Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/05/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage

  1. Sai an jima!

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.

  2. NDLEA ta kama abubuwan fashewa da aka yi niyyar safarar su zuwa Zamfara

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama wasu abubuwan fashewa a kan hanyar kai su jihar Zamfara.

    NDLEA ɗin ta ce jami’anta sun kama nakiyoyin ne a wata motar haya a ranar Asabar.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami'anta da ke aikin sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria ne suka kama motar da ke ɗauke abubuwan fashewar, wadda ta tashi daga jihar Nasarawa zuwa Zamfara.

    Hukumar ta ce binciken da suka yi wa motar ne ta kai suka gano abubuwan fashewa da suka kai 942 ɗaure a clkin buhu - inda suka kama wani da ake zargi Nura Sani mai shekara 30.

    Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayar da umarnin tsare mutumin da ake zargi da kuma abubuwan da aka gano a wurinsa, don ci gaba da bincike.

  3. Ƴansandan Brazil sun ɗakile yunkurin kai harin bam a bikin mawakiya Lady Gaga

    Ƴansanda a Brazil sun ce sun daƙile yunkurin kai harin bam a wani biki da mawakiyar Amurka Lady Gaga ke gudanarwa a Copacabana da ke birnin Rio de Janeiro ranar Asabar.

    Ƴansandan birnin tare da haɗin gwiwar ma'aikatar shari'a, sun ce ana zargin wasu sun ɗauki hayar mutane domin kai harin ta hanyar amfani da abubuwan fashewa - kuma suna son yin haka ne domin samun suna a kafofin sada zumunta.

    An kama mutumin da ke da alhakin yunkurin kai harin da kuma wani matashi, kamar yadda sanarwar ƴansanda ta bayyana.

    Mutane sama da miliyan biyu ne suka taru don halartar bikin rawar, wanda kowa ke da damar halarta ba sai an biya kuɗi ba.

    Har ila yau, ƴansanda sun ce ƙungiyar da ta shirya kai harin na ta yaɗa kalaman kiyayya, musamman kan yara da manya da kuma masu neman jinsi.

  4. Real ta doke Celta Vigo, ta ƙara matsa wa Barca lamba

    Kyilan Mbappe ya ci kwallaye biyu a wasan da Real Madrid ta doke Celta Vigo da ci 3-2 a filin wasa na Santiago Bernabeu.

    Real ta fara cin kwallo a minti na 33 ta hannun Arda Guler - sannan bayan minti shida Mbappe ya zura ta biyu, inda ya ɗaɗa kwallon daga wajen yadi na 18 har cikin raga.

    Ɗan wasan ɗan asalin Faransa ya ci ta biyu minti uku bayan komawa daga hutun rabin lokaci, inda ya karɓi kwallo daga hannun Guler - inda ya yi amfani da kafarsa ta hagu wajen zura ta a raga.

    Sai dai Celta ta farke ta hannun Javi Rodriguez a minti na 69, bayan bugun kusurwa.

    Ba a jima ba Williot Swedberg ya ci ta biyu inda wasa ya koma 3-2 a minti na 76.

    Haka kuma Celta ta yi ta kai kora har alkalin wasa ya busa tashi.

    Yanzu dai Barca ta bai wa Madrid tazarar maki huɗu - inda za su fafata a wasan El-clasico a mako mai zuwa.

    Wasa ne kuma mai muhimmanci ga duka ƙungiyoyin da ke ƙoƙarin lashe gasar Laliga.

  5. Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani kan harin da ƴan Houthi suka kai

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin mayar da mummunan martani kan harin makami mai linzami da ƴan tawayen Houthi suka kai kusa da wani filin jirgin sama a Isra'ila.

    A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, Netanyahu ya yi barazanar far wa ƙungiyar, inda ya ce: "Mun kai hari a baya, za mu kuma sake kai hari a gaba".

    Makamin mai linzami da ƴan Houthi waɗanda ke samun goyon bayan Iran suka harba daga Yemen, ya faɗa kusa da filin jirgin sama a Ben Gurion ranar Lahadi da safe, a cewar hukumomi.

    Lamarin ya jikkata mutum huɗu, yayin da wasu biyu suka jikkata a kan hanyar su ta zuwa wani matsuguni, a cewar kafofin yaɗa labaran Isra'ila.

    Mai magana da yawun sojojin Houthi, Yahya Saree ya bayyana a wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin cewa "yanzu filin jirgin saman Isra'ila ba shi da tsaron da za a iya yin tafiye-tafiye".

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya faɗa a wata sanarwa cewa: "Duk wanda ya kawo mana hari, za mu mayar da martani har sau bakwai".

  6. Yadda cutar murar jarirai ta 'Jaundice' ke illata rayuwa har mutuwa

    Duk da cewa Babatunde Fashola, wanda aka fi sani da Baba, ya kai shekara 22 har yanzu tsayinsa bai kai sentimita 70 ba, wato ƙata biyu da inchi 4.

    Yana fama da cutar murar jarirai ne, wadda ta sa yake buƙatar kula ta musamman. Ba ya iya tafiya ko magana, kuma da bututu yake cin abinci.

    Tun yana jariri iyayensa suka yi watsi da shi, amma shekara 10 da suka gabata, sai ya tsinci kansa a gidan lura da masu cutar murar jarirai da ke jihar Legas.

    "Baba na da nauyin kilogiram 12, kuma yana cikin ƙoshin lafiya," in ji mai gidan, Nonye Nweke a zantawarta da BBC.

  7. Za mu huce fushin mu a kan PSG - Arteta

    Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce za su soke fushin rashin nasarar da suka yi a hannun Borunemouth a gasar Premier ranar Asabar, a kan Paris St Germain - a zagaye na biyu na wasan daf da karshe na gasar Zakarun Turai.

    Ya ce rashin nasarar zai iya ƙarfafa musu gwiwar a fafatawar mai zafi da ke tafe ranar Laraba.

    Arteta na magana ne cikin fushi, bayan rashin nasarar duk da cewa su suka fara zura kwallo a ragar ƙungiyar a wasan da aka fafata a filin Emirates.

    "Ba mu so yin rashin nasara ba," in ji shi. "Rashin nasara ta janyo mana fushi da kuma ɓacin-rai.

    "Yanzu ya rage mu soke fushin ranar Laraba. Wannan shi ne abin da ya kamata mu yi."

    Ƙungiyar ta yi rashin nasarar ce duk da saka dukkan zaƙaƙuran ƴan wasanta a fafatawar.

    Tana da jan aiki a gabanta muddin tana son kai wa wasan karshe na Champions League.

    Tana buƙatar doke PSG a gidanta a Parc des Princes, bayan rashin nasara da ci 1-0 a wasan farko a Emirates.

  8. Barazanar rufe Facebook ba zai hana mu hukunta Meta ba - FCCPC

    Hukumar da ke sanya ido kan farashi da kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya (FCCPC), ta ce barazanar da kamfanin Meta ya yi na ficewa daga ƙasar, ba zai hana a hukunta shi ba.

    Hukumar ta ce ba za a janye shari'ar da ake yi da Meta ba duk da barazanar da ya yi.

    FCCPC ta ce kamfanin ya yi barazanar ficewa daga Najeriya ne domin a ji tausayinsa, da kuma matsawa hukumar canza matakin da ya ɗauka na cin tarar kamfanin.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da darektan hukumar, Ondaje Ijagwu ya fitar ranar Asabar.

    Hakan kuma na zuwa ne bayan wani gargaɗi da Meta ya yi da farko cewa "za a tilasta masa rufe shafukan Facebook da Instagram a Najeriya don kauce wa barazanar fuskantar hukunci".

    Hukumar ta zargi Meta da yi wa bayanan ƴan ƙasar kutse, ciki har da aika bayanan ba tare da izininsu ba da rashin mutunta masu amfani da shafukan kamar yadda ake yi a sauran ƙasashe da kuma ɓullo da tsare-tsare da ba su da kyau kan ƴan ƙasar.

    A bara ne hukumomin sanya ido uku na Najeriya suka lafta wa kamfanin tarar da ta kai fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.

  9. An kama ƴan Iran bakwai kan zargin ta'addanci a Birtaniya

    Ƴan sanda a Birtaniya sun kama mutum takwas, bakwai daga ciki ƴan Iran kan zargin ta'addanci.

    An kama mutum biyar a wurare daban-daban a Ingila ranar Asabar, bayan samun labarin suna shirin kai hari wurare na musamman, a cewar ƴansandan ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce ana ci gaba da yin binciken domin gano sauran waɗanda suke aiki tare da su don kai harin.

  10. Mele Kyari ya musanta cewa EFCC ta kama shi

    Tsohon hugaban kamfanin mai na Najeriya NNPCL, Mele Kyari, ya musanta rahotanni da ke cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama shi - kan wani bincike da ake yi na zargin almundahanar kuɗi da ya kai dala biliyan 2.9, wanda aka ware don sake gyara matatun ƙasar.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Kyari ya yi watsi da rahotannin - inda ya ce wasu ne kawai ke son ɓata masa suna.

    "A tsawon kwanaki da suka gabata, na samu kiraye-kiraye daga ƴan uwa da abokai kan rahoton da wata jarida ta yaɗa cewa ina tsare a ofishin EFCC.

    "Wannan kawai yunkuri ne na ɓata min suna da jaridar da kuma waɗanda suka ɗauki nauyinta ke son yi," in ji Kyari.

    Ya kuma ce a shirye yake wajen faɗar gaskiyar abin da ya gudanar a ofishinsa lokacin da yake shugabancin NNPCL.

    "Zan ƙara nanata cewa na riƙe mukamin da aka bisa tsoron Allah, domin ko ban faɗi gaskiya a nan ba, zan faɗa a gaban Allah, in ji shi.

    A farkon watan Afrilu ne, shugaba Bola Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasar NNPCL, inda ya maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.

  11. Ƴan Houthi sun harba makami mai linzami cikin Isra'ila

    Wani mai makami mai linzami da ƴan tawayen Houthi suka harba daga Yemen zuwa cikin Isra'ila, ya faɗa kan tashar jirgin sama na Ben-Gurion da ke tsakiyar ƙasar.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda abu ya fashe lokacin da makamin ya sauka kusa da filin jirgin.

    Aƙalla mutum biyu ne suka samu raunuka.

    An dakatar da tashi da kuma saukar jirage a filin jirgin da ke kusa da Tel Aviv na ɗan lokaci, kafin a sake buɗe shi.

    Sojojin Isra'ila sun ce suna binciken yadda na'urorin tsaron sama suka ƙasa kakkaɓe makaman.

    Ministan tsaron ƙasar Israel Katz ya ce za su mayar da martani mai muni.

  12. RSF ta kai hari cibiyar kasuwancin Sudan

    Dakarun gwamnatin Sudan sun ce a karon farko tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar, mayaƙan RSF sun kai hari da jirgi maras matuƙi a Bhar Sudan.

    Kakakin gwamnatin sojin ƙasar, ya ce hare-haren sun faɗa filin jirgin saman yankin da wasu wurare, sai dai kuma bai bayyana ko harin ya janyo asarar rai ba.

    Wannan shi ne karon farko da aka taɓa ganin mayaƙan RSF sun kai hari yankin da gwamnati ke iko da cikakken iko da shi.

    Ana kallon yankin na Bhar Sudan a matsayin cibiyar kasuwancin ƙasar.

    Tun farkon yaƙin mayaƙan na RSF sun fi ƙarfafa karɓe iko da yankin Darfur da Kurdafan da ke kudu maso yammacin ƙasar da kuma nausawa tsakiyar birnin Jazeera.

  13. Mexico ta yi watsi da tayin Amurka na aika sojojinta zuwa ƙasar

    Shugabar ƙasar Maxixo, Claudia Sheinbaum ta ce ta ƙi amincewa da tayin Shugaba Trump na aika sojojin Amurka, domin taimaka wa ƙasar yaƙi da ƙungiyoyin masu safarar muggan ƙwayoyi

    Mrs Sheinbaum ta ce a tattaunawar da suka yi da Shugaba Trump ta waya a baya-bayan nan ta shaida masa cewa Mexico ba za ta taɓa amincewa sojin Amurka su kasance a iyakokinta ba.

    Gwamnatin Trump dai na matsa wa Mexico lamba ta magance kwararrar baƙi da ƴancirani da masu safarar muggan ƙwayoyi da ke amfani da iyakokin ƙasar domin shiga Amurka

  14. Mayakan Boko Haram sun kai hari kan sansanin soji a Yobe

    Rahotonni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin soji a jihar Yobe.

    Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa ƴan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na ''27 Task Force Brigade'' da ke garin Buni Yadi, a yankin ƙaramar hukumar Gujba da tsakar daren Asabar.

    Harin na zuwa ne kwana guda bayan ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin ƙasar sun gudanar da taro a Tamaturu, babban birnin jihar da nufin magance matsalolin yankin, ciki har da matsalar tsaro.

    A baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na neman dawo da hare-hare a yankin.

    A cikin makon nan ma ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 26 a jihar Borno.

  15. Trump na shan suka kan wallafa hotonsa na AI sanye da kayan Fafaroma

    Shugaban Amurka, Donald Trump na shan suka daga wasu jagororin mabiya ɗarikar Katolika, saboda wallafa hotonsa da ya samo daga manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sanye da kayan Fafaroma.

    Mista Trump ya wallafa hoton ne a shafukan sada zumunta na fadar White House.

    Matakin na zuwa ne yayin da mabiyar ɗarikar Katolika, ke shirin zaɓen sabon Fafaroma, bayan alhinin da suke ciki na rasuwar jagoran ɗarikar, Fafaroma Francis, wanda ya mutu ranar 21 ga watan Afrilu.

    Taron mabiya ɗarikar Katorlika na birnin New York ya zargi Shugaba Trump da zolayar Addininsu.

    Wallafa hoton na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ya zolayi wani mai bayar da rahotonni da cewa ''ina son zama Fafaroma''

    Ba Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taɓa zarga da zolayar mabiya ɗariƙar Katolika ba.

    A shekarar da ta gabata ma an zargi tsohon shugaban Amurka, Joe Biden lokacin da ya sanya hannu kan alamar kuros a lokacin wani gangamin masu goyon bayan zubar da ciki a Tampa da ke jihar Florida

    A ranar Laraba mai zuwa ne fadar Vatican za ta fara shirye-shiryen zaɓen sabon Fafaroma.

  16. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Sannunmu da haɗuwa a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa