Ƙarshen rahotonni
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Ku biyo domin samun wasu sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Ibrahim Yusuf Mohammed da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Ku biyo domin samun wasu sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
A yau Lahadi ne ƙungiyar raya tattalin arziki na ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta buɗe taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar a Abuja babban birnin Najeriya yau Lahadi.
Taron karo na 68 na gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, inda za su tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi yankin.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya tarɓi baƙin da suka isa sannan ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wurin buɗe taron.
Hukumomin lafiya a Sudan sun ce wani harin jirgi maras matuƙi ya kashe mutum bakwai ya kuma raunata wasu 12 a wani asibitin sojoji da ke Kordofan.
Wani ma'aikacin lafiya ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da marasa lafiya da ke jinya a asibitin.
Asibitin babbar cibiyar lafiya ce da ake kula da fararen hula da kuma sojojin ƙasar.
Yankin da ke ƙarƙashin ikon sojin Sudan ya daɗe yana fuskantar hare-hare daga mayaƙan RSF.
Rundunar sojin Uganda ta ce tana tsare da wani limamin Katolika da aka kwashe kwanaki ana nema, wanda ta ce tana zargi da laifin cin amanar ƙasa ta hanyar haɗa baki da masu neman hamɓarar da gwamnati.
Sanarwar da rundunar ta fitar a yau Lahadi ba ta bayar da cikakken bayani ba, amma ta sha alwashin gurfanar da malamin addinin a gaban kotu.
Uganda ta daɗe tana fuskantar suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam waɗanda ke zargin ta da tsare mutane ba tare da shari'a ba, da kuma sauran ayyukan keta ƴancin ɗan Adam.
Ƙungiyoyin Musulmi da limamai a Australia sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a bakin ruwa na Bondi da ke ƙasar, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum 11 yayin bikin Yahudawa.
Cikin wata sanarwa a dandalin X, ƙungiyoyin Australian National Imams Council da Council of Imams NSW (New South Wales) sun ce Musulman Australia "na Allah wadai da harbe-harben rashin imanin a Bondi".
"Irin fitinar da tashin hankali ba su da muhalli a al'ummarmu. Dole ne a kama waɗanda suka aikata su domin su fuskanci fushin doka," a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa "muna alhini da addu'a ga mutanen da harin ya ritsa da su, da 'yan'uwansu, da duka waɗanda lamarin ya shafa".
A yau Lahadi ne 'yanbindiga biyu biyu suka buɗe wuta a bakin tekun Bondi da ke birnin Sydney a ranar, inda suka kashe mutum 11 tare da raunata kusan 30 yayin bikin Yahudawa na Hanukkah.
Ƙungiyar raya tattalin arziki na ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta buɗe taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar a Abuja babban birnin Najeriya yau Lahadi.
Taron karo na 68 na gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, inda za su tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi yankin
"Taron zai shirya muhawara kan makomar ƙungiyar, da abubuwan da yankin zai saka a gaba cikinsu har da kwanciyar hankali a harkokin siyasa, da hadin gwiwa kan tsaro, da kuma faɗaɗa harkokin tattalin arziki," kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wurin buɗe taron, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke zafafa hare-hare a ƙasashen Najeriya da Mali da Burkina Faso da Nijar.
Sai dai Nijar da Mali da Burkina Faso sun fita daga ƙungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.
Gwamnan jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya ya fice daga jam'iyyar PDP mai adawa tare da komawa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Gwamna Agbu Kefas ya tabbatar da yankar katin jam'iyyar daga shugaban APC na jihar tasa a yau Lahadi a mazaɓarsa ta Hospital da ke ƙaramar hukumar Wukari.
"Ba da daɗewa ba, na karɓi katina na jam'iyyar APC daga shugaban jam'iiyya na Mazaɓar Hospital Umaru Tanko," in ji shi. "Na yi farin ciki da kykkyawar tarɓar da shugabanni da 'ya'yan jam'iyyar APC suka yi mani."
Tun a ranar 19 ga watan Nuwamba gwamnan ya yi niyyar komawa APC a hukumance amma ya ce ya ɗaga yin hakan saboda yin garkuwa da ɗalibai mata a jihar Kebbi.
Da wannan mataki nasa, gwamnoni biyar ne suka rage wa PDP mai adawa yayin da take shirin ƙalubalantar APC a babban zaɓe na 2027.
An kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na Banagladesh guda shida, a wani hari da aka kai da jirgin sama maras matuki kan wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da ke kudancin Sudan.
Wakilin BBC ya ce Bangladesh na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi bayar da gudummawa a shirin samar da zaman lafiya na MDD.
Gwamnatin sojin ƙasar ta ɗora alhakin harin kan mayaƙan RSF, kuma ta ce hakan takala ce mai haɗari da za ta iya rura wutar rikicin ƙasar, zargin da RSF ta musanta.
An kai harin ne kan wani ginin ajiyar kaya da kuma gidan mai da ke sansanin a birnin Kaguli da ke kusa da iyaka da Sudan ta Kudu.
Babban Sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa zai iya zama laifin yaƙi.
Fitacciyar jagorar ƴan hamayyar nan ta Belarus Sviatlana Tsikhanouskaya ta gode wa Amurka a kan kokarinta na diflomasiyya da ya kai ga sakin fursunoni sama da 120 a Belarus.
Amurka ta shiga tsakani domin sakin fursunonin, inda ta yi alƙawarin ɗage wasu takunkumai a kan Belarus din.
Daga cikin waɗanda aka saki har da mai fafutuka ta ƴan hamayya, Maria Kolesnikova, da kuma mutumin da ya ci kyautar zaman lafiya ta Nobel, Ales Biyalitski.
Akwai kuma wata ƴar siyasa daga ɓangaren adawa da aka saki, Maria Kalesnikova.
Da farko dai an tsara za a tura fursunonin ne zuwa Lithuania, amma yanzu ana hasashen tura su Ukraine.
Hukumar tsaro ta intanet ta ƙasar Ghana ta kama wasu ƴan Najeriya 32 da ake zargi da aikata laifukan zamba a wani samame da ta kai a garin Kasoa-Tuba da ke yankin tsakiyar ƙasar.
Hukumar ta ce an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron ƙasar.
Jami’an sun kama kwamfutoci 31 da wayoyin hannu 15, waɗanda ake zargin ana amfani da su ne domin aikata zambar intanet.
A halin yanzu dai waɗanda ake zargin suna tsare ne don taimakawa wajen gudanar da bincike.
Hukumar tsaron Intanet ta ce kamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na magance ayyukan da ke da nasaba da zambar intanet a fain ƙasar.
A duk faɗin Afirka, ana samun ƙaruwar aikata laifuka masu nasaba da damfarar intanet.
Rahoton Interpol na shekarar 2025 ya nuna cewa akasarin laifukan da aka ruwaito an aikata a sassan nahiyar na da alaƙa da harkokin da ke gudanarwa a Intanet.
Wasu ƴan bindiga biyu sun buɗe wuta a bakin tekun Bondi na Sydney a ranar Lahadi, inda suka kashe mutane 11 tare da raunata wasu da dama.
Hari dai ya auku ne a yayin wani taron bikin Yahudawa na Hanukkah.
'Ƴan sandan yankin New South Wales sun ce masu ba da agajin gaggawa sun garzaya da wasu mutane 29 zuwa asibitoci daban-daban daga bakin tekun.
An kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da harbin, kuma na biyun yana cikin mawuyacin hali.
Ƴan sanda sun ayyana harin a matsayin sayin "harin ta'addanci" kuma sun bayyana cewa sun gano wasu "na'urori masu fashewa" a cikin wata mota kusa da bakin tekun da ke da alaka da ɗaya daga cikin maharban da aka kashe.
Shugabannin ƙasashen duniya na mayar da martani kan harbin, inda firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce Birtaniya "za ta ci gaba da kasancewa tare da Australia da kuma al'ummar Yahudawa".
Shugaban ƙasar Isra'ila Isaac Herzog ya yi alla-wadai da harin, yana mai bayyana lamarin a matsayin wani mummunan hari da aka kai wa Yahudawa.
Ƴansanda a Jamus sun kama mutane biyar kan zargin shirya kai hari wata kasuwa da ake hada-hadar saye da sayar da kayan bikin Kirsimeti, a jihar Bavaria.
Masu gabatar da ƙara na jihar da ke kudancin Jamus, sun ce tun shekaran jiya Juma'a ana tsare da mutanen - ƴan Maroko uku da ɗan Masar da kuma ɗan Syria.
Masu bincike sun ce ɗan Masar ɗin ne mai shekara 56 ya nemi ya a kai hari da mota kan kasuwar da nufin kashe ko jikkata mutane da dama.
Kasar Cambodia ta rufe kan iyakokinta da Thailand, yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa tsakanin dakarun ƙasashen biyu, duk da cewa shugaban Amurka Donald Trump a baya ya ce sun amince su tsagaita wuta.
Za a rufe iyakokin ta har sai an samu sanarwa, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Cambodia.
Tun da farko Firaministan Thailand Anutin Charnvirakul ya ce ya shaida wa Trump cewa tsagaita wuta za ta yiwu ne kawai bayan Cambodia ta janye dukkan dakarunta tare da kawar da nakiyoyin da aka binne.
Jami'an ƙasar Thailand sun ce an kashe sojoji huɗu a ranar Asabar, yayin da ɓangarorin biyu suka bayar da rahoton ci gaba da tashin bama-bamai da kuma musayar wuta.
Cambodia ba ta sabunta adadin sojojinta da suka jikkata ba.
Ma'aikatar tsaron Cambodia ta ce jiragen yaƙin Thailand sun yi ruwan bama-bamai a gine-ginen otal da wata gada, yayin da Thailand ta ba da rahoton jikkatar fararen hula da dama a wani harin roka da Cambodia ta kai.
Mutuwar da aka yi a ranar Asabar ta kawo adadin sojojin Thailand da suka mutu tun ranar Litinin zuwa 15, yayin da wasu 270 suka jikkata.
Hukumomin sun ƙara da cewa wasu fararen hula shida kuma sun jikkata.
A ranar Juma'a, Cambodia ta ce an kashe fararen hula aƙalla 11 tare da jikkata wasu 59.
Aƙalla mutane 700,000 ne aka kwashe daga kan iyakar kasashen biyu.
Gwamnan jihar Bayelsa da ke yankin kudu maso kudancin Najeriya, Douye Diri, ya bayar da umarnin a yi gwaji kan gawar mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo domin tabbatar da dalilin mutuwarsa, bayan rasuwarsa ranar Alhamis yana da shekaru 60 a duniya.
Gwamna Diri ya ba da umarnin ne a lokacin da yake karɓar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnati da iyalan marigayi mataimakin gwamnan a gidan gwamnati da ke Yenagoa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗi kan yadda ake siyasantar mutuwar Ewhrudjakpo, musamman a shafukan sada zumunta, inda ya buƙaci jama’a da su mutunta yanayin zaman makoki a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mista Daniel Alabrah ya fitar a ranar Lahadi, gwamna Diri ya roƙi jama’a da su guji yaɗa jita-jita, maimakon haka su jinjinawa hidimar da marigayi mataimakin gwamnan ya yi wa jihar bayelsa da kuma ƙasa baki ɗaya.
Da yake magana tun farko, tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya bayyana rasuwar Sanata Ewhrudjakpo a matsayin wani abin baƙin ciki ga ɗaukacin al’ummar Bayelsa.
Jonathan ya tuno da irin goyon bayan da marigayi mataimakin gwamnan ya bayar kan shirye-shiryen da gidauniyar Goodluck Ebele Jonathan ta tsara.
Daga baya Gwamna Diri da tsohon shugaban ƙasa Jonathan sun ziyarci uwargidan marigayi mataimakin gwamnan Barista Beatrice Ewhrudjakpo a gidansu dake cikin gidan gwamnati.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, za a mayar wa ƙungiyar IS mummunan martani, bayan da wani harin kwanton-ɓauna da aka kai a tsakiyar Syria, ya hallaka sojojin Amurka biyu da wani tafinta.
Wakilin BBC ya ce lamarin ya faru ne a yankin Palmyra inda ake sintri na hadin gwiwa tsakanin sojin Syria da na Amurka
Sojojin na cikin tawagar hadin gwiwa ta tsakanin Syria da Amurka da ke yaki da ta'addanci - lokacin da suke sintiri a kusa da birnin Palmyra.
Ita ma gwamnatin Syria ta fitar da sanarwa inda ta yi alla-wadai da harin.
Jami'ai sun ce an jikkata wasu jami'an tsaro uku a harin, inda aka kashe ɗan bindigar.
Ana ci gaba da ɓoye sunayen waɗanda aka kashe na tsawon sa’o’i 24 har sai an sanar da ƴan uwansu.
A baya-bayan nan Syria ta shiga cikin ƙawancen ƙasa da ƙasa don yaƙar ƙungiyar IS kuma ta yi alƙawarin haɗa kai da Amurka.
Jamaa na shirin kada kuria a zaben shugaban ƙasa na ƙasar Chile da za a yi a yau Lahadi, inda masu kaɗa ƙuri'a zasu zaɓi tsakanin ƴar takarar jam'iyyar kwaminis Jeannete Jara da kuma ɗan takarar jamiyyar masu ra'ayin rikau José Antonio Kast.
Yayinda da kyar Madam Hara ta lashe zaɓen zagayen farkon Mista Kast ya kasance ɗan takarar da ke kan gaba bayan da wasu ƴan takara masu ra'ayin riƙau suka sha kaye a zagayen farko na zaɓen.
Miyagun laifuka da batun kwararowar baƙin haure na cikin abubuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓen.
Ana sa ran Kast zai samu ƙarin ƙuri'u daga wasu ƴan takarar da ba su kai labari ba a zagaye na farko, ciki har da Sanata mai ra'ayin riƙau Evelyn Matthei da kuma ɗan majalisa mai sassaucin ra'ayi Johannes Kaiser.
Idan ya yi nasara, zai sa Chile ta zama ƙasa ta baya-bayan nan a Latin Amurka da ta koma ƙarƙashin shugaba mai ra'ayin riƙau.
Ɗaruruwan jami'an ƴan sandana na ci gaba da farautar ɗan bindigan da ya kai hari kan jama'a a harabar wata jami'a da ke jihar Rhode ta Amurka Amurka.
Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ɗalibai biyu yayin da wasu mutum tara da suka ji rauni, wasu na cikin mawuyacin hali.
Yawancin waɗanda harin ya rutsa da su dalibai ne na fitacciyar jami'ar nan ta Brown University da ke birnin Providence.
Har yanzu ana can ana farautar ɗan bindigan - wanda ƴansanda suka fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna shi sanye da kaya masu duhu, yana barin wajen bayan ya yi harbin a cikin aji.
An baza ƴansanda 400 domin farautar maharbin.
Jama'a barkamu da wannan safiya ta ranar Lahadi, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.
A yau ma za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya Asabar wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na Whattsapp da Facebook da X da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da ma tafka muhawara.
Ku kasance tare a mu.