Lionel Messi zai buga gasar FIFA World Cup ta shida a rayuwarsa bayan da aka saka shi cikin tawagar Argentina da za ta kare kofinta a gasar 2026.
Ɗan wasan gaban, wanda zai cika shekara 39 a yayin gasar, ya kasance cikin jerin mutum 26 da koci, Lionel Scaloni ya fitar. Messi ne ya jagoranci Argentina zuwa lashe Kofin Duniya na uku a tarihinta a Qatar shekaru huɗu da suka gabata bayan doke Faransa a bugun fenariti.
Da wasanni 26 da ya buga a Kofin Duniya, Messi ne ke rike da tarihin kan gaba a buga wasa a gasar. Zai kuma haɗu da Cristiano Ronaldo na Portugal a matsayin waɗandaa suka buga gasar sau shida a tarihi.
Mai tsaron raga na Aston Villa, Emiliano Martinez, wanda aka zaɓa a matsayin mafi kyawun gola a gasar 2022, yana cikin tawagar. Haka kuma akwai Lisandro Martinez na Manchester United da Cristian Romero na Tottenham, duk da cewa Romero ya rasa karshen kakar Premier League saboda raunin gwiwa.
Ƴan wasan tsakiya, Alexis Mac Allister na Liverpool da Enzo Fernandez na Chelsea su ma suna cikin ƴan wasa biyar da ke buga gasar Premier League ta Birtaniya da aka zaba domin gasar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Julian Alvarez na Atletico Madrid da Lautaro Martinez na Inter Milan suna cikin ƴan wasa 17 da suka lashe kofin 2022 da suka dawo domin kare kambun.
Argentina tana rukuni na 10 kuma za ta fara gasar ne da Algeria a Kansas City ranar 17 ga watan Yuni, kafin ta kara da Austria a Dallas ranar 22 ga watan Yuni da kuma Jordan ranar 28 ga watan Yuni.
Messi ya fita daga wasan Inter Miami a baya-bayan nan a MLS, amma ƙungiyar ta bayyana cewa bai samu rauni mai muni ba.
Ya zuwa yanzu Messi ya buga wa Argentina wasa 198, wadda za ta yi karawar sada zumunta da Honduras a Texas da kuma Iceland a Alabama.
Daga cikin manyan ƴan wasan da ba su samu gurbi ba akwai Emi Buendia na Aston Villa, wanda kwallonsa a wasan karshe na Europa League ta lashe ƙyautar mafi ƙyau a gasar, da Paulo Dybala na AS Roma wanda ya sha fama da jinya.
Haka kuma matashin ɗan wasan Real Madrid mai shekara 18, Franco Mastantuono, bai samu gurbi ba.
Dan wasan gefe na Benfica, Gianluca Prestianni, shi ma bai shiga ba bayan FIFA ta ce zai rasa wasanni biyu na farko saboda cin mutuncin Vinicius Junior.
Jerin Ƴan wasan tawagar Argentina a gasar Kofin Duniya:
Masu tsare raga: Juan Musso (Atletico Madrid), Geronimo Rulli (Marseille), Emiliano Martinez (Aston Villa).
Masu tsare baya: Leonardo Balerdi (Marseille), Nicolas Tagliafico (Lyon), Gonzalo Montiel (River Plate), Lisandro Martinez (Manchester United), Cristian Romero (Tottenham), Nicolas Otamendi (Benfica), Facundo Medina (Marseille), Nahuel Molina (Atletico Madrid).
Masu buga tsakiya: Leandro Paredes (River Plate), Rodrigo de Paul (Inter Miami), Valentin Barco (Strasbourg), Giovani lo Celso (Real Betis), Ezequiel Palacios (Bayer Leverkusen), Alexis Mac Allister (Liverpool), Enzo Fernandez (Chelsea).
Masu cin ƙwallaye: Julian Alvarez (Atletico Madrid), Lionel Messi (Inter Miami), Nicolas Gonzalez (Atletico Madrid), Thiago Almada (Atletico Madrid), Giuliano Simeone (Atletico Madrid), Nico Paz (Como), Jose Manuel Lopez (Palmeiras), Lautaro Martinez (Inter Milan).