'Har yanzu ba a kammala tantance mutanen da Tinubu ya yi wa afuwa ba'
Ministan shari'a na Najeriya Lateef Fagbemi ya ce jerin sunayen mutanen da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi wa afuwa na a 'matakin ƙarshe' na tantancewa, inda ya ƙunshi dubawa da nazari kan mutanen da ke ƙunshe a ciki.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne shugaba Tinubu ya yi wa mutane 175 da aka kama da laifi afuwa, bayan samun amincewa daga majalisar magabata ta ƙasar.
Daga cikin mutanen da shugaban ya yafe mawa akwai mutumin da ake wa kallon ɗaya daga cikin ƴan kishin ƙasa mafiya shahara Herbert Macauly, da tsohon ɗan majalisar wakilai Faruk Lawan da kuma Mamman Batsa, tsohon manjo-janar na soja wanda aka zartar wa hukuncin kisa a shekara ta 1986 bisa zargin kitsa juyin mulki.
Sai dai afuwar ta janyo martani daga sassan ƙasar, inda aka yi zargin cewa jerin waɗanda aka yi afuwar ya ƙunshi waɗanda aka yanke wa hukunci bisa laifin safarar ƙwaya da masu haƙar ma'adanai ta haramtacciyar hanya.
Wasu na ganin cewa wasu daga cikin mutanen ba su cancanci samun afuwar shugaban ƙasar ba saboda girman laifin da suka aikata.
Ɗaya daga cikin waɗanda afuwar tasu ta janyo zazzafar muhawara ita ce Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa bisa laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello.
Sai dai a wata sanarwa da ministan shari'a Lateef Fagbemi ya fitar a yau Alhamis, ya ce babu wani da ake tsare da shi a gidan yari da aka sako, a cikin jerin waɗanda shugaban ƙasar ya yi wa afuwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa: "Batun yana a mataki na ƙarshe, wanda ya ƙunshi sake yin duba na tsanaki domin tabbatar de cewa duk sunayen da aka gabatar sun cika ƙa'idojin da aka gindaya kafin ba da izinin sakin su".