Ƙarshen rahotonni
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Lahadi.
Za mu zo da wasu gobe da safe.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/10/2025.
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Lahadi.
Za mu zo da wasu gobe da safe.
Kafar yaɗa labaran gwamnatin China ta ce masu aikin ceto a Tibet na can suna kokarin kaiwa ga mutum kusan 1,000 da suka makale a wani surkuki a tsaunin Everest - wanda ya fi kowane tsauni tsawo a duniya.
Mutanen, waɗanda yawancinsu masu hawa tsauni ne, sun kasa barin wajen wanda ya fi nisan kafa 16,000 daga gindin tsaunin saboda hanyoyin komawa masaukinsu sun rufe sakamakon zubar dusar kankara mai yawa da aka yi tsawon kwana biyu.
Rahotanni sun ce dusar kankarar ta rusa tantuna ko rumfunan masaukin nasu - wasu ma cikinsu na fama da cutar tsananin sanyi.
Babban hafsan tsaro na rundunar sojin Isra'ila ya ce idan tattaunawa tsakanin ƙasar da ƙungiyar Hamas ta gagara za su koma yaƙi a Zirin Gaza.
Cikin wata sanarwa, Eyal Zamir ya ce yanayi ya sauya a Gaza, inda suke ƙoƙarin mayar da nasarar da suka samu zuwa ta siyasa.
Tun farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Hamas za ta fuskanci "mummunar shafewa" idan ta ƙi amincewa da miƙa mulki mulkin Gaza.
A gobe Litinin ne wakilan Hamas da na Isra'ila ke ci gaba da tattaunawa a birnin Al-Ƙahira na Masar domin cimma yarjejeniya kan sakin sauran mutanen da Hamas ɗin ke garkuwa da su.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da tsare jami'anta 16 saboda zargin aikata rashin ɗa'a da kuma saɓa wa dokokin aiki.
Binciken farko-farko ya nuna cewa abubuwan da suka aikata sun shafi takaicin da suka fuskanta saboda rashin samun ƙarin sakamakon kasa cin jarabawar da ta hana su cigaba a aikin, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana a ranar Asabar.
Kakakin rundunar, Birgediya Janar Gusau, ya ce wasua daga cikin manyan jami'an da ake zargi a yanzu da ma ana bincikar su da aikata wasu laifuka.
"Da zarar an kammala bincike, jami'an za su fuskanci ladartarwa bisa dokokin aiki domin tabbatar da nagartar rundunar," a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa da ma rundunar "kan yi irin wannan binicike akai-akai domin tabbatar da doka da ɗa'a".
Firaministan Georgia ya sanar da aniyarsa ta soke manyan jam'iyyun adawa.
Irakli Kobakhidze na magana ne bayan masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati sun yi yunƙurin kutsawa fadar gwamnatin ƙasar.
Ya kuma zargi ƙungiyar Tarayyar Turai da yi wa harkokin ƙasarasa katsalandan kuma ya shawarci wakilin ƙungiyar a Tblisi ya nisanta kansa daga masu zanga-zangar.
An kama aƙalla jagororin masu zanga-zangar biyar a yau Lahadi. Rikicin siyasar ya ɓarke ne a shekarar da ta gabata lokacin da jam'iyyar Georgian Dream ta dakatar da tattaunawar shiga Tarayyar Turai.
Masu suka na zargin gwamnatin da yunƙurin ƙulla ƙawance da Rasha.
Sani Adamu malamin firamare ne da ya yi ritaya a wannan shekarar, amma kuma ya ci gaba da zuwa koyar da yara a ƙwaryar birnin Kano da ke arewacin Najeriya.
"Gani na yi da na dinga zuwa wurin kalle-kalle, ko karta, ko hira gara na tara yara na dinga tuna musu karatun da aka yi musu," in ji malamin da ya shekara 35 yana koyarwa.
Salon koyarwarsa ya yi kama da irin wanda kowane yaro zai so saboda yadda yake haɗawa da nishaɗi da wasa da dariya.
Shugaban Ukraine Zelensky ya soki ƙasashen duniya masu ƙawance da Rasha bisa abin da ya kira rashin takaɓus wajen tsawata wa Putin kan hare-haren da ya ƙaddamar a ƙasarsa ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.
Harin wanda aka kai a cikin dare ya yi ajalin aƙalla mutum biyar, sannan ya jikkata wasu, tare da katse lantarkin wasu yankunan ƙasar.
Shugaban na Ukraine ya ce bai kamata ƙasashen su yi gum ba kan hare-haren na ƙasar Rasha, inda ya ce akwai buƙatar su ja wa Putin kunne.
Hukumomi a ƙasar ta Ukraine sun ce harin Rasha a cibiyar makamashin ƙasar ya katse lantarkin aƙalla mutum 100,000.
Isra'ila ta ce aƙalla mutum 900,000 ne suke tsere daga Birnin Gaza tun bayan da sojojinta suka yunƙura domin mamaye yankin.
Wannan adadin da Isra'ila ta bayyana na nufin kusan kashi 90 na Falasɗinawa ne suka bar birnin a sanadiyar hare-haren.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da batun tattauna yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin Gaza tsakanin ƙasar ta Isra'ila da Hamas, wanda ake yi a Masar.
Ana sa ran Hamas za ta saki dukkan Isra'ilawan da take garkuwa da su, sannan ita kuma Isra'ila ta saki fursunonin Falasɗinawa da dama.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta sanar da kulle wasu manyan kantunan kayan buƙatu guda biyu a babban birnin tarayya, Abuja da kuma wasu shagunan sayar da mayukan shafawa.
NAFDAC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a hafinta na X a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba, inda hukumar ta ce ta kulle manyan kantunan ne a yankin Jabi da kuma wasu shagunan sayar da mayukan shafawa guda takwas a kasuwar Wuse.
Sanarwar ta ce an rufe shagunan ne bisa saɓa dokokin kasuwanci da rarraba wasu kayayyaki bayan wasu kwastomomi sun kai ƙorafi a kuma bincike "ya tabbatar suna sayar da kayayyakin da ba suka saɓa dokokin rajista, kuma suke ɗauke da tambarin China."
Hukumar ta ce hakan ya saɓa dokokinta, "domin dole ne a sanya tambari da turancin Ingilishi a duk kayayyakin a za a sayar a Najeriya."
Sojojin Tanzaniya sun nesanta kansu daga wani bidiyo a shafukan sada zumunta, da ke nuna sojoji suna sukar gwamnati.
A bidiyon, an ga wani mutum sanye da kakin soji ya nuna rashin amincewa da matakin da gwamnati ta dauka na hana babbar jam'iyyar adawa ta Chadema shiga babban zaben kasar da za a yi nan gaba a wannan wata.
An tuhumi shugaban jama'iyyar ta Chadema Tundu Lissu da laifin cin amanar kasa bayan da ya bukaci a yi gyara a zaben kafin a gudanar da zabe.
A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Tanzaniya ta ce tana ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda aka saba.
Wakilin BBC ya ce ana kyautata zaton jam'iyyar CCM mai mulki da shugabarta Samia Suluhu ne za su lashe zaben na ranar 29 ga watan Oktoba.
Gwamnatin Somaliya ta ce an kashe mayakan Al-Shabab 7, yayin da suka kai hari kan wani babban gidan yari da ke Mogadishu babban birnin kasar a yammacin ranar Asabar.
Hukumar leken asirin kasar ce ke gudanar da gidan yarin da ake kira Godka Jilicow, da ke kusa da fadar shugaban kasar.
Yana dauke da manyan masu aikata laifuka da kuma wadanda ake da zama ya kungiyar.
Sanarwar da Kamfanin Dillancin Labaran kasar ya fitar ta ce maharan sun yi shiga irin ta sojoji ne, kuma ba a gudanar da bincike kan motarsu ba, abun da ya ba su damar wuce shingayen binciken jami'an tsaro a babban birnin kasar cikin sauki.
Sanarwar ta nuna cewa gwamnati za ta aiwatar da cikakken tsarin sa ido kan dukkan motocin da ke zirga zirga.
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta ce malaman makarantu mutane masu daraja da suka cancanci yabo da ƙarƙafa gwiwa.
Remi ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da fitar domin murnar Ranar Malamai ta bana, inda ta yi kira da a ƙara ɗaukar malamai domin ɗalibai su samu ilimi mai inganci, sannan a kula sosai da haƙƙoƙinsu.
A cewarta, "malamai gwaraza ne gaskiya da suke taimakawa wajen inganta rayuwar al'umma da ma gyara ƙasa."
"Ƙarancin malamai matsala ce da ke buƙatar ɗauki na gaggawa domin idan aka ƙarfafa malamai ne wasu ma za su yi sha'awar shiga aikin mai matuƙar daraja."
Ta ƙara da cewa, "a matsayina na tsohuwar malama, ina yabawa da ƙoƙarinku a wannan rana mai muhimmanci ta malamai."
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya gargaɗi ƴan hamayya da sauran ƴan jihar da su guji sanya siyasa a cikin matsalar tsaro, inda ya nanata cewa hakan na ƙara ta'azzara matsalar a jihar.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ƙaramar hukumar Silame a ci gaba zagayen ziyarce-ziyarcen jaje a wuraren da ƴanbindiga suka kai hare-haren a ƴan tsakankanin nan.
"Matsalar tsaro al'amari ne mai matuƙar muhimmanci, don haka ya kamata a riƙa bi a hankali a duk lokacin da ake magana game da tsaro," in ji shi kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci yadda wasu suke fakewa da sunan siyasa ko tattauna al'amuran yau da kullum ba suna kawo tsaiko a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da tsaro a jihar ta Sokoto.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro ba dare ba rana domin samar da tsaro, inda ya ce an fara ganin sakamakon ƙoƙarinsu.
Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda wasu suke taimako ƴanbindiga ta hanyar ba su bayanai, inda ya ce akwai buƙatar al'umma su taimaka wa gwamnati ta hanyar ba jami'an tsaro bayanai masu muhimmanci kan harkokin ƴanbindiga.
A ziyarar, gwamna Aliyu ya ba iyalan duk wanda aka kashe naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, inda jimilla ya raba naira miliyan 66 da buhun shinkafa 165 a yankin.
Shugaba Trump ya ba da umarnin tura dakarun tarayya dari uku zuwa birnin Chicago, don magance abin da gwamnatinsa ta kira rashin bin doka da oda wasu biranen Amurka.
Wata mai magana da yawun fadar White House Abigail Jackson ta ce shugabannin biranen da 'yan Democrat ke jagoranta sun kasa sauke nauyin da ke kansu na tabbatar da tsaro.
Jiya Assabar ne jami’an gwamnatin tarayya suka harbe wata mata da suka ce tana dauke da makamai tare da amfani da motarta wajen tare wata motar jami’an tsaro.
A halin da ake ciki, wani alkali na tarayya a birnin Portland da ke Oregon, ya hana fadar White House tura dakarun tarayya birnin.
Dubban daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawan a fadin Turai jiya Asabar.
Daya daga cikin mafi girma ita ce wadda aka yi a birnin Roma na Italiya, inda 'yansanda suka yi kiyasin cewa, sama da mutane dubu dari biyu da hamsin ne suka fito dauke da tutoci suna raira taken neman ƴancin Falasdinu.
Wasu daga cikinsu sun yi arangama da ‘yansandan kwantar da tarzoma. An kuma gudanar da zanga-zangar a biranen Bercolona na Spain, da kuma Dublin babban birnin Ireland.
A Biritaniya, 'yansanda sun kame kusan mutane dari biyar da suka gudanar da zanga-zanga a London, domin nuna goyon bayan Falasdinawan karkashin wata kungiya da aka haramta ta Palestinian Action Aide.
Tun da farko gwamnati ta yi kira da a dage zanga-zangar, saboda harin da aka kai kan wata cocin Yahudawa, inda aka kashe mutane biyu, a farkon makon nan.
Shugaba Amurka Donald Trump ya ce Isra'ila ta amince ta janye sojojinta zuwa wani wuri da aka amince dakarunta za su koma a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Hamas a zirin Gaza.
Cikin kwanaki uku na farko ne Hamas za ta sako dukkan ragowar yan Isra'ilar da take rike da su walau a mace ko a raye, sannan ita ma Isra'ila za ta saki fursunoni Falasdinawa kimanin dubu biyu, ciki har da kusan 300 da aka zartarwa hukuncin kisa.
Sai dai wakiliyar BBC ta ce Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce yana sa ran za a saki fursunonin ne yayin da dakarun Isra'ila ke ci gaba da kasancewa a cikin Gaza, wani abu da Hamas ta ce ba za ta sabu ba.
Yanzu haka surukin Mista Trump, Jared Kushner, da wakilinsa na musamman Steve Witkoff, sun kama hanyar zuwa Masar, inda za su hadu da wakilan Hamas don daddale batun yarjejeniyar da kungiyar ta bukaci a sake yin zaman keke da keke, don duba wasu batutuwa da ke cikinta.
Barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake haɗuwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye.
A yau za mu kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Ku kasance tare da mu.