Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Jama'a a nan za mu rufe wanan shafin na labaran kai-tsaye da muke kawo muku kan abubuwa da suka faru a sassan duniya.

    Da fata kun ji dadin kasancewa a tare da mu.

    Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya nuna mana.

  2. Yarima Andrew na Birtaniya ya haƙura da sarauta

    Kanin sarki Charles wato Yarima Andrew, ya ce zai haƙura mukamansa na gidan sarauta ciki har da Sarautar Duke of York.

    Yariman ya ce zargin da ake ci gaba da yi masa na lalata kawo cikas ga ayyukan Sarkin da kuma ayyukan iyalan gidan saurata.

    Wannan na zuwa ne bayan wasu sabbin bayanai game da alakarsa da marigayi Jeffrey Epstein da aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da kuma zargin alakarsa da wani ɗan leken asirin China.

    Sai dai zargi ne da ya musanta

  3. Sau 22 ma'aikatan da muka sallama suka yi ƙoƙarin yi mana ɓarna - Matatar Dangote

    Matatar Dangote ta ce hauhawar farashi da rashin tabbas a farashin ɗanyen mai ne suka sa matatar ta rage sayen ɗanyen man, wanda hakan ya rage fetur da take fitarwa, ba wai saboda matsala daga matatar ba, sannan ta ƙara da cewa ma'aikatan da kamfanin ya sallama sun yi yunƙurin yi musu ɓarna.

    Kamfanin ya bayyana haka ne a lokacin da mataimashin shugaban rukunin kamfanonin Dangote Edwin Devakumar yake zagawa da ƴanjarida cikin matatar bayan rahotanni sun ce matatar ta rage aiki.

    "Babu kamfanin da yake aiki ɗari bisa ɗari a kullum ba tare da fuskantar wata matsala ba," in Devakumar.

    Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne lura ko matsalar ta shafi abin da ake fitarwa.

    Ya ce a tsarin matatar wadda aka buɗe a farkon wannan shekarar, an tsara za a riƙa ɗan dakatawa ne a yi gyare-gyare a duk bayan shekara biyar, "ba kamar sauran tsofaffin matatu ba da suke yawan tsayawa da aiki domin gyara."

    Sai dai kafar Reuters ta ruwaito matatar ta dakata da aiki domin gyara sau huɗu a wannan shekara, wanda ba kasafai ake ganin haka ba a sababbin matatun mai irin na Dangote.

    A game da sallamar ma'aikata na kwanakin baya, Devakumar ya ce sun gano yunƙurin aikata ɓarna har sau 22 da ma'aikatansu suka yi, "ciki har da yunƙurin cinna wuta da lalata wasu kayan aiki. Mun san ranar da aka yi da ma duk ɓangaren da aka yi yunƙurin," in ji shi.

    Sai dai a cewar ƙungiyar masu matatun man fetur ta Najeriya, yunƙurin zagon-ƙasa a matatun man fetur na da wahalar gaske.

  4. 'An kashe mutum 17 a Birnin Gwari'

    Rikici tsakanin ƴanbindiga da masu haƙo ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 17, kamar yadda kafar AFP ta ruwaito daga wani rahoto da aka aika wa Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Rikicin ya auku ne a ranar Alhamis a wani wajen haƙo ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a yankin na Birnin Gwari bayan wani gawurtaccen ɗanbindiga ya je, inda ya buƙaci karɓar haraji daga masu aikin haƙo ma'adinan.

    Rahotanni sun ce masu aikin ne suka fusata, inda suka kashe ɗanbindigar, lamarin da ya sa yaransa suka yi sabon shiri suka koma domin mayar da martani. Da suka koma ne suka "buɗe wuta har suka kashe masu aikin haƙo ma'adinai guda bakwai."

    Daga baya kuma sai suka kai hari a ƙauyen Layin Ɗanauta, inda suka kashe wasu mutum tara, suka jikkata wasu mutum 13, sannan suka yi garkuwa da wasu.

    Yankin Birnin Gwari ya daɗe yana fama da matsalar ƴanbindiga, kafin aka shiga yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƴanbindigar da gwamnatin jihar, wanda ha haifar da zaman lafiya a yankin da wasu sassan jihar Kaduna da suke fuskantar matsala.

    Sai dai wannan harin ya jefa tsoro a zukatan mazaunan yankin, inda suke fargabar mayar da hannun agogo baya kasancewar sun kasance cikin zaman lafiya tun bayan sulhun.

  5. Taliban ta zargi Pakistan da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

    Wani jami'in gwamnatin Taliban na ƙasar Afghanistan ya zargi Pakistan da kai mata hare-hare a yankunan da ke bakin iyakar ƙasar.

    Ya ce kai hare-hare a ƙasar tamkar karya alƙawarin yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka shiga ne domin samar da zaman lafiya a tsakaninsu.

    Mazauna lardin Paktika sun shaida wa BBC cewa sun ju ƙugin jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa suna kai hare-hare.

    Har dai yanzu Islamabad ba ta ce komai ba kan zargin na karya alƙawarin tsagaita wuta.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake yunƙurin haɗa a ƙasashen biyu a tare a Qatar domin tattauna hanyoyin sasanta su a ƙarshen mako.

  6. Zelensky ya buƙaci Amurka ta ba Ukraine makamin Tomahawk mai linzami

    Shugaban Amurka Donald Trump ya karɓi baƙuncin takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar gwamnati ta White House, inda suka tattauna muhimman abubuwa da suka shafi ƙasashen biyu da ma duniya bak ɗaya.

    Daga cikin abubuwan da suka tattauna, akwai buƙatar da Zelensky ya miƙa da Amurka, inda buƙaci Trump ya amince a ƙara musu tallafin manyan makamai domin fuskantar Rasha.

    Daga cikin manyan makaman da Ukraine ke buƙata, har da makamin Tomahawk mai linzami wanda ke cin dogon zango.

    Sai dai tun bayan ganawar wayar tarho da Trump ya yi da Putin, ya bayyana a ranar Alhamis cewa ita ma Amurka na buƙatar da makamin saboda nan gaba zai mata amfani.

    Tun da farko, Mr Zelensky ya gana da wasu sanatoci, inda da yawa daga cikinsu suka buƙaci a ƙaƙa wa Rasha takunkumai.

  7. An fara samun zaman lafiya tsakanin Pakistan da Afghanistan

    An fara samun kwanciyar hankali a bakin iyakar ƙasashen Pakistan da Afghanistan a sanadiyar yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙasashen biyu suka shiga domin a ɗan ɗaga ƙafa daga rikicin da suke yi.

    Kakakin gwamnatin Afghanistan Zabihullah Mujahid ya shaida wa BBC cewa sun fi son a samu sasanci ta hanyar tattaunawa maimakon yaƙi, amma ya yi gargaɗin cewa za su mayar da martani idan har aka kai musu hari.

    Kafofin sadarwa na Pakistan sun ruwaito cewa za a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar, amma har zuwa yanzu ba a samu labarin ba a hukumance.

    Jami'an Afghanistan sun ce za su tura wakilai zuwa Qatar domin tattaunawa domin lalubo hanyoyin da za a kwantar da tarzomar.

    An dai ɗauki kusan mako ɗaya ana luguden wuta tsakanin ƙasahen biyu, lamarin da ya yi ajalin gomman mutane.

  8. China ta sallami sojojinta ciki har da janar daga aiki

    Ma'aikatar tsaro ta China ta ce an kori wasu manyan jami'an sojojin kasar 9 daga jam'iyyar Kwaminis mai mulki a kasar kuma a ciki akwai wani mai babban mukamin soji .

    Ta ce korar da aka yi Janarar He Weidong da sauransu nada alaka da almundahana ta makudan kudade kuma za a iya yanke musu hukunci mai tsauri.

    Wakilin BBC ya ruwaito daga kakakin ma'aikatar tsaron kasar Jan Sha Gong cewa janarar din da sauran mutun 8 sun karya ka'idojin jam'iyyar.

    Korar da aka yi wa Janarar He ita ce ta farko da zaa yi wa wani janarar da ke aiki a hukumar kula da sojojin kasar, a cikin shekaru hamsin da suka gabata

  9. An rantsar da sabon shugaban Madagascar

    An rantsar da Kanar Michael Michael Randrianirina a matsayin shugaban ƙasar Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar.

    Bayan ya sha rantsuwar kama aiki kanal Randrianirina ya ce abubuwan da zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ruwan sha da abinci da kuma kafa gwamnati.

    Sanye da tufafin fafar hula Kanal Randrianirina ya ce sojoji ba za su jagoranci gwamnatinsa ba , farar hula ne za su yi hakan amma kuma ya ce gudanar da zaɓuka a cikin kwanaki 60 kamar yadda kundin tsarin mulki da aka dakatar a yanzu ya tanada, ba zai yu ba

  10. Ƙungiyoyin agaji sun yi kira ga Isra'ila ta su damar shiga arewacin Gaza

    Ƙungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga Isra'ila ta ba su damar shiga arewacin Gaza, inda aka ayyana yunwa a watan Agusta, domin raba kayan agaji a yankin.

    Ƙofofin shiga yankin sun kasance a rufe, duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma.

    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai abinci da dama da ke shiga kudancin Gaza, amma ba su samu damar shiga arewaci domin raba abincin ba.

    WFP ya ce abubuwan fashewar da ke binne a yankin na yi musu barazanar shigar da kayayyakin zuwa yankin arewacin.

  11. An rantsar da Randrianirina a matsayin shugaban Madagascar

    An rantsar da laftanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban ƙasar Madagascar, inda ya bayyana cewa samun mukaminsa ba juyin mulki ba ne saboda kotun tsarin mulki ta amince.

    Bayan rantsar da shi, ya ce manyan abubuwan da zai mayar da hankali a kai sun haɗa da samar da ruwa da abinci, da kuma kafa gwamnati.

    Sanye da tufafin farar hula, Randrianirina ya ce gwamnatinsa ba ta soja ba ce, za ta kasance karkashin jagorancin farar hula amma ya ce yiwuwar gudanar da sabon zaɓe cikin kwana sittin, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, ba laile ya faru ba.

    Ya samu wannan mukami ne sakamakon yadda sojoji suka shiga zanga-zangar da ta tilasta tsohon shugaban, Andry Rajoelina, tserewa daga Madagascar.

  12. An kori wasu manyan sojojin China daga jam'iyyar kwamunisanci

    Ma'aikatar harkokin tsaron China ta ce an kori wasu manyan jami'an soji ciki har da mutum na biyu mafi girman muƙami - Janar He Weidong - daga jam'iyyar Kwamunisanci mai mulkin ƙasar.

    Ma'aikatar ta ce matakin korar tasu na da alaƙa zambar kuɗaɗe masu yawa da ake zargin hannunsu a ciki.

    Janar He ya kasance babban janar na farko da aka dakatar daga jam'iyyar cikin shekara 50 da suka gabata.

    Haka kuma korar tasa na da tasiri a siyasance kasancewar yana cikin majalisa ƙolin ƙasar.

  13. Ina fatan ganawarmu da Putin za ta kawo ƙarshen yaƙin Ukraine - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana fatan tattaunawar da suka shirya yi da Putin a birnin Budapest na ƙasar Hungary, za ta taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

    Firaiministan Hungary, Viktor Orban ya ce tuni aka fara shirye-shiryen ganawar bayan wayar da ya yi da Mista Trump.

    Nan gaba a yau ne Mista Trump zai gana da Shugaba Zelensky an Ukraine a Fadar White House.

    Ana sa ran zai sake kira ga Mista Trump ya amince Amurka ta sayar wa ƙasarsa makaman linzami masu cin dogon zango (da za su iya kai wa cikin Rasha).

    Wakilin BBC a Amurka ya ce Rasha na iya jan ra'ayin Mista Trump kada ya sayar wa Ukraine makaman.

    Fadar Kremlin ta ce Putin ya gargaɗi Mista Trump cewa matakin zai iya kawo illa a dangatakar Rasha da Amurka.

  14. A lokacina wanda ya faɗi zaɓe zai taya wanda ya yi nasara murna - Amupitan

    Sabon shugaban hukumar zaɓen Najeriya, Farfesa Joash Amupitan, SAN ya alƙawarta cewa a ƙarƙashin jagorancinsa, INEC ta za shirya sahihi kuma karɓaɓen zaɓe a ƙasar.

    Yayin da yake jawabi bayan majalisar dattawan ƙasar ta amince da shi, Farfesa Amupitan ya ce a zamanin mulkinsa zai tabbatar da cewa wanda ya faɗi zaɓe ya taya wanda ya yi nasara murna, saboda ingancin zaɓen.

    Sabon shugaban ya ce zai yi aiki tare da sauran hukumomi, kamar hukumar bayar da katin ɗanƙasa, domin tabbatar da komai ya fi daidai.

    “Babban burinmu shi ne yin sahihai kuma ingantattun zaɓuka da kowa zai amince da su ta yadda wanda ya yi rashin nasara sai ya kira wanda ya yi nasara da kansa domin taya shi murna'', kamar yadda ya shaida wa ƴanmajalisar.

    Amupitan ya maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar.

  15. Zelesnky ya isa Amurka don ganawa da Trump

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya isa birnin Washington domin ganawa da takwaransa na Amurka, Donald Trump.

    Ganawar tasu na zuwa ne kwana guda bayan Mista Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin -- sun amince su gana a Hungary domin tattauna batun kawo ƙarshen yain Ukraine.

    Yayin da ya isa Amurka, Mista Zelensky ya ce Rasha na gaggawar cimma yarjejeniyar ne da nufin dakatar da Amurka daga bai wa Ukraine makamin yaƙi mai linzami na Tomahawk mai cin dogon zango.

    A ranar Juma'a ya gana da wakilan kamfanin da ke ƙera makamin.

    Amma Mista Trump ya dasa shakkun yiwuwar samun makamin ga Ukraine, yana mai cewa Amurka ba za ta so yaɗuwar makaman ba.

  16. Gwamnonin jam'iyyar APC na taro a jihar Kebbi

    Gwamnonin jam'iyyar APC na gudanar da wani taron sirri a jihar Kebbi da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar.

    Rahotoni daga jihar ne cewa aƙalla gwamnoni 20 daga cikin gwamnoni 24 na jam'iyyar ke gudananar da taron ƙarƙashin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, wanda shi ne gwamnan jihar Imo.

    Ana sa san ran gwamnonin za su tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa.

    Taron gwamnonin APCn na zuwa ne kwanaki bayan gwamnan jihar Enugu ya koma jam'iyar daga PDP.

  17. Amnesty ta nemi a soke hukuncin kisa a Najeriya

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya su soke hukuncin kisa a ƙasar.

    Manajar shirye-shirye ta ƙungiyar, Mrs Barbara Magaji ce ta bayyana hakan a Abuja lokacin da take jawabi a taron masu ruwa da tsaki a Ranar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya.

    Ƙungiyar ce dai ta shira taron da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Faransa a ƙasar.

    Mrs Barbara Magaji ta buƙaci a cire dokokin da suka tanadi hukunce-hukuncen kisa daga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma dokokin wasu jihohin ƙasar.

    Ta ce ya kamata majalisar dokokin ƙasar ta duba yiwuwar soke hukuncin kisa ga duka manyan laifukan da aka tanadar wa hukuncin a kundin tsarin mulkin ƙasar.

    “Babu wata hujja da ke nuna cewa hukuncin kisa na rage aukuwar manyan laifukan'', in ji ta.

    A yanzu haka dai jihohin ƙasar 26 da Abuja ne suke da dokokin da suka tanadin hukuncin kisa ga laifukan da suka shafi garkuwa da mutane da fashi da satar shanu da tsafi.

    “Duk da tanadin hukuncin kisa a waɗannan jihohin, amma kullum ana ci gaba da samun ƙaruwar irin waɗannan laifukan, musamman garkuwa a mutane da fashi da ma sauran laifukan.''

  18. Saudiyya ta rage wa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2026

    Hukumar Alhazan Najeriya ta bayyana damuwarka kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa ƙasar wani kaso mai yawa na kujerun aikin Hajjin da aka ware mata.

    NAHCON ta yi gargaɗiin cewa matakin zai hana mutane da dama zuwa aikin Hajjin a shekara mai zuwa.

    Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce hukumomin Saudiyya sun sanar da NAHCON cewa wuraren kwanan mutum 66,910 kawai aka keɓe wa ƙasar, wani abu da ke nuna adadin maniyyatan da aka ware wa Najeriyar.

    “Wuraren kwanan da aka keɓe wa maniyyatan Najeriya a 2026 shi ne 66,910, da suka haɗa da na hukumomin alhazai na jihohi 51,513 da sauran jami'an hukumar, yayin da aka ƙebe wurare 15,397 ga kamfanonin shirya tafiye-tafiye'', in ji sanarwar.

    Hukumar ta NAHCON ta ce hukumomin Saudiyyar sun ɗauki matakin ne saboda Najeria ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a shekarar 2025.

    NAHCON ta ce a shekarar da ta gabata an samu kujeru 35,872 da ba a cike su ba.

    Ƴan ƙasar da dama sun alaƙanta rashin cike kujerun da tsadar kuɗin hajjin da aka samu a 2025.

    Matakin Saudiyyar na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci hukumar NAHCON ta rage kuɗin aikin hajjin 2026.

  19. Hamas ta ce a shirye take ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Hamas ta ce a shirye take ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila kuma tana son mayar da sauran gawarwakin mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza.

    BBC ta fahimci cewa Hamas ta ba masu shiga tsakani bayanai da hotunan wuraren da gawarwakin suke.

    Isra'ila dai na barazanar sake ci gaba da yaƙi a zirin Gaza idan har ƙungiyar Hamas ta gaza miƙa mata sauran gawarwakin mutum 19.

    A baya dai shugaba Trump ya yi watsi da duk wata barazana ga yarjejeniyar da ya jagoranta amma ya yi gargaɗi ga Hamas cewa za ta ɗanɗana kuɗarta idan har aka ci gaba da zubar da jini

  20. Assalam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke i mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyu mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.