Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 27/06/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Umaymah Sani Abdulmumin & Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu na kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gobara ta tashi a kasuwar Karu da ke Abuja

    Wata gobara ta tashi a kasuwar Karu - da ke Abuja babban birnin Najeriya - da aka fi sani da tsohon Karu.

    Shaidu sun ce gobarar da ta tashi da maraicen ranar Alhamis ta yi sanadiyyar asarar dukiya mai tarin yawa.

    Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

    Tuni dai ma'aikatan kashe gobara ke ƙoƙarin kashe wutar da ta tashi a kasuwar

  3. An fitar da ƙananan yara da ke fama da cutar kansa daga Gaza zuwa Masar

    An fitar da ƙananan yara Falasɗinawa 21 da ke fama da cutar kansa daga Gaza zuwa Masar don yi musu magani.

    Da yake jawabi a wajen asibitin Nasser, shugaban asibitocin Gaza, Dakta Mohammed Zaqout, ya ce akwai ƙarin yara da dama da ke buƙatar kulawar gaggawa.

    Dakta Zaqout ya kuma yi kiran ƙara kaimi domin taimaka wa yaran.

    Ya ce Waɗannan yara 21, akasarinsu na fama ne da cutar kansar jini, wanda za a iya warkarwa, amma a halin yanzu suna cikin hatsarin mutuwa, saboda rashin magani da kula da lafiyarsu, don haka ne suka amince da tafiyarsu.

    Wannan shi ne karon farko da aka kwashe marasa lafiya daga yankin tun farkon watan Mayu.

  4. Kotun Ƙolin Amurka ta kare kamfanin haɗa magunguna daga tuhuma

    Kotun Ƙolin Amurka ta hana aiwatar da yarjejeniyar biyan biliyoyin daloli tsakanin kamfanin haɗa magunguna na Purdue Pharma da kuma waɗanda maganinsu ya cutar, saboda yarjejeniyar ta bai wa masu kamfanin kariya daga fuskantar tuhuma.

    An ɗora wa Kamfanin Purdue Pharma alhakin matsalar da al'umma ke samu, ya kuma amince da laifin da ake tuhumarsa na cin amanar ƙasa bisa kuskuren da ya yi na rubutun da ke jikin maganinsa na cewa ko yana da illa ko kuma akasin haka.

    Biyar daga cikin alƙalan tara sun goyi bayan gwamnatin Biden wajen ƙin amincewa da yarjejeniyar.

    Tsakanin 1999 da 2019, fiye da Amurkawa 240,000 ne suka mutu sakamakon matsalar da ta jiɓanci magunguna.

  5. Tinubu ya amince da bayar da tallafin N50,000 ga iyalai 100,000 a kowace jiha har wata uku

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da matakin bayar da tallafin naira dubu 50 ga iyalai dubu 100,000 a kowace jiha a faɗin ƙasar.

    Shugaban ƙasar ya amince da matakin ne bayan tattaunawa da gwamnonin jihohin ƙasar a taron majalisar tattalin arziki ta ƙasa da ya gudana a fadar shugaban ƙasar ranar Alhamis

    Shugaba Tinubu ya kuma amince da ware naira biliyan 155 domin sayen kayan abinci da za a raba a jihohin ƙasar domin rage masu raɗaɗi.

    Haka kuma taron ya amince da fara aikin babban titin Sokoto zuwa Badagry da zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma jihar Legas.

    Sannan kuma da ci gaba da aikin babban titin bakin teku da ya tashi daga Legas zuwa Calabar, wanda tuni aka fara gina shi.

    Haka kuma Shugaban ya amince da gina layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da zai ratsa jihohin Rivers da Abia a Enugu da Benue da Nasarawa da Plateau da Bauchi da Gombeda Yobe da kuma jihar Borno.

    Sannan da na Legas zuwa Kano da shi ma zai ratsa jihohin Lagos da Ogun da Oyo da Osun da Kwara da Neja da birnin Abuja da Kaduna da kuma jihar Kano.

    Haka kuma taron ya amince da bai wa jihohin ƙasar haɗe da binin Abuja naira biliyan 10 domin sayen motocin fasinja masu amfani da man CNG.

  6. Isra'ila ta umarci mazauna Shejaya a Gaza su fice daga unguwar

    Dakarun Isra'ila sun umarci fararen hula da ke wani yanki na birnin Gaza da su fice cikin gaggawa.

    An umarci mazauna yankin Shejaya da su nufi wani yanki da ke kudancin zirin Gaza da Isra'ila ta ayyana a matsayin yanki ne na jin ƙai.

    Mazauna yankin shejaya da ke birnin Gaza sun ce sun ji ƙarar tankunan yaƙi suna tunkarar yankin bayan an kwana ana luguden wuta.

    Isra'ila na zargin Hamas da ɓoye mayaƙanta a tsakanin fararen hula.

  7. Yahaya Bello ya nemi a mayar da shari'ar da ake yi masa zuwa Kogi

    Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya buƙaci alƙalin babbar kotun tarayya da ke Abuja ya mayar da shari'ar da ake yi masa kan zargin badaƙalar kuɗi zuwa jihar Kogi.

    Yayaha Bello ya ce zai fi son agurfanar da shi a Lokoja - wurin da ake zargin ya aikata laifin - saɓanin Abuja da ake yi masa a yanzu.

    Tsohon gwamnan ya bayyana buƙatar tasa ne a ranar Alhamis ta bakin lauyansa a lokacin zaman kotun na ranar Alhamis.

    Lauyan mai suna Adeola Adedipe (SAN) ya ce sun nemi buƙatar ne saboda babbar kotun tarayya da ke Lokoja na da damar sauraron shai'ar da ake yi wa tsohon gwamnan.

    Adedipe ya ce tawagar lauyoyin tsohon gwamnan na jiran amsa daga babban alƙalin kan buƙatar tasu.

    Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban shari'a bisa tuhume-tuhume 19 da suka jiɓanci ɓarnatar da dukiya.

    EFCC na tuhuar gwamnan da badaƙalar kuɗi da suka kai naira biliyan 80.2.

    Yahaya Bello ya mulki jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, tsawon wa'adi biyu daga shekarar 2016 zuwa 2024

  8. Tsohon ɗan wasan Kamaru ya mutu a hatsarin mota

    Tsohon ɗan wasan Celtic, Landry Nguemo ya mutu bayan wani mummunan hatsarin mota a Kamaru.

    Landry Nguemo wanda tsohon ɗan wasan tawagar Kamaru ne ya taka leda a ƙungiyoyin Parkhead da Nancy a Faransa da kuma ƙasashen Turkiyya da Norway.

    Hukumomin ƙwallon ƙafar Kamaru sun tabatar da mutuwar tsohon ɗan wasan mai shekara 38 a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi.

    "Hukumar ƙwallon ƙafar Kamaru za ta ci gaba da tuna Nguemo, wanda ya taka mana leda tsakanin 2006 zuwa 2014'', in ji hukumar FECAFOOT.

    Daga ƙarshe FECAFOOT ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalai da 'yan uwan tsohon ɗan wasan da ma ilahirin masoya wasan ƙwallon ƙafa.

    N'Guemo ya buga wa Celtic wasa fiye da 40 a matsayin ɗan wasan tsakiya a kakar 2009/10.

  9. An naɗa farfesa mafi ƙarancin shekaru a matsayin shugabar Jami'ar Abuja

    An nada Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar jami'ar Abuja bayan cikar wa'adin mulkin shugaban jami'ar na shida, Farfesa Abdulrasheed Na'Allah.

    Hukumar gudanarwar jami'ar ce ta naɗa ta kan wannan muƙamin a matsayin riƙo zuwa lokacin da za a ƙaddamar da majalisar jami'ar da kuma naɗa cikakken shugaban jami'ar.

    Farfesa Maikudi, ƙwararriya ce a fannin ilimin shari'a ta duniya kuma ita ce mataimakiyar shugaban jami'ar mai kula da ɓangaren koyo da koyarwa.

    An haifi farfesa Aisha Sani Maikudi, yar asalin jihar Katsina, a birnin Zaria da ke jihar Kaduna ranar 31 ga watan Janairun 1983.

    Farfesar Maikuɗi ita ce farfesa mafi ƙanƙantar shekaru a jami'ar Abuja.

    Ta samu shaidar kammala makarantar sakandare a Queens College da ke Legas. Bayan nan kuma, ta yi digiri na farko da na biyu a jami'ar Reading da London School of Economics a Burtaniya kan ilimin shari'a.

    Ta kuma je makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya da ke Abuja daga nan kuma ta yi digirinta na uku a jami'ar Abuja duk a fannin na shari'a.

    Farfesa Aisha ta yi wa kasa hidima karkashin shirin NYSC a shekarar 2007. Sannan ta soma koyarwa a jami'ar Abuja a 2008, ta kuma zama mace ta farko kuma mafi karancin shekaru da ta shugabanci sashen koyar da ilimin shari'a a 2014, kuma mace ta farko mafi karancin shekaru da ta zama mataimakiyar shugaban sashen a 2018. Ta kuma kafa tarihin zama darakta ta farko a jami'ar ta Abuja.

  10. Attajirin Georgia ya yi wa tawagar ƙasar kyauta bayan doke Portugal

    Bidzina Ivanishvili, tsohon firaministan Georgia, ya yi alƙawarin bai wa tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar kyautar fan miliyan 8.4 bayan sun yi bajintar doke Portugal a gasar Euro 2024.

    Georgia wadda tsohon ɗan wasan Faransa Willy Sagnol ke jagoranta, ta baje Portugal ne a jiya Laraba domin samun gurbi a zagayen 'yan 16, inda za su buga da Sifaniya.

    Ivanishvili wanda ya kafa jam'iyyar Georgian Dream kuma ya zama firaminista a 2012, ya ce nasarar a kan Portugal "abar tarihi ce kuma wadda aka daɗe ana buri".

    Attajirin ya kuma ce zai ba wa tawagar ƙarin fan miliyan 8.4 (Lari miliyan 30 kuɗin ƙasar) idan suka sake doke Sifaniya.

    A ranar Lahadi ne Georgia za ta fafata da Sifaniyan a filin wasa na Cologne da ke Jamus da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.

  11. Kotu ta tabbatar da hukuncin ɗauri kan tsohon firaministan Burundi

    Wata kotu a Burundi ta tabbatar da hukunci ɗauri kan toshon firaministan ƙasar Janar Alain Guillaume Bunyoni.

    A watan Disamban 2023 ne aka samu Janar Bunyoni da laifukan da aka tuhume shi da su ciki har da barazana da rayuwar shugaban ƙasar da wasu hukumomi a ƙasar da kuma yi wa tattalin arzikin zagon-ƙasa.

    Baya ga hukuncin, kotun ta kuma umarce shi ya biya tarar dala 7,893,326 da kuma ƙwace kadarorinsa da bai bayyana wa kotun a 2021 ba.

    A lokacin sauraron ƙarar, Janar ɗin ya ce yana da gonaki 20, da gidaje da motoci 40 ciki har da na noma.

    Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara 15 ga mutum uku da aka tuhume su tare, waɗanda su ma suka ɗaukara ƙara.

    Lauyan Janar Bonyoni ya kuma ce za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

    A watan Afrilun 2023 ne aka kama shi, wata shida bayan shugaban ƙasar ya sauke shi daga muƙaminsa.

  12. Imran Khan ya yi rashin nasara a kotu

    Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan, ya yi rashin nasara a ƙarar da ya ɗaukaka kan hukuncin laifi da ya da ya sa aka garkame shi a gidan yari.

    Wani alkali ya yi watsi da yunƙurin da Mista Khan da matarsa ​​Bushra Bibi suka yi na soke hukuncin ɗaurin shekara bakwai da aka yanke musu kan karya dokokin aure na Musulunci.

    An same su da laifi a watan Fabrairu na rashin ba da tazarar lokacin da ya dace tsakanin aurensu da kuma mutuwar auren Ms Bibi da tsohon mijinta.

    Mista Khan ya shafe kusan shekara guda a gidan yari bisa wasu tuhume-tuhume da ake yi masa, waɗanda ya ce suna da alaƙa da siyasa, amma an dakatar da mafi yawa daga cikinsu bayan ya ɗaukaka ƙara.

  13. An amince da tsawaita lokacin aiwatar da kasafin kuɗin Najeriya na 2023

    Majalisar wakilan Najeriya ta amince da buƙatar ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2023 har zuwa ƙarshen shekarar 2024.

    Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Akin Rotimi, ta ce "an amince da ƙudurin ne domin amfanin ƙasa baki ɗaya, bayan zazzafar muhawara da aka tafka kan lamarin".

    Sanarwar ta ce "Majalisar wakilai ta amince da dokoki biyu waɗanda suka buƙaci tsawaita aiwatar da kasafin kuɗi na 2023 da kuma ƙaramin kasafin kuɗi na shekarar ta 2023 har zuwa watan Disamban 2024".

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya tura ƙudurorin biyu zuwa majalisar dokoki.

    A lokacin muhawara kan ƙudurorin, wasu ƴan majalisa sun nuna shakku game da buƙatar amincewa da su cikin sauri, inda suka yi fargabar kada ya kasance akwai wani abu da zai cuci al'ummar ƙasa.

    Sai dai bayan tattaunawa da kuma duba ɓangarorin dokar a matakin kwamiti, zauren majalisar ya sake zama inda ya amince da ƙudurorin.

    Hakan na nufin cewa a yanzu ƙasar za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2023 da kuma na 2024 a lokaci guda.

  14. Tinubu ya gana da gwamnoni kan albashi mafi kankanta

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima sun gana da gwamnonin jihohi 36 har da ministoci game da sabon albashi mafi kankanta ga ma'aikatan kasar da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

    Shugaban da gwamnonin sun gana a taron majalisar tattalin arziki ta kasa karo na 141 da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

    Mataimakin shugaban kasar ne ya jagoranci tattaunawar da gwamnoni da mataimakansu da kuma ministoci kafin isar shugaban kasa.

    Taron ya zo ne kwanaki biyu bayan da majalisar zartaswar gwamnatin tarayya ta jinginar da batun mafi kankantar albashin domin ba da dama a kara yin tuntuba.

    A ranar Laraba ne gwamnoni karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya suka gana a Abuja inda suka bai wa yan kasar tabbacin cewa tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu da kuma kungiyar kwadago zai yi tasiri.

    Shugaban kasar a jawabinsa na ranar dimokradiyya ya bai wa kungiyar kwadago tabbaci cewa nan ba da dadewa ba za a aike da kudiri kan sabon albashi mafi kankanta zuwa ga majalisar dokokin kasar domin amincewa.

    Ana sa ran shugaban zai dauki mataki kan shawarar N62,000 da gwamnati ta bayar da kuma bukatar yan kwadago ta neman mafi kankantar albashi a Najeriya ya zama N250,000.

  15. Kotu ta hana tube rawanin hakiman Sokoto

    Babbar kotu a jihar Sokoto ta dakatar da gwamnan jihar, Ahmed Aliyu daga tube rawanin biyu cikin hakimai 15 da gwamnatinsa ta tsige.

    Hakiman Tambuwal da Kebbe, Alhaji Buhari Tambual da Alhaji Abubakar Kassim, wadanda ke cikin hakiman da gwamnatin jihar ta tube ne suka shigar da karar.

    Gwamnatin ta dauki mataki a kan su ne bisa zargin hannu a matsalar tsaro da kuma kin yin biyayya.

    Alkalin kotun, mai shari'a Kabiru Ibrahim Ahmed ya bai wa gwamnan da alkalin alkalan jihar da fadar sarkin musulmi da su soke tubewar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da hakiman suka shigar gabansa ta hannun lauyansu Farfesa Ibrahim Abdullahi mai mukamin SAN.

    Mai shari'a Ahmed ya umarci wadanda ake kara da wakilansu da su tsaya kan matsayin da ake game da batun tsige hakiman a jihar Sokoto musamman hakiman Kebbe da Tambuwal har sai lokacin da aka kammala sauraron karar da suka shigar gaban kotu.

    Tuni dai korar hakimai 15 da kudirin da ke neman yin garambawul ga dokar kananan hukumomi a Sokoto suka janyo cece-kuce a fadin Najeriya inda mataimakin shugaban kasa, Kassim Shetiima ya nemi gwamnatin jihar ta mutunta kujerar sarkin musulmi.

  16. Yunwa ta tsananta a Sudan

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai mummunar yunwa kuma abin na ƙara ƙazancewa a Sudan, inda aka kwashe wata 14 ana yaƙi, kuma wurare da dama sun faɗa cikin ƙangin yunwa.

    Hukumar bunƙasa noma da samar da abinci ta duniya ta ce kimanin mutum miliyan 25 - fiye da rabin yawan al'ummar ƙasar na fama da ƙarancin abinci.

    Hukumar ta ce nazarin da ta yi ya nuna cewa wannan ce yunwa mafi tsanani da aka taɓa samu a tarihin ƙasar Sudan.

    Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin dakarun RSF da na gwamnati ya tursasa wa sama da mutum miliyan takwas tserewa daga gida.

    Ƙungiyar agaji ta Mercy Corp ta ce an mayar da gonaki da dazuka fagagen daga, sannan ɓangaren kiwon lafiya ya shiga cikin matsala, abin da ya jefa mutane da dama cikin haɗari.

  17. Yan sanda sun tarwatsa matasan da ke ci gaba da bore a Kenya

    Yan sanda a Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye tare da harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zanga da suka yi kokarin yin dafifi a Nairobi, babban birnin kasar, kwana daya bayan soke kudurin kara haraji da shugaban kasar ya yi.

    An girke jami'an tsaro a babban birnin kasar har da motocin sojoji da ke kai komo a wajen.

    Har yanzu harkokin kasuwanci sun tsaya cik a tsakiyar birnin.

    A ranar Laraba ne gagarumar zanga-zanga ta tilasta wa shugaba William Ruto soke kudirinsa na sa hannu kan kudurin da ya janyo fushin jama'ar kasar.

    Mutum 23 yan sanda suka kashe a ranar Talata sannan an yi kaca-kaca da ginin majalisar dokokin kasar.

    Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce wasu jami'ai na yi wa mutanen da ke da hannu a zanga-zangar dauki dai-dai.

    Wasu cikin masu zanga-zangar na neman shugaban kasar ya yi murabus inda suke zargin gwamnatinsa da rashawa.

  18. An wajabta wa ma'aikatan Ukraine koyon Ingilishi

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanya hannu kan wata doka da ta buƙaci dukkan ma'aikatan ƙasar su iya magana da harshen Ingilishi.

    A yanzu jin harshen ngilishi zai zama ka'ida ta samun aiki ga sojoji da masu shari'a da jami'an kwastam da shugabannin makarantun gaba da sakandare da sauran su.

    Duk ma'aikacin gwamnatin da ya iya magana da turancin Ingilishi zai samu ƙarin albashi da kashi 10.

  19. Halin da ake ciki kan ɓarkewar kwalara a Najeriya

  20. Bam ya kashe sojan Isra'ila a Gaɓar Yamma

    Wani sojin Isra'ila da wasu mutum 16 sun rasa rayukansu sakamakon tashin wasu bama-bamai da aka dasa a gefen hanya a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na gudanar da samame a wajen sansanin yan gudun hijra na Jenin a lokacin da bam na farko ya tashi a karkashin motarsu.

    Lokacin da karin sojoji suka isa wajen kuma, wani bam din ya sake tashi ain da ya yi ajalin soja daya da raunata wasu da dama.

    Kungiyar da ke kula da fursunoni Falasdinawa ta ce sojoji sun kama mutum 28.

    Tun bayan soma yakin Gaza ake samun karuwar tashin hankali a Gabar Yamma da kogin Jordan gami da samame da kamen mutane da sojojin Isra'ila suke yi.