Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye dangane da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya ranar 01/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Rikicin Sudan: An lalata gine-gine, an mayar da filin jirgin sama kufai a Kahrtoum

    Tawagar BBC ta samu shiga Khartoum babban birnin ƙasar Sudan, kuma ta shaida yadda wurare suka lalace, kwanaki ƙalilan bayan sojoji sun sake karɓe birnin daga dakarun RSF.

    Ta kuma shaida yadda ma'aikatun suka ƙone da bankuna da rukunin gine-gine masu tsayi, da kuma yadda filin jirgin saman ƙasa da ƙasa ya zama kufai.

    Mazauna birnin sun shaidawa BBC cewar duk da suna fuskantar tsananin ƙarancin abinci to amma hankalinsu ya kwanta saboda dakarun RSF ba sa iko da birnin a yanzu.

    RSF wadda aka zarga da cin zarafi har yanzu tana riƙe da yankuna da dama a Darfur da ke Yammacin Sudan.

  3. Za mu ɗora wa Sanata Natasha alhakin tashin duk wani rikici - Gwamnatin Kogi

    Gwamnatin jihar Kogi ta ce za ta ɗora laifin duk wani rikici da ya ɓarke a jihar kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya bayan gangamin gaisuwar Sallah da ta kai mazaɓarta.

    Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ya caccaki Sanata Natasha kan gudanar da gangamin duk haramta tata da gwamnatin jihar ta yi.

    "Laifin duk wani tashin hankali da ya ɓarke na kan Sanata Natasha, kuma abin da ta yi yunkuri ne na janyo fargaba," in ji Fanwo.

    Kwamishinan ya kuma zargi Sanatar da shirin amfani da ziyararta wajen ta da hankali a mazaɓar Kogi ta Tsakiya.

    "Ta saɓa wa haramcin da gwamnatin jihar ta saka kan tarukan siyasa da gangan, wanda aka saka domin kauce wa tashin hankali da kuma samar da zaman lafiya.

    "Maimakon mutunta doka, ta zaɓi janyo ruɗani da nuna halin ko-in-kula kan tsaro da kuma lafiyar jihar," in ji sanarwar.

    Sanata Natasha dai ta samu gagarumin tarba a yau Talata daga ɗimbim magoya bayanta, bayan gangamin sallah da ta kai mazaɓarta, duk da haramta tarukan siyasa da gwamnatin jihar ta yi.

  4. Gungun ƴan daba sun kutsa gidan yari, sun sake fursunoni 500 a Haiti

    Wasu gungun ƴan daba sun kutsa cikin garin Mirebalais da ke tsakiyar Haiti, inda suka saki fursunoni kusan 500 ranar Litinin.

    Wai mai magana da rundunar ƴan sandan Haiti ya ce an aika ƙarin jami'ai zuwa garin, wanda ke nisan kilomita 50 da arewa maso gabashin Port-au-Prince, babban birnin ƙasar.

    Jami'an ƴan sanda sun ce sun sake karɓe iko da garin Mirebalais, sai dai wasu rahotanni sun ce yawancin fursunonin da suka tsere na ci gaba da gararamba a titi.

    Ƙungiyoyin ƴan daba na iko da da yawancin babban birnin ƙasar, amma wannan sabon hari na nuna cewa suna son kama garuruwa a wasu yankunan ƙasar.

    Mirebalais na kan tsakiyar wasu hanyoyi biyu, ɗaya na kai wa arewacin Port-au-Prince zuwa teku, inda ɗayan kuma zai kai mutum Jamhuriyar Dominican.

    Mazauna ƙasar sun ce gungun masu riƙe da makamai sun yi ta harbi kan gine-gine da kuma masu wucewa da kuma cinna wa gine-gine da motoci wuta.

  5. Haaland zai shafe makonni bakwai yana jinya

    Ɗan wasan gaban ƙungiyar Manchester City Erling Haaland zai yi jinyar kusan makonni bakwai bayan raunin da ya ji a agararsa yayin wasan City da Bornemouth a gasar FA ranar Lahadi, in ji koci Pep Guardiola.

    An sauya ɗan wasan a minti na 61 bayan farke wa City kwallon da aka ci ta, inda kuma ta samu nasarar doke Bournemouth da 2-1.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna ɗan wasan ɗan shekara 24 yana barin filin wasa riƙe da karfen da yake taimaka masa wajen takawa.

    Ɗan wasan ba zai buga aƙalla wasanni shida ba, kuma ba lallai ya buga wasan ƙarshe na gasar FA Cup ba idan har Man City ta kai matakin.

    "Likitoci sun faɗa min cewa zai shafe makonni biyar zuwa bakwai yana jinya," in ji Gurdiola. "Muna sa ran dawowarsa karshen kaka - inda zai shirya buga gasar Club World Cup.

    "Wasu lokuta akwai shekarun da irin waɗannan abubuwa za su faru. Suna faruwa a tsawon kakar wasanni," in ji shi.

    Man City ta sanar a ranar Litinin cewa Haaland na buƙatar ganin kwararren likita kan raunin da ya ji.

  6. Ƴansanda sun ceto mutum 21 da aka sace a Taraba

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta ceto mutum 21 da aka yi garkuwa da su a jihar Taraba da kuma ƙwace tarin makamai a wasu jerin samame da ta kai watanni uku na farkon wannan shekara ta 2025.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Olomuyiwa Adejobi ya fitar ranar Litinin, ya ce yawancin waɗannan samame an kai su a jihar Taraba ranar 29 ga watan Maris, kan hanyar Takum zuwa Mararaba.

    Olomuyiwa ya ce an samu nasarar ƙwao mutanen ne bayan kazamin artabu a garin Muji da ke karamar hukumar Takum.

    "Jami'an mu sun ɗauki tsawon lokaci suna artabu da masu garkuwan, kafin su samu nasarar kuɓuto da mutanen 20 tare da ababen hawa da suka tsere suka bari. Biyu daga cikin mutanen da suka raunuka da samun kulawa a asibiti," in ji Olomuyiwa.

    A ɗaya gefen, mai magana da yawun rundunar ta ƴansandan Najeriya ya ce jami'ai na musamman sun kama wani mutum bisa zargin fashi da makami da yin garkuwa da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

    "Mun ƙwato bindigar AK49 da kuma harsasai yayin kamen. Ana ci gaba da bincike domin kama sauran mutanen da yake aikata ta'asar da su," in ji sanarwar.

  7. 'Za mu horas da almajirai domin goga kafaɗa da sauran ƴan Najeriya'

    Shugaban hukumar Kula da Almajirai da Yaran da ba sa zuwa Makaranta ta Najeriya, Dr Idris Idris Muhammad Sani ya ce nan ba da jimawa ba za su yaye almajirai 200 da za su goga da duk wani ɗan Najeriya a fannin Turanci ko Larabci ko kuma neman kowane irin aiki.

    Ya ce tun lokacin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba shi jagorancin hukumar ya nemi da ya ta tabbatar da babu yaron da zai kasa cin abinci har sai ya yi bara.

    "Hakan ne ya sa muka yi tsare-tsare da taruka wajen fito da hanyoyin da za mu cimma hakan.

    Ya ce sun ɗauki almajirai 200 ƴan ƙasa da shekara 16 a matsayin matakin gwaji sannan za su sake ɗaukar wasu 200 na yaran da ba sa zuwa makaranta daga kudancin Najeriya.

  8. Za a kwashe dakarun wanzar da zaman lafiya daga Kongo

    Ƴan tawayen M23 sun amince da kwashe dakarun wanzar da zaman lafiya na kudancin Afirka daga gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

    Ƙungiyar mai ƙasashe goma 16 ta amince ta kwashe dakarunta daga yankin a farkon wannan watan.

    An kashe gomman dakaru tun soma rikicin na Kongo.

  9. Ukraine na nazari kan yarjejeniyar haƙo albarkatun ƙasa da Amurka

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce gwamnatinsa na nazartar kundin yarjejeniyar baya-baya nan ta haƙo albarkatun ƙasar da Amurka ta aika masu.

    Ya ce kundin ya sha bamban da yarjeniyoyin da aka cimma tun da farko domin ci gaba da samun tallafin Amurka.

    Mista Zelensky ya ce akwai wasu batutuwa da ba a tattauna kansu ba da kuma wasu abubuwan da aka cire tun da farko.

    Ya kuma ƙara da cewa ba za su amince da duk wani abu da zai kawo wa haɗin kan Ukraine tangarɗa ba.

  10. Putin ya fara tilasta wa matasa shiga aikin soji

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya nemi matasan ƙasar 160,000 masu shekaru 18 zuwa 30 da su shiga aikin soji, irin shirin na farko na tilasta wa jama'a shiga aikin soji tun shekarar 2011, a daidai lokacin da ƙasar ke shirin faɗaɗayawan sojojinta.

    Kiran shiga aikin sojin na tsawon shekara guda na zuwa ne ƴan watanni bayan da Putin ya ce Rasha ya kamata ta ƙara yawan sojojin nata zuwa miliyan 2.39 sannan kuma yawan sojojin da ke fagen fama zuwa miliyan 1.5,

    Hakan na nufin an samu ƙarin soja 180,000 a cikin shekaru uku masu zuwa.

    Sai dai an ce sabbin sojojin ba za su je Ukraine domin fafatawa ba.

  11. An saka dokar taƙaice zirga-zirga a mazaɓar Sanata Natasha

    Shugaban ƙaramar hukumar Okehi da ke jihar Kogi, Amoka Monday, ya ayyana dokar taƙaita zirga-zirga a yankin ƙaramar hukumar sakamakon fargabar ɓarkewar rikici saboda haramta tarukan siyasa da gwamnan jihar ya yi a ranar Litinin.

    A watan sanarwa da shugaban ƙaramar hukumar ya sanya wa hannu wadda jaridar Punch ta rawaito, Amoka Monday ya ce dokar taƙaita zirga-zirgar dole ce domin samar da zaman lafiya a ƙaramar hukumar.

    Wannan dai ya biyo bayan sanarwar da Sanata Natasha ta fitar tana mai nanata cewa za ta yi gangamin siyasa a ƙaramar hukumar duk da hanin da rundunar ƴansandan jihar ta yi mata.

    A ranar Litinin ne gwamna Ododo ya haramta dukkan wani taron siyasa a jihar.

    Magoya bayan Sanata Natasha dai sun ce za su yi wannan gangami ne domin nuna goyon baya ga wakiliyar tasu.

  12. Al'amura sun tsaya cak a Zimbabwe

    Al'amura a Zimbabwe sun tsaya cak sakamakon ƙaurace wa titunan da al'ummar ƙasar suka yi maimakon fitowa su hau kan tituna domin yin zanga-zangar da aka kira da manufar matsa wa shugaban ƙasar Emmerson Mnangagwa ya sauka daga kan mulki.

    An dai girke jami'an tsaro masu yawa a kan titunan biranen ƙasar wani abun da ya sa jama'a suka tsorata suka kasa amsa kiran masu neman a fita a yi zanga-zangar.

    Sai dai duk da haka an samu tsirarun mutane da suka gudanar zanga-zangar da aka shirya ya yi a watan nan na Maris da wasu tsoffin sojoji ke jagoranta waɗanda suka zargi Mnangagwa da rashawa da cin hanci da son cigaba da mulki. Ƴan sanda sun tarwatsa su.

    Sakamkon rashin amsa kiran masu kiran a yi zanga-zangar, jagoran masu zanga-zangar, Blessed Geza ya gargaɗi al'ummar Zimbabwe a shafinsa na X da ka da su zama matsorata.

    Shugaban Emmerson Mnangagwa ya zamo shugaban Zimbabwe a 2017 bayan juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar mafi daɗewa, Robert Mugabe. Yanzu haka Mnangagwa na cikin wa'adinsa na biyu ne.

  13. Babu gudu babu ja da baya kan gangamina a Kogi - Sanata Natasha

    Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi wadda majalisar dattawan Najeriya ta dakatar na tsawon watanni shida, ta ce "babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah" da ta shirya yi a mazaɓarta.

    Rundunar ƴansanda ta jihar Kogi ce dai ta nemi da Sanata Natasha Akpoti ta soke shirinta na yin gangamin bikin Sallah a mazaɓar tata ta Kogi Central.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata, mai ɗauke da sa-hannun kakakin ƴansandan na jihar, ASP William Aya, kwamishinan ƴansandan jihar, William Ɗantawaye ya ce gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.

    “Kiran a soke gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na yin karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali. Kuma rundunar ƴansandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba." In ji sanarwar.

    To sai dai Sanata Natasha a shafinta na Facebook ta wallafa cewa "babu gudu babu ja da baya dangane da wannan gangamin na Sallah kuma duk abin da ya same mu to za mu ɗora alhakin ne kan gwamnan jihar, Ahmed Usman Ododo."

    A watan da ya gabata ne dai zauren majalisar dattawan Najeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da'a, bayan ta zargi shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.

    A baya-bayan nan ne kuma wasu jama'ar da aka ce daga mazaɓarta ne suka aike da ƙorafi zuwa hukumar zaɓe inda suke son yi mata kiranye.

    To sai dai magoya bayanta sun shirya gangamin nuna goyon baya a jihar ta Kogi,

  14. Alƙaluman mamata sun sake ƙaruwa a Myanmar sakamaon girgizar ƙasa

    Alƙaluman mutanen da girgizar ƙasa ta yi sanadiyyar mutuwarsu a Myanmar yanzu haka sun kai 2,719, kamar yadda shugaban sojoji, Min Aung Hlaing ya shaida a wani jawabi a gidan talbijin na ƙsar a ranar Talata.

    Yawan mutunen kuma da suka samu raunuka sun kai 4,521 inda kuma har yanzu ba a ga mutum 441 ba.

    Min Aung Hlaing ya ƙara da cewa akwai yiwuwar alƙaluman ka iya ƙaruwa zuwa 3,000.

    A can kuma birnin Bangkok na ƙasar Thailand an kuma samun ƙarin gawar mutum guda sakamakon rushewar wani gini mai tsayi inda yanzu haka ake da ƙididdigar mutuwar mutum 14.

  15. Sau nawa ya kamata ka yi bahaya a rana?

    A bisa tsari, bahaya wani abu ne da ake yi sau ɗaya a rana.

    Kai sau uku kake yi a rana ko kuwa? zuwa bayangida wani gagarumin abu ne da ba kasafai yake faruwa ba? Kuma menene iya yawan bahayar da kake yi yake bayyanawa game da lafiyar ka? Zauna ka natsu ka koyi kimiyar bahaya.

    Yawan zuwa bahaya ya bambanta ne daga mutun zuwa mutum. Duk lokacin da muka ci abinci, babban hanjinmu yana matsewa ya tura abincin zuwa wurin da zai narke.

    Hakan na kai wa ga sakin wasu sinadarai da ke sanya buƙatar yin bahaya. Wasu daga cikinmu sun koyi danne wannan buƙatar wanda hakan ke nufin yin bahaya sau ɗaya a rana ko ƙasa da haka ya zame musu jiki.

    ''Dukkaninmu muna nuna kamar abubuwa sunyi mana yawa bamu da lokacin yin bahaya,'' in ji Martin Veysey, wani likitan kayan ciki a asibitin Canberra da ke Australia.

    Bisa al'ada, ana ganin cewa yin bahaya sau ɗaya a rana alama ce ta lafiyar ciki. Sai dai a baya ba a san menene ''daidai'' ba idan aka zo maganar bahaya. Wani bincike ya taɓa bayyana cewa yin bahaya sau ɗaya cikin makonni ko watanni da kuma yin bahaya sau 24 a rana za a iya cewa daidai ne.

    Sai dai saboda binciken masana kimiyya kamar Ken Heaton, wani likita a asibitin Bristol Royal da ke Birtaniya, yanzu mun san gaskiya.

  16. Amurka ta ce tana sa ran kowanne ɓangare ya mutumta dokokin ƙasa da ƙasa a yaƙin Gaza, duk da cewa ba ta fayyace ko za ta gudanar da bincike mai zaman kansa ba a game da kisan ma'aikatan lafiya da na tsaro 15 da dakarun Isra'ila suka yi ba.

    Da take amsa tambaya game da kisan, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Tammy Bruce ta ce: "Duk abinda ya faru, Hamas ce sila, kuma laifinta ne.''

    Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an harba makamai kan motocin ɗaukar marasa lafiya da ke yi mata aiki, a ranar 23 ga watan Maris, inda aka kashe mutane 15 ciki harda ma'aikatan lafiya da ke sanye da kayan aikinsu.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun buɗe wuta kan wani ayarin motoci da ya tunkare su ba tare da bayyana ko su wane ne ba. Ta kuma ce daga cikin waɗanda aka kashe a wajen harda mayaƙan Hamas, amma ba ta ce komai ba game da sauran mutanen da harin ya ritsa da su.

  17. Gwamnan Edo da na Kano sun je Torankawa domin ta'aziyyar mafarauta 16 da aka kashe a Edo

    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Edo Monday Okpebholo,sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa al'ummar garin bisa kisan mafarautan nan guda 16 da aka yi a jihar Edo.

    Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda al'amarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya.

    “Wannan ziyara ba kawai ta jaje da ta'aziyya ba ce, a'a ta nuna tabbacin ƙoƙarin samar da adalci. Iyalan waɗannan mamata na buƙatar abin da ya fi kalaman baka - suna buƙatar aiwatar da duk abin da aka faɗa za a yi musu. Ba za mu zauna ba har sai mun ga an kama waɗanda suka yi wannan aika-aika, sai an yi holinsu a bainar jama'a sannan a hukunta su." In ji gwamna Abba Kabir.

    A nasa ɓangaren gwamnan jihar ta Edo, Monday Okpebholo ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan inda ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi adalci ba daɗewa ba.

  18. Bayani kan girgizar ƙasa a Myanmar

    Idan yanzu kuka shigo shafin, ga ƴar matashiya dangane da girgizar ƙasa a Myanmar da Thailand mai maƙwabtaka.

    • Da misalin ƙarfe 12:51 agogon ƙasar ne dai wannan girgizar ƙasa ta fara a daren Juma'ar da ta gabata .
    • Myanmar ta tabbatar da mutuwar mutum 2,000 inda mutum 20 kuma suka mutu a Thailand.
    • Tawagar BBC ta sauka a garin Mandalay, kusa da wurin da girgizar ƙasar ta fi ƙamari. Al'ummar garin na fama da gawarwakin mamatansu da rashin muhalli da ƙarancin abinci.
    • Myanmar ta ayyana zaman makoki da alhini na mako guda domin tuna wa da waɗanda suka mutu.
  19. Matashiya, Abin da gwamnan Kano ya shaida wa na Edo kan kisan mafaruta 16

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo da ya tabbatar da biyan diyyar mafarauta da aka kashe a jiharsa ta Edo a hanyarsu ta komawa gida domin bukuwan Sallah.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da gwamna Monday Okpebholo ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa Kano domin jajantawa gwamnati da al'ummar jihar bisa abin da ya faru na kisan matafiyan a makon jiya.

    A jawabinsa, gwamna Abba ya yaba da ƙoƙarin gwamnan na jihar Edo bisa matakan da ya ɗauka, inda ya ce a nasu ɓangaren sun ɗauki matakan da suka dace domin hana ramakon gayya, "domin mutanen Kano masu son zaman lafiya ne da maraba da baƙi .

    "Yawancin waɗanda aka kashe ɗin ƴan Kano ne. An tare su ne a jiharka a hanyarsu ta dawowa daga Fatakwal, aka gana musu azaba, sannan aka ƙone wasu daga cikinsu."

  20. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Talata. Da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Yau ma shafin BBC Hausa na labarai da rahotanni kai tsaye ya dawo muku domin samar muku da bayanai sahihai dangane da muhimman al'amuran da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan Afirka da ma duniya baki ɗaya. Ku ci gaba da kasancewa da mu. Mun gode