Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/08/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, 24/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Shugaban hukumar tattara bayanan sirri na Najeriya ya ajiye aikinsa

    Shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya, Ahmed Rufai Abubakar ya sanar da ajiye muƙaminsa.

    Yayin da yake jawabi ga maneman a fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu, Ahmed Rufai ya gode wa shugaban ƙasar bisa ba shi damar ci gaba da jagorantar hukumar bayan da ya zama shugaban ƙasa.

    Ahmed Rufai ya ce ya je fadar shugaban ƙasar domin ganawa da shi, da yi masa bayanai kamar yadda ya saba a koyaushe, bayan nan ne kuma ya miƙa masa takardar ajiye aikinsa.

    “Bayan na yi masa jawabi, na kuma gabatar masa da takardar ajiye aikina, kuma shugaban ƙasar ya karɓeta tare da amincewa da ita'', kamar yadda ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasar.

    To sai dai bai yi cikakken bayani kan dalilinsa na ajiye aikin a daidai wannan lokacin ba.

    Ya kuma ce yana alfahari bisa aikin da ya yi da shugabannin ƙasar har guda biyu.

    A watan Janairun 2018 ne dai tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar, bayan korar tsohon shugaban hukumar Ayo Oke, bisa zargin rashawa.

    Saukar shugaban na NIA na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da ƙamari a Najeriya, musamman yankunan arewacin ƙasar, inda 'yan bindiga ke zafafa hare-hare, tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

  2. Masu shigar da ƙara sun gayyaci ɗan takarar adawar Venezuela

    Masu shigar da ƙara a Venezuela sun gayyaci ɗan takarar adawa, Edmundo Gonzales domin ya amsa wasu tambayoyi ranar Litinin mai zuwa, bayan zaɓen shugaban ƙasar mai cike da taƙaddama

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shugaban ƙasar mai ci, Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    To amma jam'iyyar adawar ta wallafa wani sakamakon da ya nuna Mista Gonzalez ne ya lashe zaɓen.

    Hukumar zaɓen ƙasar dai ta ƙi wallafa cikakken sakamakon, bayan da ta yi zargin cewa masu kutse sun jirgita bayanan.

    Mista Gonzalez ya shiga wasan buya da jami'an tsaro kwana biyu bayan zaɓen.

    Mummunar zanga-zanga ta ɓarke a ƙasar bayan zaɓen, lamarin da ya haddasa mutuwar mutum 25 tare da raunata fiye da 200.

  3. Za mu ci gaba da yaƙi ko za a shekara 100 ana yi - al-Burhan

    Shugaban sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya yi watsi da tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke dauƙar nauyi a Switzerland domin kawo ƙarshen yaƙi tsakanin dakarun RSF da sojojin ƙasar.

    Da yake jawabi a Port Sudan, Janar al-Burhan ya ce sojojinsa za su ci gaba da yaƙi koda za a shekara ɗari ana yi.

    Gwamnatin mulkin sojin ta ƙi tura wakilai zuwa tattaunawar, inda ta buƙaci a koma kan matsayar da aka cimma wadda dakarun RSF suka sanya wa hannu a shekarar da ta gabata a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya.

    An kai ƙarshen tattaunawar ba tare da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba a ranar Juma'a sakamakon kasa haɗa ɓangarorin biyu a teburin tattaunawar.

  4. 'Yan sama jannatin da suka maƙale a sama ba za su sauko ba sai a shekara mai zuwa

    Hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, NASA ta ce 'yan sama jannatin nan biyu da suka maƙale a tashar sararin samaniya ba za sauko ƙasa ba, sai a cikin watan Fabrairun shekara mai kamawa.

    Shugaban hukumar, Bill Nelson ya ce kumbon 'Boeing Starliner', da ya kai 'yan sama jannatin cikin watan Yuni zai sauko ƙasa ba tare da kowa a cikinsa ba.

    Ya ƙara da cewa a yanzu wani kumbon ne mai suna 'SpaceX craft' zai sauko da mutanen biyu,

    Tun da farko dai an tsara mutunen biyu Barry Wilmore da Sunita Williams, za su yi kwana takwas a tashar samaniyar, kafin su fuskanci cikas bayan bulaguron nasu.

  5. 'Kimanin yara miliyan 4.4 ne ke fama da tamowa a arewacin Najeriya'

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta kan ƙaruwar yaran da ke fama da tamowa a yankin arewacin ƙasar.

    Daraktar sashen kula da abinci mai gina jiki na hukumar lafiyar ƙasar, Mrs Ladidi Bako-Aiyebusi ta ce kimanin yara miliyan 4.4 ne ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a yankin arewacin ƙasar.

    Yayin da take jawabi a taron masana harkokin abinci da masu ruwa da tsaki kan tsare-tsaren samar da abinci mai gina jiki a jihar Nasarawa da ke tsakiyar ƙasar, ta ce Ƙasar na fama da matsalar ƙaruwar tamowa tsakanin ƙananan yara.

    Ta ce wani bincike kan abincin mai inganci da aka gudanar a 2021 ya nuna cewa kusan yara miliyan 4.4 ne ke fama da matsalar tamowa a yankin arewa maso yammacin da arewa maso gabashin ƙasar.

    Ta kuma alaƙanta matsalar da rashin samun wadataccen abinci, da rashin tsari wajen cin abincin da kuma rashin iya kula da yara da matsalar tattalin arziki da rashin damar zuwa asibiti da rashin ilimi.

  6. Shugabannin PDP sun sayar da jam'iyyar - Dino Melaye

    Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kogi kuma ƙusa a jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, Sanata Dino Melaye, ya zargi shugabbanin jam'iyyar da sanya ta a kasuwa domin sayar da itya.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ranar Asabar, Tsohon Sanatan na Kogi ta Yamma ya ce jam'iyyar ta rasa matsayinta a fagen siyasar ƙasar.

    Melaye ya zargi shugaban jam'iyyar na ƙasar Iliya Damagum da sakatarenta na ƙasa, Samuel Anyanwu da sakataren tsare-tsaren jam'iyyar, Umar Bature da wargara jam'iyyar.

    “Ƙarshen jam'iyyar PDP ya zo bayan da Damagum da Bature da kuma Anyanwu suka wargaza ta. Za mu yi magana kan sanya jam'iyyar a kasuwa da kuma sayar da ita da suka yi. A yanzu PDP ta zama tarihi'', kamar yadda ya wallafa a shafin nasa na X.

    Maganganun Sanata Melaye na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da wasu mambobin majalisar wakilan ƙasar suka zargi Damagum da Anyanwu da shirya wa jam'iyyar abin da suka kira 'zagon-ƙasa'.

    'Yan majalisar sun zargi shugabanin da tallafa wa tsoffin 'yan majalisar dokokin jihar Rivers da suka fice daga jam'iyyar.

    Suna masu iƙirarin cewa hakan wani yunƙuri ne da shugabannin PDPn ke yi na tsige gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara.

    Siyasar jihar River da PDP ke mulki, ta shiga rikici ne tun bayan da aka samu saɓani tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da tsohon gwamna jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

  7. Gwamnatin jihar Neja ta nemi agajin sojoji bayan 'yan bindiga sun mamaye wani gari

    Muƙaddashin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kai wa al'ummar garin Alawa - da ke yankin ƙaramar hukumar Shiroro - agajin sojoji.

    Rahotonni sun ce a watannin da suka gabata ne gwamnatin tarayya ta janye sojojin da ke aiki a yankin, matakin da ya ƙare kefa al'ummar yankin cikin ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga.

    Kiran muƙaddashin gwamnan na zuwa ne kwanaki bayan da ranar Larabar da ta gabata 'yan bindiga suka kai wani sabon hari, tare da kashe manoma 13 da ke aiki a gonakinsu da ke wajen garin na Alawa.

    Harin na baya-bayan nan ya sake jefa al'ummar yankin cikin tashin hankali da firgaba, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin da dama barin yankin, don tsira da rayukansu.

  8. Harin bam ya kashe aƙalla mutum uku da jikkata wasu sama da 13 a Pakistan

    Ƴansanda a Pakistan sun ce wani bam da aka dasa ya kuma tashi a wata kasuwa a lardin Baluchistan, ya kashe aƙalla mutum uku da suka haɗa da yara biyu.

    Harin na gundumar Pishkin ya kuma jikkata aƙalla mutum goma sha uku da suka haɗa da ƴansanda biyu.

    Wani jami'in ƴansanda ya ce an ɗan bam ɗin ne a jikin wani babur, sannan aka tashe shi daga nesa.

    Ba ƙungiyar da ta fito fili ta ɗauki alhakin kai harin, amma galibi hukumomi kan zargi, masu tayar da ƙayar baya na ƴan-aware.

    Ƴan a-waren suna yaƙar jami'an tsaron Pakistan tsawon gomman shekaru, inda suke zargin gwamnati da yin babakere kan albarkatun Baluchistan.

  9. Zambia za ta riƙa katse wutar lantarki tsawon sa'a 17 kullum

    Zambia ta sanar da matakin katse wutar lantarki tsawon sa'a 17 a kullum, daga wata mai zuwa, saboda ƙarancin ruwa a madatsar ruwant da ke sama mata lantarki.

    Sai dai ministan makamashi Mista Makozo Chikote, wanda ya sanar da hakan bai bayyana har zuwa wane lokaci za a riƙa katse wutar ba.

    Ƙamfar ruwan da ƙasar ta shiga ta tsawon lokaci ta sa dam ɗinta na Kariba, wanda shi ne babbar hanyar samar da lantarkinta ya kasance da kashi goma cikin ɗari kawai na ruwan da ya kamata ya samu domin samar da lantarki.

    Domin magance matsalar ƙarancin wutar ƙasar ta shirya sayen wuta daga Afirka ta Kudu da kuma kamfanin lantarki na ƙasashen yankin Afirka ta Kudu.

  10. Hamas ta ce za ta tura tawaga tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, amma ba za ta shiga ba

    Hamas ta ce za ta tura tawaga tattaunawar neman dakatar da buɗe wuta a yaƙin Gaza, wadda za a yi a a babban birnin Masar, Alƙahirai, amma kum ta ce ba za ta shiga yarjejeniyar ba.

    Wani babba daga cikin jami'an ƙungiyar ya sheda wa BBC cewa tawagar za ta kasance ne ƙarƙashin jagorancin babban mai shiga tsakani na kungiyar, Khalil al-Hayya.

    Amma kuma jami'in ya ce babu wani abu da ya sauya a kan matsayar Hamas, ta neman janyewar Isra'ila gaba ɗaya daga muhimman wurare gud biyu a Gaza, da suka haɗa da yankin Philadelphi.

    A jiya Juma'a fadar gwamnatin Amurka ta ce an samu cigaba a tattaunawar, amma kuma akai buƙatar dukkanin ɓangarorin su haɗu kuma su yi aiki wajen aiwatar da yarjejeniyar.

  11. Albashin N70,000 ba zai canza wa ma'aikata komai ba - Gwamnan Gombe

    Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce albashin naira 70,000 ba zai canza komai ba, la'akari da karyewar darajar kuɗin ƙasar.

    Gwamnan ya shaida wa BBC cewa kamata ya yi kowace jiha ta kafa kwamiti domin duba yadda za ta aiwatar da sabon tsarin albashin mafi ƙanƙanta ba tare da cutar da wani ɓangare ba.

    Ya ce: ''Na sha faɗin cewar naira 300,000 ma bai kai ta riƙe mutum da iyalinsa ba.''

    ''To yanzun ma kuma haka yake, don an kai shi naira 70,000 ba zai canza komai ba, domin darajar kuɗin ƙasarmu ta karye'', in ji Gwamnan.

  12. Ƴansanda sun tabbatar da ceto ɗaliban likitanci 20 da aka sace a jihar Benue

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da sakin ɗaliban nan 20 da ke karatun aikin likita, waɗanda aka sace a jihar Benue a ranar Juma'a ta makon da ya gabata.

    A wata sanarwa da kakakin ƴansandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya fitar ya ce a jiya Juma'a ne ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya ceto ɗaliban da aka riƙe su a dajin Ntunkon, da ke ƙaramar hukumar ADO ta jihar Benue, ba tare da an biya wani kuɗi ba.

    Tashar talabijin ta Channels, ta ce wata majiya da ta tabbatar da ingancinta, ta tabbatar mata cewa an yi amfani da wasu jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu guda uku a aikin ceto ɗaliban, inda ta ce an kama wasu daga cikin masu garkuwar wasu kuma an kashe su.

    A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne aka sace ɗaliban na jami'ar Maiduguri da jami'ar Jos tare da likitocin da suke tare da su a kan hanyarsu ta zuwa wani taro.

    Ƴan kwanaki kaɗan bayan sace su, ƴan bindigar sun tuntuɓi iyalan ɗaliban suna son a ba su kuɗin fansa naira miliyan 50, kafin su sake su.

  13. Gwamnatin Najeriya ta amince a kori ma'aikata masu takardar karatu ta bogi daga ƙasar Benin da Togo

    Gwamnatin Najeriya ta bayar da amince a kori duk ma'aikata na gwamnati da waɗanda ba na gwamnati ba, waɗanda suke da takardar shedar karatu ta bogi, da suka samu daga Jamhuriyar Benin da Togo,

    Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman shi ne ya bayyana haka a, yayin wani taron manema labarai, jiya Juma'a a Abuja, lokacin da yake bayyana irin nasarorin da ya ce ya samu a tsawon shekara ɗaya a ma'aikata.

    Mamman ya ce an amince da matakin ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta ƙasar kwanan nan.

    Ministan ya bayyana cewa ƴan ƙasar sama da 22,500 ne ke ɗauke da takardar shedar karatu ta bogi da suka samu daga ƙasashe irin su, Jamhuriyar Benin da Togo, a tsakanin 2019 da 2023.

    Ya ce sama da ɗalibai 21, 600, suka samu takardun shedar karatun daga jami'o'in da ba a tabbatar da ingancinsu ba a Jamhuriyar Benin yayin da 1,105 su ma suka samu irin waɗannan takardu daga jami'o'in da ba a tabbatar da ingancin nasu ba a Togo.

    Ya ƙara da cewa a don haka ne gwamnati ta kafa wani kwamiti na musamman na haɗin gwiwa tsakanin ma'aikatu domin gudanar da bincike kan takardun shedae karatun, cibiyoyin da ke wannan cuwa-cuwa a ciki da wajen Najeriya.

  14. Gwamnatin Mali ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan ambaliya

    Gwamnatin Mali ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ambaliyar ruwa bayan mutuwar mutum sama da 30 tare da shafar wasu mutanen 47,000, tun bayan da damuna ta sauka.

    Gwamnatin ta yi zama na musammtan domin nazarin matsalar tare da ware dala miliyan bakwai domin samar da agajin abinci da sauran tallafi.

    Yawancin shekaru a yankin Afirka ta Yamma da kuma Afirka ta Tsakiya ana fama da ambaliyar ruwa a tsakanin watan Yuni da Satumba.

    Ambaliya ta shafi sama da mutum 716,000 a fadin yankin zuwa yanzu a wannan damunar.

    A yankin Sahel, ambaliyar ta kashe sama da mutum 200 a Nijar da Chadi, baya ga ɗimbin dukiya da ta lalata

  15. Sojojin Amurka sun ce sun kashe wani kwamandan ƙungiyar da ke da alaƙa da Al Qaeda a Syria

    Dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya sun ce sun kashe wani babban kwamandan kungiyar da ke kai hare-hare daga Syria mai alaka da Al Qaeda.

    Sojojin na Amurka sun bayyana sunansa a matsayin Abu Abdul Rahman al-Makki, mamba a kungiyar Hurras al-Din Shura.

    Kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria, ta ce harin da aka kai da jirgi marar matuki a lardin Idblib ya kashe dan kasar Saudiyyar.

    Amurka na da sojoji kimanin 900 a Syria, daga cikin rundunar hadaka da ke yaki da mayakan IS

  16. Hukumar leƙen asiri ta Amurka ta dakatar da jami'anta saboda harin da aka kai wa Trump

    Hukumar leken asiri ta Amurka, CIA, ta tura wasu jami'anta guda biyar hutun dole sakamakon binciken da ake yi kan yunkurin da aka yi na halaka tsohon shugaban kasar kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam'iyyar Republican, Donald Trump a watan jiya.

    Majiyoyi sun ce ɗaya daga cikinsu shi ne shugaban wani reshen hukumar .

    Hukumar leken asirin na fuskantar bincike kan gazawarta wajen hana maharin samun isa wurin da Trump yake gangamin yakin neman zabe.

    Harbin dai ya samu tsohon shugaban a kunne sannan mutum ɗaya ya mutu, biyu kuma sun jikkata, a harin.

    Jami'an tsaro sun kashe maharin a lokacin.

  17. Ƴansandan Jamus na farautar wani mutum da ya hallaka mutum uku da wuƙa

    'Yansanda a yammacin Jamus na farautar wani mutum da ya kashe mutum uku ta hanyar daba masu wuka tare da raunata wasu hudu a wani wurin biki a birnin Zolayen Solingen.

    Sun ce an kafa shingayen bincike kan hanyar birnin amma kuma an fadada bincike har zuwa wasu biranen. ‘Yan sanda ba su bayar da cikakken bayani ba kan maharin.

    Lamarin ya faru ne a lokacin murnar cikar birnin shekara dari shida da hamsin da kafuwa.

    Hukumomin birnin sun yi kira ga jama'a da su kaurace wa wata kasuwa (Fronhof), yayin da 'yansanda ke kafa shingaye don kama maharin.

    Magajin garin ya ce birnin na cikin alhini da kaduwa da bakin ciki.

  18. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Asabar, 24/08/2024.

    Ni, Muhammad Annur Muhammad zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba. A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Kowa rai ya yi wa daɗi baran me shi ne