Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/06/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/06/2024

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Bam ya kashe mutum shida a Borno

    Rahotanni daga garin Goza na jihar Barno, sun ce wani abu da ake zargin bam ne ya fashe daga jikin wata mata mai goyo.

    Jami’in huɗɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Barno, ASP Nahum Daso ya shaida wa BBC cewa, al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe uku na yammacin yau Asabar.

    Ya ce al’amarin ya faru ne a wani waje da ake kira Mararraba Motor Park, kuma ya yi sanadin mutuwar matar mai goyo da wasu mutum shida, wasu aƙalla 15 kuma suka ji munanan raunuka.

    An garzaya da waɗanda suka samu raunin zuwa babban asibitin Gwoza.

  2. Hukumomi a Ukraine sun ce Rasha ta kashe mutum 11 a sabbin hare-hare

    Hukumomi a Ukraine sun ce harin da Rasha ta kai ranar Asabar, a Kudu da kuma gabashin ƙasar ya kashe mutane aƙalla sha ɗaya.

    Jagoran gwamnatin yankin Zaporizhzhia ya ce harin makami mai linzamin da Rasha ta kai garin Vilniansk ya kashe fararen hula bakwai, ciki harda ƙananan yara biyu, ya kuma raunata wasu sha ɗaya.

    Ivan Fedorov ya yi bayanin cewa harin ya kuma rusa gine-gine da dama a yankin.

    A yankin Donetsk da ke Gabashi ma an kashe mutum hudu, a wasu hare-hare da aka kai ƙauyukan yankin.

    Shugaba Zelensky ya ƙara jaddada kiran sa ga ƙawayen Ukraine, na neman tallafin makamai, ciki harda na tabbatar da tsaron sararin samaniya.

    Tun da farko dai rundunar sojin Rasha ta ce ta mamaye wani yanki na birnin Donetsk, wanda ke kusa da garin Toretsk da ta daɗe tana neman ƙwacewa.

  3. An yi waje da Italiya a Euro 2024 mai rike da kofin 2020

  4. Pezeshkian na neman ƙarin goyon baya a zaɓen Iran

    Ɗan takara mai sassaucin ra'ayi a zaɓen shugaban ƙasar Iran ya nemi magoya bayansa su fito baki ɗaya domin kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu da za a yi ranar Juma'a.

    Massoud Pezeshkian ya ce ta haka ne kawai za a iya ceto ƙasar daga ƙangin talauci da jagorancin yaudara da kuma rashin adalci.

    Mr Pezeshkian ya samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaɓen da aka yi ranar Juma'a, amma ya gaza samun kashi 50%.

    Zai fafata da Saed Jalili, wanda ya fito daga ɓangaren masu tsatsauran ra'ayi.

    Mutane ba su fito sosai ba a zaɓen na ranar Juma'a, lamarin da rahotanni ker alaƙantawa da yadda mutane suka dawo rakiyar gwamnatin ƙasar.

    Wanda ya yi nasara a zaɓen zai maye gurbin marigayi shugaba Ebrahim Raisi, wanda ya rasu a wani haɗarin jirgin sama a watan Mayu.

  5. Firaiministan Serbia ya kore alaƙar addini da harin birnin Belgrade

    Firaiministan Serbia, Milos Vucevic ya bayyana harin da aka kai wa wani ɗan sandan ƙasar mai gadin ofishin jakadancin Isra'ila a Belgrade, a matsayin ''babban harin ta'addanci.''

    Da yake martani a kan harin, a ranar Asabar, Mr Vucevic ya jaddada cewa harin wani laifi ne na mutum ɗaya, kuma bai kamata a danganta shi da wani addini ba.

    Tun da farko, ministan harkokin cikin gidan ƙasar, Ivica Dacic ya yi zargin cewa maharin yana da alaƙa da ƙungiyar Wahhabi mai tsattsauran ra'ayi.

    Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce an kai harin ne bayan an tashi aiki a ofishin jakadancin nata, kuma babu wanda ya sami rauni.

    Hukumomi sun ƙara tsaurara matakan tsaro a sassan Belgrade.

  6. Biden ya yi watsi da kiran janyewar takarar sa

    Shugaban Amurka Joe Biden ya mayar da martani ga masu sukar sa saboda yawan shekarunsa, inda ya bai wa magoya bayan sa tabbacin samun nasara a zaɓen watan Nuwamba.

    Da yake jawabi ga magoya bayan sa a North Carolina, bayan muhawarar da ake ganin bai yi ƙoƙari ba, Mr Biden ya ce ''Ina sane cewa ni ba matashi bane, amma na iya faɗin gaskiya kuma na san aiki na''

    Mr Biden mai shekara 81, ya ce yan da yaƙinin cewa zai kammala wa'adin mulki na biyu cikin lafiya, kuma akwai nasara a tafiyar tasa.

    Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban Amurkan ya jaddada cewa shugaban mai shekara 81 ba zai janye daga takarar ba, duk da rashin taɓuka abin gani a muhawarar da suka yi da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

    Manyan makusantan Mr Biden da dama sun fito suna bayyana goyon bayan su gare shi, tare da kare ƙoƙarin da ya yi a wajen muhawarar.

    A wani mataki na nuna ƙarfafa gwiwa, tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, kuma jigo a tafiyar Biden ya wallafa a shafinsa na X cewa "Ana samun ɓacin rana a wajen muhawara".

  7. Bai kamata 'yancin matan Afghanistan ya shiga ajandar taron MDD ba - Taliban

    Ƙungiyar Taliban a Afghanistan ta ce 'yancin mata batu ne na cikin gida, don haka bai kamata a tattauna shi a taron Majalisar dinkin Duniya da za a fara ranar Lahadi a birnin Doha ba.

    Mai magana da yawun jagororin gwamnatin Taliban ta Afghanistan, Zabihullah Mujahid, ya ce suna koƙarin matsalar a cikin gida.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama sun yi allah wadai da hana matan Afghanistan halartar taron da za a yi a Qatar, wanda batun 'yancin ɗan'adam zai kankane ajandarsa.

    Tun bayan ƙwace mulkin Afhanistan kusan shekara uku da suka wuce, ƙungiyar Taliban ta hana mata da 'yan mata zuwa makarantu da wuraren aiki.

  8. IMF ya amince da bai wa Ghana ƙarin dala miliyan 360

    Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF ya amince da bai wa Ghana ƙarin dala miliyan 360 daga cikin rancen dala biliyan uku da ƙasar ta nema daga Asusun a cikin wani shiri.

    Hakan na zuwa ne bayan kammala nazarin shirin na shekara uku, wanda kawo yanzu ƙasar ta ƙarbi dala biliyan 1.56 tun fara shirin cikin watan Mayun shekarar da ta gabata.

    Ƙasar Ghana - wadda ta fi kowace ƙasa arzikin cocoa da zinare - na fuskantar matsin tattalin arziki mafi muni a tarihi, lamarin da hukumomin ƙasar ke alaƙantawa da tasirin annobar Corona da yaƙin Ukraine.

    To sai dai masu suka a ƙasar, na alaƙanta lamarin da rashin kyakkyawan shugabanci.

    Duk da cewa Asusun na IMF ya yaba wa ƙasar ƙarƙashin shirin karɓar rancen, 'yan ƙasar na cewa har yanzu ba su fara jin tasirin shirin a rayuwarsu ta yau da kullum ba.

    Hukumar ƙididdigar ƙasar, ta ce 'yan ƙasar miliyan 7.3 ne ke fama da talauci ta fuskoki daban-daban.

    Hauhawar farashi a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 54 a shekarar 2022, kodayake ya sauka zuwa kashi 23, amma har yanzu darajar kuɗin ƙasar na ci gaba da faɗuwa.

  9. Sojojin Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da sace ƙarafunan layin dogo

    Rundunar sojin Najeriya da ke aiki da runduna ta ɗaya da ke jihar Kaduna sun kama mutum 47 bisa zargin ɓarnatar da layin dogo.

    Mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Laftanar Kanar Musa Yahaya ne ya bayyana haka ranar Asabar a Kaduna.

    Laftanar Kanar Yahaya ya ce dakarun rundunar sun kama mutanen ne a lokacin wani samame da suka kai unguwannin Kakau Daji da Anguwan Ayaba da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, ranar 26 ga watan Yuni.

    Ya ce an kama mutanen ne lokacin da suka loda mota biyu na ƙarafunan layin dogon da suka sata.

    Jami'in sojin ya ce waɗanda ake zargin sun bayyana wa sojojin cewa wani mutum ne mai suna Alhaji Babawo ke sanya su aikin sace ƙarafunan.

    Najeriya - wadda a baya-bayan nan ke ƙoƙarin farfaɗo da sufurin jiragen ƙasa - na fama da matsalolin sufurin jiragen, inda a lokuta da dama wasu mutane ke ɓarnatar da titin jirgin ta hanyar sace ƙarafunan.

  10. Ambaliya ruwa ta kashe sojojin Indiya biyar a kan iyakarta da China

    Rundunar sojin Indiya ta ce dakarunta biyar ne suka mutu a lokacin da ambaliya ruwa ta yi awo gaba da tankar yaƙin da suke ciki a yankin Ladakh, da ke kusa da kan iyakar ƙasar da China.

    Dakarun na ƙoƙarin tsallaka kogi ne a tankar yaƙin da suke ciki, a lokacin wani atisaye da suke yi cikin dare lokacin da ruwan ya ƙaru a kogin - da ya raba tsakanin ƙasashen Indiya da China - ba tare da aune ba.

    Duka ƙasashen biyu na da tarin dakaru da tankunan yaƙi a kan iyakar - da ƙasashen suka jima suna taƙun saƙa a kai.

    Lamura sun ƙara munana a kan iyakar shekara huɗu da suka gabata lokacin da aka kashe sojojin Indiya 20 da na China huɗu a wata arangama tsakanin dakarun ɓangarorin biyu a yanki na Ladakh.

  11. Nahcon na ci gaba da jigilar alhazan Najeriya zuwa gida

    Hukumar alhazan Najeriya na ci gaba da jigilar alhazan ƙasar daga ƙasa mai tsarki zuwa gida.

    A makon da ya gaba ne hukumar ta fara jigilar mahajjatan ƙasar bayan kammala aikin hajjin bana.

    Cikin wata sanarwa da hukumar alhazan ta wallafa a shafinta na X, ta ce kawo yanzu jirage 32 sun mayar da alhazan ƙasar kimanin 13,642 zuwa Najeriya.

    Alhazan Najeriya fiye da 50,000 ne suka sauke farali a wannan shekarar.

  12. 'Yan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani gari a gabashin DR Kongo

    'Yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun ƙwace gari mai muhimmanci a gabashin DR Kongo.

    Mayaƙan ƙungiyar sun ƙwace iko da garin Kanyabayonga bayan mummunan faɗa tsakaninsu da sojojin Kongo.

    Garin na tsakanin manyan garuruwan Butembo da Beni, waɗanda suka kasance cibiyoyin kasuwanci a yankin arewacin lardin Kivu.

    Dubban mutanen da rikicin 'yan tawayen ya raba da muhallansu ne ke zaune a garin.

    Yankin arewacin lardin Kivu na fama da matsalar tsaro tun 2021, lokacin mayaƙan ƙungiyar M23 suka koma kai hare-hare.

  13. Zaɓen zagaye na biyu: Pezeshkian da Jalili za su fara yaƙin neman zaɓe

    Nan gaba kaɗan ne manyan 'yan takara biyu da ke kan gaba a sakamakon zaɓen Iran za su fara yaƙin neman zaɓen zagaye na biyu da za a gudanar ranar Juma'a mai zuwa.

    Dokar zaɓen Iran ta yi tanadin cewa 'yan takara za su fara yaƙin neman zaɓen zagaye na biyu, daga lokacin da aka sanar da sakamakon zagayen farko a hukumance.

    Tuni ma'aikatar cikin gida ta aike da sakamakon ga majalisar magabata, mai mambobi 12 domin su nazartarsa kafin tabbatar da shi a hukumance.

    Za a yi zaɓen zagaye na biyun ne tsakanin Massoud Pezeshkian mai ra'ayin kawo sauyi da Saeed Jalili, mai ra'ayin riƙau a ranar Juma'a da ke tafe.

    'Yan takarar biyu za su ci gaba yaƙin neman zaɓe har zuwa sa'o'i 24 kafin lokacin fara zaɓen.

  14. Zaɓen Iran: Fiye da ƙuri'u miliyan guda ne suka lalace

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iran, ta ce kimanin ƙuri'u 1,056,159 – kusan adadin tazarar da ke tsakanin Pezeshkian da Jalili – ne suka lalace a zaɓen shugaban ƙasar.

    Cikin wata gajeriyar sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Ahmad Vahidi ya fitar ya ce ''an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, sai dai an samu fafatawa mai zafi tsakanin 'yan takara biyu''.

    Kashi 40 cikin 100 ne na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a suka fito zaɓen, duk kuwa da kiran fitowar da jagoran addinin ƙasar ya yi gabanin zaɓen.

    A ranar Juma'a ne za a yi zagaye na biyu na zaɓen tsakanin Massoud Pezeshkian, tsohon likitan zuciya mai ra'ayin kawo sauyi da Saeed Jalili, tsohon mai shiga tsakani na ƙasar, bayan da kowannensu ya gaza samun kashi 50 cikin ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen.

  15. Labarai da dumi-dumi, Pezeshkian da Jalili: Za a je zagaye na biyu a zaɓen Iran

    Zaɓen shugaban ƙasar Iran ya kai mataki zagaye na biyu, bayan da 'yan takara biyu da ke kan gaba a sakamakon suka gaza samun kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen na ranar Juma'a.

    Ɗan takara mai ra'ayin kawo sauyi, Massoud Pezeshkian, ya samu ƙuri'a miliyan 10 da rabi, kimanin kashi 42.5 na ƙuri'un, inda ya bai wa babban abokin fafatawarsa a zaɓen, Saeed Jalili mai ra'ayin riƙau - da ya samu kashi 38.6 - tazarar ƙuri'a miliyan guda.

    To sai dai duk da haka bai samu adadin da ake buƙata don bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen ba.

    An samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen, lamarin da masu aiko da rahotonni suka alaƙanta da raguwar farin jinin tsarin gwamnati a ƙasar.

    Rahotonni na cewa kashi 40 cikin 100 na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a ne suka fito zaɓen, adadi mafi ƙaranci da suka fito zaɓe a tarihin ƙasar.

    A Iran dole ne duka 'yan takara su samu sahalewar majalisar magaba, wadda jagoran addinin ƙasar, Ayatoullah Ali Khamenei ke naɗa duka mambobinta.

    A ranar Juma'a mai zuwa ne za a gudanar da zaɓen zagaye na biyun.

    Zaɓen shugaban ƙasar ya taso ne bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgi, lokacin wata ziyara a yankin arewacin ƙasar, cikin watan Mayun da ya gabata.

  16. Sojojin Kenya za su tallafa wa 'yan sanda dawo da zaman lafiya - Ministan Tsaro

    Ministan tsaron kenya, Adan Duale ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa a kan titunan ƙasar, har sai an maido da kwanciyar hankali bayan kwashe mako guda ana zanga-zanga a ƙasar.

    Ƙasar na cikin yiyuwar fuskantar ɓarkewar sabuwar zanga-zanga cikin mako mai zuwa, bayan gangamin da ya tilasta wa shugaban ƙasar, William Ruto janye ƙudurinsa na ƙarin kuɗin haraji.

    Kalaman ministan na zuwa ne a daidai lokacin da wani alƙalin ƙasar ya haramta wa jami'an tsaro yin amfani da ƙarfi kan masu zanga-zangar.

    Mista Duale ya ce za a girke sojojin ne domin su taimaka wa 'yan sanda, waɗanda masu zanga-zangar suka ci ƙarfinsu.

    Aƙalla mutum 30 ne aka kashe a lokacin da 'yan sanda suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar a farkon wannan makon, kamar yadda ƙungiyar kare haƙiƙin bil adama ta Humar Right Watch ta bayyana.

    Ƙungiyar ta ce jami'an tsaron sun buɗe wuta kan mazu zanga-zangar, waɗanda ke ƙoƙarin guduwa.

    Matasan da ke zanga-zangar na buƙatar gwamnati ta soke muƙaman gwamnati da babu su a kundin tsarin mulki, da janye sauran haraje-haraje, tare da korar jami'an gwamnati masu tabon laifi.

  17. Sakamakon zaɓen Iran: Jalili da Pezeshkian na kankankan

    Ɗan takara mai ra'ayin riƙau, Saeed Jalili da mai ra'ayin kawo sauyi, Massoud Pezeshkian na kankankan a sakamakon zaɓen shugaban Iran da ake ci gaba da ƙidayawa.

    'Yan takarar biyu sun samu kusan kashi 40 na ƙuri'a fiye da miliyan takwas da aka ƙidaya kawo yanzu, inda suke rige-rige da juna a sakamakon.

    Zaɓen zai je zagaye na biyu - ranar Juma'a - idan har babu ɗan takarar da ya samu kashi 50 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Kofofin yaɗa labaran ƙasar sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaro biyu, a wani hari da suka kai wa wata motar da ke ɗauke da akwatunan zaɓe a lardin Sistan-Baluchestan.

    Mista Pezeshkian, tsohon likitan zuciya kuma tsohon ministan lafiya, ya alƙawarta kawo sabon salo a ƙasar, yana mai cewa akwai gyara kan yadda jami'an hukumar hisbah ke aikin tabbatar dokar tufafin mata a ƙasar.

    An gudanar da zaɓen ne domin maye gurbin tsohon shugaban ƙasar, Ebrahim Raisi, da ya mutu ranar 19 ga watan Mayu a wani hatsarin jirgin sama, tare da wasu manyan jami'an ƙasar bakwai.

    Mutum miliyan 61.5 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a Iran, to sai dai an samu ƙarancin fitowar masu zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri'ar, duk kuwa da kiran fitowar masu kaɗa ƙuri'ar da jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya yi gabanin zaɓen.

  18. Trump ya buƙaci a saki mutanen da suka mamayi majalisar Amurka

    Dan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya buƙaci sakin mutanen da suka mamayi majalisar dokokin ƙasar a ranar 6 ga watan Janairu.

    Mista trump na magana ne bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, da ke cewa masu gabatar da ƙara sun zaƙe, wajen amfani da dokar hana tayar da zaune tsaye yayin gurfanar da mutanen a gaban kotu.

    Tsohon shugaban ƙasar na Amurka ya kuma jefa ayar tambaya kan goyon bayan da ƙasar ke bai wa Ukraine, bayan ya yi iƙirarin nasara a muhawarar da suka fafata da shugaba Biden na jam'iyyar Democrat.

    Donald Trump ya ce shi ya zama gwarzon muhawarar ''duk da cewa abokin muhawarata ya samu duka abubuwan da yake so kafin fara muhawarar, kamar ranar da yake so, a kafar da yake so, da alƙalan da yake so, amma duk da haka ya kasa kare kansa''.

    A nasa bangaren, a wani gangami a Arewacin Carolina Shugaba Biden ya amince da rashin kataɓus a muhawarar, sai dai ya ce hakan bai hana shi faɗin gaskiya ba.

  19. Yunƙurin Juyin mulki a Bolivia: Shugaba Luis Arce ya ƙara samun ƙwarin gwiwa

    Shugaban ƙasar Bolivia, Luis Arce, ya ce gwamnatinsa ta samu ƙwarin gwiwa sakamakon goyon bayan da ya samu bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba.

    Wannan ya kasance ɗaya daga cikin kalamansa na farko tun bayan yunƙurin juyin mulkin a ranar Laraba.

    Wani alkali ya umurci tsohon hafsan sojin kasar Juan Jose Zúñiga da ya yi zaman gidan yari na jiran shari'a na tsawon watanni shida bisa zarginsa da laifin tayar da ƙayar baya da kuma tayar da zaune tsaye a ƙasar.

    Janar Zúñiga ya yi iƙirarin cewa shugaba Arce ne ya umarce shi da ya yi yunƙurin juyin mulkin, domin ƙara farin jininsa a wajen jama'a.

  20. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gar lafiya, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta da domin tafka muhawara kan laraban da muke wallafawa.