Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/08/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Aisha Bappa da Abdullahi Bello

  1. Gwamnatin jihar Enugu ta umarci coci-coci da masallatai su cire duk lasifikarsu ta waje

    Gwamnatin jihar Enugu a Najeriya ta umarci dukkanin majami'u da masallatai a jihar su cire duk wata lasifika da suka sa a wajen gine-ginensu cikin kwana 90, sannan kuma su dauki matakan tabbatar da cewa hayaniya ko karar abubuwan da ake yi a cikin wuraren ibadar ba ta fitowa waje.

    An dauki matakin ne a yau Alhamis, a lokacin wani taro tsakanin hukumomin da shugabannin Kiristoci da Musulmi a jihar, kan aiwatar da tsarin gwamnatin jihar na takaita hayaniya.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar raya babban birnin jihar ta Enugu, Uche Anya, wanda ya bayar da umarnin ya ce hayaniya da kara sun zama babbar matsala ga jihar.

    Shugaban ya nuna takaicin yadda ofishinsa ya samu koke sama da 1,000, daga masu gidaje a kusa da wasu coci-coci da masallatai da wuraren rawa ko shaye-shaye da makamantansu a kan kara ko hayaniya da ke damunsu

    A shekarar da ta wuce, 2023, gwamnatin jihar, da ke kudu maso gabas, a wani mataki na sake tsarin raya biranenta, ta umarci dukkanin wuraren nishadi da sharholiya da shaye-shaye da kade-kade da sauran abubuwa na walwala da su takaita hayaniyar da ake yi a wuraren, a babban birnin jihar, musamman ma a unguwannin da gidajen jama'a suke.

  2. Kananan hukumomi 14 na fuskantar hadarin ambaliya a jihar Kano - NEMA

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta yi gargadin cewa garuruwa 362 a kananan hukumomi 14 a jihar kano na cikin hadarin bala'in ambaliya.

    Shugabar hukumar ta NEMA, Zubaida Umar, ce ta yi gargadin a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan zubar da shara da shirya tunkarar ambaliya, a Kano, yau Alhamis.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar kula da harkokin da suka shafi ruwa ta kasar ta yi hasashen cewa al'umma 3,749,200 na cikin hadarin ambaliya a jihar ta Kano.

    Kananan hukumomin da ambaliyar za ta iya shafa a cewar hukumar sun hada da, Rimin Gado, da Tofa, da Kabo, da Madobi, da Garun Malam, da Bebeji, da Rano, da Dawakin Kudu, da Warawa, da Wudil, da da Sumaila, da Ajingi, da Kura da kuma Dala.

    NEMA ta ce, bala'in ambaliyar da aka gani a 2012 da 2022, ya nuna muhimmancin hada hannu a tsakanin dukkanin matakan gwamnati wajen tunkara da magance bala'o'i.

    Shugabar hukumar ta kuma jaddada muhimmancin wayar wa da jama'a kai kan hanyoyin zubar da shara da kuma ankarar da jama'a kan hadarin.

  3. Gwamnatin Kano da UNICEF sun ware naira biliyan daya domin yakar Tamowa

    Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF, da gwamnatin jihar Kano sun ware naira miliyan dubu daya domin samar da abinci na musamman da ake bai wa yara 'yan kasa da shekara biyar masu fama da cutar tamowa.

    Jami'in asusun kan abinci mai gina jiki a jihar ta Kano Mista Oluniyi Oyedekun wanda ya yaba da bayar da naira miliyan 500 da gwamnatin jihar ta yi, a lokacin bude taron kwana biyu na masu ruwa da tsaki a jihar, ya ce asusun zai bayar da nasa kason na naira miliyan 500 na samar da abincin na musamman.

    A jiya Laraba jami'in na UNICEF, ya ce kashi 56.9 cikin dari na yara 'yan kasa da shekara biyar a jihar ta Kano, sun tsumbure saboda rashin isasshen abinci mai gina jiki.

    Haka kuma asusun tare da gwamnatin jihar a yayin taron na yau Alhamis, sun jaddada kudurinsu na magance matsalar karancin jini ga mata masu juna biyu a jihar.

  4. Shugaba Biden na Amurk ya bi sahun masu neman a sake zabe a Venezuela

    Shugaban Amurka Joe Biden ya bi sahun sauran takwarorinsa na kasashen duniya wajen yin kira da a gudanar da sabon zabe a Venezuela, bayan zaben da aka gudanar a watan da ya gabata.

    Mista Biden ya shaida wa manema labarai a Washington cewa ya goyi bayan shawarar da Brazil da Colombia suka bayar ta a sake zaben shugaban kasar.

    'Yan hamayya a kasar ta Venezuela sun zargi Shugaba Nicolas Maduro sa tafka magudi.

    Shugaban Brazil Lula da Silva ya ce kafa gwamnatin hadaka zai iya warware rikicin siyasar Venezuela.

    An kama sama da mutum 2,000 dubu biyu yayin zanga-zangar kin amincewa da nasarar Mista Maduro.

  5. Dalilin da ya sa muke tsare da shugaban hukumar alhazai ta Najeriya - EFCC

    Wata majiya mai karfi daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, ta EFCC ta tabbatar wa BBC cewa hukumar na ci gaba da tsare, shugaban hukumar alhazan Najeriya, Jalal Arabi tare da sakataren hukumar Abdullahi Kontagora.

    Ana zargin shugaban da yin sama da fadi da wani bangare na naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta ba hukumar a matsayin tallafi ga aikin hajjin 2024 da ya gabata.

    Hukumar ta ce an gano kudin da yawansu ya zarta Riyal dubu 300 daga hannun shugaban da wasu manyan jami’an hukumar hajjin ta Najeriya.

    EFCC ta kara da cewa bincikenta ya gano shugaban hukumar ya yi amfani da wani bangare na naira biliyan 90 din da gwamnatin Najeriya ta bai wa hukumar aikin hajjin a matsayin kudaden tallafi wajen biyan kansa da manyan jami’an kudaden da suka wuce kima.

    Bayanan sun nuna cewa hukumar na neman bahasi ne game da yadda aka kashe naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa NAHCON a matsayin tallafi ga mahajjatan Najeriya na 2024 da aka kammala a watan Yuli.

    Kazalika, hukumar EFFCn ta ce a kasafin kudi na bana ainihin kudaden da aka warewa kwamishinoni da manyan daraktoci da ma’aikatan hukumar sun saba yadda suka tsara nasu tare da wawure kaso mafi yawa daga abin da aka kayyade ma kowanensu.

    Majiyar ta EFCC ta kara da cewa ana zargin shugaban hukumar hajjin da ware wa kansa Riyal dubu hamsin a maimakon riyal dubu goma sha biyar da dari tara da shirin da tara da aka ware masa a hukumance, yayin da kwamishinonin hukumar uku da aka ware wa riyal dubu goma sha biyar da dari tara da ashirin da tara kowanensu sai ga shi an biya su riyal dubu arba’in.

    Tun a ranar 30 ga watan Yuli ICPC ta gayyaci shugaban hukumar alhazan, Jalal Arabi, domin ya yi mata bayani game da yadda hukumar ta gudanar da aikin Hajjin da ya gabata.

    Wata sanarwa daga hukumar ta ce an gayyace shi ne kawai bisa tsari kamar yadda hukumar ta saba yi duk bayan kowane aikin Hajji.

    Tun da farko naira miliyan hudu da dubu dari tara ne hukumar ta tsayar a matsayin kuɗin kujerar zuwa aikin Hajjin da maniyyata za su biya, amma sai ta mayar da shi miliyan shida da dubu dari takwas tana mai ɗora alhakin kan karyewar darajar naira.

    Bayanin ya kara da cewa an gano zunzurutun kudin da yawansu ya kai riyal miliyan takwas da dubu dari shida da sha hudu da aka cire daga cikin naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta bayar da aka canza su zuwa dalar Amurka inda suka kama dala miliyan sittin da biyu da dubu dari uku da bakwai da dari da sittin da hudu, da kuma aka saka su asusun ajiyar hukumar aikin hajjin da ke Saudiyya.

    Kuma har yanzu ita kanta hukumar aikin hajjin ta kasa yin cikakken bayanin yadda sauran kudaden suka yi batan-dabo.

    Ba ya ga biyan wasu kamfanoni da ke kasar Saudiyya miliyoyin kudaden da ba a san takamaiman aikin da suka yi ba.

    A kwanan baya a hirarsa da BBC, Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba, tsohon wakilin Sokoto ta Kudu a Majalisar Dattijai ta Najeriya ya ce irin badaƙalar da bincikensu ya gano game da ayyukan wasu daga cikin jami'an Nahcon, ya hada da badakalar kama wa mahajjata dakunan kwana a otal da ya wuce kima inda a maimakon a kama na kwana 40 sai a kama na kwana 90 domin a saka wasu daga baya a yi kashe-mu-raba tsakanin NAHCON da masu otal-otal din.

  6. Za a fara biyan masu sanya bidiyo a Facebook a Ghana

    Masu ƙirƙirar bidiyo don wallafawa a dandalin sada zumunta na Meta a Ghana na ci gaba da bayyana murnarsu, kan matakin kamfanin na amincewa a fara biyan ƴan ƙasar masu ɗora bidiyo a shafinsu na Facebook.

    Daman tun a baya kamfanin na Meta mai Facebook da Instagram da WhatsApp ya sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Yuli na 2024 zai fara biyan wadanda suka cancanta, da ke sanya hotunan bidiyo a shafukansu na Facebook.

    Ana sa ran wannan matakin zai haifar da bunƙasar tattalin arziki, tare da samar da dubban ayyuka ga mutane musamman matasa yayin da ake fuskantar matsanancin rashin aikin yi a kasat ta yammacin Afirka.

    An dade ana fatan ganin ranar da daya daga cikin manyan kamfunan sada zumunta a duniya na Facebook zai fara biyan `yan kasar ta Ghana masu kirkiro bidiyo suna dorawa a kan shafin.

    Dubban matasa ne a Ghana suka rungumi sana`ar kirkiro bidiyo suna wallafawa a kan intanet don rufa wa kai asiri yayin da matsalar rashin aiki ta yi kamari.

    Duk da yake masana na son barka da wannan cigaba amma suna kiran gwamnati da ta kara jajircewa a wajen sa ido a kan irin abubuwan da masu kirkio bidiyo za su rinka dorawa a kan shafukansu.

    Musamman yayin da ake shirin gudanar da babban zaben kasar ta Ghana a watan Disamba mai zuwa, ganin cewa wasu ka iya amfani da wannan dama wurin yada farfaganda ko labaran kanzon-kurege da cin zarafi, ko kyama, wanda haka zai iya janyo tarzoma.

  7. Shugaba Tinubu da takwaransa na Equatorial Guinea sun kulla yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu na najeriya tare da takwaransa na Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, sun kulla wata yarjejeniyar aikin shimfida bututun iskar gas a tsakanin kasashen.

    Shugabannin biyu sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a babban birnin kasar ta Guinea, Malabo a yau Laraba, yayin ziyarar kwana uku da shugaban na Najeriya yake yi a can.

    Yarjejeniyar ta kunshi aikin shinfida butun, da tura iskar gas da sauran al'mura da suka jibanci harkar tura gas din.

    Shugaba Tinubu ya ce, yarjejeniyar za ta bude damarmaki na hakar iskar gas da kuma samar da ayyukan yi.

    A nasa bangaren shugaban na Equatorial Guinea, ya ce alaka tsakanin kasarsa da Najeriya wadda ta tsawon shekaru ce, tana haifar da alfanu, ida ya bukaci kara zurfafa ta har zuwa wasu fannonin.

    Ministocin waje na kasashen biyu su ma sun sanya hannu a kan yarjejeniyar.

    Haka kuma Shugaba Mbasogo ya ce, burin Afirka na samun kujerar dindindin a Majaisar dinkin duniya na da muhimmanci sosai ga bunkasar nahiyar, inda ya bayar da tabbacin cewa kasarsa za ta yi aiki da Najeriya domin cimma wannan buri.

  8. Wani hari ya kashe wani mai bayar da shawara na sojin Iran a Syria

    Rahotanni sun ce wani mashawarci ga rundunar sojan Iran da ke Syria ya mutu sakamakon raunukan da ya ji a wani hari ta sama a cikin wasu makonni da suka wuce.

    Kamfanin dillacin labaran Iran, Fars, ya ce mutumin, Kanar Ahmedreza Afshari, jami'i ne bangaren mayakan sama na rundunar sojin juyin-juya hali.

    Amurka da Isra'ila kan kai hari ta sama a-kai-a-kai kan mayaka masu alaka da Iran a Syria, wadanda suka mara wa Shugaba Bashar Al Assad baya sosai.

    A watan Afirilu, Iran ta kaddamar da hari na farko kan Isra'ila bayan wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gidan jami'an jakadancin Iran a Damascus.

  9. An kai wa mahaifin ɗan ƙwallon Sifaniya Yamal farmaki

    Mahaifin matashin ɗan wasan ƙwallon Sifaniya, Lamine Yamal, mai suna Mounir Nasraoui, ya fuskanci fushin wasu fusatattun mutane, waɗanda suka kai masa hari, tare da yi masa dukan na kawo wuƙa.

    Kamar yadda rahotanni daga Sifaniya suka nuna, wasu matasa ne da cacar baki ta wakana a tsakaninsu da da mahaifin ɗan wasan da rana suka kai masa farmakin a yankin Mataró, da ke Arewacin Barcelona a daren ranar Laraba.

    Ƴan sandan yankin Catalan sun tabbatar da kama mutum uku da ake zargi a ranar Laraba, sannan an tsare na huɗun a safiyar Alhamis.

    An kai Mista Nasraoui wani asibiti a birnin Barcelona cikin yanayi marar kyau, amma zuwa yanzu ya samu sauƙi.

    An kai masa farmakin ne kusa da Rocafonda, inda Yamal ya taso.

    Har yanzu dai ba a tabbatar da dalilin matasan na ɗaukar wannan matakin ba.

    A wani rahoton da jaridar intanet ta wasanni ta Relevo ta ce Mista Nasraoui zai ci gaba da zama a asibiti zuwa kwana biyu ko uku ana kula da lafiyarsa.

    Lamine Yamal, dai shi ne matashin da ya fi ƙarancin shekaru da ya taɓa wakiltar ƙasar Sifaniya, inda ya samu nasarar lashe Gasar Euro ta bana, sannan ya lashe kambun matashin gasar mafi ƙwazo.

  10. Kotu a Rasha ta ɗaure matar da ta taimaka wa ƴan Ukraine

    Wata kotu a Rasha ta ɗaure wata mata mai suna Ksenia Karelina, shekara 12 a gidan yari bisa laifin cin amanar ƙasa, saboda ta tallafa wa wata gidauniya da $51 (£39) domin ayyukan jin ƙai a Ukraine.

    Karelina, wadda take da shaidar zama ƴar ƙasar Amurka da Rasha, an same ta da laifin ne bayan zaman da kotun ta yi ba tare da masu sauraro ba.

    An kama ta ne a lokacin da ta kai wata ziyara birnin Yekaterinburg kimanin kilomita 1,600 ta Gabashin Moscow a watan Janairun da ya gabata.

    Masu gabatar da ƙara sun buƙaci kotu ta ɗaure ta ne tsawon shekara 15.

    Kotun ta same ta da babban laifin cin amanar ƙasa, sannan ta yanke mata hukuncin zama a gidan yarin.

    Rundunar tsaron FSB ta Rasha ce ta gabatar da Karelina a gaban kotu, tana zarginta da tara kuɗi domin tallafa wa ƙungiyoyin agajin da suke ayyukansu a Ukraine, waɗanda suke taimakon ayyukan soji.

    Lauyan da ke kare ta,Mikhail Mushailov, ya ce Karelina ta amince ta tura kuɗi ne kawai, wanda ta ce ta yi amannar za a yi amfani da shi ne domin taimakon waɗanda yaƙin ya shafa daga kowane ɓangare.

    Ta bayyana wa kafofin watsa labarai a Rasha cewa za ta ɗaukaka ƙarar a kan hukuncin.

  11. Farashin kayan abinci ya sauka karon farko cikin wata 19 a Najeriya

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta sanar a ranar Alhamis cewa, farashin kaya a ƙasar ya sauka a karon farko da kashi 33.4 cikin 100 a watan Yuli inda aka kwatanta da kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin shekarar da muke ciki.

    Kayayyakin da farashin nasu ya sauka sun haɗa da shinkafa da masara da ƙwai da burodi da man fetur.

    To sai dai kuma farashin makamashi na ci gaba da hauhawa a cikin shekara ɗaya da ta wuce a cewar hukumar.

    Najeriya dai ta fara aiwatar da manufofin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar tun a bara.

    Ƙasar ta dauki matakai kamar cire tallafin man fetur da kuma farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, naira.

    Shugaba ƙasar Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen na da matukar muhimmanci kuma ya zama dole da nufin farfaɗo da tattalin arziƙin.

    A farkon watan Augusta ne ƴan kasar suka gudanar da zanga-zanga a kan matsin rayuwa ta kwana 10 don matsawa gwamnati ɗaukar matakan sassauta al'amura.

  12. Wane tasiri sace takardun kotu zai iya yi ga sharia?

  13. Hotunan yadda ake fafata yaƙi a Ukraine

  14. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum bakwai a Bauchi

  15. NNPCL ya bankaɗo haramtattun matatun mai 63 a Najeriya

  16. Gwamnatin India ta sha alwashin hukunta waɗanda suka yi wa likita fyade

  17. M23 ta sake ƙwace iko da wani gari a Kongo