Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo arshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu zo muku da wasu sabbin labaran.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo arshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu zo muku da wasu sabbin labaran.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya
Wani jirgin Rasha maras matuƙi ya kai wa wata mota ɗauke da fasinjoji hari a yankin Dnipropetrovsk DNipro-petrosk da ke Ukraine.
Jami'ai sun ce mutum 15 ne suka mutu yayin da bakwai suka jikkata.
Tun da farko jirage marasa matuƙan sun kai hari wani asibitin haihuwa a Zaporizhzhia inda mutane shida suka samu muggan raunuka.
Ukraine ta sanar da cewa tana aiki da Elon Musk don kare hanyoyin sadarwarta daga harin Rasha.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafar matan Arsenal na fafatawa da Corinthians ta Brazil a wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Mata ta Duniya.
Gasar ce ta farko tun bayan sabuntata, inda zakarun mata daga nahiyoyin duniya shida ke halarta.
Duk ƙungiyar da ta lashe gasar za ta samu kyautar dala miliyan 2.3.
A karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙin basasa a Sudan shekaru uku da suka gabata, jirgin sama ɗauke da fasinjoji ya sauka a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Khartoum.
Jirgin na sudan ya sauka daga jihar Port Sudan da gomman matafiya a ciki.
An sayar da tikitin jirgin a kan dala hamsin.
A watan Maris din shekara ta 2025 ne dakarun gwamnati sun karɓe birnin khartoum daga dakarun RSF, to amma an ci gaba da gwabza yaƙi a Yammacin Sudan.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce yana da yaƙinin Tehran za ta iya cimma yarjejeniya da Washington kan shirin nukiliyar ƙasarsa.
Yayain wata hira da kafar yaɗa labarai ta CNN, Abbas Araghchi ya ce Iran ta rasa aminci ga Amurka a matsayinta na abokiyar tattaunawa, amma musayar saƙonni ta hanyar abin da ya kira ƙasashe ƙawayen Amurka a yankin na samar da damar tattaunawa mai amfani da gwamnatin Trump.
A Iran kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ce Erfan Soltani - wanda shari'arsa ta ja hankalin duniya bayan an kama shi a lokacin zanga-zangar baya-bayan nan da aka ce an yanke masa hukuncin kisa - an bayar da belinsa.
Wani jami'in Iran ya kuma ce dakarun juyin juya halin Musulunci ba su da wani shiri - kamar yadda aka ruwaito a baya - na gudanar da atisayen sojin ruwa a mashigin Hormuz a yau da kuma gobe Litinin
Hukumomi a Jamhuriyar dimokaraɗiyyar Congo sun zargi ƙungiyar ƴan tawaye na M23 da yin barazana ga rayukan fararen hula, bayan da sama da mutane 200 suka mutu sakamakon ruftawar mahaƙar ma'adinai a garin Rubaya mai arzikin Coltan.
Gwamnati ta ce an haramta ayyukan hakar ma'adinai a yankin tun a shekarar da ta gabata, inda ta bayyana ci gaba da yin amfani da albarkatun a matsayin "abin da ya saɓawa ƙa'ida."
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Congo ta ce ana ci gaba da haƙar ma'adinai a Rubaya ba tare da mutunta ka'idojin tsaro ba, duk da haramta irin waɗannan ayyukan.
Ƴan tawayen M23 sun ƙwace garin Rubaya da ke gabashin Congo a shekarar 2024.
Wurin yana ɗauke da kashi 15 cikin ɗari na coltan da ke duniya - wani ma'adinin da ake amfani da shi wajen ƙera wayoyin hannu da kwamfutoci.
An kashe wani ƙan ƙasar Kenya da aka ɗauka domin yaƙi tare da sojojin Rasha a gabashin Ukraine, a cewar hukumar leken asiri ta ƙasar Ukraine.
Hukumar ta ce ta bayyana sunan marigayin da Clinton Nyapara Mogesa, ɗan ƙasar Kenya mai shekara 29 da haihuwa.
Rahotanni sun ce an gano gawarsa a wani wurin da Rasha ke riƙe da shi a yankin Donetsk bayan wani hari da suka kai wanda bai yi nasara ba.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar 31 ga watan Janairu, hukumar leƙen asiri ta Ukraine ta ce Mista Mogesa ya taɓa zama kuma ya yi aiki a Qatar kafin ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da sojojin Rasha.
An ce daga baya an tura shi rundunar masu kai hare-hare samun abin da jami'an Ukraine suka bayyana a matsayin 'horo na gajeren lokaci'.
Sanarwar ta kuma gargaɗi ƴan ƙasashen waje da su guji zuwa Rasha ko karɓar aiki a can.
Lamarin dai na zuwa ne makonni kadan bayan da gwamnatin Kenya ta ce an ceto ƴan ƙasar Kenya 18 da ke taya Rasha yaƙi aka kuma mayar da su gida.
Jam'iyyar LP ta saka ranar da za ta guanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabin shugabanni da za su jagoranceta har zuwa babban zaɓen 2027.
Gwamnan jihar Abia - wana shi kaɗai ne gwamnan da jam'iyyar ke da shi - ya ce tuni jam'iyyar ta sanar wa hukumar zaɓen ƙasar shirin gudanar da babban taron nata cikin watan Maris.
A lokacin da yake jawabi a taron manema labarai a jihar, Gwamna Otti ya ce tuni shirye-shirye sun yi nisa don tunkarar taron.
Ya ce tuni jam'iyyar na ci gaba da sabunta rajistar ƴaƴanta gabanin taron nata.
Gwamnan ya kuma bayayna takaicinsa kan ficewar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Pete Obi wanda ya koma jam'iyar ADC, sai dai ya yi masa fatan alkairi.
Ya ce duk da rashin muhimman mambobinta a majalisar dokokin ƙasar, har yanzu jam'iyyar na nan da ƙarfinta.
Babban ministan lardin Balochistan na Pakistan ya ce hukumomi sun samu gargadin cewa ƴan tawayen ƙabilar Baloch na shirin kai hari gabanin harie-haren haɗin gwiwa da aka kai ranar Asabar.
Sarfraz Bugti ya ce sama da ƴan ta'adda 140 ne aka kashe a lokacin hare-haren da kuma gabanninsu.
Sojoji sun ce kusan wurare goma, ciki har da babban birnin lardin Quetta, har yanzu a rufe suke, bayan da ƴan tawaye suka kai hari kan ofisoshin sojoji da gidajen yari da kuma bankuna, inda suka kashe mutane da dama.
Haramtaciyar ƙungiyar Balochistan Liberation Army ta riga ta ɗauki alhakin kai hare-haren.
Ya zuwa yanzu dai ba a iya tabbatar da sahihancin bayanan ɓangarorin biyu ba.
An fara buɗe mashigar kan iyakar Rafah da ke tsakanin zirin Gaza da Masar, sai dai Isra'ila ta ce a matakin gwaji ne kawai.
Hukumomin Isra'ila sun ce za su ba da damar takaitaciyar zirga-zirgar Falasɗinawa kaɗai na wani tsawon lokaci, amma ba za a shigar da ayarin motocin agaji ba.
Wakilin BBC na Gaza ya ce babu tabbas ko za a bai wa mutane izinin ficewa a yau.
Wani jami'in Falasɗinawa ya ce ana gudanar da bincike don tabbatar da cewa an dukkan tsare tsaren tantancewa da na sarrafa kaya da kuma na sadarwa suna aikia yadda ya kamata.
Dubban Falasɗinawa ne ke son fita ƙasashen waje domin kula da lafiyarsu.
Isra'ila ta ce Falasɗinawa da suka fice a lokacin yaƙin ne kadai za a bari su su koma cikin Gaza.
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun yi nasarar kashe wani babban jigo na ƙungiyar Boko Haram/ISWAP mai suna Abu Khalid.
An kashe Khalid wanda shi ne babban kwamandan Boko Haram na biyu a dajin Sambisa, tare da wasu mayaƙansa 10 a wani samame da suka kai cikin dare a jihar Borno.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar-Kanar Sani Uba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
“Sa’o’i 24 bayan sojoji sun kawar da gawurtacen kwamandan Boko Haram/ISWAP, Julaibib, wanda ke aiki a yankin Gujba, dakarun haɗin gwiwa sun yi artabu da mayaƙa a yankin ƙaramar hukumar Komala da ke Konduga da misalin ƙarfe 11 na dare.'' in ji sanarwar
A cewarsa, sojojin sun samu nasarar kwace bindigogi ƙirar AK-47 guda biyar, da alburusai, da kekuna da dama, da kayan aiki iri-iri da kayan abinci, da kuma magunguna masu tarin yawa.
Uba ya ce ba a rasa ko soja ɗaya ba a yayin samamen, kuma rundunar tana ci gaba da gudanar da aikin fatattakar mayaƙan Boko Haram/ISWAP da ke addabar yankin.
Babban jami'in tsaron Iran da kuma shugaba Trump sun ce ƙasashensu na tattaunawa a yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan cewa Amurka za ta iya ƙaddamar da harin soji a kan Iran.
Mr Trump ya ce tattaunawar da ake yi da Tehran ta yi zurfi sosai.
Shugaban majalisar ƙoli kan harkokin tsaro na Iran, Ali Larijani, ya ce an samu ci gaba sosai a tattaunawar da ake yi.
Amurka ta tura wata tawaga ta sojojin ruwa zuwa yankin.
Wakilin BBC ya ruwaito cewa mutane na cikin fargaba sosai sakamakon kasancewar sojojin Amurka a kusa da Iran.
Kazalika fashe fashen abubuwan da aka ji a sassan Iran a jiya Asabar da hukumomin ƙasar suka ce fashewar iskar gas ne, ya ƙara sanya fargaba a zukatan ƴan ƙasar.
Gamayyar ƙasashen Sahel da ta ƙunshi ƙasashen da suka haɗa da Mali da Nijar da Burkina Faso sun yi Allah-wadai da harin da aka kai a tashar jirgin sama da ke Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda suka bayyana wadanda suka kai harin a matsayin 'matsorata'.
A cikin wata sanarwa da shugaban sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore ya fitar ranar Asabar, ƙungiyar ta zargi ƙasashen ƙetare da ke ɗaukar nauyin masu tayar da ƙayar baya a ƙasashensu.
Rahotanni sun ce ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai harin tsakanin daren Laraba zuwa safiyar Alhamis, inda ta ce ya yi matuƙar ɓarna.
Sai dai hukumomin Nijar sun dage cewa an ƙashe maharan giuda 20 tare da kama wasu 11.
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tiani ya zargi ƙasashen Faransa da Ivory Coast da Benin da goyon bayan maharan ba tare da ya gabatar da wata shaida ba.
Yayin da ya ke mayar da martani kan zargin, kakakin gwamnatin Benin ya yi watsi da zargin na Tiani a matsayin "maganar banza."
Firaiministan Slovakia Roberto Fico, ya amince da murabus din mai bashi shawara kan harkokin tsaro Miroslav Lajcak.
Murabus ɗin nasa ya biyo bayan bayanan da suka fito cewa sun yi musayar bayanai tare da Jeffrey Epstein, mutumin da aka kama da laifukan lalata.
Ma'aikatar shari'a ta Amurka ce ta fitar da wasu kunshin bayanai a ranar Jumma'ar da ta gabata inda a cikinsu ne aka samu sakonnin da Mr Lajcak ya aikewa Epstein.
Ba a dai zarge shi da aikata ba daidaiba, amma cikin sakonnin da suka yi musaya an ga suna magana akan batun mata.
An samu mace ta biyu da ta yi zargin cewa mutumin da aka kama da laifukan lalata Jeffrey Epstein, ya aike da ita Birtaniya domin ta yi lalata da ƙanin sarki Charles, Andrew Mountbatten- Windsor.
Lauyan matar ya shaida wa BBC cewa zagin da matar ke yi ya faru ne a gidan ajiye baƙi na Yariman a shekarar 2010.
Lauyan ya ce a lokacin da abin ya faru matar tana shekarunta na 20.
Har yanzu Andrew bai ce komai ba a kan zargin, amma dai a baya ya sha nanata cewa bai aikata ba daidai ba.
Tun da farko firaiministan Birtaniya Keir Starmer, ya bai wa tsohon yariman shawara akan ya gurfana a gaban majalisar dokokin Amurka don yin bayani a game da alaƙarsa da Epstein.
Sir Keir Starmer ya gayyaci firaministan Japan Sanae Takaichi da ta ziyarci Birtaniya bayan tattaunawa da shugabannin biyu suka yi a Tokyo, yana mai cewa dangantakar dake tsakanin ƙasashen ta kasance "mafi karfi a cikin shekaru da dama".
Firaministan ya isa ƙasar Japan ne bayan ziyarar kwanaki huɗu da ya kai China, inda ya yi yunƙurin sake farfaɗo da dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da Beijing.
Shugabannin ƙasashen Birtaniya da Japan sun ce sun tattauna kan "haɗin gwiwa" da kuma tsara shirye-shiryen ƙarfafa hulɗar kasuwanci da tsaro, gami da inganta tsaro da haɗin gwiwa a duk faɗin yankin Indo-Pacific.
Duk wata ziyarar da firaministar ta Japan za ta kai Birtaniya za ta dogara ne kan sakamakon zaɓukan da za a gudanar a ranar 8 ga watan Fabrairu, inda jam'iyyar Liberal Democratic Party ta Takaichi ke neman komawa kan karagar mulki.
Aƙalla mutane 32 ne suka mutu sakamakon wasu hare-hare da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai a zirin Gaza a ranar Asabar, a cewar hukumomin yankin.
Hukumomi a Gaza sun ce mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda aka kashe.
Sun ƙara da cewa, a wani harin jiragen yaƙi masu saukar ungulu sun yi luguden wuta a kan wani tanti da ke garin Khan Younis da ke kudancin Gaza.
Falasɗinawa dai sun bayyana waɗannan hare-haren a matsayin mafi muni tun bayan da zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Amurka Trump ya jagoranta a watan Oktoban da ya gabata ya fara aiki a farkon watan Janairu.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa an kai wasu hare-hare a matsayin martani kan abin bayyana a matsayin karya yarjejeniyar da Hamas ta yi a ranar Juma'a.
Isra'ila da Hamas dai na zargin juna da karya yarjejeniyar tun bayan da ta fara aiki a bara.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.