Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarai daga duniyar wasanni na 25/06/2024

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 25 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Nan muka zo karshen rahotanni da muke kawo muku na irin wainar da ake toyawa a fagen kwallon kafa, musamman ma Gasar Euro 2024.

    Mu tara da ku gobe idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke cewa asuba ta gari.

  2. An fitar da Serbia daga gasar Euro 2024

    Serbia ta kasa samun damar zuwa zagaye na gaba a gasar Euro 2024 bayan tashi canjaras da Denmark.

    Sai dai ita Denmark ta kai zagaye na ‘yan 16, a fafatawa da kungiyoyin biyu suka yi a filin wasa na Munich.

    Denmark ta samu damarmaki na zura kwallo a raga, amma ba ta yi amfani da su ba, a wasa da kungiyoyin biyu suka taka wanda ɗauki hankalin ‘yan kallo yadda aka yi tsammani ba.

    Serbia, wadda ta san cewa za ta fice daga agsar muddin ta kasa samun nasara saboda tashi canjaras da Ingila ta yi da Slovenia a rukuni na ‘C’, kora ɗaya kawai ta kai wanda ya kusa ya shiga raga ana dab da tashi wasa.

  3. Brazil ta fara Copa America da canjaras

    Brazil ta fara wasan gasar Copa America da canjaras tsakaninta da Costa Rica a birnin Los Angeles na Amurka.

    Duk da cewa wasan ya tashi babu ci, Brazil mai kofin guda tara ce ta riƙe kashi 74 cikin 100 na ƙwallon, tare da buga shot 19 amma duk da haka ba ta iya zira ƙwallo a raga ba a wasan Rukunin D.

    Marquinhos ya jefa ƙwallo a raga a minti na 30 amma sai na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa ta ce an yi satar gida.

    Kociyan Brazil Dorival Jr ya saka matashin ɗan wasan Real Madrid Endrick da kuma Savio daga baya, amma ba su iya aikata komai ba.

    Lucas Paqueta ya bugo tirke amma kuma ya ɓarar da dama biyu masu kyau a filin wasa na SoFi da ke birnin.

    Sakamakon ya bar Brazil a mataki na biyu da naki ɗaya, yayin da Colombia ta doke Paraguay 1-0 kuma ta ɗare saman teburin rukunin na D.

  4. Faransa na kutsa bayan Poland, 31' France 0-0 Poland

    Tawagar Faransa ƙarƙashin jagorancin Mbappe a cikin fili na kai wa Poland hari ba ƙaƙƙautawa.

    Poland ta ci gaba da kare gida zuwa yanzu - duk da cewa wasan ba shi da wani amfani a wajensu.

  5. Wasannin da za a buga a yau, Euro 2024

    Yau ce rana ta biyun ƙarshe a wasannin rukuni na gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024.

    Ƙasashe takwas ne za su fafata a yau daga rukunnan C da D.

    Rukunin C:

    England (8:00) Slovenia

    Denmark (8:00) Serbia

    Rukunin D:

    France (5:00) Poland

    Netherlands (5:00) Austria

  6. Mbappe ya ƙagu ya buga wasan yau - Deschamps

    Kocin Faransa Didier Deschamps ya ce Kylian Mbappe na "samun sauƙi a kullum" kafin wasan ƙarshe da za su buga da Poland a yau Talata.

    Mbappe ya fasa hanci a wasan farko da suka buga da Austria kuma bai buga wasa na biyu da Netherlands ba, wanda suka tashi 0-0.

    Tuni aka fitar da Poland daga gasar a Rukunin D, yayin da Austria ke neman tsira a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe huɗu mafiya ƙoƙari a mataki na uku - amma dole ne sai ta ci Netherlands a yau kafin ta samu hakan. Faransa da Netherlands sun samu gurbi a mataki na gaba.

    Ɗan wasan na gaba wanda zai fara taka wa Real Madrid leda a kaka mai zuwa, bai buƙaci wata tiyata ba amma kuma zai ci gaba da saka takunkumin kariya idan zai buga wasa.

    "Ya ji sauƙi yau ɗin nan sama da jiya da kuma shekaran jiya. Ya matsu ya dawo bakin fama saboda ya yi ta atasaye," in ji Deschamps.

    "Kumburin ya sace kuma ya saba da takunkumin. Ya ƙagu sosai ya buga wasan gobe [yau]."

  7. Tsohon haziƙin ɗan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry na cikin mutanen da hukumar ƙwallon ƙafa ta Wales ke duba yiwuwar ɗauka a matsayin kocinta domin maye gurbin Rob Page.

    Henry wanda tsohon mai horarwa ne a Monaco da Mntreal Impact, yanzu haka shi ne kocin tawagar Faransa 'yan ƙasa da shekara 21 kuma yana shirin jagorantar ta zuwa gasar Olympics da ƙasar za ta karɓi baƙunci.

    Tsohon ɗan wasan gaban mai shekara 46 na da alaƙa da hukumar ƙwallon Wales Football Association of Wales (FAW) sakamakon yin aiki tare da su lokacin da yake koyon aikin zama koci.

    FAW ta kori mai horarwa Page ranar Juma'a da ta wuce bayan ya shafe shekara uku da rabi a muƙamin sakamakon gaza samun gurbin zuwa gasar Euro 2024.

  8. Euro 2024: Ingila ta kai zagayen 'yan 16 tun kafin wasa da Slovenia, England (8:00) Slovenia

    Tawagar Ingila ta kai zagayen 'yan 16 a gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 yayin da saura wasa ɗaya a kammala wasannin rukuni.

    Ingila ta tsallake ne sakamakon rashin nasarar da Albania ta yi a hannun Sifaniya a jiya Litinin da dare, inda wasa ya tashi Spain 1-0 Albania.

    Nasarar da Sifaniyan ta yi na nufin har wa yau Netherlands da Faransa duka sun samu gurbi a zagayen daga Rukunin D.

    Ingila za ta kammala wasannin rukunin a yau Talata da Slovenia a birnin Cologne na Jamus da misalin ƙarfe 8:00 agogon Nijar da Najeriya.

    Tawagar ta Gareth Southgate na da maki huɗu cikin wasa biyu bayan doke Serbia 1-0 da kuma canjaras 1-1 da Denmark, saboda haka rashin nasarar Albania na nufin Ingila za ta wuce aƙalla cikin tawaga huɗu mafiya hazaƙa da suka ƙare a mataki na uku a cikin rukuni.

    Har wa yau, Ingila za ta jagoranci rukunin na C idan ta doke Slovenia, za kuma ta iya yin hakan idan ta yi canjaras amma Denmark ta kasa cin Serbia.

    Da a ce Albania ta doke Sifaniya to da dole sai Ingila ta buga wasan ƙarshe a yau kafin ta san makomarta.

    Zuwa yanzu Sifaniya ce kaɗai ta ci duka wasanninta uku kuma ta wuce abinta da maki tara.

  9. Barka

    Kun shigo shafin labarin wasanni kai-tsaye tare da Umar Mikail.

    Ku biyo mu domin sanin yadda take kasancewa a gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024 da kuma sauran labarin wasanni.