Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 7/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan daƙile juyin mulki a Benin

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba wa "jarumtar" da dakarun sojin ƙasar suka nuna a ranar Lahadi wajen kare afkuwar juyin mulki a Jamhuriyar Benin mai maƙwaftaka.

    A wata sanarwa da shugaban ƙasar ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, Tinubu ya ce "sojojin sun hanzarta wajen mayar da martani kan buƙatar da gwamnatin Benin ta miƙa ta ceto dimokuraɗiyyar ta shekara 35."

    Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya ɗauki mataki bayan samun buƙatar neman ɗauki biyu.

    "Da farko Tinubu ya bayar da umarnin tura jiragen yaƙin Najeriya waɗanda suka karɓe iko da sararin samaniyar Jamhuriyar Benin domin taimakawa wajen kawar da masu iƙirarin juyin mulki daga ginin gidan talabijin na ƙasar da kuma wani sansanin soji," in ji sanarwar.

    "A buƙata ta biyu kuma mahukuntan Benin sun buƙaci yin amfani da kayan aikin rundunar sojin sama ta Najeriya wajen tattara bayanai da kai ɗaukin gaggawa bisa jagorancin hukumomin Benin."

  2. Ecowas ta tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin don dakile juyin mulki

    Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka - Ecowas - ta sanar da tura rundunar ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin wajen kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki.

    A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin yau Lahadi, ta ce “Shugaban Ecowas, bisa ga amincewar shugabannin kasashen kungiyar ya amince da tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Jamhuriyar Benin nan take.

    “Dakarun za su kunshi sojoji daga kasashen Najeriya da Saliyo da Cote d’Ivoire da kuma Ghana.

    “Dakarun za su taimaka wa gwamnati da kuma dakarun Jamhuriyar Benin wajen kare martabar kundin tsarin mulki da na kasar ta Benin.”

    A safiyar yau ne wasu sojoji suka bayyana a tashar talabijin ta kasar inda suka sanar da karbe iko da kasar, sai dai daga bisani ministan harkokin cikin gida na kasar ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewa sojojin kasar sun samu nasarar tarwatsa shirin juyin mulki .

  3. Rasha na ci gaba da kai hare-hare a Ukraine

    Rasha ta ci gaba da kai munanan hare-hare kan Ukraine.

    Hukumomi a yankin Kremenchuk sun ce hare-haren sun lalata muhimman wuraren sarrafa makamashi.

    Lamarin ya janyo katsewar lantarki da ƙarancin ruwa da kuma tsananin zafi.

    Shugaba Zelensky ya ce a wannan makon kaɗai, Rasha ta kai wa ƙasarsa hare-hare da jiragen sama marasa matuƙa har guda 1,600, da kuma wasu manyan makaman.

    Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da neman kawo zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu, a wani zama da Amurka ke jagoranta a birnin Washington.

  4. MDD ta buƙaci taliban ta cire takunkumin da ta ƙaƙabawa mata

    Majalisar Dinkin Duniya ta sake kira ga gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta janye takunkumin da ta sanya wa mata da ya haramta masu yin aiki a ofisoshin MDD.

    Shugabar hukumar kare ƴancin mata ta MDD a Afghanistan, Susan Ferguson ta ce takunkumin da aka sanar tun cikin watan Satumba ya janyo koma-baya ga aikin ceton rayukan jama'a.

    Ta ce a yanzu matan da ke yi masu aiki a ƙasar ba su iya zuwa aiki, duk da cewa ana matuƙar buƙatar aikinsu a ofisoshin MDD, domin yi wa jama'a hidima.

  5. An rufe runfunan zaɓen ƴan majalisa a Hong Kong

    An rufe runfunan zaɓe a Hong Kong, a wani zaɓe da ake ganin zai nuna matsayar jama'ar ƙasar bayan gobarar da ta kashe mutane fiye da 160 a wani rukunin gidaje.

    Ƙasa da kashi ɗaya bisa huɗu na kujerun majalisar dokokin Hong Kong ne kaɗai jama'a ke zaɓa kai tsaye, kuma ana sanya tsauraran matakan tantance ƴan takara.

    Gwamnati ta sha wahala sosai wajen neman mutane su fito domin kaɗa ƙuri'a.

    Hukumomi sun ce yawan mutanen da suka fito zaɓe ya zarce wanda aka samu a 2021.

  6. Gobara ta kashe mutum 25 a India

    Wata gobara da ta tashi a wani shahararren gidan rawa da ke yankin Goa da ke gaɓar tekun Indiya ta kashe mutane 25, kamar yadda jami’an yankin suka sanar.

    Ƴan sanda sun yi imanin cewa wata tukunyar iskar gas ta fashe a cikin kicin na gidan rawar, wanda ke kusa da wani shahararren bakin teku.

    Wurin ya cika maƙil waɗanda da suka zo suraron wani mai haɗa na Bollywood.

    Mutane huɗu ƴan dangi ɗaya daga birnin Delhi da kuma wasu ma'aikatan gidan rawar guda 21 na daga cikin waɗanda abin ya shafa, in ji ƴansandan Delhi.

    An kama manajan gidan rawar tare da bayar da sammacin kama mai gidan.

    Shugaban ƴan sandan yankin Alok Kumar ya ce gobarar ta ta’allaka ne a kusa da ɗakin dafa abincin gidan rawar.

    Babban Ministan Goa Pramod Sawant ya shaida wa manema labarai cewa mutane uku ne suka mutu sakamakon ƙonewa, yayin da wasu kuma suka mutu sakamakon shakewa.

    Wasu shida kuma suna samun kula a asibiti.

  7. An kama sojojin da su ka yi yunƙurin juyin mulki a Benin

    Rahotanni daga jamhurriyar Benin na nuni da cewa an kama sojoji da dama bayan wani yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da safiyar Lahadi.

    Mutanen da aka kama sun haɗa da waɗanda ake zargi da jagorantar yunƙurin juyin mulkin.

    Bayanai sun ce an kama sojoji 13 waɗanda akasarinsu ke da hannu wajen kutsawa gidan talabijin na ƙasar domin sanar da juyin mulkin, ciki har da wani soja da aka kora a baya.

    A wata sanarwa da ya yi a gidan talabijin, ministan harkokin cikin gidan ƙasar Alassane Seidou, ya bayyana cewa dakarun ƙasar sun yi nasarar daƙile yunƙurin bayan da sojoji suka bayyana a gidan talabijin na ƙasar suna iƙirarin cewa sun tsige shugaba Talon.

    Mista Seidou ya ce wasu ƴan tsirarun sojoji ne da manufarsu ita ce tada zaune tsaye a Benin.

    Tuni dai wani mai bai wa shugaban ƙasa shawara ya shaida wa BBC cewa shugaban na cikin ƙoshin lafiya.

    Jami'an diflomasiyyar Faransa sun musanta rahotannin farko da ke cewa ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Faransa da ke Cotonou, birni mafi girma a Benin kuma cibiyar gwamnatin ƙasar.

  8. Adadin waɗanda suka mutu a ambaliyar ruwa a Indonesia ya haura 900

    Adadin waɗanda suka mutu a Indonesiya sakamakon ambaliyar ruwa na baya-bayan nan ya zarta 900, yayin da wasu ɗaruruwa suka ɓace.

    Sama da gidaje 100,000 ne suka ruguje a lokacin da wata mahaukaciyar guguwar ta taso daga mashigin Malaca a makon da ya gabata, wanda ya janyo mamakon ruwan sama da zabtarewar ƙasa a sassan ƙasar da ke kudu maso gabashin Asiya.

    Ana ci gaba da ƙoƙarin kai ɗaukin ga mutane a yankunan da hanyoyi suka lalace, inda ake jefo kayan agaji daga jiragen sama a wasu wuraren.

    Ambaliyar ruwan ta Indonesiya na ɗaya daga cikin mumunan bala'o'i masu nasaba da yanayi da suka afkawa nahiyar Asiya a cikin ƴan makonnin nan, inda adadin waɗanda suka mutu a Sri Lanka da Thailand da Malaysia da Vietnam ya kusan 2,000.

    Kafofin yaɗa labaran Indonesiya sun ce an sako fursunonin daga wani gidan yari a lokacin da ambaliyar ruwa ta yi barazanar mamaye ginin, inda jami'ai suka ce babu inda za a aika da su.

    An katse hanyoyin shiga yankuna biyu, birnin Sibolga da Tapanuli ta tsakiya, har zuwa ranar Lahadi, inda aka samu cikas wurin kai musu agaji.

    An samu rahotannin sace-sace a manyan kantuna a wasu wuraren.

  9. Tawagar ‘yanmajalisar Amurka ta isa Najeriya don bincika iƙirarin kisan Kiristoci

    Tawagar 'yanmajalisar Amurka ta isa Najeriya a yau Lahadi domin bincika gaskiyar iƙirarin yi iwa Kiristoci kisan gilla.

    Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.

    “Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.

    Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.

    Ribadu ya ce sun tattauna matakan yaƙi da ta’addanaci, da zaman lafiya a Afirka, da hanyoyin ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

  10. Rundunar sojan Benin ta daƙile yunƙurin juyin mulki - Minista

    Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin ɗin ƙasar domin sanar da cewa yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi bai yi nasara ba.

    Wani rukunin sojojin ƙasar ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ya sanar da hamɓare Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da tsarin mulki a kafar talabijin ɗin.

    "Da safiyar Lahadi, 7 ga watan Disamban 2025, wasu tsurarin sojoji sun yi yunƙurin ƙwace mulki domin tayar da fitina a ƙasa da kuma ma'aikatu," a cewar Minista Alassane Seidou.

    "Ganin wannan lamari, sai rundunar sojan Benin, kamar yadda suka sha rantsuwa, suka ci gaba da mara wa ƙasarsu baya. Matakin da suka ɗauka ya ba su damar shawo kan lamarin kuma suka daƙile yunƙurin."

  11. Za mu tura sojoji don taimaka wa Benin daƙile juyin mulki - Ecowas

    Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ce a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Benin da sojoji domin daƙile juyin mulkin da wasu sojoji suka yi iƙirarin yi.

    Matakin na Ecowas na zuwa ne bayan wani rukunin sojoji ya sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ɗin ƙasar a yau Lahadi tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta ɗora wa sojojin alhakin "duk wani rai da aka rasa" sakamakon yunƙurin nasu.

    "Ecowas za ta taimaka wa gwamnati da al'umma da duk abin da ya kamata, ciki har da aika dakarun ko-ta-kwana domin kare tsarin mulki da kuma 'yancin Benin," a cewar sanarwar da hukumar Ecowas mai hedikwata a Abuja ta fitar

    Sai dai hukumomi a ƙasar sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulkin.

    "An shawo kan lamarin. Mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban ƙasa baya - kuma muna ƙara shawo kan al'amuran," kamar yadda Ministan Harkokin Waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.

  12. Faransa za ta taimaka wa Najeriya magance matsalar tsaro a Arewa - Macron

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa za ta taimaka wa Najeriya shawo kan matsalar tsaro a arewacin ƙasar.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X, Macron ya ce ya nemi sauran ƙasashe ƙawayensu da su "ƙara ƙaimi a hulɗarsu" da Najeriya.

    "Na yi magana da Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shaida masa goyon bayan Faransa game da matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya," a cewar Macron.

    "Kamar yadda ya [Tinubu] buƙata, za mu ƙarfafa hulɗarmu da hukumomi da kuma taimaka wa al'ummomin da lamarin ya shafa. Bai kamata mu zama 'yankallo ba."

    Kalaman Macron na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke zargin gwamnatin Najeriya da ƙyale 'yanbindiga suna yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla, iƙirarin da gwamnatin Tinubu ta musanta.

  13. Hukumomi a Benin sun yi iƙirarin daƙile yunƙurin juyin mulki

    Hukumomi a Jamhuriyar Benin sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulki da wani rukunin sojoji ya yi da safiyar yau Lahadi, inda suka yi iƙirarin kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon.

    Sai dai babu tabbas game da abin da faruwa yanzu haka yayin da tuni sojojin suka sanar ta kafar gidan talabijin na gwamnati cewa sun dakatar da kundin mulki da kuma kafa Kwamatin Soja na Sake Gina Ƙasa.

    Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasar sun ce Shugaba Talon na nan ƙalau duk da iƙirarin sojojin na hamɓarar da shi.

    Sun kuma yanzu komai ya lafa ta yadda sojojin ƙasar ne ke kula da tsaron Cotonou babban birnin da ma ƙasar baki ɗaya. An toshe tituna yayin da sojoji ke karakaina a wurare da dama.

    A watan Afrilun shekara mai zuwa ne ya kamata Shugaba Talon ya sauka daga mulki inda zai kammala wa'adin mulki na biyu, kuma a lokacin ne za a yi sabon zaɓe.

  14. An ji harbe-harbe kusa da gidan Shugaban Benin Talon

    Wani saƙo daga ofishin jakandancin Faransa a Benin ya bayyana cewa an ji ƙarar harbe-harbe a kusa da gidan Shugaban Ƙasa Patrice Talon a Cotonou, yayin da sojoji ke iƙirarin juyin mulki.

    A yau Lahadi ne wani rukunin sojoji suka bayyana a kafar talabijin ɗin ƙasar suka sanar da ƙwace iko da kuma kifar da gwamnatin shugaban.

    Sai dai wasu jami'ai na kusa da shugaban sun ce yana nan ƙalau, kuma sojojin ba su samu goyon bayan rundunar sojan ƙasar ba.

    "An shawo kan lamarin. Mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban baya - kuma muna ƙara shawo kan al'amuran," kamar yadda Ministan harkokin Waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.

    Wata majiya a fadar shugaban ƙasar ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP: "Wani ƙaramin rukunin sojoji ne da suka kama iko da gidan talabijin ɗin kaɗai. Birnin da ƙasar na hannun gwamnati baki ɗaya."

  15. Labarai da dumi-dumi, Sojoji sun sanar da juyin mulki a Benin

    Wani rukunn sojoji sun yi iƙirarin kifar da gwamnatin Shugaban Benin Patrice Talon tare da ƙwace ikon ƙasar.

    Sojojin da suka bayyana ta kafar talabijin ɗin gwamnatin ƙasar a safiyar yau Lahadi sun ce sun kafa abin da suka Kwamatin Soja na Sake Gina Ƙasa.

    Sun kuma sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin ƙasar, da rusa gwamnati, da rusa jam'iyyun siyasa.

    An yi imanin sojojin na ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigri, kuma zuwa yanzu ba a san inda Shugaba Talon yake ba.

    Sai dai kamfanin labarai na AFP ya ruwaito fadar shugaban ƙasar na cewa yana cikin ƙoshin lafiya.

  16. Matuƙa jirgin sojan Najeriya sun tsira bayan hatsari a jihar Neja

    Matuƙa jirgin yaƙi na sojan Najeriya sun tsira da rayukansu sakamakon hatsarin da jirgin nasu ya yi a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.

    Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito cewa jirgin ya rikito ne a kusa da sansanin sojan sama da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa a ranar Asabar.

    Mai magana da yawun rundunar sojan sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda rundunar ta ce matuƙa jigrin "sun nuna bajinta".

    "Sun yi nasarar kawar da jirgin daga kan gidajen al'umma cikin ƙwarewa kafin su fice daga ciki," in ji shi.

  17. Kotun Amurka ta ɗaure ɗan Najeriya shekara 20 kan zambar kuɗaɗe

    Wata kotun Amurka ta ɗaure ɗan Najeriya Oluwaseun Adekoya shekara 20 a gidan yari saboda kama shi da laifin zama jagoran masu aikata zambar kuɗaɗe da suka kai dala miliyan biyu a faɗin ƙasar.

    A farkon wannan shekarar ne tawagar masu taimaka wa alƙali ta kama Adekoya, wanda kuma ake kira Legendary, mai shekara 40 da laifin zambatara banki, da haɗa baki, da halasta kuɗin haram, da wasu laifuka tara na satar kamanni.

    Ana sa ran zai biya diyyar dala miliyan 2.2 sannan kuma a mayar da shi ƙasarsa ta haihuwa bayan kammala zaman bursin.

    A cewar hukumomin Amurka, Adekoya ya dinga yin amfani da hanyoyin fitar da bayanai na fili wajen tantance mutanen da ke da kadara a faɗin Amurka. Daga nan kuma sai ya ɗauki lambarsu ta ɗan ƙasa, da lambobin asusu ta shafuka kamar Telegram.

    Daga nan kuma sai ya miƙa bayanan ga wani gungun mutane da ke da takardun bogi waɗanda su kuma suke zuwa su fitar da kuɗi daga asusun mutanen da aka saci bayanansu.

    A watan Disamba na 2023 hukumar FBI ta kama shi, inda ta ƙwace kayayyakin alfarma daga hannunsa ciki har da agogon hannu ƙirar Rolex, da zoben neman aure mai darajar dala 51,000, da jakunkuna, da takalma, da kuɗi kusan dala 26,000 a asusunsa na banki.

  18. Sudan ta zargi RSF da kashe mutum 79 a harin jirgi maras matuƙi

    Gwamnatin Sudan ta ce wani hari da jirgi maras matuƙi da aka kai ranar Alhamis a Kudancin Kordofan ya faɗa kan makarantar rainon yara, inda ya kashe mutum 79 ciki har da yara 43.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na sada zumunta, ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke Khartoum ta zargi RSF da kai harin a garin Kalogi.

    Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya kira harin abin tashin hankali wanda kuma ya take haƙƙin yara.

    Babu wani martani daga mayaƙan na RSF zuwa yanzu, yayin da Sudan ke fama da yaƙin basasa da ya ɓarke fiye da shekara biyu da suka wuce.

  19. Assalamu Alaikum

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na ranar Lahadi.

    Za mu kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya, da Nijar, da maƙwabtansu.

    Ku biyo mu.