Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/06/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/06/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, yau a nan za mu kintse shafin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa sai gobe.

  2. Lafiya Zinariya: Kan amfani da mayukan sauya fata zuwa fara

  3. Da gaske kocin Super Eagles ya ajiye aikinsa?

    Kocin Super Eagles, Finidi George ya tabbatar da ajiye aikinsa na horas da tawagar Najeriya.

    Finidi ya tabbatar wa BBC cewa labarin ajiye aikin nasa ''gaskiya'' ne.

    A baya-bayan nan kocin mai shekara 53 ya fuskanci matsin lamba bayan rashin nasara da tawagar ƙasar ta yi a hannun Benin da ci 2-1 a wasan neman gurbin shigar gasar Kofin Duniya.

    Super Eagles ba ta yi nasara ba a duka wasanninta huɗu da ta buga a baya-bayan nan.

    Bayan rashin nasarar tawagar ne, ministan wasani na ƙasar, Sanata John Enoh ya nemi bahasin hakan daga hukumar ƙwallaon ƙafar ƙasar, kan mummunan sakamako da tawagar ke samu a wasannin neman gurgin gasar Kofin Duniya, yana mai cewa abu ne da ''ba za a lamunta ba''.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ƙwallon kafar ƙasar ta fitar ranar Alhamis ta ce za ta ɗauki ƙwarrarren mai horaswa cikin makonni masu zuwa, gabanin sauran wasannin neman gurbin gasannin Afcon da Kofin Duniya.

    Salon kamun ludayin kocin bai yi wa 'yan ƙasar da dama daɗi ba, ciki har da fitaccen ɗan wasan gaban ƙungiyar, Victor Osimhen, wanda a shafinsa na Istagram ya yayi bayani kan ɓarakar da tawagar ke fuskanta, ƙarƙashin jagorancin Finidi.

    A cikin watan Mayu ne dai aka naɗa Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagles bayan murabus ɗin Jose Peseiro - wanda ya jagoranci ƙasar ta kai wasan ƙarshe a gasar Afcon.

    A yanzu haka dai Najeriya na mataki na biyar a rukunin C na neman gurbin zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026.

  4. Yadda mahajjata suka gudanar da tsayuwar Arfa

  5. Hira da tsohon gwamnan Sokoto Sanata Aliyu Wamako

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata a Najeriya, Aliyu Magatakarda Wamakko ya fadi manyan abubuwan da zai iya tunawa a shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

    Ya kuma bayyana matsayarsa kan irin rawar da Tinubu ya taka a shekara guda na mulkinsa.

    Sanata Wamako ya kuma zayyano wasu matakan da za a ɗauka don kawo wa ‘yan Najeriya sauƙin matsin rayuwar da ake fuskanta.

  6. Gasar sarauniyar kyau da masu wasa a teku cikin hotunan Afirka

  7. Wata Hajiya daga Kaduna ta rasu a Makkah

    Wata Hajiya daga jihar Kaduna ta rasu a asibitin 'King Fahad' da ke birnin Makkah.

    Mai magana da yawun Hukumar Alhazan Jihar, Malam Yunusa Muhammad ne ya bayyana haka ga manema labarai a filin Arfa ranar Asabar.

    Mallam Yunusa Muhammad ya ce tuni aka yi wa gawar hajiyar rajista hukumar Alhazan jihar.

    Ya ƙara da cewa hukumar Alhazan jihar ta sanar da iyalan marigariyar labarin mutuwarta.

    ''Hukumar ta kuma jajanta wa iyalan marigariyar game da rashin nata'', in ji shi.

    A yau ne dai aka gudanar da tsayuwar Arfa, ɓangare mafi muhimmanci a aikin Hajji.

    Fiye da mutum miliyan 1.8 ne daui suka yi tsayuwar Arfar a yau Asabar.

  8. Mahajjata fiye da miliyan 1.8 ne suka yi tsayuwar Arfa

    Shafin X na Haramain a Saudiyya ya ce adadin Mahajjatan da suka yi tsayuwar Arfa ya kai miliyan 1,833,164.

    Ɗaya daga cikin manyan limaman ƙasar, Sheikh Maher Al-Muaigly ya gabatar da huɗubar mai tsara zuciya da ta yi kamanceceniya da huɗubar da Annabi S.A.W ya gabatar a Hajjin bankwana.

    ''Annabi S.A.W yana cewa ''na bar muku abubuwa guda biyu, Alqur'ani da Sunnah, idan kuka bi su ba za ku taɓa ɓata ba'', kamar yadda Sheikh Maheer ya bayyana.

    Babban limamin masallatai biyu masu tsarki, Sheikh Abdurrahman Sudais na daga cikin fitattun mutanen da suka yi tsayuwar Arfar a wanan rana.

  9. Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta sake nazarin sunayen sabbin 'yan sanda da za a ɗauka aiki

    Rundunar 'yan sandan Najeriya - ƙarƙashin jagorancin Babban Sifeton 'yan sandan ƙasar Kayode Egbetokun - ta ce za ta sake nazarin sunayen mutanen da suka yi nasarar jarrabawar shiga aikin 'yan sandan ƙasar, wadda hukumar kula da aikin 'yan sanda ta ƙasar ta shirya.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce jarrabawar ɗaukar sabbin 'yan sandan cike take ta kura-kurai.

    A lokacin da aka saki sunayen ranar 4 ga watan Yuni, shugaban hukumar kula da aikin 'yan sanda ta ƙasar, Solomon Arase ya ce an bi ƙa'ida wajen tantance mutanen da aka fitar da sunayen nasu.

    To sai dai Olumuyiwa Adejobi ya ce da yawa daga cikin sunayen da hukumar ta fiar ba su ma cike takardun neman aikin ba.

    Mai magana da yawun rundunar ya ce bayan nazari mai zurfi, kan sunayen da hukumar kula da aikin ɗan sanda ta ƙasarta fitar a shafinta, rundunar ta gano kura-kurai masu yawa kamar haka:.

    i) Mafi yawan sunayen ba su ma taɓa cike takardar neman aikin ɗan sanda ba, sannan ba su shiga kowane irin aiki na matakan ɗaukar aikin ba.

    ii) Haka kuma wasu sunayen sun ƙunshi jerin mutanen da suka kasa samun nasara a jarrabawar kwamfuta ko suka yi rashin nasara a atisayen motsa jiki.

    iii) Akwai kuma waɗanda aka cire kan matsalar lafiya da suke da ita, amma sai aka ga sunayensu cikin jerin sunayen da aka fitar.

    vi) Babban abin tayar da hankalin kuma shi ne yadda aka yi zargin amfani da kuɗi ko cin hanci wajen fitar da sunayen, lamarin da ya sa sunayen waɗanda ba su cancanta ba suke fito a jerin.

    Kan haka ne Adejobi ya ce babban sifeton ‘yan sandan ƙasar ya rubuta wa shugaban hukumar wasiƙar ƙin amincewa da sunayen, tare da aniyar sake nazarinsu.

    Kwanaki shida bayan fitar da sunayen ne, shugaban ƙasar Bola tinubu ya sauke Arase daga muƙamin nasa, tare da maye gurbinsa da Hashimu Argungu, tsohon mataimakin babban sifeton 'yan sandan ƙasar.

  10. 'Yan matan Najeriya da aka yi safararsu zuwa Ghana sun koma ƙasar

    Hukumar Kula da 'yan Najeriya mazauna ƙetare NIDCOM, ta ce an mayar da 'yan matan ƙasar kimanin 10 da aka yi safararsu zuwa Ghna.

    Cikin wata sanarwa da shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa a shafinta na X, ta ce a ranar Juma'a ne 'yan matan waɗanda aka kuɓutar daga Ghana suka koma ƙasar.

    Ta ce 'yan matan - waɗanda mafi yawansu 'yan jihar Imo ne - na tare da wakilan gwamnatin jihar.

    Ms Dabiri ta ce hukumarta ta samu bayanan 'yan matan ne daga hukumar yaƙi da safarar bil-adama ta ƙasar (NAPTIP).

    'Yan matan - waɗanda dukansu 'yan ƙasa da shekara 18 ne - wani mutum ne da ba a ambaci sunansa ba ya yi safararsu zuwa Ghana.

    Tuni dai 'yan sanda Ghana suka cafke mutumin, inda suke ci gaba da gudanar da bincik.

    Ms Dabiri kungiyar 'yan Najeriya mazauna ƙetare reshen ƙasar Ghana ne suka taimaka wajen kuɓutar da yaran.

  11. Sheikh Maher ya gabatar da huɗuba a filin Arfa

    Daya daga cikin manyan Limaman harami, Sheikh Maher Al-Muaiqly, ya jagoranci huɗuba a filin Arfa.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ce huɗubar malamin ta yi kamanceceniya da huɗubar da Annabi S.A.W ya gabatar a Hajjin Bankwana.

    Limamin ya umarci musulman duniya su yi biyayya ga biyayya ga umarnin Allah S.W.T, sannan su kauce wa abin da ya haramta, domin samun tsira da nasara a duniya da lahira.

    “Aikin Hajji alama ce ta nuna tsarkake ubangiji a ibada, kuma ba wuri ba ne na ambaton kalaman siyasa,” in ji shi.

    “Ya ku mahajjata da ke ziyara a ɗakin Allah, ku yi addu'a ga Ubangiji, ku nemar wa iyayenku da 'yan uwanku gafarar ubangijinku. Duk wanda ya yi wa ɗan uwansa addu'a a bayan idonsa, mala'iku za su yi masa kwatankwacin addu'ar.” in ji limamin

  12. Alƙaliyar da ɗan sanda ya harba a kotun Kenyan ta mutu

    Alƙalin Alƙalan Kenya ya ce alƙaliyar da ɗan sanda ya harba a lokacin da take tsaka da jagorantar shari'a a mutu a asibiti.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Justice Martha K Koome ya ce alƙaliyar kotun Makadara, Mai shiari'a Monica Kivuti ta "rasu sakamakon munanan raunukan da ta samu".

    A ranar Alhamis ne wani babban jami'in ɗan sanda ya harbi Ms Kivuti a tsakiyar kotun, lokacin da ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da belin matarsa.

    Bayan buɗe wa alƙaliyar wuta ne, 'yan sandan ta ke ganin kotun suka mayar wa jami'in ɗan sandan mai suna Samson Kipchirchir Kipruto martani, inda suka kashe shi bayan harbin da suka yi masa.

    Musayar wutar da 'yan sandan suka yi da shi ta sa uku daga ciki sun samu raunuka, inda suka karɓar magani a asibiti.

  13. An sake zaɓar Ramaphosa a matsayin shugaban Afirka ta Kudu

    'Yan majalisar dokokin Afirka ta Kudu sun sake zaɓar shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa a wa'adi na biyu.

    Mista Ramaphosa ya sake zama shugaban ƙasar ne bayan jam'iyyarsa ta ANC ta ƙulla ƙawance da jam'iyyar DA, wadda ta jima tana hamayya a ƙasar.

    Jam'iyyar ANC ta nemi ƙulla ƙawancen ne bayan da ta rasa rinjaye a majalisar dokokin ƙasar karon farko cikin shekara 30.

    Cyril Ramaphosa ya taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawar da ta kawo ƙarshen mulkin wariya na tsawon shekara 30 a ƙasar.

    Jam'iyyar DA ta yi fice wajen wakiltar fararen fata marasa rinjaye a ƙasar, wani batu da ta sha musantawa.

    Abin jira a gani yanzu shi ne yadda Mista Ramaphosa zai raba muƙaman ministocin gwamnatinsa, da za su haɗa da na jam'iyyar DA.

  14. Hotunan Mahajjata a filin Arfa

  15. Mahajjata na gudanar da tsayuwar Arfa

    Al'ummar musulmai da ke gudanar da aikin hajjin bana na tsayuwar Arfa a yau 9 ga watan Dhul-Hijja.

    Tsayuwar Arfa na daya daga cikin ginshikan aikin Hajji, inda ake bukar maniyyata su tsaya a wajen domin gudanar da addu'o'i.

    Wakiliyar BBC da ke filin ta shaida mana cewa kasancewa ana tsananain zafi a filin, an tanadi ruwan sanyi domin amfanin mahajjata.

    Likitoci sun shawarci maniyyata su yawaita shan ruwa don kauce wa illa daga tsananin zafin ranar da ake yi a filin.

  16. Assalamu Alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Musamman a wannan rana ta 9 ga watan Dhul Hijja da maniyyata ke tsawuyar Arfa.