Babban hafsan dakarun Najeriya, Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa Hedikwatar Tsaro za ta tura wani Rukunin Dakaru na Musamman, mai suna ‘Savanah Shield’, domin yaƙar masu iƙirarin jihadi a tsakiyar jihohin Kwara da Neja.
A wani jawabi ga ‘yan majalisa a Abuja ranar Talata, Janar Oluyede ya ce rundunar tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa Najeriya ta kasance ƙasa mai zaman lafiya ga ‘yan kasa da masu zuba jari.
“Muna kokarin samar da hanyoyi daban-daban domin shawo kan waɗannan ƙalubale na tsaro da ke addabar ƙasar. An naɗa kwamandan dakarun na musamman kuma muna kokarin samun kayayyakin domin mamaye wannan yanki,” in ji shi.
Sai dai babban hafsan sojin ya bayyana cewa ba zai yi wu rundunar ta iya mamaye duk faɗin Najeriya ba.
Don haka, ya buƙaci a ƙarfafa ayyukan hukumomi kamar ’Yan sanda da Hukumar Tsaro da Kula da Fararen Hula (NSCDC) domin aikin hadin gwiwa da sojoji.
Ba a dai yi wani ƙarin bayani ba kan wannan aikin sojin, amma alamu na nuna cewa sojojin za su gudanar da ayyukansu domin daƙile yiwuwar hare-hare, bayan sake bazuwar ayyukan ‘yanbindiga zuwa kudancin Najeriya, bayan aikata ɓarna da sace mutane a Arewa maso Gabas na tsawon lokaci.
Hare-haren da aka kai kan al’ummomi a Kwara sun nuna taɓarɓarewar matsalar tsaro a Najeriya da yaƙin da sojoji ke yi tun tsawon lokaci kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ‘yan ta’adda da masu iƙirarin jihadi.
A makon da ya gabata, gwamnatin Kogi ta sanar da rufe wasu kasuwanni da tashoshin mota a sassan jihar a matsayin matakin tsaro don dakile ayyukan ƴanbindiga.
Gwamnatin jihar ta kuma rufe makarantu a wasu wurare domin hana yiwuwar hare-hare.
Kogi na makwabtaka da jihar Kwara, inda sama da mutum 100 suka rasa rayukansu a Woro da wasu al’ummomi sakamakon farmakin masu iƙirarin jihadi.
Najeriya na ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da dama, yayin da Amurka ta kai hare-haren kan ‘yanbindiga a ƙasar.