Ministan Abuja, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce zai fice daga dukkan yarjeniyoyin sulhu da aka shiga a baya domin sulhunta ɓangarorin da suke da saɓani a babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.
Haka Wike ya ce zai cigaba da gwargwarmaya, har sai "an tabbatar da adalci."
Sai dai kuma a wannan karon, Wike ya bayyana gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda tsohon na hannun damansa ne a matsayin wanda yake rura wutar rikicin a yanzu, "saboda ƙin ɗabbaƙa wasu matakai da aka ɗauka na sulhu."
Wike ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi mai taken, "Rikice-rikicen PDP: Matsayata."
A cikin sanarwar ya ce daga cikin matsayar da aka ɗauka, akwai tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin babban sakataren PDP kamar yadda Kotun Ƙoli ta tabbatar, sannan mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a na ƙasa zai janye ƙarar da ya shigar kan dokar ta-ɓaci na Rivers.
"Amma abin mamaki shi ne yadda Seyi Makinde ya haɗa baki da Gwamna Peter Mba na Enugu, inda suka yi wani taro, suka ce matuƙar ba a bar Ude Okoye a matsayin sakatare ba, za su fice daga PDP. Sannan Makinde ya sake haɗa wani taron, inda suka ƙulla cewa mataimakin babban sakataren ya zama sakataren riƙo, wanda shi ma ya saɓa da yarjejeniyar da aka ƙulla tun da farko."
Wike ya ce abin ban haushin ma shi ne yawancin gwamnonin da suke jawo matsalolin, "na taimaka wajen samun nasararsu a zaɓe, amma ban taɓa buƙatar komai daga wajensu ba, kuma ba zan taɓa yi ba. Don haka na fice daga dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla a baya."