Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/08/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/08/2024

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muke sallama da ku a wnnn rana ta Asabar, sai kuma gobe Lahadi idan Allah Ya kai mu.

    Da fatan za ku tara, a madadin kowa da kowa ni MUhammad Annur Muhammad nake mana fatan alheri

  2. Uwa da 'ya'yanta biyar sun rasu bayan cin ɗanwake a karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano

    Wata mata da 'ya'yanta biyar sun rasu gaba daya bayan da suka ci dan'wake, a kauyen Karkari da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano.

    Wani makwabcin iyalan, Garba Muhammad ya sheda wa jaridar Daily Trust wadda ta ruwaito labarin, cewa, saboda fatar da talauci da kuma yunwa da iyalan gidan suke fama da su, matar wadda daman mijinta ya rasu, wadda kuma daman ita ke kula da 'ya'yan nata biyar ta yi amfani da garin da ya lalace domin dafa musu dan'wake.

    Jaridar Daily Trust ta riuwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, a gidan mijin matar, marigayi Malam Abdulkarin.

    Mutumin ya ce, ''Cin wannan abinci ne ya yi sanadin mutuwar iyalan gidan su shida hadi da mahaifiyar.''

    Wadanda suka rasun sun hada da, mahaifiyar mai suna Alhakatu Abdulkarim da 'ya'yan nata biyar -; Bashir, da Firdausi, da Hafsat, da Usman da kuma Jamilu.

    Kakakin rundunar 'yansanda a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce iyalan su shida da suka ci abincin aka garzaya da su babban asibitin Gwarzo, kuma a can likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

    Sai dai ya ce, an fara gudanar da bincike domin tabbatr da ainahin abin da ya yi sanadin rasuwar tasu.

  3. Shafin X ya dakatar da aikinsa a Brazil

    Shafin sada zumunta da muhawara na X, ya ce ya dakatar da aikinsa a Brazil saboda wata takaddama da ke tsakaninsa da Kotun Kolin kasar a kan wasu shafuka da ya toshe.

    Babban alkalin kotun, Alexandre de Moraes, ya bayar da umarnin cewa dole ne a ci gaba da dakatar da shafukan wadanda ake zargi da yada labaran karya, yayin da ake gudanar da bincike a kansu.

    Yawancin shafukan suna da alaka ne da tsohon shugaban kasar mai ra'yin rikau, Jair Bolsonaro.

    Shafin na X, ya zargi alkalin da hana gudanarwa, sannan kuma ya ce mai shari'ar ya yi barazanar kama lauyan shafin da ke kasar ta Brazil, muddin kamfanin bai bi umarnin ba.

    Kamfanin ya ce zai dakatar da gudanar da aikinsa, amma kuma ya ce duk da haka al'ummar Brazil za su iya ci gaba da shiga shafin.

  4. Masu kashe gobara na ƙoƙarin shawo kan wutar daji da ta addabi Turkiyya

    Ƴan kwana-kwana na can suna ta kokarin kashe wata gobarar daji da ta tashi a larduna biyar a Turkiyya.

    Tun a jiya Juma'a wutar ta watsu har kusa da gidaje inda ta kone gine-gine tare da tilasta kwashe mutane. Jami'an gandun daji sun yi gargadi cewa wutar za ta iya ci gaba da ci a lardunan Arewaci da Yammacin Turkiyya har tsawon kwana 10 saboda tsananin zafi da iska mai karfi.

    Turkiyya kamar sauran kasashen duniya na fuskantar wutar daji a lokutan bazara saboda sauyin yanayi.

  5. Majalisar Wakilai ta yi kira ga jami'an tsaron Najeriya su gaggauta ceto ɗaliban likitanci 20 da aka sace

    Majalisar Wakilai ta Najeriya ta bukaci Babban Sufeton 'yansanda da sauran hukumomin tsaro na kasar da su gaggauta daukar matakin ceto dalibai 20 masu karatun aikin likita da aka sace a jihar Benue.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi, Jr. ya fitar a yau Asabar, ya ce Majalisar tana tare da kungiyar likitoci ta Najeriya da kungiyar dalibai ta kasar, wajen neman jami'an tsaron sun yi duk abin da ya wajaba wajen ceto daliban lami lafiya.

    Sanarwar ta ce, shugaban kwamitin kula da harkokin lafiya na Majalisar Dennis Idahosa, ya jaddada cewa, “Lafiyar dalibanmu na likitanci na da muhimmanci sosai, kuma wannan lamari ba hari ba ne a kan wadannan matasan kwararru ba ne kawai, hari ne a kan makomar tsarinmu na kula da lafiya.''

    Ya kara da cewa, ''ba za mu sake mu kara rasa karin wasu rayuka ba saboda matsalar tsaro da take addabar kasarmu ba. Ba wani dalibi da zai kasance yana jin tsoron gudanar da harkokinsa da doka ta yarda da su ba a kasar.''

    ''A don haka muke bukatar matakan gaggawa na ba-sani-ba-sabo daga hukumomin tsaronmu wajen dawo da wadannan dalibai gida lafiya,'' in ji Idahosa.

    Majalisar ta ce tana cigaba da goyon bayan duk wani mataki da za a dauka da zai inganta tsaro da lafiyar duk 'yan Najeriya, kuma za ta ci gaba da sa ido kan lamarin sosai.

    Rahotanni dai sun ce, an sace daliban ne 12 daga Jami'ar Jos da 8 daga Jami'ar Maiduguri, a ranar Alhamis, 15 ga watan Agustan nan, a kan hanyarsu ta zuwa wani taro da kungiyar daliban likitanci ta Katolika ta shirya a Enugu.

  6. Ƴan hamayya na gangamin ƙin yarda da sakamakon zaɓen Venezuela

    Magoya bayan ƴan hamayya a Venezuela sun fara gangami a babban birnin ƙasar, Caracas da sauran birane domin fara zanga-zangar ƙin amincewa da nasarar Shugaba Nicolas Maduro ta zaɓen da aka yi a watan da y gabata.

    Shugabar ƴan hamayya Maria Corina Machado, wadda ake sa ran za ta shiga gangamin, ta buƙaci jama'a da kada su ji tsoro.

    An sanya ƴansanda da sojoji cikin shirin kar-ta-kwana, sannan kuma su ma magoya bayan Mista Maduro na shirin gudanar da na su gangamin.

    Maduro ya kafe cewa ya yi nasara a zaɓen inda zai yi karo na uku na wani wa'adin shekara shida a kan mulki, amma kuma ;yan hamayya na ganin su suka yi nasara.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta Venezuela ta ƙi fitar da cikakken sakamakon zaɓen, duk da matsin lamba daga wasu ƙasashen yankin.

  7. 'Yankin kudancin Afirka na buƙatar dala biliyan biyar don yaƙi da fari'

    Shugabannin Ƙungiyar Ƙasashen yankin kudancin Afirka sun buƙaci tallafin dala biliyan biyar don magance illolin mummunan fari da yankin ke ciki.

    Shugaban ƙungiyar mai barin gado, wanda kuma shi ne shugaban ƙasar Angola, Joao Laurenco, ya ce fiye da mutum miliyan 68 ne mummunan farin ya shafa a yankin a tsawon gomman shekaru.

    Mista Laurenco ya kuma yaba da zaman lafiyar da aka cimma tsakanin ƙasashen Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo da Rwanda, da shirin wanzar da zaman lafiya da ya yi nasara a arewacin Mozambique.

    Shirin da Shugaban ya ce ya samar da kwanciyar hankali a yankin Cabo Delgado, inda fiye da mutum miliyan ɗaya suka rasa muhallansu a lokacin rikicin.

  8. Harin Isra'ila ya kashe aƙalla mutum 15 a Gaza

    Rahotonni daga Gaza na cewa aƙalla mutum 15 ne suka mutu sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai tsakiyar birnin.

    Mai magana da yawun rundunar tsaro da bayar da agaji ta Hamas, ya ce cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da ƙananan yara tara da mata uku 'yan gida guda.

    Sojojin Isra'ila sun ce suna sane da rahoton kuma suna bincike a kan harin.

    Ana dai ci gaba da matsa ƙaimi don tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yayin da sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ke kan hanyarsa ta zuwa yankin.

    Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce ana dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar bayan shafe kwana biyu ana tattaunawa a birnin Doha.

  9. Ma'aikatar lafiyar Indiya ta buƙaci likitocin ƙasar su janye yajin aiki

    Ma'aikatar lafiyar Indiya ta buƙaci likitocin ƙasar da ke yaƙin aiki, su koma bakin aikinsu, inda ta alƙawarta kafa kwamitin da zai riƙa ba su kariya a aikinsu.

    A ranar Asabar ne likitoci a faɗin ƙasar suka soma yajin aikin gama-gari don nuna damuwarsu da kisan da aka yi wa wata matashiyar likita a asibitin Kolkata, bayan yi mata fyaɗe a makon da ya gabata.

    To sai dai yajin aikin, likitocin bai shafi ayyukan gaggawa a faɗin asibitocin ƙasar ba.

    Shugaban ƙungiyar likitocin ƙasar ya shaida wa BBC cewa kashi 60 cikin 100, na likitocin ƙasar - miliyan guda - mata ne, don haka dole ne hukumomi su yi abin da ya dace domin kare su.

    A yau ne ake cika kwana bakwai da ake gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar kan batun.

    Tuni aka kama wanda ake zargi da laifin aka kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

  10. 'Fiye da gidaje 2,000 ne suka rushe sakamakon ambaliya a Gummi'

    Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce ambaliya ruwa ta haddasa asarar rayukan aalla mutum takwas da rushewar gideje a yankin ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar.

    Daraktan hukumar kiyaye aukuwar bala'o'i ta jihar, Hassan Usman Dauran ya shaida wa BBC cewa ambaliyar ta shafi kusan rabin gidajen garin Gummi.

    ''Gidajen da suka rushe sakamakon ambaliyar sun haura gida 2,000'', in ji daraktan hukumar.

    Ya ƙara da cewa lamarin ya shafi gonaki fiye da 3,000, da amfanin gona mai tarin yawa.

    Mazauna yankin sun ce ruwan saman da aka shafe tsawon ranar Juma'a ana tafkawa a yankin ne tare da fashewar wani gulbi a garin ne suka haddasa bala'in.

  11. Hezbollah ta harba rokoki zuwa arewacin Isra'ila

    Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta harba makaman roka zuwa arewacin Isra'ila, bayan wani hari da Isra'ila ta kai birnin Nabatieh da ke kudancin ƙasar ya kashe a ƙalla mutum 10.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce aƙalla makaman roka 50 aka harba cikin garin Ayelet HaShahar da ke arewacin ƙasar. Kuma babu rahoton rasa rai.

    Ministan lafiyar Lebanon, Firass Abiad ya shaida wa BBC cewa ginin da aka kai wa hari a ƙasar, sansanin 'yan gudun hijirar Siriya ne.

    Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da harin ne kan cibiyar makaman ƙungiyar Hezbollah.

    Zaman tankiya da nuna wa juna yatsa tsakanin Isra'ila daLebanon ya ƙara a makonnin baya-bayan nan, bayan da Isra'ila ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar a birnin Beirut, wani abu da Hezbollah ta sha alwashin mayar da martani.

  12. Ra'ayi Riga: Kan albashin 'yan majalisar dokokin Najeriya

  13. Ambaliya a Jigawa: Gwamna Namadi ya jajanta wa 'yan jihar

    Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi ya jajanta wa al'ummar jihar, waɗanda iftila'in ambaliyar ruwa ta shafa.

    Aƙalla ƙananan hukumomin jihar 13 ne suka fuskanci ambaliyar, wadda ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

    Yayin da yake jawabi a wajen rabon tallafin abinci ga mabuƙata, da gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar gwmanatin jihar suka samar, Gwamna Namdi ya ce gwamnatin jihar da ta tarayya na ƙoƙari don tallafa wa mutanen da ambaliyar ta shafa.

    Mutum 25 ne dai suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a faɗin jihar, kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, SEMA, Dakta Kabiru Mairiga, ya shaida wa BBC.

    Gwamna Namadi ya kuma aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu sakamakon iftila'in, tare da jajanta wa mutanen da suka rasa dukiyoyi da gidajensu, da kuma Allah ya mayar da alkairi.

  14. Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar ƙwace lasisin gidajen man da ke ɓoye mai

    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA) ta yi barazanar ƙwace lasisin gidajen mai da 'yan kasuwar da aka samu da laifin ɓoye man fetur don sayar wa 'yan bumburutu.

    Babban daraktan hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana haka cikin wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, lokacin wata ziyarar bazata da wata tawagar hukumar ta kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.

    A 'yan kwanakin baya-bayan nan ana fuskantar ƙarancin man fetur ɗin a wasu manyan birane da jihohin ƙasar.

    A wasu jihohi, musamman da ke yankin arewacin ƙasar, ana fuskantar ƙarancin man, lamarin da ya tilasta wa wasu gidajen mai da dama rufewa, abinda kuma ya haifar da dogayen layuka a gidajen man da ke bayar da man.

    Hukumar ta kuma ce sayar wa 'yan bumburutun man a jarakuna saɓa doka ne tare, sannan kuma hakan na haifar da barazana ga kariyar muhalli.

  15. 'Babu maganar fifita Lagos a gidajen da muke ginawa'

    Ministan gidaje da raya birane, Arch Ahmed Musa Ɗangiwa ya ce gwamnatinsu na gina rukunin gidaje da birane a jihohin ƙasar, ba tare da fifita wani ɓangare ba.

    Ya ce saɓanin raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa, gwamnatin Bola Tinubu na samar da gidajen 'Renewed Hope Housing' a birane irinsu Lagos da Kano da Abuja da Enugu da Maiduguri da Lafiya da kuma Fatakwal .

    Ya ce gidajen da za su gina a ƙarƙashin shirin ƙawancen gwamnati da 'yan kasuwa sun zarce 2,000 a biranen.

    A cewarsa, gwamnatin kuma na gina rukunin gidaje a wasu jihohi guda 12 da suka zaɓa a matakin farko, da karaɗe sauran jihohin ƙasar a cikin shekaru.

    Akwai tsarin ginna gidajen iri biyu ne, akwai 'Renewed Hope Cities' da za a gina manyan gidaje wasu manyan biranen ƙasar ciki har da Abuja da ɗaya a sauran ɓangarorin ƙasar shida. Sannan akwai 'Renewed Hope Estate' da za a gina ƙanan gidaje masu rangwame a duka jihohin ƙasar 36.

  16. Lebanon ta ce harin Isra'ila ya kashe mutum tara a ƙasar

    Hukumomin lafiya a Lebanon sun ce aƙalla mutum tara ne suka mutu a wani harin da Isra'ila ta kai kudancin ƙasar.

    Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar adana makaman ƙungiyar Hezbollah.

    Tun da farko, shugaba Biden n Amurka ya yi kira ga ɓangarorin da ke rikici a yankin su guji aikata abin da zai dagula ƙoƙarin tattabatar da zaman lafiya a Gaza .

    Ya bayyana kyakkyawan fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan tattaunawar kwanaki biyu tsakanin Isra'ila da masu shiga tsakani a Qatar.

    Hamas dai ba ta shiga tattaunawar ba, saboda zargin Isra'ila da sauya buƙatunta.

  17. Amurka ta ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Shugaba Biden ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su.

    Mista Bide ya ce zai tura sakataren harkokin wajensa Antony Blinken zuwa Gabas ta Tsakiya bayan tattaunawar kwana biyu tsakanin jami'an Isra'ila da masu shiga tsakani na Amurka, Masar da Qatar.

    Hamas ba ta shiga tattaunawar ba, yayin da take zargin Isra'ila da sauya buƙatunta.

    A baya an ɗage tafiyar Anthony Blinken yayin da Amurka ke sa ido kan ko Iran za ta kai wa Isra'ila hari.

    Shugaba Biden ya yi gargaɗi ga ɓangarorin biyu na kauce wa yin wani abin da zai kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya.

  18. Likitocin Indiya sun fara yajin aiki kan fyaɗe da kisan da aka yi wa wata likita

    Likitoci a Indiya sun fara yajin aikin gama gari a ci gaba da nuna fushin da ake yi kan fyade da kisan da aka yi wa ɗaya daga cikin abokiyar aikinsu a wani asibitin Kolkata a makon jiya.

    Kungiyar likitocin ƙasar ta ce - lokaci ne da ya kamata hukumomi su ɗauki matakai na tabbatar da tsaron lafiyarsu a asibitoci.

    Ayyukan asibitoci da ba na gaggawa ba, za su kasance a rufe a faɗin ƙasar a ranar Asabar.

    An shafe kwanaki mata na zanga-zanga tun bayan da aka tsinci gawar wata matashiyar likita a makon da ya gabata.

    An kama mutum guda tare da tuhumarsa da aikata laifin, amma masu zanga-zangar sun ce matakin bai isa ba.

  19. Assalamu alaikum

    Masu wannan shafi na BBc Hausa kai-tsaye barkanmu da da wannan lokaci.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kada ku manta da leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa