Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Lahadi, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.
Mu kwana lafiya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/04/2025
Abdullahi Bello Diginza
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Lahadi, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.
Mu kwana lafiya
Gidan talabijin na Turkiyya ya ruwaito cewa shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasar, Ibrahim Kalin ya gana da wakilan jagororin Hamas domin fahimtar halin da ake ciki a Gaza.
Rahotanni sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ayyukan jinƙai da zirin ke buƙata, da yiwuwar tsagaita wuta da kuma uwa-uba hanyoyin da za a bi domin dakatar da yunƙurin canja wa mutanen zirin matsuguni zuwa wasu ƙasashen daban.
Ms Kalin ya ya nanata wa wakilan cewa Turkiyya za ta cigaba da ba su gudunmuwa kamar yadda ta saba.
Tattaunawar ta zo ne a daidai lokacin da dangantaka take ƙara tsami tsakanin Turkiyya da Isra'ila, wanda ya samo asali daga saɓani da sojojin ƙasashen biyu suke samu a Syria.
Yantawayen Houthi a Yemen sun ce mummunan harin da Amurka ta kai sashen mai a bahar maliya ya haifar da gurɓacewar muhalli.
Ƙungiyar ta yi ikirari cewa man da ya kwarara sakamakon harin a tashar Ras la wanda ya kashe aƙalla mutum 80 zai iya lalata ruwan da ƙasar ke amfani da shi abin da zai sa a dakatar da kamun kifi.
Houthi ta nemi ƙasashen waje su taimaka mata wajen ɗaukar mataki.
Amurka dai ta zafafa hare-hare bayan ƙungiyar ta ɗauki alwashin cigaba da kai wa jiragen dako hare-hare a matsayin rashin nuna rashin jin daɗi game da hana shigar da kayan agaji Gaza da Isra'ila ta yi.
Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce ta damu ƙwarai game da yadda Islamabad ta tilasata wa ƴangudun hijirar Afghanistan ficewa daga Pakistan.
Cikin wata sanarwa da Taliban ta fitar bayan ganawarta da ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ta nemi a guji cin zarafin ƴan Afghanistan.
Mista Dar ya tabbatar wa jagororin Afganistan cewar za a duba ƙorafe-ƙorafen ƴangudun hijirar.
Islamabad ta ɗauki alwashin ƙara inganta tsaron iyakokinta a daidai lokacin da Pakistan ke cigaba da ƙaƙarin mayar da dubban ƴangudun hijira dafa Afghanistan waɗanda aka soke izinin zamansu a ƙasar.
Wakilin BBC ya ce dangantaka tsakanin Islamabad da shugabannin Taliban na Afghanistan ta yi tsami a baya-bayan nan, Pakistan ta zargi Kabul da goyon bayan ƴan taliban su kai hari iyakokinta, zargin da Kabul ta ƙaryata.
MDD ta ce fiye da rabin waɗanda aka tilasta wa ficewar yara ne ƙanana da suka haɗa da ƴan mata waɗanda Taliban ta hana ci gaba da karatu.
Ruwan sha na da matuƙar muhimmanci ga rayuwa. Hukumomin Duniya da dama sun bayar da shawarar cewa mata su riƙa shan aƙalla lita biyu na ruwa a kowace rana yayin da aka buƙaci maza su riƙa shan lita biyu da rabi.
To sai masana kimiyya na cewa ruwan da buƙa buƙatar sha ya danganta da wasu dalilai.
Rashin shan wadataccen ruwa kan haifar da rashn ruwa a jiki, to sai dai shan ruwan da yawa kuma kan zama matsala.
Ruwa shi ke samar da kashi 60 cikin 100 na nauyin jikinmu, yakan shiga cikin ƙwayoyin halitta da gaɓoɓi da jini da kuma hanyoyi masu yawa na jikinmu.
Tun bayan sanar da tsagaita wuta da shugaban Rasha Putin ya yi a yaƙinsa da Ukraine, wanda ya ce saboda bikin Easter ne, rahotanni na cewa ƙasashen biyu sun yi musayar fursunonin yaƙi.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce sun yi musayar fursunoni 246 da ƙasar Ukraine.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa an yi musayar waɗanda suka jikkata, inda Ukraine ta mayar da mutum 15, ta karɓo mutum 31 da suke jinya.
Rasha ta ce waɗanda ta karɓo da sukka jikkata ɗin za a kai su asibiti na musamman domin samun waraka daga raunukan da gyara tunaninsu.
A rubutun da ya wallafa a shafinsa na X, Zelensky ya bayyana komawar jami'an tsaron ƙasarsa guda 277 da "ɗaya daga cikin labarin masu daɗi da za a iya samu."
"Ina godiya ga duk waɗanda suka taimaka domin samun wannan nasarar, musamman Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bisa shiga tsakani.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya kai ziyarar aiki Vatican, inda zai gana da sakataren harkokin wajen hedkwatar ta Katolika, Pietro Parolin.
Mr Vance kirista ne da ya koma bin ɗarikar Katolika, kuma ana tunanin zai buƙaci ganawa da Fafaroma Francis.
Fafaroma Francis yana yawan sukar wasu matakan na gwamnatin Trump, musamman kan yaƙi da baƙin haure.
Cardinal Parolin ya ce a shirye yake ya yi aiki da gwamnatin Trump domin wanzar da zaman lafiya a duniya.
Rahotanni daga Rasha na bayyana cewa shugaban ƙasar Vladimir Putin ya sanar da tsagaita wuta a yaƙinsa da Ukraine saboda bikin Easter.
Har yanzu dai Volodymyr Zelensky bai ce komai ba, amma Rasha ta ce tana fata abokiyar karawarta Ukraine ma za ta amince da tsarin.
Ana tunanin Rasha za ta dakata da kai hare-haren da misalin ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfen 8 na daren 20 ga watan Afrilun, wanda tsakar dare ne a Moscow kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Sai dai har yanzu babu tabbacin ko wannan tsagaita wutar za ta buɗe sabon babin shiga yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.
Wannan ne zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yunƙurinsa na cire hannu a ƙoƙarinsa na samar da maslaha tsakanin ƙasashen biyu.
Amurka da Iran sun kammala tattaunawa karo na biyu kan shirinta nukiliyar ƙasar a birnin Rome.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce ''an samu gagarumin ci gaba'' a muhimman abubuwan da aka tattaunan - kodayake babu bayanin abin da aka cimma.
Ɓangarororin biyu sun amince da sake wata tattaunawa a mako mai zuwa.
An yi zaman na ƙeƙe-da ƙeƙe - da Oman ta shiga tsakani - da nufin samo hanyoyin da Iran za ta taƙaita shirin nukiliyarta.
Shugaba Trump ya sha gargaɗin ɗaukar matakin soji idan aka kasa daidaitawa ta hanyar diplomasiyya.
Hamas ta ce ta gano gawar mambanta da ke kula da ɗan Amurka asalin Isra'ilan nan, Edan Alexander da ƙungiyar ke garkuwa da shi a Gaza.
A farkon makon nan ne, ƙungiyar ta ce ba ta ji daga mayaƙanta da ke riƙe da mutumin ba bayan wani harin Isra'ila.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa tun daga lokacin ba ta ji labarin mayaƙin nata mai shekara 21 ba.
A makon da ya gabata ne ya bayayna cikin wani bidiyo da ƙungiyar ta fitar.
Isra'ila ta sha musanta kai hari kan wuraren da ta yi imanin ana tsare da Isra'ilawa a Gaza.
Jami'ai a Indiya sun ce aƙalla mutum 11 ne suka mutu bayan wani gini mai hawa huɗu ya faɗi a Delhi, babban birnin ƙasar.
Tawagar jami'an bayar da agajin gaggawa ta ƙasar na ci gaba da aikin lalubo waɗanda ke da sauran numfashi a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin da ke unguwar Mustafabad.
Mutane da dama ne suka jikkata a lamarin, waɗanda a yanzu ke asibiti domin samun kulawar likitoci.
Tuni hukumomi suka ƙaddamar da bincike domin gano abin da ya haddasa faɗuwar ginin.
Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta saka ranar Alhamis 24 ga watan Afrilu a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar, ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da kumar ta ce muhimman matakan da ta ɗauka da kuma dauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin.
Dr Fabian Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar - wadda ke ɗauke da muhimman bayanai dangane da jarrabawar.
Ya ƙara da cewa akwai bayanin wuri da lokacin mutum zai zana jarrabawar da sauran muhimman bayanai game da yadda tsarin zaman ɗakin jarrabawar zai kasance duka a jikin katin.
Dubban ɗaliban Najeriya ne ke rubuta jarrabawar JAMB a kowace shekara, domin samun damar shiga makaratun gaba da sakandire.
Shugaban riƙo na Syria, Ahmed al-Sharaa ya gana da wani ɗan majalisar Amurka a birnin Damascus, a wata ziyara ta farko da wani ɗan siyasar Amurka ya kai ƙasar tun bayan hamɓarar da gwamnatin Basahr al-Assad.
An bayar da rahoton cewa Cory Mills, wanda ɗan jam'iyyar Republican ne, ya tattauna da al-Sharaa kan batun takunkuman da Amurka ta sanya wa Syria da Iran.
Sabuwar gwamnatin Syria ta yi ta matsa lambar ganin an cire mata takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙa ba mata da maido mata da tallafin da aka dakatar tsawon shekara 14 da suka gabata.
Tun 2012 aka rufe ofishin jakadancin Amurka a birnin Damascus.
Fadar shugaban Najeriya, ta musanta wasu rahotonnin da ke zargin cewa an hana mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima shiga fadar shugaban ƙasar ta Villa.
A ƴan kwanakin nan an yi ta yaɗa jita-jitar cewa jami'an tsaro sun hana mataimakin shugaban ƙasar shiga fadar shugaban ƙasar.
To sai dai cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, da ke aiki da ofishin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce labarin ba shi da tushe balle makama, ''ƙarya ce tsagwaronta da aka shirya domin nuna wa jama'a cewa akwai saɓani tsakanin manyan jami'an gwamnatin''.
''An shirya wannan labarin ƙarya ne domin haddasa ruɗani da saɓani a fadar shugaban ƙasa, haka kuma labari ne da ke son haddasa ruɗani a zukatan ƴanƙasa'', in ji sanarwar.
Fadar shugaban ƙasar ta ce ta fahimci masu yaɗa labaran ƙarya ne ke son raba kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin shugaban ƙasar da mataimakin nasa, kuma haƙarsu ba za ta cimma ruwa ba, kamar yadda fadar ta bayyana.
Sanarwar ta ce matamakin shugaban ƙasar na mayar da hankalinsa kan ayyukan da ke gabansa na tallafa wa shugaban ƙasa wajen ciyar da Najeriya gaba, don haka ba ma shi da lokacin ɓatawa.
Daga ƙarshe sanarwar ta yi kira ga al'umma su yi watsi da labaran da suka fito da majiyoyi marasa tushe.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama a amurka sun yi maraba da matakin Kotun Ƙolin Ƙasar na dakatar da fitar da gomman ƴan ciranin Venezuela daga jihar Texas ta Amurkan.
Ƙungiyar kare haƙƙin fararen hula ta 'The American Civil Liberties' ne ta shigar da ƙara domin neman hana fitar da ƴan ciranin bayan kama su tare da tsare su.
Ƙungiyar ta ce ta ti farin ciki da matakin, tana mai cewa wasu daga cikin ƴan ciranin ka iya shafe tsawon rayuwarsu a gidajen yarin Venezuela idan suka koma ƙasar.
Amurka na zargin ƴanciranin da alaƙa da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Inda ake zargin tana ƙoƙarin amfani da dokokin yaƙi na ƙarni na 18 wajen fitar da ƴanciranin.
Gwamman jihar Edo, Monday Okpebholo ya ce gwamnatinsa a shirye take wajen sanya hannu kan dokar da ta tanadi hukuncin kisa ga waɗanda aka kama da laifin garkuwa da mutane.
Gwamnan ya bayyana haka a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki na al'ummar garin Uromi, inda ya tattauna da shugabannin al'ummar Arewa da ke ƙasar Esan, kamar yadda gidan Talbijin na Channels ya ambato sanarwar sakataren yaɗa labaran gwamnan.
Mista Okpebholo ya ce tuni majalisar dokokin jihar ta yi dokar da ta haramta ayyukan masu garkuwa da mutane a faɗin jihar.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci matsalar tsaro da kashe mutane ko sace su domin karɓar kudin fansa ba.
Inda ya alƙawarta ɗaukar matakin ba sani ba sabo da masu aikata laifuka a faɗin jihar
Hukumomi a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 20 a wani hari da wasu ƴanbidiga suka kai a yankin Sankera da ya ƙunshin ƙananan hukumomin Ukum da Logo.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Sewuese Anene ta fitar ranar Juma'a ta ce bayanan da suka samu sun nuna cewa wasu mahara ne ɗauke da makamai suka far wa yankin Sankera, inda nan take ƴansanda suka kai ɗauki a Gbagir, inda kafin zuwansu ƴan bindigar suka kashe mutum biyar.
SP Anene ta ci gaba da cewa yayin da ƴan bindigar ke gudanar da harinsu a Gbagir, wasu gungun ƴanbindigar kuma suka far wa ƙaramar hukumar Logo mai makwabtaka, inda suka kashe mutum 12.
''Idan aka haɗa alƙaluman mutanen da suka kashe a Gbagir da waɗanda aka kashe a Logo ya kai mutum 17 kenan'', in ji sanarwar.
To sai dai cikin wata sanarwar da gwamnan jihar, Dr. Hyacinth Iormem Alia ya wallafa a shafinsa na X, ya ce mutum 20 aka kashe a hare-haren, bayan da mazauna garuruwan suka gano wasu ƙarin gawarwaki bayan harin.
Gwamnan ya ƙara da cewa mutanen da aka kashe a harin galibi tsofaffi ne da ƙananan yara.
Hare-haren na zuwa ne aƙalla kwanaki biyu bayan wasu mahara sun far wa wasu garuruwa uku a ƙaramar hukumar Otukpo da ke jihar.
Jihar Benue na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci da addini.
A makon da ya gabata ma wasu mahara sun ƙaddamar da wani mummunan hari a yankin ƙaramar hukumar Bassa da ke jihar Plateau inda suka kashe fiye da mutum 50
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, Joseph Kabila ya koma ƙasar inda ya sauka a birnin Goma da ke ƙarƙashin ikon ƴantawayen M23 bayan shafe kusan watanni goma sha takwas ba ya ƙasar.
Ba a dai ji ɗuriyar Kabila ba har sai a baya-bayan nan da shugaba Tshisekedi ya fara zarginsa da kitsa maƙarƙashiya tare da Rwanda.
Mista Kabila ya ce yana son samar da maslaha ga matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Tun farko, jami'ai sun ƙwace motoci da dama da sauran kayayyaki bayan da suka kai samame kan wani gida mallakin Mista Kabila a Kinshasa, babban birnin ƙasar.
Joseph Kabila ya shafe tsawo shekara 18 yana jagorantar DR Kongo a matsayin shugaban ƙasa, tun daga 2001 har zuwa 2019.
Iran da Amurka za su shiga zagaye na biyu na tattauna batun taƙaita shirin nukiliyar Tehran a yau Asabar.
Masu shiga tsakani za su haɗu a birnin Roma bayan zagayen farko na tattaunawar da aka yi a makon jiya a Oman.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce za a iya cimma yarjejeniya idan Amurka ba ta gabatar da wasu sharuɗa da Tehran ba za ta yi bi ba.
Shugaba Trump ya sha yin barazanar yin amfani da ƙarfin soji idan Iran ta ƙi amincewa da wata yarjejeniya.
Ana ta samun bayanan da suka ci karo da juna game da abubuwan da Washington za ta gabatar da yarjejeniyar.
Tehran ta yi bayani ƙarara cewa ba za ta taɓa yadda da batun rushe shirinta na nukiliya baki ɗaya ba.
Ma su bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.