Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/12/2024
Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Manyan jami'ai daga Amurka da Turkiyya da kuma wasu ƙasashen Larabawa sun goyi bayan kafa sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali a Syria.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken wanda ya goyi bayan sanarwar ministocin, ya ce Washington ta fara tattaunawa da ƴan tawayen da suka ƙwace gwamnati a Syria, kuma za su yi aiki domin tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce a wannan yankin da ma wasu wurare, mun ga yadda hamɓarar da gwamnati ke buɗe kafar tashin hankali da rikici.
Su ma ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa sun yi Alla-wadai da yadda Isra'ila ta yi kutse cikin Syria a daidai lokacin da ake neman mafita.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ƙaddamar da jirgin ruwa mai samar da mai a Dubai.
Jirgin, mallakin kamfanin Oriental Energy zai iya adana ganga miliyan ɗaya na man fetur, kuma zai fara ne da samar da ganga 17,000 a rana kafin ya ƙara zuwa ganga 30,000. Ana kuma sa ran jirgin zai iso Najeriya a farkon shekarar 2025.
Shettima wanda ya wakilci shugaban Bola Tinubu wajen ƙaddamarwar a Dubai, ya ce hakan wani babban ci gaba ne aka samu a ɓangaren mai da kuma ƙara karfin tasirin Najeriya a duniya.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce abin da ya sa Najeriya ta ƙere wa wasu ƙasashe shi ne ganin yadda ta fahimci inda duniya ta dosa.
"Jirgin ruwan na samar da mai babban ci gaban fasaha ne, kuma hakan ya nuna zimmar Najeriya na shiryawa buƙatun da duniya ke so. Karkashin jagorancin shugaba Tinubu, muna ganin sauye-sauye da dama a ɓangaren mai da iskar gas, wanda shi zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin mu," in ji Shettima.
An bayyana cewa darajar jirgin ruwan mai samar da mai ya kai dala miliyan 315.
Ƴan sandan Brazil sun kama tsohon ministan tsaron ƙasar wanda kuma ya kasance ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar, Walter Braga Netto.
An tsare shi a Rio de Janeiro, inda aka yi bincike gidansa kafin a miƙa shi hannun sojoji.
Ana zargin mista Braga Netto da hannu a yunkurin juyin mulki na shekara ta 2022 da niyyar ganin shugaban ƙasar da ya sha kaye Jair Bolsonaro, ya ci gaba da zama kan mulki.
Ya kasance mataimaki ga mista Bolsonaro a zaɓen da shugaba Lula da Silva ya samu nasara.
An zargi mista Bolsanaro da gomman masu taimaka masa kan yunkurin juyin mulki.
Liverpool ta tashi 2-2 da ƙungiyar kwallon kafa ta Fulham a wasan mako na 16 da suka kara a Anfield.
Fulham ce ta fara cin kwallo ana minti 11 da fara wasa ta hannun Andreas Pereira.
Jim kaɗan ne kuma alkalin wasa ya kori ɗan wasan Liverpool Robertson bayan da ya taka Harry Wilson na Fulham.
Sai dai yaran Arne Slot sun koma da karfinsu bayan hutun rabin lokaci, inda suka farke kwallon da aka ci su ta wajen Cody Gakpo.
Amma Rodrigo Muniz ya kara saka Fulham a gaba a minti na 76 da kwallon da ya ci.
Haka aka yi ta fafatawa har sai ana daf da tashi, Diogo Jota ya sake farke kwallon da aka ci Liverpool, inda aka tashi wasan 2-2 duk da cewa ƙungiyar ta Anfield ta kare da ƴan wasa 10.
Hukumar zaɓe a Najeriya INEC, ta yi watsi da rahotanni da ake yayatawa kan mutuwar shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar, wanda ya samu sa hannun sakataren yaɗa labaran shugaban, Rotimi Oyekanmi, ya ce labarin kanzon kurege ne.
Sanarwar ta ce: "hankalin mu ya kai ga labaran karya da ake yaɗa wa a kafafen sadarwa da ke iƙirarin cewa shugaban hukumar zaɓen Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya mutu a wani asibiti a birnin Landan. Wannan ba gaskiya bane," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce mutane su yi watsi da labarin mutuwar shugaban na INEC, inda ta ce yana cikin koshin lafiya, kuma bai ma yi wata tafiya zuwa birnin Landan ba a cikin shekaru biyu da suka wuce.
An dai fara yayata batun mutuwar Farfesa Yakubu a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba a kan kafofin sada zumunta.
Sai dai INEC ta ce shugaban nata ya ma halarci wani zama da kwamitin majalisar wakilai kan ɓangaren zaɓe ranar Laraba, 11 ga Disamban 2024.
Hukumar tabbatar da tsaro da kare hakkin al'umma ta Civil Defense ta ce ta gano wani gida da ake ɓoye haramtaccen mai a jihar Ribas.
Gidan wanda ke karamar hukumar Obio/Akpo na jihar, an gano yana ɗauke da tankokin ajiya da dama da kuma jarakuna, cike da ɗanyen mai da aka sato.
Kwamandan hukumar ta Civil Defense a jihar, Joachim Okafor wanda ya jagoranci tawagar hukumar zuwa wurin, ya bayyana cewa sun samu nasarar gano wurin ta hanyar amfani da wata fasaha da ke bin diddigin irin waɗannan wurare da ake ajiye haramtaccen mai.
Okafor ya ce ayyukan masu satar ɗanyen mai, na janyo babban barazana ga muhalli da kuma lafiyar al'ummar.
Majalisar dokokin Geogia mai cike ta taƙaddama ta naɗa tsohon ɗan ƙwallon Manchester City, a matsayin shugaban ƙasar.
Matakin na zuwa ne bayan shafe kwanaki 17 ana zanga-zangar goyon bayan shigar kasar ƙungiyar EU manyan birane da garuruwan ƙasar.
Mikheil Kavelashvili, mai shekara 53, tsohon ɗan majalisa ne daga jam'iyya mai mulki , kuma shi kaɗai ne ya nuna sha'awar muƙamin.
A ranar Asabar wakilan masu zaɓe 224 daga cikin 225 suka zaɓe shi a matsayin.
To sai dai manyan jam'iyyun hamayya huɗu - waɗanda suka ƙaurace wa zaman majalisar - sun yi watsi da naɗin Kavelashvili, inda suka dage cewa an murɗe zaɓen da aka yi cikin wata Octoba.
Tun da farko shugabar ƙasa ta yanzu, Salome Zourabichvili, ta ƙi sauka daga kan karagar mulki inda ta ce ba za ta amince da nasarar da jam'iyyar Georgia Dream ta samu a zabukan baya-bayan nan ba.
Bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad da aka yi a Syria, Isra'ila tana kai hare-hare ƙasar.
Ko mene ne dalilan kai waɗannan hare-hare.
Ga wasu bayanai da muka tattaro
Hukumomi a Koriya ta Kudu sun tabbatar da naɗin firaministan Koriya ta Kudu a matsayin shugaban ƙasar na riƙo.
A jawabina na farko bayan naɗinsa, Han Duck-soo ya ce abin da zai mayar da hankali a kai shi ne ''daidaita al'amura a ƙasar tare da kwantar wa jama'a hankali''.
"A matsayina na ɗan'adam da ya damu da al'amuran ƙasarmu, ina amfani da wannan dama wajen bai wa mutanen Koriya haƙuri,'' in ji Han.
Shugaban riƙon ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin ƙasar ta inganta al'amuran ƙasar.
Aƙalla mutum uku ne suka mutu gommai suka jikkata bayan fashewar wani abu da aka jefa cikin dandazon jama'ar da ke halartar wani biki a Thailand.
Lamarin ya faru ne cikin tsakar daren da ya gabata, a lardin Tak da ke arewacin ƙasar.
'Yansanda dai sun kama mutum biyu, sai dai babu wata tuhuma da aka yi musu zuwa yanzu, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.
Ƙalla mutum 48 ne suka jikkata, ciki har da mutum shida da suka samu munanan raunuka, a cewar 'yansandan.
Cikin wata sanarwa da tawagar aikin ceton ta fitar, ta ce an jefa abin fashewar ne a ƙasa a kan dandamalin da masu bikin ke rawa.
Tuni dai aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Firaministar ƙasar, Paetongtarn Shinawatrata jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta umarci jami'an 'yansanda su yi bincike kan musabbabin aukuwar lamarin.
Jaridar Bangkok Post da ake wallafa wa a shafin intanet ta ce akwai mutum 8,000 zuwa 9,000 a wurin bikin lokacin da fashewar ta faru.
Hukumomin Koriya ta Kudu sun dakatar da shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol a hukumance.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an dakatar da shugaban ƙasar daga ayyukan ofishinsa.
Matakin na zuwa ne bayan da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar tsige shi ɗazu-ɗazun nan.
Shugaban Koriya ta Kudu ya ce zai tsayar da ayyukansa na wucin gaɗi.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Mista ya ce ''zai dakata da ayyukansa na wucin gadi'', bayan majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige shi.
"Na yi tunanin dakatawa a yanzu, amma gina ƙasarmu da na faro kusan shekara biyu da rabi ba zai tsaya ba. Ba zan haƙura ba. Zan jurewa shan suka da yabo da goyon daga gare ku, kuma har zunciyata na ƙudiri aniyar bauta wa ƙasarmu har ƙarshen mulkina,'' in ji sanarwar
Kakakin majalisar dokokin Koriya ta Kudu, Woo Won-shik, ya ce za a dakatar da shugaban ƙasar ne da zarar majalisar dokokin ƙasar ta kai masa kwafin takardun tsige shi, shi da kotun tsarin mulkin ƙasar.
Firaministan ƙasar, Han Duck-soo na dab da karɓar ragamar jagorancin ƙasar.
Ko da an dakatar da shi, Mista Yoon zai ci gaba da zama a ofishinsa har zuwa lokacin da kotun tsarin mulkin ƙasar za ta ɗauki matsaya kan matakin majalisar na tsige shi.
Dubban masu zanga-zangar kiran tsige shugaban Koriya ta Kudu da suka taru a wajen ginin majalisar dokkin ƙasar, sun ɓarke da sowa bayan da majalisar ta kaɗa kuri'ar amincewa da tsige shugaban.
Mutanen sun yi ta rera waƙoƙin kishin ƙasa da dimokraɗiyya.
Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Kashim, ya sauka daga muƙaminsa.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Muktar Gidado ya fitar ranar Juma'a da maraice.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan jihar Bala Mohammed ya amince da murabus ɗin sakataren gwamnatin nasa, tare da gode masa bisa aikin da ya yi da gwamnatinsa.
“Gwamna ya umarci shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jiha, Dakta. Aminu Gamawa, ya riƙe muƙamin a matsayin riƙo'', in ji sanarwar.
A yayin da 'yan majalisar dokokin Koriya ta Kudu suka kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar, yanzu ya rage wa kotun tsarin mulin ƙasar ta tabbatar da matakin.
Tsige shugaban ƙasa na dindindin kan ɗauki makonni a ƙarƙashin dokokin ƙasar, saboda dole ana buƙatar sauraron batun a gaban kotun tsarin mulkin ƙasar.
Kotun na da alƙalai tara, don haka ana buƙatar amincewar shida daga cikinsu domin tabbatar da tsigewar ta dindindin.
Idan hakan ta tabbata, za a shirya zaɓen sabon shugaban ƙasa cikin kwanaki 60 bayan hukuncin kotun.
Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol.
'Yan majalisa 204 ne suka goyi bayan ƙudirin a zaman majalisar da aka gudanar yau Asabar
Hakan na nufin mista Yoon zai gaggata barin ofishin shugaban ƙasar, kuma firaminista ƙasar zai jagoranci ƙasar a matsayin shugaban riƙo.
Dubban jama'a na taruwa a wajen majalisar dokokin Koriya ta Kudu gabanin ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar.
Kwanaki 11 ke nan da Shugaba Yoon Suk Yeol ya harzuƙa ƙasar bayan furka kalaman ayyana dokar mulkin soji.
Mista Suk Yeo ya ƙi yin murabus duk kuwa da kiraye-kirayen hakan da matsin lamba da yake shan kan ya yi hakan.
Abin da ya sa ‘yan majalisar suka tilasta masa sauka daga muƙamin a wannan lokaci.
Yunkurin farko na tsige shi dai ya ci karo da cikas, bayan da ƴan majalisar jam’iyya mai mulki suka ƙaurace wa ƙuri'ar tsige shin da majalisar ta kaɗa.
Sai dai wasu ‘yan majalisar sun ce wannan karon sun goyi bayan ƙudirin ganin yadda al'ummar ƙasar suka ƙara kafewa.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkan mu da wannan rana ta Asabar.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.