Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 14/11/2025.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Gwamnatin sojin Mali ta dakatar da wasu gidajen talbijin Faransa

    Gwamnatin mulkin sojin Mali ta dakatar da wasu gidajen talbijin biyu na Faransa a ƙasar daga bayar da rahotonnin ayyukan masu iƙirarin jihadi.

    Hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labaran ƙasar, ta ce shirye-shiryen da gidajen biyu suka yaɗa sun ƙunshi cewa zargin cewa masu iƙirarin jihadi na dab da shiga Bamako, babban birnin ƙasar.

    Haka ma an zargi kafafen biyu da ƙaryar cewa gwamnati ta hana sayar da man fetur.

    A watannin baya-bayan nan, masu iƙirarin jihadi na kai hare-hare kan tankokin dakon mai da ke ɗauko man fetur zuwa Mali, lamarin da ya haifar da ƙarancinsa a faɗin ƙasar.

    Masu iƙirarin jihadin sun kuma ƙwace iko da wasu yankunan arewaci da gabashin Mali, duk kuwa da wanzuwar sojojin hayar Rasha a ƙasar.

    A shekarar 2020 ne dai soljoji suka ƙwace mulki a Mali a wani juyin mulki, tare da alƙawarin maido da tsaro a ƙasar.

    Sai dai bisa ga alama har yanzu matsalar na neman gagarar kundila.

  2. Shugaban Afirka ta Kudu ya ce za a yi bincike kan zuwan wasu Falasɗinawa ƙasar

    Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ce za a gudanar da bincike kan wani jirgi da aka yi shatarsa zuwa ƙasar ɗauke da Falasɗinawa fiye da 150 daga Gaza

    Falasɗinawan, da suka haɗa da iyalai da ƙananan yara, ba a ba su damar yin bulaguron na tsawon sa'a 10 zuwa ƙasar ba, sakamakon rashin sahihin hatimi a kan takardun izininsu.

    An dai ba su damar zama a ƙasar ne bayan shiga tsakani da wata ƙungiyar bayar da agaji ta yi.

    23 cikin mutunen sun fice daga ƙasar zuwa wasu ƙasashen yayin da sauran suka zauna a ƙasar.

    Kawo yanzu ba a san yadda zuka baro Gaza ba.

    Hukumomin Isra'ila sun ce mutanen sun fice daga Gaza ne bayan samun amincewar wata ƙasa ta daban.

    To amma ba ta fayyace sunan ƙasar ba.

  3. Gwamnan Kano zai gabatar da kasafin kuɗin tiriliyan ɗaya a 2026

    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai gabatar da kasafin kudin jihar na 2026 da ya kai naira tiriliyan ɗaya mafi yawa a tarihin jihar.

    Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin wani zama na musamman kan kasafin kuɗin 2026.

    Sanarwar ta ce a mako mai zuwa ne ake sa ran gwamnan zai gabatar da kasafin ga gaban majalisar dokokin jihar domin yin muhawara a kai.

    Wannan ne karo na farko da jihar za ta kashe kuɗi mafiya yawa a kasafin kudin ƙasar.

    Gwamnan Abba Kabir ya kuma danganta ƙaruwar kuɗin kasafin da yadda aka samu bunƙasar hanyoyin tara kuɗin shigar jihar a cikin gida.

    “Gwamnatinmu ta ƙarfafa hanyoyin tara kudin shiga a cikin gida tare da toshe hanyoyin da kudaɗen ke zurarewa, inda hakan ya ba mu damar yunƙurin aiwatar da manyan ayyuka a 2026,'' in ji gwamnan.

    Abba Kabir ya ce kasafin kuɗin wannan shekara zai mayar da hankali kan noma da ilimi da kiwon lafiya tare da ƙarfafa matsakaita da ƙananan sana'o'i.

  4. Cutar Marburg ta kashe mutum shida a Ethiopia

    Wata cuta da ta ɓarke a ƙasar Ethiopia da ake kyautata zaton cutar Marburg ta kashe mutum aƙalla shida.

    Wannan ne karon farko da cutar da Marburg ta ɓulla a ƙasar.

    Hukumar Lafiya da Duniya ta ce cutar na da matuƙa illa ga ɗan'adam.

    Shugabar hukumar ta WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yaba wa hukumomin ƙasar kan abin da ya kira matakan daƙile cutar da suka ɗauka.

    WHO ta bayar da tallafin dala 300,000 da ƙwararru domin taimaka wajen daƙile cutar.

    Ana kamuwa da cutar daga tsuntsayen da ke cin kayan marmari, sannan tana yaɗuwa tsakanin mutane ta hanyar haɗa jiki.

  5. Musulmai ne suka fara shan uƙubar Boko Haram - Shugaban AU

    Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar AU, Mahmoud Youssouf ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa an keɓance kiristocin arewacin ƙasar da kashe-kashen ƴanbindiga.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a shalkwatar MDD da ke birnin New York, Mista Youssouf ya ce matsalar tsaron da ake fama da ita a arewacin Najeriya ba kisan kiyashi ba ne.

    A baya-bayan nan ne dai Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya kan abin da ya kira aikata kisan kiyashi kan Kiristocin ƙasar.

    Sai dai shugaban gudanarwar na AU ya ce al'ummar Musulmai ne mutanen farko da suka fara ɗanɗana uƙubar Boko Haram.

    “Mutanen farko da suka fara fuskantar wahalar Boko Haram, Musulmai ne, ba Kiristoci ba, kuma ina faɗar haka ne da hujjojin da ke rubuce'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ƙungiyar AU na yawan fayyacewa a rahotonninsu cewa babu batun kisan kiyashi a arewacin Najeriya.

  6. Dangantaka tsakanin Japan da China na ƙara muni

    Rashin jituwar da ke tsakanin Japan da China kan Taiwan na ƙara muni, bayan da Japan ta miƙa wa jakadan China da ke ƙasarta sammaci domin nuna ɓacin ranta kan kalaman da ɗaya daga cikin abokan aikinsa ya faɗi.

    Babban jami'in diflomasiyyar China a Japan, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sada zumunta, wanda ake ganin shaguɓe ne ga Firai ministar Japan, Sanae Takaichi wadda a makon da ya gabata ta ce Japan za ta mayar da martani kan duk wani hari da aka kai wa Taiwan.

    China ta kuma ce za ta murƙushe Japan.

  7. Tinubu ya tsawaita wa'adin Buba Marwa a shugabancin NDLEA

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tsawaita wa'adin Buba Marwa a matsayin shugaban hukumar NDLEA mai yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Juma'a, ta ce Shugaba Tinubu ya amince da da ƙarin wa'adin shekara biyar ga Buba Marwa.

    Tsohon shugaban Najeriya, Marigari Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a watan Janairun 2021.

    Amincewa da tsawaita wa'adin Marwa - wanda tsohon gwamnan soji na jihohin Lagos da Borno ne - na nufin zai kasance shugaban hukumar NDLEA har nan da 2031.

  8. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta umarci PDP ta bai wa Sule Lamido damar yin takarar shugabanci

    Babbar kotun tarayya a Najeriya ta umarci jam'iyyar adawa ta PDP ta bai wa tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido damar shiga takarar shugabancin jam'iyyar.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Mai Shari'a Peter Odo Lifu na cewa kuskure ne PDP ta hana Lamido damar sayen tikitin takarar.

    Baya ga haka, kotun ta umarci PDP ta dakatar da taron na Asabar saboda gazawa wajen wallafa jadawalin taron a kan lokaci domin sanar da 'ya'yanta kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.

    Wannan ne umarnin kotu na uku da ke hana PDP yin taron, wanda zai ba ta damar zaɓen sababbin shugabanni a mataki na ƙasa.

    Sai dai jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Umar Ilya Damagun ta ce ba za ta fasa ba saboda ita ma akwai ktoun da ta bayar da umarnin ta ci gaba da shirin gudanar da taron.

  9. 'Yanfafutika sun kai ƙarar Wike majalisar Birtaniya

    Wata gamayyar masu fafutika da rajin tabbatar da dimukuradiyya a Najeriya sun rubuta wa ‘yanmajalisar dokokin Birtaniya wasiƙa game da zargin Ministan Abuja Nyesom Wike da yunƙurin durƙusar da tsarin.

    A cikin wasikar, 'yan gwagwarmyar sun zargi gwamnatin APC da yin amfani da Mista Wike wajen karya lagon ‘yan'adawa tare da yunƙurin mayar da ƙasar mai bin jam’iyya daya.

    Sun kuma buƙaci ƙasashen Birtaniya da Amurka su ɗauki tsauraran matakai kan ministan da masu taimaka masa domin kyautata mulkin dimukuraɗiyya.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Bashir Zubairu Ahmad:

  10. MDD za ta fara binciken kisan ƙare-dangi a El-Fasher na Sudan

    Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kaddamar da bincike a hukumance kan zargin kisan ƙare-dangi da aka yi a birnin El-Fasher na Sudan a watan da ya gabata.

    Yayin da aka soma wani taron gaggawa, shugaban hukumar Volker Turk ya fada wa taron cewa lamarin da ya faru abu ne da za a iya hasashen faruwarsa kuma a kauce masa.

    Ya ce zalincin da aka yi a El-Fasher abin kunya ne ga kasashen duniya.

    Volker Turk ya ce wajibi ne ƙasashen duniya su ɗauki mataki kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni da ke rura wutar yaƙin kuma su ke amfana da shi.

    Ana zargin mayakan RSF din sun kashe aƙalla mutum 2,000.

  11. 'Yansandan Kaduna sun kama mutum uku da zargin safarar yara

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta kama mutum uku da zargin satar yara tare da ceto wasu yaran 17 a garin Zariya.

    Kakakin rundunar SP Mansir Hassan ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an kama mutanen ne bayan tattara bayanan sirri kan wasu yara da aka gani a ƙarƙashin Gadar Danmagaji.

    Ya ce jami'an rundunar da suka far wa wurin sun gano yara masu shekaru daban-daban da ake shirin safarar su zuwa Abuja babban birnin Najeriya da wasu yankunan ƙasar.

    Rundunar ta ce mutanen da take zargi sun fito ne daga jihohin Katsina da Kano, kuma a cewarta sun amsa laifukan lalubo yaran daga sassa daban-daban da zimmar kai su Abuja.

  12. Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe mayaƙan Iswap tara a jihar Borno

    Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan ƙungiyar Iswap tara masu iƙirarin jihadi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis ta ce dakarun rundunar Desert Sernity ne suka gwabza da "yanta'addan" a yankin Yanaga Ari na ƙaramar hukumar Mafa ranar Laraba.

    "Yayin fafatawar, an kashe 'yanta'addan kuma aka ƙwace bindigar AK-47 da adakokin harsasai masu yawa," in ji sanarwar da Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar.

    A ranar ne kuma rundunar ta ce ta yi nasarar tserartar da masu yi wa ƙasa hidima 74 daga barazanar garkuwa da su daga 'yan Boko Haram bayan motarsu ta lalace a jihar ta Borno.

  13. Tinubu ya karɓi shawarwarin sojoji kan matsalar tsaron Najeriya

    ‎Shugaban MNajeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan ƙasar 'Yan Aji na 33 a kwalejin horon soja ta National Defence College (NDC) a ranar Alhamis.

    Da yake jawabi bayan karɓar rahoton, Tinubu ya ci alwashin yin nazari kan shawarwarin da suka bayar game da yadda za a shawo kan matsalar tsaron ƙasar.

    "Dole ne mu ci gaba da gina Najeriya, kuma haƙƙinmu ne samar da mafita daga shawarwarin da kuka bayar," in ji shi.

    Shawarwarin nasu na zuwa ne daidai lokacin da ake fargaba da kuma tafka muhawara game da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump ta kutsawa Najeriya domin kare Kiristocin ƙasar bisa iƙirarin da ya yi - ba tare da hujja ba - cewa ana yi musu kisan gilla.

    Kwamandan kwalejin, Rear Admiral Abdullahi Ahmed, ya ce Aji na 33 ya ƙunshi ɗalibai 99, ciki har da jami'ai 25 na sojan ƙasa, 16 daga sojan ruwa, 12 daga sojan sama, biyar daga rundunar 'yansanda, 18 daga ma'aikatun gwamnati.

  14. Ukraine ta ce hare-haren Rasha sun kashe mutum uku a Kyiv

    Rasha ta kaddamar da wani harin makami mai linzami da kuma jirage marasa matuka a Kyiv babban birnin Ukraine da ma wasu yankuna na kasar.

    Rundunar sojin kasar ta ce hare-haren sun kashe akalla mutum uku sannan wasu 12 suka ji raunuka a da aka kai a Kyiv.

    Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Telegram, magajin garin birnin na Kyiv, Vitaly Klitchko, ya ce wasu sun ji rauni ne bayan baraguzan gini sun rufta a kansu sakamakon wani harin da ya faɗa kan wani gida mai hawa biyar.

  15. Wakilan PDP sun fara isa Ibadan kafin babban taronta

    Wakilai sun fara isa garin Ibadan na jihar Oyo a kudancin Najeriya domin halartar babban taron jam'iyyar PDP mai adawa mai cike da cecekuce, kamar yada rahoton jaridar Daily Trust ya ruwaito.

    Mazauna birnin sun shaida wa jaridar cewa tun daga ranar Alhamis yanayi ya fara sauyawa saboda baƙin da ke karakaina domin taron da za a gudanar gobe Asabar da kuma Lahadi.

    PDP ƙarƙashin shugabancin Umar Damagun ta haƙiƙance cewa taron zai gudana yadda suka tsara duk da umarnin kotuna biyu da ya ce a dakata, yayin da ɓangaren da ke biyayya ga Ministan Abuja Nyesom Wike ke adawa da shi.

    A gefe guda kuma, wasu daga cikin 'yan jam'iyyar na neman a kafa kwamatin riƙo domin sasanta rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam'iyyar.

    "Abin da ya kama ku sani shi ne za mu gudanar da taron nan, babu wata maganar kwamatin riƙo, ba mu tanadi komai game da hakan ba," kamar yadda shugaban riƙo na sashen kudu maso kudu, Elder Emmanuel Ogidi, ya faɗa wa Daily Trust.

    Wakilan za su zaɓi sababbin shugabanni a matakin ƙasa kan muƙamai daban-daban, ciki har da shugaba na ƙasa.

    A yau Juma'a ake sa ran wata kotu za ta bayar da nata hukuncin kan ƙarar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya shigar yana mai ƙorafin hana shi tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar.

  16. BBC ta nemi afuwar Trump kan yadda ta gabatar da fim a kansa

    BBC ta bai wa Shugaban Amurka Donald Trump haƙuri kan yanke wani ɓangare na jawabinsa game da tarzomar da magoya bayansa suka yi a majalisar dokokin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa, BBC ta ce bidiyon da aka nuna ya nuna kamar Shugaba Trump ya yi kira da a kai hari kan majalisar ta Amurka, wanda kuma hakan kuskure ne.

    Sai dai BBC ta yi watsi da batun bukatarsa na biyan diyya tana mai cewa babu wata hujja ta ɓata suna a cikin bidiyon.

    Tuni lauyoyin Mista Trump suka yi barazanar gurfanar da BBC a kotu kan rashin biyan diyyar.

  17. Maraba

    Barkanmu da hantsin Juma'a, barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo rahotonni na abubuwanda ke faruwa daga sassan duniya daga yanzu har zuwa 10,00 na daren yau.

    Umar Mikail ne zan fara kawo rahtonnin zuwa ƙarfe 4:00.