Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran wasannin BBC Hausa 2 zuwa 7 ga watan Maris, 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Litinin 2 ga watan Maris, zuwa Asabar 7 ga watan Maris, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Mohammed, Ibrahim Haruna

Arsenal ta ci gaba da riƙe wuta a saman teburin Premier

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta ci gaba da zama kan teburin gasar Premier a Ingila bayan ta lashe wasanta da Chelsea da ci 2-1.

An dai ci duka ƙwallayen ne ta hanyar bugun ƙusurwa.

Duk da cewa Arsenal ba ta buga ƙwallo mai ƙayatarwa ba a wasan, to amma nasarar da ƴanwasanta suka yi na zura ƙwallo biyu ta sanya ƙungiyar ta ci gaba da zama ɗare-ɗare kan teburi da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City wadda ke a matsayi na biyu.

A yanzu Arsenal ta ci ƙwallaye 16 ke nan ta hanyar ko dai bugun tazara ko na ƙusurwa a wannan kaka, inda ta fi kowace ƙungiya ta wannan fanni a kakar.

A wasan na ranar Lahadi, mai tsaron baya William Sliba ne ya jefa ƙwallon farko ta hanyar kara wa ƙwallon kai bayan bugun ƙusurwa da Bukayo Saka ya ɗauko.

Sai dai gab da zuwa hutun rabin lokaci Chelsea ta rama ta hanyar bugun ƙusurwa, inda Piero Hincapié ya ci gida, ya kara wa ƙwallon kai ta faɗa ragar Arsenal.

Can bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma Jurrien Timber ya jefa ƙwallo ta biyu a ragar Chelsea bayan bugun ƙusurwa da Declan Rice ya dauko.