Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Muhammad Namadi ya ce makiyayan da ke yi wa manoma ta'adi a gonakinsu, suna yi ne da nufin martani ga ƙwace musu wuraren kiwo.
Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Juma'a a cikin shirin 'Sunrise Daily' na gidan talbijin na Channels, lokacin da yake magana kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Mallam Umar Namadi ya ce mafi yawan abin da ke haddasa rikici tsakanin manoma da makiyaya shi ne manoma sun ƙwace wa makiya burtalai, da wuraren kiwo da mashayar dabbobinsu.
''A kan haka ne suke ganin kamar ana zaluntarsu, don haka suna buƙatar ɗaukar fansa, don haka suna yi ne da nufin ɗaukar fansa'', in ji gwamnan.
''Saboda tsoron kisa da manoman ke yi, ya sa suke barin gonakinsu, suna komawa amfani da kudi wajen sayen abin da za su ci''.
Gwamna ya kuma ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne yi wa kowane ɓangare adalci ta yadda zai ji a zuciyarsa cewa ba a nuna masa bambanci.
''Da Bafulatani da Bahaushe da Kanuri kowa yana da 'yanci a ba shi damar ya gudanar da harkokinsu''.
Gwamna ya ce a lokacin da ya karɓi mulki ya yi ƙoƙarin magance wannan matsala, ya kuma kawo yanzu ana samun ci gaba.
''Jihar Jigawa, jiha ce mai albarkar noma, don haka dole ne gwamnati ta yi duk abin da ya dace domin samar wa manoma yanayi mai kyau domin inganta sana'ar''.
Jihar Jigawa dai na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da rikicin manoma da makiya, lamarin da ke haddasa asarar rayuka a wasu lokuta