sauke shi daga muƙaminsa bayan da aka zarge shi da zuwa Uganda ba tare da izini ba, don ganawa da jagororin ƙungiyar M23.

    Dakarun sojin DR Kongo sun shafe fiye da shekara biyu suna faɗa da mayaƙan ƙungiyar M23 a kan iyakokin gabashin ƙasar.

  12. Sojojin Najeriya za su kama masu amfani da tufafin sojoji

    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce za ta fara kama mutanen da ke amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba.

    Cikin wata sanarwa da kakain rundunar, Commodore A Adams Aliu ya fitar,ya ce tana gargaɗin mutane domin su fahimci abubuwan da doka ta tanada da kuma illar da ke tattare da amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba.

    Matakin na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun yi zargin cewa wasu mutane waɗanda ba sojoji ba sanya tufafin sojojin ba tare da izini ba.

    "Ya zama dole mu tunatar da jama'a cewa yin amfani da tufafin sojoji ba tare da izini ba laifi ne, kamar yadda sashe na 12, ƙaramin kashi na 110 (1) da (2) na kundin aikata laifuka ya bayyana, laifi ne ga duk mutumin da ba ya aiki cikin rundunar sojin Najeriya, ya sanya tufafin sojoji ko wani abu da ke kama da tufafin," in ji sanarwar.

    Rundunar ta bayyana ƙarara cewa bin wannan umarnin na da matuƙar muhimmanci, kuma rashin bin umarnin na iya haifar da kamawa da kuma gurfanar da mutum a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada.

  13. Obama ya nuna goyon bayansa ga Kamala Harris

    Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama ya nuna goyon baya ga mataimakiyar shugaban ƙasar, Kamala Harris a matsayin ƴar takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Democrat.

    Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa tare da mai ɗakinsa Michelle Obama, sun yaba wa Ms Harris kan "hangen nesanta da kyawawan ɗabi'unta, da kuma ƙwarin gwiwar da ake buƙata a wannan lokaci da suka bayyana da ''mawuyaci''.

    Rahotonni sun ce Mista Obama na cikin fitattun ‘yan jam’iyyar Democrat fiye da 100, da Harris ta tuntuɓa bayan Shugaba Biden ya sanar da janyewa daga takarar a ranar Lahadin da ta gabata.

    Harris ta sami goyon bayan akasarin wakilan da za suyi zaɓen fitar da ɗan takara, da za a yi a babban taron jam'iyyar a watan Agusta.

  14. Babu wasu mutane da suka mamaye gwamnatina da ake kira 'cabal' - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa babu wasu mutane ko wata ƙungiya da ke yin tasiri a sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasar.

    Shugaban ya kuma jaddada cewa shi ne ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensa da kansa ba tare da wani hakki na mutane ko hukumomi ba.

    A yayin ganawarsa da tawagar shugabannin addinin Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau a fadar gwamnati ranar Alhamis, Tinubu ya danganta nasarar zaɓen da ya samu da sa hannun Ubangiji, da tsare-tsare da kuma goyon bayan ƴan Najeriya.

    "Babu wasu mutane da ke juya gwamnatina da ake kira da 'cabal'. Ba ni da waɗanda suka tallafa min ko kuma ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓe na, duk wani kuɗi da aka kashe lokacin yaƙin zaɓena daga aljihuna suka fito, a wasu lokutan ma, irin ƙalubalen da na fuskanta a lokacin sai a hankali, amma Allah Madaukakin Sarki ya riga ya ce ni zan zama shugaban Nigeriya." in ji Tinubu.

    Shugaban ya kuma jaddada bukatar mayar da hankali kan makomar ƴan kasar, inda ya ce, “Abin da ya kamata ya mu sanya a zukatanmu shi ne makomar ƴaƴanmu. Muna da abubuwa da yawa da za mu koya musu a kan abin da ake bukata don zama ɗan ƙasa nagari."

  15. Kamala Harris ta buƙaci a kawo ƙarshen yaƙi a Gaza

    Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris, wadda ake sa ran za ta zama ƴar takarar jam'iyyar Democrat a zaɓen shugaban kasa mai zuwa ta buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza.

    Ta buƙaci hakan ne a yayin tattaunawarta da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a fadar White House

    Harris ta nuna matukar damuwarta game da hasarar rayukan da aka yi a Gaza tare da jaddada muhimmancin yadda Isra'ila ke gudanar da aikin kare kai.

    "Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan yakin," in ji ta bayan ganawarsu.

    Ta kuma bayyana wajabcin bin hanyar sasantawa tsakanin ƙasashe biyu sannan ta bukaci Amurkawa da su fahimci sarkakiyar da ke tattare da yaƙin.

    Tun da farko dai a ranar Alhamis, Netanyahu ya gana da shugaba Joe Biden, wanda kwanan nan ya sauka daga yaƙin neman zaɓensa na sake tsayawa takara.

    Ziyarar Netanyahu a Fadar White House ta biyo bayan wani jawabi mai zafi da ya yi a Majalisa inda ya sha alwashin "kawo ƙarshen ƙungiyar Hamas".

    Firaministan na fuskantar ƙarin matsin lamba a cikin gida da waje domin kawo karshen yakin Isra'ila da Gaza na tsawon watanni tara.

  16. Bazoum na cikin hatsarin fuskantar hukuncin kisa - Lauya

    Shekara ɗaya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, ƙasar na ci gaba da fuskantar sabbin ƙalubale.

    Har yanzu dai hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum da iyalensa na tsare a hannun sojojin da suka yi juin mulki.

    Ana kuma nuna damuwa kan cewa za a iya tuhumar Bazoum da laifin cin amanar ƙasa da kuma yiyuwar fuskantar hukuncin kisa.

    Moussa Coulibaly, lauyan Bazoum, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin mulkin soji na shirin gurfanar da hambararren shugaban a wata kotu ta musamman da ba ta da 'yancin kai da kuma nuna son kai.

    Idan aka same shi da laifi, Bazoum na iya fuskantar hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga.

    Gwamnatin ƙasar ba ta tabbatar da ko musanta wadannan zarge-zargen ba.

    Shekara ɗaya bayan juyin mulkin ƙasar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani, har yanzu ba a san makomar ƙasar ba.

    Sojojin sun hau mulki ne da alkawuran magance matsalar rashin tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar. Sai dai masana sun lura cewa duk da waɗannan alƙawuran, an kashe sojoji da dama, kuma rashin tsaro na ci gaba da yin tasiri ga rayuwar fararen hula.

  17. Tinubu na alhinin rasuwar shugaban ƙungiyar ƙabilar Ibo ta Ohanaeze

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan, shugaban ƙungiyar haɗin kan ƙabilar Ibo da aka fi sani da Ohanaeze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu.

    Mista Iwuanyanwu, mai shekara 82, ya rasu ne ranar Alhamis a Abuja bayan wata gajeriya jinya.

    A cikin sakon ta'aziyyar da Tinubu ya aike wa iyalan marigariyin, ya bayyana Mista Iwuanyanwu a matsayin ƙwararren ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan siyasa.

    Cikin sanarwar ta'aziyyar da kakakin shugaban, Ajuri Ngelale ya sanya wa hannu, Shugaban ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnatin jihar Imo da abokansa da kuma al'ummar Ibo.

    Shi ma tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nuna alhininsa kan rasuwar Mista Iwuanyanwu, inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Najeriya

    Buhari ya ce Najeriya ba za ta manta da irin gudunmowar da ya bai wa ƙasar a fannonin yaɗa labarai da siyasa da wasanni da kuma fannin kasuwanci.

  18. Guguwar Gaemi ta isa China bayan kashe mutane a Taiwan da Philippines

    Mahaukaciyar guguwar nan da ke tafe da mamakon ruwan sama ta isa ƙasar China , bayan da ta yi ɓarnar gaske a Taiwan da Philippines.

    Tuni aka kwashe fiye da mutum 150,000 da ke zaune a lardin Fujian da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    Mahaukaciyar guguwar, ta yi mummunan ta’annati a kan hanyarta ta zuwa Chinan, inda ta nutsar da manyan jiragen ruwa na kasuwanci – da suka haɗa da wani na dakon mai a gaɓar tekun babban birnin Philippines, Manilla, abin da ya haddasa malalar mai a tekun, malalar da ake ganin za ta kasance mafi girma a tarihin ƙasar.

    Guguwar wadda ke tafe da zaftarewar laka ta kashe mutum 21 a Taiwan da Philippines.

    Bayanai dai na cewa duk da ta isa China, zuwa yanzu an samu raguwar ƙarfin iskar, amma duk da haka ba a saki jiki ba domin tuni an riga an sama wa dubban jama’a mafaka a wuraren da ba za su fuskanci hadarin guguwar ba, a matsayin kanda-garki.

    Harkokin sufuri, da suka haɗa da na jiragen ƙasa da na sama, sun dakata a wasu sassan kudu maso gabashin ƙasar ta China.

    Duk da cewa an bayar da rahotannin raguwar ƙarfin guguwar a yau, amma duk da haka ana cike da fargabar samun gagarumin ruwan sama a ƙasar, wanda ka iya haddasa ambaliya irin wadda aka samu bayan mahaukaciyar guguwa da ruwan da aka yi mai lakabin Doksuri, a bara.

    Ambaliyar da a lokacin ta yi ɓarna sosai hatta a gonakin shinkafa da ke yankin arewa masu gabashin China.

  19. Xi Jinping ya gayyaci Tinubu ziyara zuwa China

    Shugaban ƙasar China Xi Jinping, ya gayyaci takwaransa na Najeriya Bola Tinubu, domin kai ziyarar aiki ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da kakain shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce mataimakin ministan ƙasashen wajen China, Chen Xiaodong, ne ya je da saƙon gayyatar ca wata ziyara da ya kai Najeriya.

    Mista Xiaodong ya yaba wa Shugaba Tinubu kan irin tsare-tsarensa, da irin rawar da shugaban ke takawa a matsayinsa na jagoran kungiyar Ecowas.

    “Kai shugaba ne mai haƙaza da fikira. Mun yi imanin cewa ganawar ka da Mista Jinping zai kawo damarmaki masu yawa ga Najeriya da Afirka,’’ in ji shi.

    A nasa ɓangaren shugaban na Najeriya ya yaba wa shugaban China, bisa ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa alaƙa da Najeriya da ƙasashen nahiyar Afirka.

    “Mun yi imani da alaƙar da ke tsakaninmu, kuma muna son yauƙaƙa danƙon zumuncin da ke tsakaninmu , musamman ta hukumomin MDD da ƙungiyar BRICS da G20.'', in ji sanarwar.

    Haka kuma shugaban ya yaba da saƙon gayyatar da shugaban na China ya aika masa na ziyarar aiki zuwa China.

  20. Maraba lale

    Masu bin wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da Juma'a, Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.