Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 6 ga watan Satumba, 2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi namu na labaran kai-tsaye na wannan rana ta Asabar.

    Sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya nuna mana.

    Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

  2. An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa aƙalla 150 a Birtaniya

    An yi mummunar arangama tsakanin ƴansandan Landan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.

    Tuni rundunar ƴansandan birnin ta sanar da kama aƙalla mutum 150 da ta ce suna da alaƙa da zanga-zangar, wadda ƙungiyar Palestine Action ke jagorantar shiryawa.

    Wannan ce zanga-zanga ta baya-bayan nan tun bayan da gwamnatin Birtaniya ta ɗauki matakin haramta ayyukan ƙungiyar goyon bayan Falasɗina, wadda ta alaƙanta da ta'addanci.

    Dubban mutane suka shiga zanga-zangar, kuma ƴansanda sun kama da dama a cikin su. Kafin zanga-zangar dai ƴansanda sun ji gargaɗin cewa ɗaukar tambarin ƙungiyar babban laifi ne ga ƙasa.

  3. Na fita daga Jam'iyyar NNPP - Abdulmumi Jibrin

    Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai, Abdulmumi Jibrin ya sanar da ficewarsa daga Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya ce ya amince da matakin korarsa da jam'iyyar ta yi.

    Jibrin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam'iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba.

    Tun da farko, jam'iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta.

    Ya ce, "na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na yi amannar cewa tattaunar da na yi ba su yi nauyin da za su ja min kora ba," in shi, inda ya "ban janye komai ba a cikin abin da na fada."

    Ya ce ba a gayyace shi ba domin ya kare kansa kan abin da ake zarginsa da aikatawa, "ko a mulkin soja, ana ba wanda ake zargi dama ya kare kansa."

    Ya ce ya so a ce ya ci gaba da zama a jam'iyyar, "Amma tunda jam'iyyar ta kore ni, dole in amince da matakin da ta dauka."

    Dan majalisar ya ce nan gaba kadan zai sanar da matakin da zai dauka a game da makomarsa a siyasa.

  4. Aƙalla mutum shida sun rasu, 20 sun ɓata a wajen haƙar zinare a Sudan

    Hukumomi a arewacin Sudan sun ce ana ci gaba da neman masu rai a wani wajen haƙar zinare da ya rufta da mutane a lokacin da suke aiki.

    Mutum shida aka tabbatar sun mutu, yayin da ake fargabar wasu 20 sun maƙale sakamakon ruftawar ramin haƙar ma'adanan a jiya Juma'a.

    Kawo yanzu ba a tantance abin da ya janyo ruftawar ba, amma hukumomi sun ce ana gudanar da aikin haƙar zinare a yankin ne ba tare da cika ƙa'ida ba.

  5. Mutum biyar sun rasu a haɗarin kwale-kwalen aikin ceto na ambaliyar Pakistan

    Mutum biyar, ciki har da ƙananan yara huɗu ne suka rasu bayan wani kwale-kwalen aikin ceto ya kife a ambaliyar da wani kogi da ya yi sila a lardin Purjab da ke ƙasar Pakistan.

    Hukumomi a ƙasar sun ce kwale-kwalen ya kife ne a garin Multan a daidai lokacin da igiyar ruwa a kogin na Chenab ta fi ƙarfinsa, wadda ta tuntsurar da kwale-kwalen mai ɗauke da mutane.

    Ana dai ci gaba da aikin ceto domin tseratar da waɗanda ambaliyar ta rutsa da su, wadda ta tilasta sama da mutum miliyan ɗaya barin muhallainsu.

  6. Mayaƙan Boko Haram sun kashe mutum 55 ciki har da sojoji biyar a Maiduguri

    Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya a wani hari da suka kai kan wasu mutane da suka koma garinsu daga sansanin ƴan gudun hijira, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito daga wani ma'aikacin ƙungiyar agaji a yau Asabar.

    Harin ya auku ne a daren ranar Juma'a a garin Darul Jama a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, garin da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.

    Wata majiya ta shaida wa AFP cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin guda 55, har da sojoji guda biyar, da kuma wani ɗan sa-kai guda ɗaya.

    Mazauna yankin sun ce mayaƙan sun ƙaddamar musu da harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda suka ce maharan sun kutsa garin ne a kan babura ɗauke da muggan makamai, inda suka fara harbe-harben kan mai uwa da wabi, sannan suka riƙa ƙone gidaje.

    Wani wanda ya tsira mai suna Malam Bukar da ya tsere tare da iyalansa a cikin daren, ya bayyana wa AFP cewa da suka koma gida da safe, sun ga gawarwakin mutane aƙalla guda 55 a yashe.

  7. NSCDC ta tabbatar da kashe jami'anta takwas a Jihar Edo

    Rundunar tsaro ta NSCDC ta tabbatar da cewa wasu mahara sun kai farmaki kan jami'anta inda suka kashe guda takwas daga ciki a wani harin kwantar ɓauna da suka kai musu.

    Rundunar ta ce an kai harin ne kan jami'anta a garin Okpella da ke ƙaramar hukumar Etsaka ta Gabas a jihar Edo a kudancin Najeriya a ranar 5 ga watan Satumba.

    Kakakin rundunar, Afolabi Babawale ne ta tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda tashar NTA ta gwamnatin Najeriya ta ruwaito.

    Ya ce jami'an na NSCDC suna aiki ne domin ba wasu ƴan ƙasar China kariya a wani kamfani mallakin BUA da suke aiki, sannan ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ƴan Chinan guda biyar ya ɓace, amma ya ce "jami'anmu na bakin ƙoƙari wajen ganin sun ceto shi."

  8. Isra'ila ta sake nanata buƙatar Falasɗinawa su bar birnin Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta buƙaci Falasɗinawa su tsere daga birnin Gaza domin a cewarta sojojinta na yunƙurin kutsawa cikin birnin wanda shi ne mafi girma a zirin.

    Kimanin awanni kaɗan bayan gargaɗin sojojin na Isra'ila ne kuma wani harin ƙasar ya tarwatsa wani babban girni a birnin, wanda ya ke cikin manyan bene a cikin birnin.

    Ministan tsaron Isra'ila ya wallafa wani bidiyo wanda ke nuna yadda benen mai suna Sussi Tower ya tarwatse yana faɗi a ƙasa tare da gargaɗin cewa, "za mu ci gaba."

    Isra'ila ta ce ƴan Hamas na amfani da benen, duk da cewa ƙungiyar ta musanta haka.

    An dai shawarci mazauna Gaza su matsa zuwa guraren da suke cikin aminci ta can kudancin zirin domin tsira daga abin Isra'ila ta ce zai iya faruwa a yunƙurinta na ƙwace birnin Gaza.

  9. NNPP ta kori Abdulmumin Kofa daga jam'iyyar

    Jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta kori ɗanmajalisar tarayya Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam'iyyar tana mai zargin sa da cin amanarta.

    Shugaban jam'iyyar na Kano, Hashim Dungurawa ya faɗa wa BBC cewa sun kori ɗanmajalisar mai wailtar mazaɓar Kiru da Bebeji saboda dalilai na cin amana da kuma tallan wani ɗantakara.

    "Mun same shi da cin amanar jam'iyya a matakai daban-daban," in ji Dungurawa. "Na farko, mun same shi da tallata ɗantakarar shugaban ƙasa na wata jam'iya da ba namu ba.

    "Na biyu, ya ce zai iya fita daga jam'iyyar. Wannan ba ƙaramin cin amana ba ne. Na uku, ba ya biyan kuɗin haraji na jam'iyya, duk da cewa akwai doka cewa duk wata akwai abin da zai bayar domin cigaban jam'iyyar.

    "Na huɗu, ba ya zuwa mazaɓarsa. 'Yan mazaɓarsa kan yi kusan wata biyar ba su ji ɗuriyarsa ba."

    Zuwa yanzu ɗanmajalisar bai mayar da martami ba.

    Ɗanmajalisar ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na APC ziyara a watan Yuli, kuma a kwanan nan aka jiyo shi yana bayyana goyon baya ga shugaban.

  10. Isra'ila ta sake umartar Falasɗinawa su fice daga Birnin Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta umarci Falasɗinawa su fice daga gidajensu a Birnin Gaza yayin da take ƙara rushe gidaje da gangan a yankin na Zirin Gaza.

    'Yan awanni bayan ba da umarnin, IDF ta sake lalata wani dogon gini wanda shi ne na biyu cikin kwana biyu.

    Ministan tsaro ya wallafa bidiyon Ginin Sussi tare da gargaɗin, "Muna ci gaba". Isra'ila ta ce Hamas ce ke amfani da ginin, amma ƙungiyar ta musanta.

    Isra'ila ta sha umartar Falasɗinawa su koma yankunan da take cewa suna da aminci a kudanci, duk da cewa babu inda ba ta kai hari a zirin.

  11. Mutum shida sun mutu, 20 sun maƙale a mahaƙar ma'adanai a Sudan

    Mutum shida sun mutum yayin da ake fargabar wasu 20 sun maƙale sakamakon ruftawar ramin haƙar ma'adanai a arewacin ƙasar Sudan.

    Lamarin ya faru a jiya Juma'a a yankin Um Aud da ke yammacin jihar Kogin Nilu, a cewar Hassan Ibrahim Karar, jami'in lardin Berber na jihar.

    "Ana ta aikin ceton waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai," in ji Karar ba tare da ya yi ƙarin bayani game da musabbabin faruwar lamarin ba.

    Sai dai rahotonni na cewa mahaƙar ma'adanan ba mai lasisi ba ce a hukumance.

  12. Kifi ya kashe ɗanwasan zamiya a ruwan Australiya

    Wani babban kifi ya kashe wani mutum da ke wasan zamiya a shahararriyar gaɓar ruwan birnin Syndey na ƙasar Australia, kamar yadda rundunar 'yansandan ƙasar ta bayyana.

    Lamarin ya faru ne a yau Asabar lokacin da mutumin mai shekara 57 ya je wasan zamiya a ruwan tare da abokansa shida a ruwan Pacific da ke kusa da wuraren shaƙatawa na Sydney.

    Kifin ya karairaya ƙasusuwan mutumin, a cewar 'yansandan yankin New South Wales yayin wani taron manema labarai.

    Suka ƙara da cewa an ga gawarsa na yawon a saman ruwa ne bayan shi da kayan wasansa sun nitse tun da farko.

  13. Muhimmancin ganye da kayan marmari ga lafiyar ɗan'adam

    Hukumar kula da abinci da aikin gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya FAO ta bayyana ganyayyaki a matsayin wani rukunin abinci da ke da muhimmanci ga lafiyar al'umma.

    A 2021 ne hukumar ta ayyana shekarar a matsayin shekarar ganyayyaki domin jan hankalin al'umma ga amfaninsu wajen haɗa abinci mai inganci.

    Ita ma hukumar Lafiya ta Duniya (Who) ta bayar da shawarar mutum ya ci 'ya'yan itatuwa da ganyayyaki da suka kai nauyin giram 400 a kullum.

    Filin Lafiya Zinariya na wannan makon ya duba muhimmancin ganyayyaki ga lafiyar ɗan'adam. Ku latsa hoton ƙasa domin sauraron shirin:

  14. 'Yansandan jihar Kogi sun kama matashiya ɗauke da bindiga da kuɗaɗe

    Rundunar 'yansanda Najeriya reshen jihar Kogi ta ce ta kama wata matashiya Charity Williams a wani otel da zargin mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar, William Aya, ya ce sun ƙwace bindiga ƙirar gida da ƙunshin harsasai shida, da kuɗi naira miliyan 2,047,300, da miyagun ƙwayoyi, da gatari, da wayoyin salula huɗu daga wajen matashiyar mai shekara 23.

    Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun rundunar sun kama matashiyar ne ranar Juma'a a garin Oguda bayan samun rahoton sirri.

    A cewarsa, ɗakin da aka kamata wani ne mai suna Christopher Christopher Kadiri ya kama shi, kuma yanzu haka sun ƙaddamar da aikin neman sa shi ma.

  15. A shirye muke mu tattauna da Amurka - Shugaban Venezuela Maduro

    Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce bai kamata wasu bambance-bambancen da ke tsakanin ƙasarsa da Amurka su janyo rikicin soji ba.

    Shugaban ya yi wannan jawabin ne jiya Juma'a yayin da Amurka ta aike da ƙarin jiragen yaƙi 10 zuwa Puerto Rico a kan sojojin da aka jibge a ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce Shugaba Maduro ko shakka babu ba shi jin daɗin abin da shugaban Amurka ke yi wa ƙasarsa, kuma hakan ne ya sa a jiya ya ce yanzu kasarsa a shirye take ta tattauna kan abubuwan da Amurka ke buƙata.

    Gwamnatin Trump ta ce tana murƙushe ƙungiyoyin 'yandaba da ke ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, waɗanda ya ce suna aika su cikin Amurka.

  16. Gwamna Zulum zai bai wa ɗalibai da iyayensu kuɗaɗe don ƙarfafa gwiwa

    Gwamnan jihar Borno a arewacin Najeriya, Babagana Zulum, ya amince da bai wa iyaye maza N250,000 da iyaye mata N50,000 na ɗalibai 90 a garin Gajiganna da ke jihar.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da yake ƙaddamar da makarantar Islamiyya ta Higher Islamic College Gajiganna, inda ya yi alƙawarin ciyar da ɗaliban kyauta a kullum.

    "Za mu bai wa kowane uba N250,000, da kowace uwa N50,000. Kowane ɗalibi kuma zai samu N50,000 domin biyan buƙatunsa," in ji wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar.

    Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne domin ƙarfafa wa iyaye gwiwa wajen kai yaransu makarantar da ke arewacin Borno, yankin da yaƙin Boko Haram ya ɗaiɗaita.

    Gajiganna mai mutane kimanin 50,000, ɗalibai 90 ne kacal ke zuwa makaranta a garin, a cewar Gwamna Zulum.

    "Dole ne mu tabbata waɗannan ɗalibai 90 sun kammala karatunsu. Nasararsu za ta zama babban zakaran gwajin dafi a ɓangaren cigaban ilimi a arewacin Borno," kamar yadda ya bayyana.

  17. Trump ya sauya wa ma'aikatar tsaron Amurka suna zuwa ta yaƙi

    Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan umarnin shugaban ƙasa wajen sauya wa Ma'aikatar Tsaro ta Amurka suna zuwa "Ma'aikatar Yaƙi".

    Da yake jawabi a ofishinsa, Mista Trump ya ce sunan da ma'aikatar za ta koma yanzu zai yi daidai da yadda al'amura suka sauya a duniya.

    Sakataren harkokin tsaron kasar ya ce sauya wa ma'aikatar suna zai dawo da martaba da kimar mutanen da suka nuna bajinta a baya a kasar, yana mai cewa idan aka sauya sunan komai ma zai sauya a ma'aikatar.

    Akwai buƙatar majalisar dokokin kasar ta amince da wannan matakin, kodayake ana ganin ba za ta ƙi amincewa ba saboda 'yan jam'iyyar Republican ne mai mulki ke da rinjaye a dukkan majalisun dokokin kasar biyu.

  18. Ya kamata Isra'ila ta daina azabtar da fararen hula a Gaza - Who

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (Who), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi kira ga Isra'ila da ta daina azabtar da fararen hula da yunwa a Gaza.

    Akalla mutum 370 ne suka mutu saboda karancin abinci mai gina jiki a Gaza tun bayan fara yaki da kuma kawanyar da Isra'ila ta yi wa yankin.

    Dr Tedros ya ce wannan mummunan mataki ne da ba za a amince da shi ba.

    Tun da farko rundunar sojin Isra'ila ta lalata wani katafaren gini a cikin Gaza. Ta ce Hamas ce ke amfani da ginin, amma wani babban jami'i a kungiyar ya musanta hakan.

    Hukumar tsaron farin kaya a Gaza ta ce wasu hare-hare da Isra'ila ta kai a jiya Juma'a sun yi sanadin mutuwar mutum 42.

  19. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Asabar.

    Za mu kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku zuwa ƙarfe 4:00.