Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mika'il da Ibrahim Yusuf Mohammed da Aisha Babangida

  1. Boko Haram na sake taruwa a yankin tafkin Chadi da tsaunukan Mandara - Zulum

    Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana damuwarsa kan yadda ya cce mayaƙan Boko Haram na sake taruwa a yankin Tumbus da ke yankin tafkin Chadi da tsaunukan Mandara a dajin Sambisa.

    Zulum ya bayyana hakan ne a birnin Maiduguri lokacin da yake karɓar baƙuncin ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar da babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa, da sauran manyan sojojin ƙasar, kamar yadda Jardiar Daily Trust ta ruwaito.

    Haka kuma gwamnan ya yaba da ƙoƙarin jami'an tsaron ƙasar a yaƙin da suke yi da mayaƙan na Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

    Gwamnan Zulum ya ce Mayaƙan Boko Haram na yawonsu a yankin tafkin Chadi ba tare da wata tsangwama ba, don haka ya ce akwai buƙatar sojojin su ƙara ƙaimi wajen kakkaɓe su.

  2. Ƙarin miliyoyin 'yan Najeriya za su auka cikin talauci nan da 2027 - Rahoto

    Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya yi hasashen cewa za a samu ƙarin miliyoyin ƴan Najeriya da za su auka cikin talauci nan da shekarar 2027, inda bankin ya ce talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin 100.

    An gabatar da rahoton ne yayin taron bazara na asusun IMF da Bankin Duniya da ake gudanarwa a birnin Washington D.C. na Amurka.

    Rahoton ya bayyana cewa dogaro da Najeriya ke yi kan man fetur, da raunin tattalin arziƙi, da kuma matsalolin shugabanci ne manyan dalilan da za su haifar da ƙarin talauci a ƙasar.

    "Talauci a ƙasashen da ke da albarkatu amma kuma suke fama da rauni, ciki har da manyan ƙasashe kamar Najeriya da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, ana sa ran zai ƙaru da kashi 3.6 cikin 100 tsakanin shekarar 2022 da 2027," in ji rahoton.

    Duk da cewa sashen da ba na fetur ba a Najeriya ya samu ɗan bunƙasa a rubu'i na ƙarshe na shekarar 2024, Bankin Duniya ya yi gargaɗi cewa wannan ci gaban ba zai yi tasiri sosai wajen rage talauci ba saboda har yanzu ana fama da matsalolin kasafin kuɗi da gazawar hukumomi.

  3. Tawagar Najeriya ta isa fadar Vatican domin halartar jana'izar Fafaroma

    Tawagar wakilan gwmanatin Najeriya ta isa fadar Vatcian domin wakilatr ƙasar a taron jana'izar Fafaroma Farncis da ya rasu a ranar Litinin.

    Tawagar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, Godswill Akpabio ta aike da saƙon ta'aziyya ga marigayin a madadin gwamnatin Najeriya.

    A ranar Asabar ne za a gudanar da jana'izar fafaroman a majami'an Basilica da ke birnin Vatican.

  4. Syria ta yi kira ga MDD ta sa Isra'ila ta janye daga yankunanta

    Syria ta yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya matsa wa Isra'ila lamba ta janye dakarunta daga yankinta.

    Tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Bashar al Assad, Isra'ila wadda take kallon sabbin shugabannin Syria a matsayin barazana a gareta, take kai hare hare ta sama a Syria, sannan kuma ta ƙaddamar da wasu hare haren ta ƙasa a yankunan Syria.

    Kiran na Syria ya zo ne a ranar da ministan harkokin wajen Syria ya ɗaga sabuwar tutar ƙasar a shalkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

  5. Sauya sheƙa da ƙulla ƙawance ginshiƙai ne a tsarin dimokraɗiyya - Atiku

    Jagoran adawar Najeriya , Atiku Abubakar ya ce sauya sheƙa da kuma ƙulla ƙawance da wasu ƴan siyasar ƙasar ke yi na daga cikin manyan ginshiƙan tsarin dimokraɗiyya.

    Cikin wani saƙo da tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam'iyyar PDP, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce ƴan siyasa na da damar yin duka waɗanann abubuwa, domin an yi haka a baya, kuma nan gaba ma za a ci gaba da yi.

    Kalaman Atikun na zuwa ne yayin da ake tsaka da raɗe-raɗen cewa jam'iyyun hamayyar ƙasar za su ƙulla ƙawance domin tunkarar APC mai mulki a 2027.

    A cikin mako ne kuma Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori tare da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa - wanda shi ne ya taya Atiku takara a matsayin mataimaki a zaɓen 2023 - suka fice daga PDP, inda gwamnan ya bayyana komawarsa jam'iyyar APC, mai mulkin ƙasar.

    A baya-bayan nan ne dai Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wani abu da aka yi ta sukarsa da shi.

    To sai dai Atikun ya kare matakin da cewa ya ziyarci Buharin ne a matsayinsa na dattijon ƙasa a fagen siyasar Najeriya.

    ''A 2013 an yi ƙawancen haɗakar ƴan adawa, kuma ko a lokacin an nemi shawarwarin tsoffin shugabannin ƙasar nan irin su Obasanjo da Babangida'', in Atiku.

    Haka kuma Atiku ya ce zaɓen 2027, ba wai yaƙi ne tsakanin PDP da APC ko LP da APC ba, yaƙi ne tsakanin ƴan Najeriya da gwamnatin da ta sanya su cikin uƙuba.

  6. Ƴan wasan Barca da Real da za su kara a wasan ƙarshe na Copa del Rey

    A ranar Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Sifaniya, Real Madrid da Barcelona za su ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey.

    Wasan wanda ake yi wa laƙabi da el-classico - na ɗaya daga cikin wasannin da suka fi jan hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.

    Ƙungiyoyin sun kawo wannan matakin ne bayan da Real ta doke Real Sociedad da ci 5-4 a wasa gida da waje.

    Ita ma Barcelona ta kawo matakin ne bayan fitar da Atletico Madrid da ci 5-4 gida da waje.

    Barcelona ce ƙungiyar da ta fi ɗaukar kofin na Copa del Rey a tarihi, bayan da ta ɗauki kofin har sau 31, yayin Real Madrid ta ɗauki kofin sau 20.

    A yanzu haka Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 76, yayin Real Madrid ke matsayi na biyu da maki 72, inda ya rage wasa biyar a ƙarƙare gasar ta bana.

    Wasu fitattun ƴan wasan ƙungiyoyin na fama da jinya ciki har da Robert Lewandowski da Eduardo Camavinga, don haka ba za su buga fafatawar ba.

  7. Ƴan Sudan na cin gawayi da ganyayyaki domin su rayu - Hukumomin agaji

    Hukumomin bayar da agaji a Sudan sun shaida wa BBC cewa ƴan ƙasar da dama sun koma cin gawayi da gayayyanki domin su rayu.

    Shugaban ƙungiyar tallafa wa yangudun hijira ta ƙasar Norway, Noah Taylor, ya shaida wa BBC cewa ''halin da ƴan Sudan ke ciki a matuƙar tayar da hankali.

    ''Mutane na ficewa daga birnin El-Fasher zuwa Tawila, amma da zarar sun isa suke mutuwa saboda yunwa ko kuma ƙishirwa a yayin da yanayin zafi a ƙasar ya kai digiri 40 a ma'aunin celcius.i'', in ji Taylor.

    Tafiya tsakanin sansanin ƴan gudun hijira na Zamzam zuwa garin Tawila na da nisan kilomita 40, kuma yawanci sukan taka da ƙafa a cewar Mista Taylor.

    Mista Taylor ya bayyana irin mummnan yanayin da ake ciki a garin Tawila a yayin da mutum fiye da 100,000 suka guje wa faɗan da ake a yankin.

    A yammacin yankin Darfur mai girman gaske, yaƙin da ake yi na ƙara tsananta, a baya-bayan nan an samu yunƙurin da mayaƙan RSF ke yi na kwace ikon El Fasher da kuma korar mutane daga sansanonin yan gudun hijira.

    Cikin mutanen da suka tserewa fadan akwai wata yarinya da mayaƙan suka riƙa yi wa fyaɗe a yayin da ta yi ƙoƙarin kai wa ga garin inda daga bisani ta mutu saboda raunin da aka ji mata.

  8. Za a sake zaɓar Tinubu a 2027 - Gwamnan Edo

    Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a sake zaɓar Shugaba Tinubu a 2027, musamman yanzu da jam'iyar APC ke ƙara samun yawan jihohi a ƙasar.

    Yayin da yake maraba da takwaransa gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori, wanda ya koma jam'iyyar APC mai mulki cikin makonnan, Mista Okpebholo ya ce kasancewar a yanzu APC na iko da jihohi uku cikin shida na yankin kudu maso kudancin ƙasar yankin zai samu kulawar gwamnatin tarayya.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua ya fitar, gwamnan ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba gwamnonin jihohin Bayelsa da Rivers da kuma Akwa Ibom za su koma APC, wani abu da ya ce zai ƙara wa yankin tasiri a siyasance.

    Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta lashe yankin kudu maso kudu a zaɓen 2027.

    Mista Okpebholo ya kuma ce zai tabbatar da ingantuwar alaƙa tsakanin jiharsa da makwabtan jihohi domin cimma muradin jam'iiyarsa.

  9. Akpabio zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa jana'izar Fafaroma Francis

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio zuwa birnin Vatican domin halartar jana’izar Fafaroma Francis a ranar Asabar 26 ga watan Afrilu.

    Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ta ce tawagar za ta miƙa wata wasiƙa ta musamman da ke ɗauke da sakon jaje daga shugaba Tinubu zuwa ga muƙaddashin shugaban fadar Vatican.

    Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ƙaramar ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu da Archbishop Lucius Iwejuru Ugorji da Shugaban Majalisar Bishop-bishop ɗin Katolika na Najeriya kuma Babban Bishop na cocin katolika na Sokoto, Archbishop Matthew Hassan Kukah da kuma Archbishop na Abuja, Archbishop Ignatius Ayua Kaigama.

    A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne shugaba Tinubu ya bi sahun mabiya ɗarikar katolika da kiristoci a faɗin duniya domin nuna alhinin rasuwar Fafaroma Francis, wanda ya bayyana a matsayin bawan Allah mai mai matuƙar tausayin talakawa, kuma wanda kasance abin koyi ga miliyoyin mutane a duniya baki ɗaya.

  10. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 50 a cikin sa'o'i 24 a Gaza

    Aƙalla Falasdinawa 50 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a ranar Alhamis, a cewar jami’an kiwon lafiya.

    Mutane tara ne suka mutu da safe bayan da wani makami mai linzami ya faɗa kan ofishin ƴansanda a kasuwar garin Jabalia da ke arewacin yankin.

    Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ce ta kai hari kan wata "cibiyar bayar da umarni" ta Hamas da ƙawayenta na Jihad Islami na Falasdinawa a Jabalia da ake amfani da ita wajen shirya hare-hare.

    Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce an kashe ƙarin mutane 23 bayan da aka kai harin bam a wani gida a yankin Ard Halawa na Jabalia.

    Rundunar ta IDF ta ce ta kai harin ne kan wani "ƙasurgumin ɗan ta'adda na Hamas wanda ke yin barazana sosai" ga dakarunta. Amma dai ba ta bayyana sunansa ba.

    Da farko dai hukumar kare fararen hular ta bayar da rahoton cewa mutane 12 ne suka mutu a harin, amma daga baya ta sauya alƙaluman na ta a ranar Juma’a bayan da jami’anta suka ƙara zaƙulo wasu gawarwaki 11 cikin dare.

    An kuma samu rahotonnin kashe wasu ƙarin mutane 29 a sassa daban-daban na yankin.

  11. Rasha za ta ci gaba da riƙe Crimea - Trump

    Yayin da tsare-tsaren zaman lafiya daban-daban ke ɓullowa, a wata hira da ya yi da manema labarai, shugaban Amurka Donald Trump ya ce "Crimea za ta ci gaba da kasancewa tare da Rasha".

    Jiya Trump ya ce ''babu ruwa na da batun Crimea'' bayan ya gana da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre, inda ya ce, tsohon shugaban Amurka Barack Obama ne ya lanƙaya masa wannan batu da ake ta cece-kuce a kai.

    Crimea wani yanki ne da ke kudancin Ukraine da Rasha ta mamaye da ƙarfi a shekarar 2014.

    Shugaban Ukraine Zelensky ya sha yin watsi da ra'ayin amincewa da yankin a matsayin na Rasha.

    A wannan makon, Trump ya caccaki Zelensky, yana mai cewa "idan yana son Crimea, me ya sa ba su yi faɗa akan ta ba shekara goma sha ɗaya da suka wuce?"

    A cikin wannan hirar, shugaban na Amurka ya zargi Kyiv da fara yaƙin da Rasha, yana mai cewa: "Ina tsammanin abin da ya sa aka fara yakin shi ne lokacin da suka fara magana game da shiga Nato."

  12. An kashe matashiya a wani hari da aka kai wata makaranta a Faransa

    An kashe wata yarinya tare da raunata wasu dalibai uku a wata makaranta mai zaman kanta da ke yammacin Faransa.

    An kai harin ne a makarantar Notre-Dame-de-Toutes-Aides da ke Nantes da yammacin ranar Alhamis.

    An ce an kama maharin bayan da wani malami ya yi kukan kura ya kama shi da kokawa.

    An aike da tawagar jami'an ƴansanda da masu bayar da agajin gaggawa zuwa makarantar, inda aka kwashe ɗaliban da ke cikinta.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da harin a shafinsa na dandalin a X, inda ya jinjinawa jaruntakar malaman makarantar.

    Bayan harin, Firaminista François Bayrou ya buƙaci a "ƙarfafa" matakan bincike domin daƙile harin da ake kai wa da wuƙaƙe a sassan ƙasar.

    An ce babban mai gabatar da ƙara na Nantes Antoine Leroy ya ziyarci makarantar kuma zai yi taron manema labarai a cikin kwanaki masu zuwa.

  13. Aƙalla mutane 250,000 ne ake sa ran za su halarci jana'izar Paparoma

    Aƙalla mutane 250,000 ne ake sa ran za su halarci jana'izar Paparoma Francis a gobe Asabar.

    Dubban mutane sun riga sun isa birnin Vatican a cikin kwanaki biyun da suka gabata domin nuna girmamawa ga marigayi Fafaroma Francis.

    Kuma ana sa ran aƙalla wakilai 100 ne daga ƙasashe daban-daban na duniya za su halarci jana'izar inda ake tunanin za a ƙara tsaurara matakan tsaro.

    Duk da dai an saba ganin jami'an tsaro a fadar Vatican, cikin kwanakin nan lamarin ya ɗan sauya inda tun bayan rasuwar Paparoma aka sami ƙaruwar matakan tsaro a fadar vatican da kewaye.

    Da safiyar yau Juma'a, an kafa shingayen bincike na ƴansanda kuma jami’an na gudanar da bincike kan waɗanda ke shiga dandalin St Peter.

  14. Amurka ta kama wani ɗan Rwanda bisa zargin aikata kisan ƙare dangi

    An kama wani mai kiwon zuma dan ƙasar Rwanda da ke zaune a Amurka bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a ƙasarsa a shekarar 1994.

    Ana zargin Faustin Nsabumukunzi da aikata munanan ayyukan ta'addanci a ƙasashen waje a lokacin da ya kasance shugaban al'umma a lokacin da aka fara aikata kisan ƙare dangi, in ji ma'aikatar shari'ar Amurka.

    An kuma tuhumi wanda ake zargin mai shekaru 65 da laifin zamba ta hanyar neman biza ba bisa ƙa'ida ba a lokacin da ya koma Amurka a shekara ta 2003.

    Bai dai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba kuma an bayar da belin sa.

    John Durham, wani mai shigar da ƙara na tarayya ya ce "Nsabumukunzi ya sha yin ƙarya don ɓoye hannu da yake da shi a cikin mummunan kisan ƙare dangi da aka yi a Rwanda yayin da yake neman zama halataccen mazauni kuma ɗan ƙasar Amurka."

    A cikin kwanaki 100 kacal a shekarar 1994, kimanin mutane 800,000 ne masu tsattsauran ra'ayi na ƙabilar hutu suka kashe a Rwanda.

    An yi zargin cewa galibin mayaƙan Tutsi da suka karɓi mulki bayan kisan kiyashin sun kashe dubban ƴan Hutu a ƙasar ta Rwanda a matsayin ramuwar gayya.

    An kama wasu mutane da dama da suka tsere daga ƙasar Rwanda zuwa wasu ƙasashe bisa zarginsu da hannu a kashe-kashen, yayin da ƙasar da ke gabashin Afirka ke ci gaba da neman ƙarin wadanda ake zargi da kisan kare dangi daga maɓoyarsu a ƙasashen ƙetare.

  15. An kashe janar ɗin Rasha a wani harin bam a birnin Moscow

    Majiyoyin da dama a cikin Rasha sun ce an kashe Janar Yaroslav Moskalik, mataimakin babban jami'in gudanarwa na hafsan hafsoshin sojin ƙasar, bayan an dasa masa bam a motarsa a birnin Moscow.

    Kamfanin dillancin labaran TASS ya rawaito cewa jami’an tsaro sun tabbatar da cewa wani bam ne ya haddasa fashewar wani abu a yankin gabashin birnin Moscow na Balashikha.

    Kwamitin bincike na Rasha ya tabbatar da mutuwar Janar Yaroslav Moskalik a wani fashewa da aka yi a birnin Moscow.

    Da ta ke tsokaci game da kisan, mai magana da yawun kwamitin binciken Svetlana Petrenko ta ce: “Wata mota ƙirar Golf ta fashe bayan wani bam da aka dasa acikinta ya tashi.”

    Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kai wa wasu sojojin Rasha hari ba tun farkon yaƙin amma ba kasafai ake samun kashe kashen da ake yi a birnin Moscow ba.

    A watan Fabrairun wannan shekarar, Armen Sargsyan, shugaban wata ƙungiyar sa-kai da ke goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine, ya mutu a asibiti bayan da wani abu ya fashe a kofar shiga wani rukunin gidaje da ke arewa maso yammacin Moscow.

  16. Ukraine na iya haƙura da wasu yankunanta domin a zauna lafiya - Klitschko

    Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko, ya shaida wa BBC cewa, mai yiwuwa ne Ukraine ta haƙura da wasu yankunanta a wani ɓangare na neman a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha, a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ke ci gaba da matsin lamba kan Ukraine domin ta amince da hakan.

    "Daya daga cikin zaɓin da ke akwai shine ... haƙura da wasu yankuna. Ba daidai ba ne. Amma don a zauna lafiya, zaman lafiya na wucin gadi, wataƙila yana iya zama mafita, na wucin gadi," in ji shi.

    Sai dai tsohon zakaran damben boksin da ya koma siyasa ya jaddada cewa al'ummar Ukraine ba za su taɓa amincewa da zama a ƙarƙashin ikon Rasha ba.

    Yana magana ne sa'o'i bayan harin makami mai linzami da Rasha ta kai a Kiev ya kashe mutane 12 tare da jikkata sama da 80.

    Wannan dai shi ne hari mafi muni da Rasha ta kai a babban birnin Ukraine cikin watannin baya bayan nan.

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ƙaddamar da cikakken mamayar ƙasar Ukraine a shekarar 2022, kuma a halin yanzu Moscow tana iko da kusan kashi 20% na yankunan Ukraine.

    A halin yanzu Klitschko yana ɗaya daga cikin manyan ƴan siyasar Ukraine da ya fito fili ya nuna cewa cewa ƙasarsa na iya haƙura da wasu yankunanta, ko da kuwa na wucin gadi ne.

    Magajin garin Kyiv da Zelensky abokan hamayya ne na siyasa inda ya sha zargin shugaban ƙasar da tawagarsa da yunƙurin yi masa zagon ƙasa.

  17. Sojojin Isra'ila sun amince da kashe ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun amince da kashe wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya (UN) , bayan da a baya suka musanta yin hakan, a wani lamari da ya faru a zirin Gaza a watan jiya.

    Bayan waan kashe wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da aka kai hari kan wani ginin Majalisar da ke Deir al-Balah a ranar 19 ga Maris, rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta ce ba ita ta kai harin ba.

    Sai dai ranar alhamis rundunar ta IDF ta bayyana cewa sakamakon farko na binciken da ta gudanar kan lamarin ya nuna cewa a haƙiƙa sojojinta sun kashe ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya bayan kuskuren bayyana ginin a matsayin wanda ke dauke da mayaƙan Hamas.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: "An kai harin ne bayan samun bayanan cewa akwai abokan gaba a yankin, kuma sojojin ba su tabbatar da ginin a matsayin na majalisar Ɗinkin Duniya ba.''

    Ta ƙara da cewa: "IDF ta yi nadamar wannan mummunan lamari kuma tana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don koyan darussan aiki da kuma tantance ƙarin matakan hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.''

    Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar ma’aikaciyar Majalisar Dinkin Duniya Marin Valev Marinov ƴar ƙasar Bulgeria tare da jikkata wasu jami’an Majalisar guda biyar, kuma ya zo ne kwana guda bayan da Isra’ila ta dawo da kai hare-hare kan ƙungiyar Hamas bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon watanni biyu ta ruguje.

  18. Duk wanda ke son barin PDP ya tafi tun yanzu — Saraki

    Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce duk waɗanda ke da niyyar barin jam’iyyar adawa ta PDP gwamma sun fice tun yanzu domin bai wa masu kishin jam'iyyar damar sake gina ta.

    Saraki ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar alhamis inda ya mayar da martani bayan wasu jiga-jigan Jam'iyyar a jihar Delta sun sanar da ficewarsu a cikin makon nan.

    A ranar Laraba ne Sheriff Oborevwori, gwamnan jihar ta Delta ya bar jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ke shirin komawa jam’iyya mai mulki nan ba da jimawa ba.

    Oborevwori ya gaji Okowa a matsayin gwamnan Delta bayan ya lashe zaɓen 2023 a ƙarƙashin inuwar P D P.

    Saraki ya ce ya samu kiraye-kiraye da dama daga ƴan jam’iyyar da abin ya shafa da kuma matasa masu goyon bayan dimokraɗiyya game da rugujewar reshen jam'iyyar ta jihar Delta a kwanakin baya. “Waɗanda ke son barin PDP su bari tun yanzu, su bar sauran mu da ke son ci gaba mu mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar,” in ji sanarwar.

    Saraki ya bayyana cewa adawa mai ƙarfi na da matukar muhimmanci ga ɗorewar dimokraɗiyya, inda ya ƙara da cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba a matsayin ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba.

    "Don ɗorewar dimokraɗiyya, dole ne a tabbatar da cewa mutane na da zaɓin da ya dace a kowane lokaci," in ji shi.

  19. Ma'aikatan hukumar NIMET sun janye yajin aiki a Najeriya

    Ƙungiyar ma'aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NIMET) sun sanar da janye yajin aikin da suka fara kwana biyu da suka gabata bayan wata ganawa da suka yi da ministan sufurin ƙasar.

    Yajin aikin da ma’aikatan suka kira, ya haifar da cikas a filayen jiragen sama na cikin gida inda fasinjoji da dama suka kasa yin balaguro.

    Ma’aikatan sun yi yajin aikin ne saboda rashin ingantacen yanayin aiki, rashin gudanar da ayyukansu ya kawo cikas a zirga-zirgar jiragen sama a fadin ƙasar ranar Alhamis

    Ma’aikatan sun nuna damuwa kan rashin aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙaƙanta, da batun wasu alawus-alawus, da kuma yin watsi da muhimman shirye-shiryen horas da ma'aikatan da dai sauransu.

    Amma bayan wata ganawa da ministan sufurin jiragen saman ƙasar Festus Keyamo a Abuja, ƙungiyar ma'aikatan ta yanke shawarar janye yajin aikin.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.