Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/09/2024

Taƙaitattu

  • Trump ya zargi baƙin haure da ƙwace wani birni a Amurka
  • Ambaliya ruwa na ci gaba da yi wa ƙasashen Turai barazana
  • Farashin masara da shinkafa ya fara sauka a kasuwannin arewacin Najeriya
  • NNPCL ya kammala shirin fara shigar da man Dangote kasuwa a yau Lahadi
  • Gwamnatin Borno ta yi kira ga mutane su ɗauki matakan kiwon lafiyarsu
  • Jirgin yaƙin Sudan ya yi kuskuren kai hari sansanin soji a El Fasher

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Muhimmancin Maulidi a Musulunci

    Al’ummar Musulmi a faɗin duniya na bikin zagayowar Ranar Haihuwar Annabi Muhammadu (S.A.W) wadda akasari ke yi a rana mai kamar ta yau 12 ga watan Rabi’ul Awwal wadda a bana ta zo daidai da 15 ga watan Satumban 2024.

    Malamai na cewa shi ne Fiyayyen Halitta kuma Annabi Ƙarshe a jerin manzonnin da Allah ya aiko wa duniya domin su zama haske sannan su jagoranci al’umma zuwa shiriya.

    Albarkacin zagayowar wannan rana, BBC ta zanta da Sheikh Halliru Maraya, wanda ya yi mana bayani a kan muhimmancin bikin Mauludi.

    Malamin ya ƙara da cewa bikin Mauludi, manuniya ce ta girmama Ma’aikin Allah da nuna soyayya a gare shi.

  2. Firaministan Jordan ya sauka daga muƙaminsa

    Firaministan Jordan, Bisher Khasawneh ya sauka daga muƙaminsa shi da majalisar ministocinsa, kwanaki bayan zaɓen majalisar dokokin ƙasar, wanda ya bai wa jam'iyyar hamayya kujeru masu yawa.

    Sarki Abdullah na ƙasar ya ayyana Jafar Hassan, tsohon shugaban ma'aikatan fadarsa, kuma tsohon ministan kasafi da tsare-tsare a matsayin wanda zai zama sabon firaministan.

    Zaɓen na ranar Talata ya maido wa jam'iyyun hamayya rinjaye, to sai dai jam'iyyar IAF ta ninƙa adadin kujerunta har sau uku.

    Ana ganin jam'iyyar ta samu wannan nasara ne sakamakon fushin da al'ummar ƙasar ke yi game da yaƙin Gaza da kuma raguwar masu yawon buɗe idanu, wani gagarumin fannin fanin tattalin arzikin masarautar.

  3. Harin makami mai linzamin mayaƙan Houthi ya faɗa tsakiyar Isra'ila

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya gargaɗi mayaƙan Houthi da ke Yemen da cewa za su ɗanɗana kuɗarsu bayan wani harin makami mai linzami da suka kai tsakiyar Isra'ila.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce makamin ya faɗa ne a wani wurin da babu mutane ranar Lahadi da safe, to amma faɗuwar makamin ya fito da irin gazawar na'urorin kakkaɓo makaman ƙasar, da suka kasa lalata shi tun kafin ya shiga sararin samaniyar ƙasar.

    Sojojin ƙasar sun ce suna bincike kan lamarin, sannan sun ce akwai alamun ya tarwatse a sama tun kafin ya faɗi.

    Ɓurɓushin makamin sun lalata tashar jiragen ƙasa da ke gabashin birnin Tel Aviv.

    Ƙungiyar 'yan tawayen Houthin sun bayyana harin a matsayin somin-taɓi, wanda suka ce ya yi amfani da sabuwar fasahar makamai.

    Sun kuma ce sun kai harin ne domin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawan da ke Gaza.

  4. Har yanzu ba a ga mutum 40 da kwale-kwalensu ya kife ba a Zamfara

    Hukumomi jihar Zamfara na cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutum fiye da 40 da kwale-kwalensu ya kife a garin Gummi na jihar Zamfara.

    Lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe lokacin da kwale-kwalen ya kife da kusan mutum 50 a cikinsa galibinsu mata da ƙananan yara da ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki.

    Daraktan hukumar kare aukuwar bala'o'i ta jihar Dakta Hassan Usaman Duran ya tabbatar wa BBC cewa zuwa yanzu ba a ga mutum fiye da 40 ba, bayan kifewar kwale-kwalen.

    'A lokacin da lamarin ya faru an ceto mutum bakwai, kuma daga baya an lalubo gawar mutum biyu, daga nan kuma har yanzu ba a iya gano kowa ba tukunna,''in ji shi.

    Shi ma shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Amb. Bala Ahmad ya shaida wa BBC cewa jami'ansu na ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo ragowar mutane fiye da 40 da har yanzu ba a gani ba.

    Lamarin dai ya tayar da hankulan mutanen yanki, yayin da wasu 'yan'uwa suka fitar da rai daga ceto 'yan'uwan nasu a raye.

  5. Mutum takwas sun nutse bayan kifewar kwale-kwalen 'yan cirani a tekun Faransa

    Mutum takwas sun nutse cikin teku yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa daga Faransa zuwa Ingila a ƙaramin jirgin ruwa.

    Kwale-kwalen 'yan ciranin ya nutse jim kaɗan bayan tashinsa a arewacin Boulogne-sur-Mer na Faransa.

    Masu aikin ceto sun ce da safiyar yau aka sanar da su batun nutsewar kwale-kwale jim kaɗan bayan tashinsa, ɗauke da mutum kusan 50.

    Kawo yanzu 'yan cirani 45 ne suka mutu a tekun a wannan shekara.

  6. Jirgin yaƙin Sudan ya yi kuskuren kai hari sansanin soji a El Fasher

    Aƙalla sojojin Sudan biyar ne suka mutu, wasu tara suka jikkata bayan da rundunar sojin ƙasar ta ce ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ya yi kuskuren kai harin bam kan wani sansanin sojinta da ke birnin El Fasher.

    Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, lokacin sojojin saman ƙasar ke yunƙurin dakatar da dakarun RSF daga shiga cikin birnin.

    Faɗa ya rincaɓe a birnin cikin kwanaki uku da suka gabata, inda rahotonni suka ce yanayin ya munana musamman ga mutanen da ke maƙale a birnin.

    Asibitoci ƙalilan ne ke aiki a birnin, bayan da aka zargi RSF da kai hari kan asibitocin yankin tare da lalata su.

    Abinci ya yi ƙaranci a birnin. Masu bayar da agaji sun ce tallafin abinci ba ya isa ga dubban ƙananan yara da ke fama da tamowa a yankin.

  7. Gwamnatin Borno ta yi kira ga mutane su ɗauki matakan kiwon lafiyarsu

    Gwamnatin jihar Borno ta yi gargaɗi ga mazauna birnin Maiduguri da suka fuskanci mummunar ambaliya, game da kiwon lafiyarsu.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labaran jihar ta fitar, ta yi kira ga al'umma su ɗauki matakan kare lafiyarsu da tsaron da muhimmanci fiye da komai.

    Ma'aikatar ta zayyana wasu shawarwari da take son jama'a su kula da suka haɗa da:

    Kauce wa saye ko sayar da ko kuma cin abincin da ya gurɓarta da ruwa ambaliya. Saboda a cewarta duk bincin da ya gurɓata da ruwan ambaliyar zai iya haifar da hatsari ga lafiya.

    Sannan da saye ko sayar da ko cin naman dabbobin da suka mutu (Mushe), ''Kowane irin mushe na ƙunshe da guba'', a cewar ma'aikatar.

    Hukumar ta kuma gargaɗi mutane su guji sace ko ɓarnatar da kayan gwamnati ko na wasu mutane.

    Daga ƙarshe ta kuma yi kira ga mutane su kauce wa yin ninƙaya ko wanka a ruwan da ke tsaye.''Shi gurɓataccen ruwa koda an tafasa shi, ba za ka raba shi da matsalolin da za su iya yi wa lafiya illa ba'', kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.

    Ma'aikatar yaɗa labaran ta ce duk wanda aka samu da laifin fatali da waɗannan shawarwari zai fuskanci fushin hukuma.

    A farkon makon da muke bankwana da shi ne dai wata mummunar ambaliya da ba ataɓa ganin irinta ba cikin sama da shekara 30, ta auka wa birnin Maiduguri, lamarin da ya shafi kusan mutum miliyan biyu a cewar gwamnan jihar.

    Ambaliyar ta kuma yi sandin mutuwar aƙalla mutum 37, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA ta bayyana.

  8. NNPCL ya kammala shirin fara shigar da man Dangote kasuwa a yau Lahadi

    Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya ce ya kammala duk wasu shirye-shirye don fara ɗauko tataccen man fetur daga matatar mai ta Dangote domin shigar da shi kasuwannin ƙasar a yau Lahadi.

    NNPCL ɗin ne dama ya sanya yau Lahadi, 15 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai fara dakon man na Dangote.

    Cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa a a shafinsa na X, ranar Asabar ya ce ya shirya manyan motocin dakon mai a harabar matatar da ke unguwar Ibeju-Lekki a birnin Legas, domin lodin man.

    Ana sa ran shigar man Dangoten kasuwa, zai kawo sauƙi ga matsalar mai da ƙasar ke fuskanta a baya-bayan nan.

    A baya-bayan nan ne dai NNPCL ya sanar da ƙarin kuɗin man fetur a ƙasar, lamarin da 'yan ƙasar da dama ke kokawa a kansa.

  9. Ambaliya ruwa na ci gaba da yi wa ƙasashen Turai barazana

    Ana cigaba da hasashen yanayi mara kyau a yau Lahadi a sassa da dama na tsakiya da gabashin Turai bayan mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliyar da tayi sanadin rayukan akalla mutum huɗu tare da lalata gidaje aƙalla 5,000 a Romania.

    Shugaba Klaus Lohannis ya ce ƙasarsa na fuskantar matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.

    A Jamhuriyar Czech, ma'aikatar agajin gaggawa na cikin shirin-ko-ta-kwana. Mutane da dama sun ɓata, sannan gidaje 50,000 na fama da rashin lantarki.

    An kuma rarraba wa mutane buhunhunan ƙasa domin hana ruwa shiga gidajensu.

    Kasar Poland kuma ta kwashe mutanen da ke kan iyakarta da Jamhuriyar Czech bayan ɓallewar ruwa daga wani kogi.

    Firaminista Poland, Donald Tusk da ya ziyarci yankin ya ce rabon da su ga irin wannan tun 1997, lokacin da mutum 100 suka mutu.

    A can Austria ma haka ake fama da iska mai karfin gaske tafe da ruwan sama.

  10. Trump ya zargi baƙin haure da ƙwace wani birni a Amurka

    Ɗan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Repblican, Donald Trump ya cigaba da sukar da yake yi a kan birnin Springfield na Ohio, tare maimata zarginsa cewa baƙin-haure sun karɓe ikon harkokin birnin.

    Tsohon shugaban ƙasar ya soma irin waɗannan zarge-zarge ne tun lokacin da ya yi iƙirarin a lokacin muhawarar da ya tafka da Kamala Harris cewa baƙi 'yan Haiti na cinye karnuka da kyanwoyin mutane

    Magajin garin ya buƙaci Mista Trump ya daina irin waɗannan kalamai.

    Robert Rue ya shaida wa BBC cewa kalaman Trump sun tilasta kashe ƙarin kuɗaɗe wajen tabbatar da tsaro saboda barazanar harin bam da ya biyo baya.

    Wannan yanayi a yanzu ya tilasta rufe makarantu da gine-ginen gwamnati.

  11. Assalamu alaikum

    MAsu bibiyar mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu...