Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/06/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Trump ya ce Iran na neman a yi sulhu, Ayatollah Khamenei ya ce ƙarya ne

    Shugaba Trump yaƙi ya bayyana ko Amurka za ta shiga wannan yaƙin ko kuma za ta yi kokarin ganin an yi sulhu ne, yayin da aka shiga rana ta shida jere ana luguden wuta.

    A tsokacin baya-bayan nan, Shugaba Trump ya ce wataƙil ya shiga, wataƙil kuma ba zai shiga ba.

    Ya yi iƙirarin cewa Iran na son ya ba ta dama ta zo fadarsa ta White House a tattauna, amma ya ƙi yarda.

    A cewarsa tuntuni da aka ba ta dama ya kamata ta nemi hakan - ba yanzu ba da karfinta ya ƙare.

    Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi gargaɗi cewa Iran za ta mayar da mummunan martani idan Amurka ta ɗauki matakin soji kan ƙasar.

  2. Isra'ila ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa Tehran

    A yayin taronta na manema labarai na yau da kullum, rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan cibiyoyin ƙera makama masu linzami na ƙasar Iran.

    Rundunar ta ƙara da cewa a wani jerin hare-hare na sa'a uku, ta ragargaza cibiyar samar da makamashin nukiliya na Iran.

  3. Iran ta sake kai hare-haren makamai masu linzami

    Iran ta sake harba wasu makaman masu linzami kamar yadda gidan talbijin na ƙasar ya sanar, inda makaman suka isa wurin da aka nufa cikin nasara.

    Dakarun Isra'ila ba su ce uffan ba dangane da harin da ya sauka a gine-ginen tsaron Isra'ilar amma dakarun sun ce su ma ƙasarsu ta aike da makamai masu linzami zuwa cibiyar ƙera makamai masu linzami na Iran.

  4. Mene ne LRBM, mugun makamin da Iran ke yi wa Isra'ila ruwan wuta da shi?

    Bayan hare-haren da Isra'ilata ƙaddamar kan cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma manyan sojojinta, Iran na mayar da martani ta hanyar harba manyan makamai masu linzami kan Isra'ila, inda wasu suka faɗa inda aka harba su.

    Duk da cewa Isra'ila na cewa tana kakkaɓo da dama cikin makaman, wasu masu yawa sun samu tsallake tsaron sararin samaniyar ƙasar, inda suke faɗawa inda aka tura su, ciki har da Tel Aviv, babban birnin ƙasar, lamarin da ya haifar da gagarumar ɓarna da rasa rayuka.

    Babu cikakkun bayanai game da girman makaman masu linzami da Iran ke amfani da su, to amma an yi imanin cewa makaman na ɗaya daga cikin manyan makamai masu haɗari da ake da su a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Waɗannan makaman sun bambanta dangane da tazarar da za su iya tafiya, akwai mai cin gajeren zango da ake yi wa laƙabi da SRBM.

    Akwai kuma masu cin matsakaicin zango, da ake kira da MRBM/IRBM da kuma masu cin dogon zango, LRBM, waɗanda za su iya tafiyar dubban kilomita.

  5. Mafi yawan Amurkawa ba sa son Amurka ta yaƙi Iran - Sanata Kaine

    Sanatan da ke wakiltar Virginia ɗan jam'iyyar Democrat, Tim Kaine ya ce mafi yawancin Amurkawa ba sa son Amurka ta saka kanta a yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran.

    Ya ce wannan ra'ayin al'ummar da yake wakilta ne na Virginia jihar da ya bayyana da "mai son yaƙi".

    "Mummunar shawara ce idan Amurka ta sake shiga wani yaƙi a Gabas ta Tsakiya," in ji Kaine.

    Ya ƙara da cewa idan Amurka ta shigar wa Isra'ila ta yaƙi Iran , Iran za ta mayar da martani.

    "Babu buƙatar mu yi wannan abu," inda ya ƙara da cewa "kuma na faɗi wannan a matsayin mutumin da ya goyi bayan bai wa Isra'ila dukkan tallafin da aka ba ta."

  6. Iran ta gargaɗi mazauna Haifa na Isra'ila su fice daga birnin

    Iran ta yi kira ga mazauna birnin Haifa na Isra'ila su fice daga birnin, kada su jefa rayukansu cikin hatsari.

    Birnin na Haifa ya fuskanci hare-haren Iran cikin makon nan.

    Isra'ila ta ce ka samu nasarar kakkaɓo mafiya yawan hare-haren, kodayake wasu sun faɗa wasu yankunan birnin.

  7. Tinubu ya buƙaci jami'an tsaro su kamo masu hannu a kashe kashen Benue

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya buƙaci jami'an tsaron ƙasar su tabbatar da kamo masu hannu hare-haren da suka haddasa mace-mace masu yawa a jihar Benue.

    Yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar, Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴansanda da sojojin asar su ƙara ƙaimi don tabbatar da kamo waɗanda suka aikata kashe-kashen.

    Fiye da mutum 100 ne dai suka mutu yayin da sama da 6,000 suka rasa muhallansu a hare-haren baya-bayan nan a jihar da ke tsakiyar Najeriya, a cewar hukumar NEMA.

    “Ku ƴansanda, in fatan jami'anku za su ƙara ƙaimi wajen samo bayanai game da maharan, me ya sa har yanzu ba wanda aka kama? Na yi tsammanin an kama masu laifin,'' in ji Tinubu.

    “Kai ma Christopher (babban haftsan tsaron ƙasar), ka yi iya ƙoƙarinka. Na saurari bayananka, ka yi matuƙar ƙoƙari. Oloyede da babban hafsan sojin sama, duka mun gode muku, amma muna buƙatar ƙara jajircewa, mu kwamo masu laifin nan. Shugaban hukumar tattara bayanan sirri da na hukumar tsaron farin kaya, ku ƙarfafa hanyoyin samun bayananku, domin samun bayanan sirri ta yadda hakan ba zai sake faruwa ba''.

  8. Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 144 a cikin kwana guda - Ma'aikatar Lafiyar Hamas

    Ma'aikatar Lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce an kai gawarwaki 144 zuwa asibitocin Gaza a cikin kwana guda, yayin da Isra'ila ke ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a yankin.

    Ma'aikatar Lafiyar ta ce fiye da Falasɗinawa 500 aka kai asibiti sakamkon raukan da suka samu.

    Tun da farko jami'an lafiya da hukumar tsaron fararen hula ta civil defence da ke Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 11 a tsakiyar Gaza, waɗanda ke jiran kayan agajin Majalisar Dinkin Dinkin Duniya.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ''tana ƙaddamar da hare-hare ne domin karya ƙarfin mayaƙan Hamas''.

    shugaban hukumar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Lazzarini, ya ce hare-hare kan ''mutanen da yai da yunwa suka ɗaiɗaita sun zama abubuwa na yau da kullum''.

  9. Hotunan Tinubu na duba marasa lafiya a ziyarar zuwa Benue

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya duba marasa lafiyar da ke kwance a asibiti bayan raunukan da suka samu a hare-haren jihar Benue.

    Rahotonni sun ce fiye da mutum 200 aka kashe a hare-haren bayan-bayan nan da wasu masu ɗauke da makamai suka ƙaddamar.

    Wannan ne karo na farko da shugaban ke ziyartar mutanen da ke fama da tashen-tashen hankula a ƙasar.

    Masu suka na zargin shugaban da kasa kare al'ummar ƙasar, yayin da ake samun ƙaruwar rikice-rikice a wasu sannan ƙasar.

    Fiye da mutum 6,000 ne dai suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren.

  10. Bidiyon caje rigar maman ɗalibai mata na ci gaba da shan suka a Najeriya

    Wani ce-ce-ku-ce ya ɓarke a Najeriya bayan ɓullar wani bidiyon yadda ake caje rigar maman wasu ɗaliban jami'a kafin shiga ɗakin jarrabawa.

    A cikin bidiyon - wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta - an ga yadda wasu malaman Jami'ar Olabisi Onabanjo da ke jihar Ogun ke taɓa wa ɗalibai mamansu a wani mataki na caje su a lokacin da suke kan layin shiga ɗakin jarrabawar.

    Jami'ar ta ce tana da tsauraran dokokin da suka yi tanadin cewa ''dole kowace ɗaliba ta sanya rigar mama kafin shiga jarrabawa'', a wani ɓangare na tsohon tsarin jami'ar kan dokar sanya tufafi.

    Masu suka sun yi Allah wadai da tsarin, wanda suka bayyana da tsohon yayin da ke ƙarfafa lalata, yayin da wasu ke bayyana shi da cin zarafin lalata.

  11. Wane ne Ayatollah Ali Khamenei, jagoran addini na ƙasar Iran?

    Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini na Iran na biyu bayan juyin-juya halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979, kuma tun a shekarar 1989 yake riƙe da muƙamin.

    Shi ne jagoran askarawan ƙasar, ciki har da dakarun juyin juya-halin ƙasar wato Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).

    Yana riƙe ne da madafun iko mai ƙarfin gaske - yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon zaɓa ko naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.

    Matasan ƙasar yawanci sun taso ne suna ganin sa a matsayin jagoran addininsu.

  12. 'Har yanzu ba a ga fiye da mutum 700 ba bayan ambaliyar Mokwa'

    Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu ba a ga fiye da mutum 700 ba bayan ambaliyar da ta shafi garin Mokwa a jihar da ke tsakiyar Najeriya.

    Yayin da yake jawabi a lokacin da Manjo Janar Hamza Al-Mustpha ya kai masa ziyarar jaje, Gwamnan Bago - wanda mataimakinsa ya wakilta ya ce mutum 207 aka tabbatar da mutuwarsu sakamkon ambaliyar.

    A farkon watan nan ne wata mummunar ambaliya ta auka wa garin Mokwa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukoiyoyi masu ɗimbin yawa.

    “Har yanzu ba mu ga fiye da mutum 700 ba, kuma ba mu iya gano inda suke ba, bayan ambaliyar - wadda ta lalata gine-gine fiye 3,000,'' in ji mataimakin gwamnan.

    Gwamnatin jihar ta ce tana aiki hannu da hannu da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran hukumomi domin gano musabbin ambaliyar domin ɗaukar matakan da suka dace.

  13. Tinubu ya isa Benue a ziyarar da yake yi bayan kashe-kashen jihar

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya a wata ziyara da yake yi bayan wasu kashe-kashe da aka samu a wasu yankunan jihar.

    Rahotonni sun ce fiye da mutum 200 aka kashe a hare-haren bayan-bayan nan da wasu masu ɗauke da makamai suka ƙaddamar.

    Wannan ne karo na farko da shugaban ke ziyartar mutanen da ke fama da tashen-tashen hankula a jihar.

    Masu suka na zargin shugaban da kasa kare al'ummar ƙasar, yayin da ake samun ƙaruwar rikice-rikice a wasu sannan ƙasar.

    Fiye da mutum 6,000 ne dai suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren.

  14. Yadda kawuna suka rabu a Amurka kan taimakon Isra'ila a yaƙi da Iran, Sharhi daga Bernd Debusmann Jr da Max Matza

    Tsaka mai wuyar da Amurka ke ciki kan ko za ta tallafa wa Isra'ila wajen kai wa Iran hari, ko kuma ta tsame hannunta kacokan daga rikicin ya fallasa rarrabuwar kawunan da ke tsakanin masu goyon bayan shugaba Donald Trump.

    Rahotanni sun nuna cewa shugaban na Amurka na tunanin tallafa wa Iran wajen tarwatsa cibiyoyin sarrafa nukiliya na Iran, bayan tattaunawar da ya yi da masu ba shi shawara kan tsaro a fadar White House, ranar Talata.

    Masu goyon bayan taken Trump na 'fifita Amurka a kowane yanayi' sun dage kan cewa Trump ya ci alwashin kauce wa tsoma Amurka cikin "dagayen yaƙe-yaƙe" irin waɗanda suka janyo kashe-kashen ɗimbin dakarun Amurka a Afghanistan da Iraqi.

    Sai dai ƴan ina-da-yaƙi na jam'iyyar Republican mai mulki na ingiza Trump ya afka wa Iran.

    Sanata daga Kudancin Carolina, Lindsey Graham ya ce abu ne da zai amfani Amurka idan aka hana Iran mallakar makamin nukiliya.

    Iran dai ta dage kan cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.

  15. NEMA ta tarbi ƴan Najeriya 147 da aka dawo da su daga Nijar

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA), reshen jihar Kano ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 147 da aka dawo da su daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce mutanen sun sauka ne a filin Jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:48 na rana a ranar 16 ga Yunin 2025.

    Hukumar kula da ƙaura ta Duniya (IOM) ta ce tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi masu kula da harkokin 'yan ci-rani suka jagoranci dawo da su gida.

    NEMA ta ce, waɗanda aka dawo da su sun ƙunshi maza 143, da mace guda da kuma ƙananan yara uku.

    An kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka dawo da su na fama da rashin lafiya, kuma ya samu kulawar gaggawa daga ƙungiyar agaji ta Red Cross da ke wajen bayar da taimako a wurin.

  16. INEC ta ƙi amincewa da buƙatar PDP na gudanar da babban taronta na NEC

    Hukumar Zaɓen Najeriya (INEC) ta bayyana cewa jam’iyyar adawa ta PDP ba ta cika ƙa'idoji ba a yunƙurinta na gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100.

    A wasiƙar da ta aike wa PDP, hukumar ta INEC ta ce wasiƙar buƙatar amincewarta da PDP ta aike mata ba ta cika ƙa'idojin tanade-tanade da hukumar ta shimfiɗa ba.

    A ranar 30 ga Mayu ne, PDP ta aike wa INEC wasiƙa domin sanar da ita shirin jam'iyyar na gudanar da taronta na NEC, da za ta gudanar a hedikwatarta da ke Abuja.

    A cikin wasiƙar, shugaban riƙo na jam'iyyar, Umar Damagum ne kaɗai ya sanya mata hannu.

    INEC ta bayyana cewa sanarwar taron na PDP ya kamata a samu sanya hannun shugabanta na ƙasa da kuma sakatarenta na ƙasa.

    Jam'iyyar dai na fama da rikic kan kujerar sakataren jam'iyyar ƙasa, inda Samuel Anyanwu da Sunday Udeh-Okoye ke jayayya kan wanda ya dace da wannan matsayi.

  17. Za mu yi wa Amurka lahanin da ba zai gyaru ba idan ta kai mana hari - Ayatollah

    Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi gargaɗi cewa Iran za ta mayar da mummunan martani idan Amurka ta ɗauki matakin soji kan ƙasar.

    Cikin wani jawabi da jagoran ya gabatar wa al'ummar ƙasar aka kuma yaɗa a gidan talbijin na ƙasar, Ayatolla ya ce Iran ba za ta lamunci hari daga Amurka ba.

    “Idan Amurka ta yi amfani da karfin soja, za ta fuskanci lahani da ba za a iya gyarawa ba.”

    "Mutane masu hikima waɗanda suka san Iran da mutanenta da tarihinta, (sun san cewa) ba a yi musu barazana, domin Iraniyawa ba mutane ne da ke miƙa wuya ba," in ji Khamenei a cikin sanarwar.

  18. Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram da suka yi ƙoƙarin kutsawa sansaninsu

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Hadin Kai sun daƙile wani yunkurin kai hari da 'yan Boko Haram da ISWAP suka yi a sansanin sojojin ruwa da ke Tafkin Chadi, a yankin Fish Dam, inda suka halaka da dama daga cikin su a wani samame na haɗin gwiwa.

    Rundunar ta faɗi hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

    Sanarwar ta ce mayaƙan Boko Haram ɗin sun fara harin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, da nufin lalata sabbin motocin ruwa na musamman da gwamnatin Jihar Borno ta tanada domin share hanyoyin ruwa a Tafkin Chadi.

    Sai dai ƙoƙarinsu ya ci tura, domin sojojin ruwa a sansanin Tafkin Chadi sun yi musu kwanton-ɓauna tare da samun ƙarin goyon baya daga sansanin Baga.

    "An samu musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin da ƴan Boko Haram din har na tsawon sama da sa'o'i biyu, inda daga ƙarshe suka janye ba tare da cimma burinsu ba kuma sojojin sun samu nasarar halaka da dama daga cikin su tare da ƙwato wasu makamai da na haɗa bam." in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma ce a yayin harin, mayakan sun samu damar lalata wasu kayayyaki guda uku ciki har da motar ɗaukar marasa lafiya da wasu motocin aiki biyu.

    Haka kuma, wasu dakarun rundunar sun samu raunuka a lokacin musayar wutar.

  19. 'Hare-haren Isra’ila sun shafi wasu cibiyoyin inganta makamashin uranium a Iran'

    Hukumar kula da makaman nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IAEA) ta bayyana cewa hare-haren sojojin Isra’ila sun shafi wasu wurare biyu da ke inganta makamashin uranium Tehran da Karaj na Iran.

    Hukumar IAEA ce ta sanar da hakan a safinta na X a ranar Laraba.

    Wannan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun ƙarin tashin hankali tsakanin Iran da Isra’ila.

  20. Najeriya za ta kwashe mutanenta daga Isra'ila da Iran

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin kwashe ƴan ƙasarta da suka maƙale a ƙasashen Isra’ila da Iran, bayan tsanantar rikici tsakanin ƙasashen biyu.

    A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya ce jakadun Najeriya a Tel Aviv da Tehran na ci gaba da tuntuɓar ’yan ƙasar da rikicin ya rutsa da su, tare da aikin tabbatar da cewa an kwashe su cikin aminci da kariya.

    Ma’aikatar ta buƙaci ’yan Najeriya da ke zaune a Isra’ila da Iran da su bi dukkan matakan tsaro da hukumomin ƙasashen suka shimfiɗa, sannan kuma su hanzarta tuntuɓar ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa domin yin rajista da samun ƙarin shawarwari.

    Ma’aikatar ta yaba wa jajircewar ofisoshin jakadancin Najeriya a Isra’ila da Iran wajen tuntuɓar ’yan ƙasar a wannan lokaci mai cike da ƙalubale, tare da jaddada cewa kariyar lafiyar ’yan Najeriya da ke kasashen waje na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci.

    “Ma’aikatar harkokin waje na sanar da cewa sakamakon rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin tarayya na kammala shirye-shiryen kwashe ’yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen biyu.” in ji sanarwar.

    Sanarwar ta zo ne bayan hare-haren sama da Isra’ila ta kai a ranar Juma’a, inda ta hari wurare kimanin 100 a fadin Iran, ciki har da cibiyoyin nukiliya da na soji inda hare-haren suka hallaka manyan jami’an sojin Iran da dama.