Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Shugaban Hukumar kare Hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce Sudan ta kwashe kusan shekara uku cikin masifa.
Yayin da ya ke jawabi a jihar Port Sudan, Volker Turk ya bayyana yadda ya ji labarai masu firgitarwa daga waɗanda suka tsira daga hare-hare a Dafur da Kordofan, yankunan da suka zaman sansanin gwabza faɗa tsakanin soji da dakarun RSF.
Volker Turk ya fara ziyarar kwanaki huɗu a Sudan, ta farko tun bayan ɓarkewar rikici a watan Afirilun shekara ta 2023.
Jami'in Majalisar Dinkin Duniyar ya ƙara da cewa an kashe makudan kuɗaɗe wajen sayan makamai musamman jirage marasa matuƙa maimakon taimaka wa waɗanda rikicin ya shafa.
Amurka ta buƙaci ƙasashen duniya su biya biliyoyin daloli idan suna son samun kujerar dindindin a kwamitin jagorancin sake gina Gaza.
Bayanai sun ce an aika ƙudirin da ƙasashe 60, domin gayyatarsu zama mambobi a kwamitin ''zaman lafiyar Gaza'' da Trump ke kafawa.
An shaida wa BBC cewa biyan bai shafi ƙasashen da ke matsayin mambobin wucin-fadi a kwamitin.
Kuma za a yi amfani da kuɗin wajen aikin sake gina yankin.
Kawo yanzu ƙasar Hungary ce kawai ta amince da biyan kuɗin don zama mamban dindindin a kwamitin.
Rahotonni daga Colombia na cewa faɗa ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ƴantawaye a yankin Amazon, lamarin da ya kai ga mutuwar aƙalla mutum 27.
Rundunar sojin ƙasar ta aika dakaru yankin domin kwantar da tarzomar.
Ƙungiyoyin ƴantawayen biyu da suka rabe daga tsohuwar ƙungiyar ƴantawayen FARC na faɗa da juna domin ƙwace iko da mallakar ƙwayoyi da safararsu a yankin Guaviare
Shugaban ungiyar Tsaro ta NATO Mark Rutte ya ce ya gana da Shugaba Trump na AMurka kan halin da ake ciki a Greenland da kuma yankin.
Cikin wani sao da ya wallafa a shafinsa na X, jim kaan bayan ganawar, Rutte ya ce ''Za mu ci gaba da aiki kan haka, kuma za mu sake ganawa a birnin Davos cikin mako mai zuwa.''
Trump zai halarci taron Duniya kan tattalin arziki da za a yi a birnin Davos na ƙasar Switzerland, inda shugabannin ƙasashen Faransa da Jamus da Netherland da Finland za su halarta.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe ƴanbindiga fiye da 40 a wasu hare-haren haɗin giwwa ta sama a yankunan Azi da Musarram da ke jihar Borno.
Cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a a rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar a ranar Lahadi ya ce harin ya wargaza shirin ƴanbindigar na ƙaddamar da harin da suka shirya tare da bai wa sojojin ƙasa damar inganta ayyukansu a yankunan.
Ejodame ya ce rundunar ta kai hare-haren ne a ranakun 15 da 16 ga watan Janairun da muke ciki, bayan samun bayanan sirri da kuma haɗin kan dakarun sojin ƙasa da ke yankin.
Ya ƙara da cewa jirgin sojin saman ya kai ɗaukin gaggawa bayan da rundunar da samu rahoton cewa sojojin ƙasa na fafatawa da ƴanbindiga a yankin.
Ya ci gaba da cewa jirgin ya sake kai hari bayan da ya fahimci ƴanbindigar na sake taruwa a ƙarkashin wata bishiya a yankin, lamarin da ya haifar da kashe da dama cikinsu.
Sanarwar ta kuma ce kwana guda kafin nan jirgin yaƙin sojin saman ya kai wani hari kan wasu ƴanbindiga a gaɓar ruwar Tumbuns.
''Mun hango wasu jiragen ruwa 10 ɗauke da mayaƙa fiye da 40 na shirin kai hari garin Baga da madatsar kamun kifi, nan da nan aka kai musu hari tare da wargaza shirinsu'', in ji sanarwar.
Ƴan majalisar dokokin Mozambique sun amince su ba da gudummawar albashinsu na kwanaki biyu -- kusan dala dubu arba'in da biyu -- don tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa da ta kashe mutane sama da ɗari.
Mai magana da yawun hukumar majalisar ya ce kuɗaɗen za su tafi ne kai-tsaye zuwa Cibiyar kula da bala'i ta ƙasa domin rabawa mutanen da lamarin ya shafa.
An shafe makonni ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙasashen Mozambique da Afirka ta kudu da kuma Zimbabwe, inda ake ci gaba da gudanar da aikin ceto yayin da ake fargabar ci gaba da samun ambaliyar ruwa.
An samu fashewar wani abu wata masana'antar saffara ƙarafa a arewacin kasar China, inda ta kashe aƙalla mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce fashewar -- a birnin masana'antu na Baotou da ke yankin inner Mongoliya -- tana da ƙarfin gaske wanda ya kai ga "ƙasa ta girgisa" a kusa da masana'antar.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe ginin masana'antar.
Kamfanin Baogang mallakar gwamnati ne ke gudanar masana'antar kuma shi ne ke tafiyar da al'amura a ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin masana'antun sarrafa ƙarafa a China.
An fara nune-nunen yatsa tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da 'ƴan tawayen M-23 da ke samun goyon bayan Rwanda kan iƙirarin da ƙugiyar ta yi na janyewa daga garin Uvira da ke gabashin ƙasar.
Wani mai magana da yawun gwamnati, Patrick Muyaya, ya ce sanarwar ta ranar Asabar magana ce kawai ta fatar baki, yana mai gargaɗin cewa akwai yiwuwar ƙungiyar ta bar jami’ai a baya domin kutsawa cikin jama’a da niyyar kai hare-hare nan gaba.
A cikin watan Disamba ne ƴan tawayen suka ƙwace garin mai matuƙar muhimmanci da ke kusa da kan iyakar ƙasar ta Burundi, kafin su sanar da janyewa a hankali sakamakon matsin lamba daga Amurka.
Amurkar dai ta buƙaci ƙungiyar da ta dakatar da kutsen da ta ke yi a swasu sassan kasar domin tallafawa ƙoƙarin samar da zaman lafiya.
Sojojin Amurka na cikin shirin ko-ta-kwana don yiwuwar tura su zuwa Minneapolis, kamar yadda wani jami'in tsaron Amurka ya shaidawa CBS News, abokiyar hulɗar BBC na Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump na da zaɓin aikewa da sojoji 1,500 da ke Alaska a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da hukumar shige da fice da kwastam (ICE) a birnin.
Ya zuwa yanzu dai ba a yanke shawara kan ko za a tura sojojin daga Alaska ba, in ji jami'in.
Jami'an gwamnatin Minnesota sun buƙaci masu zanga-zangar da su kasance cikin lumana yayin gudanar zanga-zangar da ta ɓarke bayan da wani jami'in hukumar ICE ya harbe wata mata ƴar Amurka Renee Good a farkon wannan watan.
Jami'an gwamnati jihar dai sun ce Good ta je wurin ne a matsayin mai lura da ayyukan ICE.
Sai dai gwamnatin Trump ta bayyana ta a matsayin ƴan ta'addar cikin gida.
Jami'ai a Ukraine sun ce da safiyar yau Rasha ta kaddamar da wasu sabbin hare hare ta sama a ƙasar.
Magajin garin birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin ƙasar ya ce aƙalla mutum guda ya rasa ransa inda wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wani harin jirgi mara matuƙi da ya faɗa kan gidajen jama'a.
Wani hari kuma da aka kai birnin Sumy ya raunata mutum huɗu ciki har da wani ƙaramin yaro.
Jami'an hukumar agajin gaggawa a Odessa sun ce hare haren na Rasha sun faɗa kan wasu ababen more rayuwa na fararen hula.
Hare-haren na baya-bayan nan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan wata tawagar ƙasar ta Ukraine ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban ma'aikatan shugaba Zelensky, ta isa Amurka domin ci gaba da tattaunawa kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Rasha.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe wata mata da ƴaƴanta shida a unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.
A cewar wata sanarwa damai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Lahadi, kamen ya biyo bayan wani samame da jami’an ƴansanda suka gudanar bisa umarnin sufeto janar na ƴan sandan ƙasa Kayode Egbetokun.
Sanarwar ta ce, an kama waɗanda ake zargin ne bayan a wani aiki da aka gudanar da daren ranar Asabar 17 ga watan Janairu.
Ƴan sandan sun ce bayan binciken farko da aka gudanar wanda aka bayyana a matsayin jagoran ƙungiyar, wanda kuma ɗa ne ga an'uwan matar da aka kashe, ya amsa laifin sa.
Ya kuma yi bayanin cewa ƙungiyar na da hannu a wasu munanan hare-hare a jihar.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun hada da tufafi ke jiƙe da jini, da wayoyin hannu guda biyu na wanda aka kashe, da adda, da kulake, da wasu kuɗaɗe da sauran makaman da ake zargin an yi amfani da su a yayin harin.
Rundunar ƴan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kira taron majalisar tsaron ƙasarsa, a matsayin martani ga naɗe-naɗen da shugaba Trump ya yi a kwamitin zaman lafiya na zirin Gaza.
Jami'an Isra'ila sun nuna damuwarsu kan mutanen da kwamitin ya ƙunsa, suna masu cewa tsarin kwamitin ya saɓawa manufofin ƙasar, kuma ba a tuntuɓi Isra'ila kafin a kafa kwamitin ba.
Kwamitin zartaswartar da za ta sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin Gaza bayan yaƙinta da Isra'ila, ya haɗa da jami'ai daga Turkiyya da Qatar - ƙasashe biyu da suka soki yadda Isra'ila ta gudanar da yaƙin.
Falasdinawa ma sun nuna damuwa kan rashin samun wakilci a kwamitin.
Wani ɗan siyasar Falasdinu (Mustafa Barghouti) ya shaida wa BBC cewa da alama kwamitin dai na Amurka da wasu ƙasashen duniya ne.
Wuta gobara da ta tashi a wasu rukunin shaguna a birnin Karachi na Pakistan ta yi sanadin rasa rayukan aƙalla mutum biyar.
Gobarar ta tashi ne a rukunin shaguna na Gul Plaza a yammacin jiya Asabar da kuma har kawo yanzu ba a kammala kashe ta ba.
Jami'an kashe gobara sun ce tsananin zafin da kuma yadda wutar ke ci sosai suna na kawo cikas ga aikin ceton da ake kuma ana fargabar adadin waɗanda mutu zai iya ƙaruwa saboda akwai waɗanda suka maƙale a cikin shaguna.
Gobarar ta ginin na Gul Plaza mai ɗauke da shaguna sama da dubu ɗaya ta tashi ne da yammacin Asabar.
Wani mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ya shaidawa BBC cewa za a iya ɗaukar kwanaki kafin a iya kashe wutar.
Barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na sanya sabon haraji kan wasu ƙasashe takwas da ke adawa da shirinsa na karɓe iko da yankin Greenland ya janyo suka daga shugabannin ƙasashen Turai.
Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya ce matakin ba daidai ba ne, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana lamarin a matsayin "abin da ba za a amince da shi ba".
Kalaman na zuwa ne bayan da Trump ya sanar da ƙarin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su Amurka daga Denmark da Norway da Sweden da Faransa da Jamus da Burtaniya da Netherlands da kuma Finland, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Fabrairu.
Mr Trump ya ce zai iya ƙara harajin zuwa kashi 25 - kuma zai ci gaba har sai an cimma yarjejeniya.
Bayan barazanar Trump, Tarayyar Turai ta kira taron gaggawa da karfe a Brussels ranar Lahadi.
Taron dai zai samu halarcin jakadu daga ƙasashe 27 na ƙungiyar ta EU, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
A halin da ake ciki kuma, dubban mutane sun fito kan tituna a yankin Greenland da Denmark a ranar Asabar din da ta gabata don nuna adawa da shirin Amurka na mamaye yankin.
Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika (CAF) CAF ta yi watsi da iƙirarin da hukumar kwallon kafa ta Senegal (FSF) ta yi game da rashin adalci a tsare-tsaren da ake yi gabannin wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a Moroccoi.
A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta jaddada cewa ta yi ƙoƙarin tabbatar da daidaito tsakanin dukkan tawagogin da suka halarci gasar ta bana.
"Hukumar CAF ta himmatu kan tabbatar da adalci da gaskiya da kuma bin ƙa'idojinta ," in ji sanarwar.
Ta kuma ƙara da cewa CAF ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da kwamitin tsare-tsaren gasar na cikin gida (LOC) don tabbatar da yanayi iri ɗaya ga dukkan tawagogin da ke halartar gasar.
Martanin na CAF dai na zuwa ne bayan Senegal ta fitar da wata sanarwa inda ta yi zargin rashin adalci a tsare-tsaren da suka shafi walwala da tsaron ƴanwasa gabannin wasan da za ta fafata da Morocco mai masaukin baƙi.
An dawo amfani da shafukan intanet a Uganda bayan rufewar da aka yi a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala a ƙarshen makon jiya.
Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta ce, an daƙile intanet ɗin ne domin kiyaye zaman lafiyar jama’a da kuma hana yin amfani da kafafen sadarwa na zamani, da sauran manhajoji wurin yaɗa labaran da ka iya haddasa ɓarkewar rikici.
Amma ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Dinkin Duniya ya soki matakin, wanda ya bayyana a matsayin abin da ya haifar da "matuƙar damuwa."
Cire dakatarwar na iya nuni da ƙwarin gwiwa da hukumomin tsaro ke da shi cewa ƙasar ta kaucewa barazanar tarzoma.
Tun da farko dai hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana shugaba Museveni a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kashi 72 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine, wanda ya samu kashi 25 cikin 100, ya yi watsi da sakamakon tare da yin kira da a gudanar da zanga-zangar lumana don ƙalubalantar sakamakon.
Jami'an gwamnatin Amurka sun ce dakarun asar sun kai wani hari da ya hallaka wani shugaban ƙungiyar Al-Qaeda "wanda ke da alaƙa kai tsaye" da ƙungiyar 'yan ta'adda ta IS da ke da alhakin kai harin kwanton ɓauna da ya kashe Amurkawa uku a ƙasar Siriya.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta Centcom ta fitar ta ce an kashe Bilal Hasan al-Jasim a harin da aka kai a ranar Juma'a, wanda aka kai a arewa maso yammacin Siriya.
Sanarwar ta ce yana da alaƙa da ɗan bindigar ƙungiyar IS wanda ya kashe tare da jikkata jami'an Amurka da na Syria.
BBC ba ta tabbatar da iƙirarin na Amurka Amurka ba.
Tun bayan mutuwar Amurkawa uku a ranar 13 ga watan Disamban 2025 a yankin Palmyra da ke tsakiyar ƙasar Syria, Amurka ta kai hare-hare da dama kan mayaƙan IS a Syria, a ƙarƙashin wani shiri da ta yi wa laƙabi da 'Operation Hawkeye Strike'.
A farkon wannan watan, Centcom ta ce ta kashe ko kuma ta kama ƴan ƙungiyar IS kusan 25 a cikin ayyuka 11 da ta gudanar tsakanin ranakun 20 zuwa 29 ga watan Disamba.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi.
Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku biyo a shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.