Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 23 ga watan Maris 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ƴanbindiga sun kashe ƴansanda shida a Kenya

    Ƴanbindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar Al-Shabaab ne sun kashe ƴansandan Kenya guda shida.

    Ƴanbindiga sun kashe ƴansandan ne a wani hari da suka kai a sansaninsu da ke Garisa, kusa da iyakar ƙasar da Somalia.

    Bayan waɗanda suka rasu, wasu guda huɗu sun jikkata, inda yanzu haka suke jinya a wani asibitin ƙasar.

    Ƴan ƙungiyar Al-Shabaab dai suna kai farmakin kan mai uwa da wabi ne kan jami'an tsaro da fararen hula a ƙasar Kenya.

  2. Firaminstan Canada ya buƙaci a dawo zaɓen ƙasar baya

    Sabon Firaministan Kanada, Mark Carney ya buƙaci a gudanar da zaɓen wur-wuri a wata mai kamawa.

    Za a dai a kaɗa ƙuri'a ne a ranar 28 ga watan Afrilu mai kamawa.

    Ya nemi da a gudanar da zaɓen ƴan majalisun ƙasar domin samun cikakkiyar sahalewar jama'a ta hanyar zaɓe da ƙarfafa mulkinsa.

    Ya ce ƴan ƙasar na fuskantar matsi da ba a taɓa shiga ba sakamakon matakin da shugaba Trump ya ɗauka na ƙaƙaba wa ƙasar haraje-haraje.

  3. Girke-girken Ramadan: Yadda ake "chicken corn soup", wato romon kaza mai masara da dankali

    A filinmu na girke-girken Ramadan na yau, Salma Salisu Adam wacce aka fi sani da Chef Salma za ta nuna muku yadda ake yin "chicken corn soup", wato miyar kaza mai masara da dankali, ana farfesun ba tare da wani abin haɗi ba.

  4. An ceto sojar Najeriya da aka sace a Abuja a jihar Nasarawa

    An ceto sojar ruwan Najeriya Cynthia Akor, wadda aka sace a Abuja a jihar Nasarawa da ke maƙwabtaka da babban birnin ƙasar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an tsaron DSS da mafarauta da ƴan bijilante ne suka yi aikin ceto ta a cikin Narasawa.

    Jaridar ta ce an sace sojar ce tare da wasu mutum biyu a rukunin gidaje na ƙofar shiga Mamman Vatsa da ke unguwar Mpape a Abuja da misalin ƙaref 7:34 na daren Juma'a, inda jim kaɗan masu garkuwar suka kira suna neman kuɗin fansar naira miliyan 500 ga sojar, da kuma naira miliyan 400 ga sauran mutun biyun.

    Babban jami'in ɗansanda mai kula da aikace-aikace na musamman, DCP Isiyaku Sahru ya tabbatar da ceto sojar, inda ya ce an ceto ta ne a jihar Nasarawa.

  5. Ni kaɗai ne zan iya dakatar da Putin - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi kaɗai ne yake da ikon iya dakatar da Shugaban Rasha Vladimir Putin a game da yaƙin ƙasarsa da Ukraine.

    Trump ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a jirgin Air Force One, inda ya ce duk duniya babu wanda zai iya tsayar da Putin "sai ni kaɗai."

    A tattaunawar, ya ƙara da cewa, "ina ganin kuma zan yi ƙoƙarin dakatar da shi."

    "Mun tattauna da shi, ni dai kawai ina so ne a daina kashe mutuwa," in ji Trump.

  6. Hare-haren Rasha sun kashe mutum uku a Ukraine

    Hare-haren da Rasha ta kai Ukraine da tsakar dare sun yi sanadiyyar kashe mutum uku tare da raunata wasu da dama, a cewar jami'an yankin Kyiv.

    Wani shaida ya ce "mutane sun fara ihu da guje-guje" bayan ɓaraguzai sun faɗo kan wani rukunin gidaje.

    Rundunar sojin sama ta Ukraine ta ce ta harbo jirage marasa matuƙi kusan 60 cikin 147 da Rasha ta aika mata.

    A gefe guda kuma, ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce ta harbo irin waɗannan jiragen na Ukraine kusan 60, amma wani mutum ɗaya ya mutu bayan wata mota ta kama da wuta.

    Bayan harin a kan babban birninsu, Shugaban Ukraine President Zelensky ya nemi ƙasashen duniya su ƙara matsa wa Rasha.

  7. Mutanen da hare-haren Isra'ila suka kashe a Gaza sun zarta 50,000, in ji ma'aikatar lafiya

    Sama da mutum 50,000 aka kashe a Zirin Gaza tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare, kamar yadda alƙaluman ma'aikatar lafiya ta yankin suka nuna.

    Adadin na 50,021 ya kai kusan kashi 2.1 cikin 100 na yawan al'ummar zirin miliyan 2.3 - ko kuma a ce 1 cikin mutum 50.

    Haka nan, jimillar mutum 113,274 ne suka ji rauni sakamakon hare-hare ta sama da ƙasa da kuma ruwa da sojojin Isra'ila ke kaiwa.

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da ƙungiyoyin duniya kan yi amfani da lissafin na ma'aikatar lafiyar Hamas a matsayin sahihi, amma Isra'ila ta sha musanta cewa adadin bai kai haka ba.

    Isra'ila ta hana 'yanjaridar ƙasashen waje shiga Gaza, ciki har da BBC, saboda haka ba za a iya bincike kan adadin da ake bayarwa ba.

    Adadin da ma'aikatar ke fitarwa ba shi bambance tsakanin sojojin Hamas da kuma fararen hula, amma akasarinsu mata ne da ƙananan yara.

  8. 'Yanbindiga sun kashe jami'an tsaro 10 na jihar Zamfara

    'Yanfashin daji sun kashe dakarun rundunar tsaro a jihar Zamfara 10 a wani kwanton ɓauna da suka yi musu ranar Asabar.

    Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ce shida daga ciki dakarun tsaron gwamnatin jihar ne da ake kira Askarawa, huɗu kuma 'yan sa-kai ne.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya ƙara da cewa akwai dakarun Asakarawa biyu da ɗan sa-kai ɗaya da suka ɓata.

    "Lamarin ya faru ne bayan farmakin da gamayyar jami'an tsaro [ciki har da Askarawa] ƙarƙashin jagorancin sojojin Najeriya suka kai wa sansanin 'yanbindiga a Dajin Sunƙe, wanda aka samu gagarumar nasarar kashe da dama tare da ƙwato makamai masu tarin yawa," in ji Gwamna Lawal.

    Ya ce tuni aka yi jana'izarsu a yau Lahadi, yana mai cewa ya bayar da umarnin ɗaukar "matakin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka ji raunuka" da kuma "bayar da tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasu".

  9. An ga Fafaroma Francis karon farko tun bayan fara jinya

    Fafaroma Francis ya bayyana ta tagar asibiti a birnin Rome karon farko tun bayan da ya fara jinya ranar 14 ga watan Fabrairu.

    Za a sallami dattijon mai shekara 88 a yau Lahadi kuma zai samu hutun aƙalla wata biyu a fadar Vatican, a cewar likitocin da suka kula da shi.

    Wata biyar da suka wuce ya yi fama da manyan matsaloli biyu, "inda rayuwarsa ta shiga haɗari", in ji Dr Sergio Alfieri, ɗaya daga cikin likitocin.

    Fafaroman bai gama warkewa ba amma kuma yanzu ba shi ɗauke da cutar sanyin haƙarƙari {lumoniya), kuma yanzu jikinsa ya ɗan warware.

  10. Mahaifiyar Gwamnan Katsina Dikko Radda ta rasu

    Mahaifiyar gwamnan Katsina, Hajiya Safara'u Umaru Baribari, ta rasu tana da shekara 93.

    Fadar gwamnatin jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya ce ta sanar da rasuwar mahaifiyar Gwamna Dikko Umaru Radda a yau Lahadi cikin wata sanarwa amma ba ta bayyana musabbabin rasuwar tata ba.

    Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai Ibrahim Kaula Mohammed ya sanya wa hannu ta ce za a yi jana'izar marigayiyar da misalin ƙarfe 4:00 a yau.

    "Daga cikin 'ya'yan da ta bari akwai mai garin Radda Kabir Umar Radda, da Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar tsohon shugaban Najeriya marigayi Umar Musa Yar'adua," in ji sanarwar.

    Za a yi jana'izar a garin Radda mai nisan kusan kilomita 70 daga Katsina babban birnin jihar.

  11. Dole ne a binciki zargin yunƙurin cin zarafin lalata tsakanin Sanata Natasha da Akpabio - Amnesty

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta duniya Amnesty International ta ce ya zama wajibi a bincika zarge-zargen da Sanata Natasha Akpoti ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio na neman yin lalata.

    Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta zargi shugaban majalisar da tauye wa sanatan haƙƙin wakiltar jama'ar mazaɓarta na jihar Kogi sakamakon matakin majalisa na dakatar da ita tsawon wata shida kan rashin ɗa'a ga majalisa.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar a Najeriya ya fitar, Isa Sanusi ya ce: "Amnesty na kira ga mahukuntan Najeriya da su fara gudanar da sahihin bincike cikin gaggawa game da zargin lalata da Natasha ta yi wa Akpabio.

    "Girman zargin ɗaya ne daga cikin dalilan da za su sa a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma sahihi.

    "Idan hukumomin Najeriya suka gaza bincika wannan zargi zai jawo matsala mai girma, ciki har da kawo tsarin da zai dinga hana waɗanda aka ci zarafi ta hanyar lalata samun adalci."

  12. 'Yan'adawa a Isra'ila na neman a shiga yajin aiki

    Jagoran adawa a Isra'ila Yair Lapid ya yi kiran gudanar da yajin aikin gama-gari idan har gwamnatin Benjamin Netenyahu ta dage kan korar shugaban jami'an tsaron cikin gida.

    Mista Lapid ya yi wannan kiran ga dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv.

    Wakilin BBC ya ce Firaministan Netanyahu ya dage cewa dole ne Ronen Bar ya tafi duk da cewa Kotun Koli ta dakatar da korar tasa.

    Wasu masu zanga-zangar sun yi kiran da a kawo karshen yakin Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, wasu kuma suna rike ne da hotunan kananan yaran Falasdinawa da hare-haren Isra'ila ta sama suka kashe a wannan makon.

  13. Masu iƙirarin jihadi sun kashe masallata 44 a Nijar

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ayyana makoki kwana uku bayan wasu 'yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 44 yayin da suke sallar Juma'a.

    Rahotonni sun ce harin ya jikkata mutum 13, huɗu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali a harin da aka kai garin Kokorou da ke kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.

    Wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida Mohamed Toumba ya fitar ta ce maharan da ke biyayya ga ƙungiyar Islamic State wato Islamic State in the Greater Sahara (ISGS) ne suka kai harin a ranar Asabar.

    "Da misalin ƙarfe 2:00 na rana, daidai lokacin da Musulmai ke yin sallar Juma'a maharan suka kewaye masallacin domin aikata kashe-kashen da ba a saba gani ba," in ji ministan.

    Kazalika, sun cinna wa "kasuwa da gidajen mutane wuta," kamar yadda ya bayyana.

    Kwana biyu kafin wannan hari rundunar sojin Nijar ta ce ta kashe mambobin ISGS 45.

  14. Isra'ila ta kashe babban jami'in Hamas a Gaza

    An kashe wani babban jami'in Hamas a harin da Isra'ila ta kai ta sama a kudancin Gaza.

    Wakilin BBC ya ce Hamas ta ce an kashe Salah al-Bardaweel da matarsa ne a Khan Younis.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutum 32 Isra'ila ta kashe cikin sa'a 24.

  15. Barka

    Barkanmu da hantsin Lahadi, sannumu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Ni ne Umar Mikail zan kawo muku rahotonnin daga sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu a wuin yau.